Mejo Najeeb Page 35 By Autar Alheri
“Kallon juna akayi tsakanin Isseta da halima kamin Isseta tayiwa wannan baiwar Allah kyakkyawar runguma tana fashewa kuka cikin kukan take faɗar”Alhmdllh Allah alhmdllh ammina wayyo daɗi halima ammina tasamu lafiya Allah nagodema Ammi tadawo hayyacinta alhmdllh sekuma tasake sake saka kuka cikin mugun farin cikin datakeji aranta…ahankali Ammi taɗago hannunta Itama tana ɗan buga bayan Isseta alamar rarrashi Itama idonta tab da ƙwallah sedai kuma murmushi takeyi, sunjima ahakan kamin Isseta taɗago daga jikinta tana kallonta tana sakin dariyar farin ciki….halima ma ahankali tarungume ta tareda faɗar “tabbas kuwa Isseta Ammi tasamu lafiya doline kiyi kuka amma na farin ciki Allah mungode ma dakabawa wannan baiwa taka lafiya, Taƙarasa zancen tana ɗagowa daga jikinta Itama tana murmushi.Itadai Ammi da ido kawai takebinsu tana murmushin yaƙe amma takasa cewa komai, ganin Hakan yasa innar halima cewa “sannu baiwar Allah. “Ido tazubawa innar halima ɗin kafin tabuɗe bakinta dake mata mugun nauyi tace yawwa sannu,,,tana cewa Hakan sekuma tabi gidan da kallo tare da maida idonta akan innar halima tace “baiwar Allah dan Allah nan inane? A,ina nake? Ina hubbey? Ina jazlan? Ina yayana? Ina matarshi ? Mikuma nakeyi anan ɗin? Kuɗin suwaye? Duk atare tarinƙa jerowa innar halima tambaya babu ko pustop 🤩”Nisawa innar halima tayi kana tace “nan garin gombe ne baiwai Allah kuma duk waƴannda dakike tambaya mu bamusan kowa ba daga cikinsu kekawai muka sani…idon Ammi ne suka ƙara cikowada ƙwallah tace “gombe inane kuma gombe? Tatambaya ga dukkan alamu tunkamin wannan matsalar tasameta batasan inane gombe ba. “Garine baiwar Allah acikin ƙasar Nigeria yake keba ƴar Nigeria bace halan? Ƙwallar data cika idontace tazubo mata kamin tace niba ƴar Nigeria bace minene zekawoni Nigeria kuma? Innalillahi wa’inna ilaihiraji’un dan Allah kukaigi gun ahalina Ina matuƙar kewarsu, Taƙarasa zancen cikin kuka.Isseta da halima ma kukan sukeyi suna kallonta…yayinda innar halima ke share ƙwalla afakaice kar yaran nata suga rauninta tace “wlh baiwar Allah bamusan komaiba gamedake domin wannan yarinyar dakike gani itace sanadiyar haɗuwarmu dake kamar yadda suka bani labari tace wata rana tafito zataje isilamiyya ne taganki kwance bakida lafiya agefen wani shago babu kowa awurin, tayi ƙokarin temakawa takaiki gidanki domin atunaninta ke ƴar uguwarce sekuma Taga batasankiba data tambeki ananne tagano akwai alamun hauka ataredake dubada kalar shigar jikinki dakuma yanayinki to daganan setakaiki wani kangon gidan biredi ta’ajiye ki taje tasiyo ruwa tawanke Miki baki tukunnah tabaki maganin ciwon ciki sekikaƙi sha abin yabata mamaki sosai sedai ganin yadda kiketa dafe cikine yasa tayi tunanin ko yunwace kikeji Hakan yasa tanufi gidansu taɗauko Miki abinci abinmamaki kuwa sekika karɓe abuncin dasauri kika hauci wannan abin yatsawa wannan yarinyar arai sosai daga wannan lokaci tafara dawainiyar kulawa dake tamkar mahaifiyata tamaida Miki gidan biredi tamkar gidanki kullun tana kan hanyar gyaranki keda muhallin datayi Miki kayan abinci kayan anfani omo sabulu komai ajiye Miki takeyi kamar yadda ake ajiyewa kowacce