Gargadar So Chapter 59 By M Shakur
Koo kadan jikin Hawwa ba karfi jin abubuwan da su Baba suka fadi, dafe katifa tayi tazauna ahankali tai shiruuu tana tunani, duka abubuwan da Ni’ima tamata abaya she kind of give her excuse sabida Aliyu duk shi yaja da sauransu, so tasan ba kowa ya iya handling kishi ba, kuma tasan yanda Ni’ima ke mugun son Aliyu, so tamata excuse dudda she goes as far as tana zagin iyayenta tana tonamata asiri, but this! Yaushe ta dauki wayanta harta dauki number Khaleel dabatai saving ba? Takasa yarda still, kodai Khaleel sheri yayi mata da karya sabida ya tsaneta? Sai kawai ta tashi da sauri ta dauki wayanta takira Abraham ringing daya ya dauka tace “Abraham I remember kataba cewa kasa wani invincible CCTV camera an office dina right?” Dasauri yace “yes Miss Hawwa” ahankali tace “can you send me footage na jiya at about 1Pm zuwa 2pm” Dasauri yace “sure give me 3mins” ta katse wayan ta zauna tana kada kafa she really don’t wanna believe Ni’ima did all this dasu Baba suka fadi noo! Ni’ima tai nadaman everything datayi abaya, she’s a changed person, kishin Aliyu yasa tayi all those things ada.3min basu cikaba Abraham yaturo mata video ta watsapp dasuri tashiga downloading yana gamawa tabude dasauri tashiga kallo gabanta na mugun faduwa tana cewa kanta No No Ni’ima can’t do this to her, aiko saiga Ni’ima na daukan wayanta tana daukan number tana kallon kofa atsorace, wani irin runtse idanu Hawwa tayi murya araunane dake cikeda mamaki tace “Ni’ima!” Ijiyan zuciya ta sauke ta fuzar da iska mai dumu ta ijiye wayan a gefe, she’s really hurt dudda bataga text dinba but for Ammi to slap her this hard that means she said alot tabata mata suna, dole Khaleel yaji ba dadi zaiga tana crucifying nashi on something da itama tanayi, fuzar da iska tayi bataso tayi kuka akan Ni’ima yau but zuciyanta namata wani iri kaman ma idan tai kuka zaifi rage mata zafin dayake mata yanzu.Hawwa na zaune a wajen idanunta sunyi ja almost 1hr dafitan su Baba da Ammi taji ana bude kofanta dasauri tadago kai, ganin Khaleel again saida gabanta yafadi da sauri taboye wayan dake hannunta na video akasan bedsheet sabida karya ga video, yana shigowa babu wata wata kawai yazo inda take zaune tana kallonshi, hannunshi yasa yakamata yadagata yajata turjewa tayi tace “stop touching me ina zaka kaini kuma”? Cikin bacin rai Khaleel yace “i want to show you wacece wacce kikai considering as true friend” kawai yajata takalmi tasaka sukai waje takasa kwace hannunta Salman yabude musu bayan mota ita tafara shiga sannan shima ya shiga aka rufe motan aka ja, to her biggest suprise hanyar office nata taga sunyi, dasauri takalleshi tace “ina zaka kaini?” Banza yamata yaki amsata har office nasu, parking yayi yana rikeda hannunta suka wuce ciki har zuwa office na DIG kai tsaye Khaleel yabude office din batare dayama yi knocking ba, DIG Hawwa tagani tareda Abraham duk zaune, DIG na ganinshi da sauri DIG yatashi yace “Mr Ibrahim I……” hannu Khaleel yadagamai strictly yace “did you bring her here yes or no?” Rai abace DIG yace “not just she duk ma wani wanda ke gidansu cus I will never take this defamatory statement likely” yakalli Abraham yace “bring everyone in” wucewa yayi yafita chan saiga wasu manyan yan sanda guda biyu sun shigo da Mama da Ammi sai Baba da Ni’ima dake sanye da doguwan rigan atampa dukansu sunyi zuru zuru dan duk suna zaune suna magana agida wasu yan sanda sukazo sukace ana inviting nasu to police station dukansu haka suka taho, Baba na ganin Khaleel da Hawwa yace “Ibrahima me kukeyi anan? Munje gidansu yarinyar nan ana cikin magana saiga yan sanda akace muzo chaji opis” ahankali Khaleel yace “nina turasu Baba” hannun Hawwa yasaki gently yasa hannu ya karbi karafunan Baba ya zaunar dashi a kujeran wajen yakalli Ammi yace “Mom sit” zuwa Ammi tayi ta zauna, gaban Mama dana Ni’ima suka shiga bugawa especially gaban Ni’ima dabatasan meke faruwa ba gabanta sai fadi yake cus su Baba dasukazo cewa sukayiwa Mama basuson yarta tareda Hawwa basuce komiba, kawai faduwa gabanta yake dudda bata kawo text messages na jiyaba dan batajin za’a iya gano ita bane, Hawwa takalla cikin makirci tace “Best is everything okay? Why did you call us here”? Wani daci Khaleel yaji aranshi yanda take kiran matarsa wani best azafafe yace “wlh kika amsa that beast sai ranki yabaci” yafadama Hawwa dake kallon Ni’ima jikinta yagama sanyi da Ni’ima sosai, faduwa gaban Niima yayi itama Hawwa tadauke kai kawai Ammi saitaji wani son Khaleel ya lullubeta.Anatse DIG yakalli daya daga cikin yar sandan mata dake taredasu Mama, ba zato ba tsammani Ni’ima taji saukan bulalaaa akafanta dayasa kawai ta zube akasa tace “wayyooo Allah na” dasauri Hawwa ta juyo jin karan bulala da dukan Ni’ima, Yar sandan tace “mai laifi kneeling yakeyi ba tsayuwa ko zama ba a police station” rawa jikin Mama yafara dasauri ta duke itama kusa da yarta, DIG yakalli Ni’ima da kafafunta ke bari sabida zafin wayan inji yace “kece Ni’ima?” Gyadamai kai Ni’ima tayi tace “eh yallabai nice” gyadamata kai yayi yace “an shigo da karanki office dina daga Mr Ibrahim akan kinyi defaming matarsa, dakuma ni, da yaron aiki na” yanuna Abraham dake tsaye ransa abace yana kallon Ni’ima, DIG yace “No body ya isa yabata min suna, idan kowa na dakin nan yabarki ni bazan barki ba!” Faduwa sosai gaban Ni’ima yake tace “yallabai bantaba ganin ka bama, saidai wanchan na sansa ta dalilin Hawwa amman me dalilina dazaisa nabata maka suna wani sherin aka kulla min ne? Best something yafaru ne”? “stop calling matana da Best!” Khaleel yafada aharzuke kowa ya kalleshi har Hawwa dasauri dan kaman zai rufe Ni’ima da duka, DIG yace “calm down Mr Ibrahim” rike kansa Khaleel yayi kirjinshi na tafarfasa yayi punching air, DIG yace “jiya wuraren 2:16 kin tura sakonni marasa dadi zuwa wayan Mr Ibrahim”? Faduwa sosai gaban Ni’ima yayi ta zaro idanu tareda dafa kirjinta Mama na kallonta hankalinta atashe Ni’ima tace “Yallabai an ina zan sami number sa har na turamai sako? Ni kuma? Sheri akamin” Dan murmushi DIG yayi yakalli Abraham yace “play the first evidence” saramai yayi yace “yes sir”.

