Hausa novels

Harijin Tsoho Page 1 Romantic Hausa Novel

…..Ƙwaƙwalwarsace ta shiga aykin gaggawa yayinda zuciyarshi ta tafi dogon tunanin wasu abubuwa da suka faru abaya. Inba mantawa yayiba tabbas zahra tasha alwashin bazata taɓa kawo masa budurcintaba gidansa in har yaƙi janye batun auransa da ita, to ko in har hakane meyasa yanzu yajita arufe maana bata taɓa sanin wani ɗa namijiba a rayuwarta, to fice ficen da take agidansa da auransa akanta da nufin ta tafi clubs da guraren iskanci ina take zuwa kenan? duk safiya inta dawo daga yawon darenta setayi wankan tsarki kamin tayi sallah, to nameye wankan takeyi inhar ba na kwanciya da wani bane? Me hakan yake nufi, dama duk wannan shekarun data kwashe agidanshi budurwace kenan? Rasa amsoshin tambayoyin nasane yasa a hankali ya mirgine daga kanta ya koma gefe ya kwanta ya lumshe idanunsa. Zahra wacce ta fara jin azabar daren farkonta da uncle Abu Ayman jin yasauka akanta batare daya karɓi budurcin nata bane yasa ta buɗe idanunta tana kallonshi. Ƙara jan bargo yayi ya rufe jikinshii,yasa hannu ya kunna fitilar gefen gadon nasu, ya kai dubansa inda take itama kallonshi take, “Zahra meyasa kika kawomin budurcinki gidan aurena?” cewar uncle fuskarsa babu alamun wasa. Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta ƙasa tace akunyace “sabida kaine ka dace dashi uncle amatsayinka na mijina” ta faɗi kanta aƙasa. “zamana mijinki be zama dalilin da zesa ki kawomin budurcinkiba, zahra budurci anawa wanda ake sone kyautarsa wanda kinsani nasani babu soyayya atsakaninki dani,matsayina gurinki zahra ban dace da budurcinkiba” ya faɗi yana ƙoƙarin sakkowa agadon. Sgigice zahra ta kamo hannunsa bakinta na rawa tace “Uncle ka yafemin don Allah tabbas nayi kurakurai abaya amma a zamana dakai na fahimci kaine mafi alkhairi agareni, wallahi kafi kowa dacewa dabudurcina” tafaɗi hawaye na biyo idanunta. “Zahra nasan muhimmancin alƙawari kince inma na aureki dan budurcinkine to zaki rabar dashi atiti sede insamu sauran wasu, kuma na aurekine dasa ran sauran wasun zan samu, meyasa zaki kawo budurcin gidan tsohon kwanon dake da zuciya irinta yara?” cewar uncle yana murmushi. Runtse ido tayi ta fashe da kuka tabbas ta jima tana yiwa uncle rashin mutunci be taɓa ɗaga ido ya kalletaba se yau data gama tsara zata bashi surprise na samunta budurwa dazeyi adarensu na farko wanda ta kyautata zaton a soyayyar da yake mata da zata ƙarune kamar yadda tasha gani a novels da finafinai se taga ita anata ɓangaren ba haka bane. “Uncle ka yarda dani wallahi kaf duniya ba namijin da nakeso sama da kai, kayafemin abubuwan da nai maka abaya don Allah” ta faɗi cikin kuka. Murmushi yayi ya zura gajeren wandonshi yasa hannayensa duka biyu ya tallabo fuskarta yace “na gina sonki azuciyatane a matsayin mutuniyar banza zahra, ba wannan kamilalliyar zahran ba, in har kina son na yarda dake to dole se kin kaiwa wanda kikeso budurcin naki sannan ki dawomin a fankon ashanar da kikaimin alƙawarin zan sameki, komai runtsi mu dena mancewa da alƙawari zahra, mu zamo masu cikashi domin abun tambayane ranar gobe ƙiyama” yana kaiwa nan yasa kai ya fice daga ɗakin nata zuwa nashi. Kifewa zahra tayi agurin tana kuka me tsuma zuciya, wannan wacce irin lukutar masiface ace mijinka na aure yace bayason budurcinka se kaje ka rabar dashi atiti sannanne ze karɓeka a matsayin mata” Sake rushewa tayi da kuka data tuno cewa koma menene itace ta jawa kanta uncle beda laifi, itace tayiwa rayuwarsa tsatsan da yasa har yace duk abinda yace ɗin. Ta biyewa sharrin zuciya da soyayyar da takewa habib yau gashi mijin nata na aure na shirin kubcemata kamar yadda shima habeeb ɗin ya kubce. Gashi mahaifinta yayi rantsuwa da duk ranar da ta sake uncle ya rabu da ita to karta sake kiranshi da sunan mahaifinta ya yafewa duniya ita.wayyo zahra wai me ta aykatawa rayuwarta har hakane?

Back to top button