mace dudda cewar bakyayin anfani dakomai Sedai idan itace tazo tayi Miki kuma tundaga lokacin kike zaune agidan biredin Bakije ko inaba kina zaune aƙarƙashin kulawar ta har inda akazo lokacinda tamaidaki asibitin mahaukata dake garinnan domin sama Miki lafiya abisa temakon wata baiwar Allah wadda Bama jinsinmu ɗaya da itaba, bayan Maryama tayi aurene ƴar uwarta taci gabada kula dake acan asibin har izuwa yau da ita wannan baiwar Allah tace suɗaukoki sukawoki wurina kuma tabasu maganin dasukayi Miki anfani dashi cikin iyawar Allah da buwayarsa gashi kinsamu lafiya…..tunda innar halima tafara magana Ammi takafeta da ido ko kiftawa batayi babu abinda kemata yawo akai se kallimar hauka, tambayar datake yiwa kanta ɗaya ce wai itace mahaukaciya? Itace tayi hauka? To garin yaya? Ina ahalinta suke? Miyakawota Nigeria? Gabaki ɗaya ƙwaƙwalwarta tatoshe..wani irin kukane yazo mata me cinrai sosai takeyinshi tana girmama ubangijinta dayayi mata wannan jarabawar domin haqiqa shine kawai ze iya jarabtar bayinsa aduk ta hanyarda yaso babu mahani…..Isseta ma kukan takeyi hakama halima…sosai Ammi tayi kuka tajima tanayi kamin tatsagaita tashiga rarrashin su Isseta Hakan tasakasu ajikinta tana shafa bayansu, cikin muryar kuka tace “ngd ngd sosai yarnan sekuma kuka yaƙara cin ƙarfinta…cikin sauri Isseta tarufe mata baki tare da faɗar”dan Allah kiyi shiru Ammi dan Allah karkice komai ni wlh duk abinda nayi Miki nayine sabida Allah kuma wlh tamkar mahaifiyata Hakan nakejinki araina bantaɓa yimiki wani kallo wanda bana uwa ba dan Allah idan har kin ɗauke ni ƴarki karki ƙara yimana dogiya albarkarki kawai muke buƙata Ammi…ɗan murmushi Ammi tayi kana tace “Allah yayi muku albarka Allah yabiyaku da gidan aljannah Allah yabaku wanda Zasu bauta muku fiye da yadda kukayimani Allah yafaranta kuma kamar yadda kuka faranta mini banida bakinda zanfadi farin cikina agareku sedai zan dawwama inamuku addu’ar fatan alkhairi arayuwarku….wani irin daɗi ne yalulluɓe ƴaƴantan cikin farin ciki suka ƙara rungumeta suna amsawa da amin ya Allah…innar halima ma amsawa tayi tana murmushi.Kamin Ammi takalleta Itama tana murmushi tayi mata godiya Sosai kamin tace “Inason komawa ƙasarmu bawai Allah domin nasan awanne hali ahalina suke ciki sabida idan nafahimta Dede awannan labari dakika bani dakuma yanayin jikina dana kallah ya tabbatar min dacewar nayi shekaru cikin wannan lalurar..”Muryar umaima suka tsinkayo tana faɗar “Hakane kam tabbas kinyi shekaru baki tare da ahalinki kuma suma suna buƙatarki kamar yadda kike buƙatarsu to Amma kisani lokacin haɗuwa dasu beyiba kiɗan ƙara haƙuri kaɗan dakansu Zasu bayyana agareki in sha Allah, takasa maganar tana shigowa cikin gidan….dukkansu da kallo suka bita, innar halima tace “wacece ke? “Umaima ce innarmu aminiyar maah ɗita, Isseta tafaɗa tana murmushi. “Ayya Allasarki yi haƙuri bawai Allah nayi mamaki ne jin kawai kinsaka baki acikin zancenda mukeyi kuma naga bansankiba…”Karki damu bakomai bane yanzudai zan ɗauki maryama namaidata gidan mijinta domin lokacinda nayiwa mijinta alkawarin medata yayi…”wacece maryama? Ammi ta tambaya. “Yartaki ce maryama gatanan, innar halima tanuna mata Isseta…wani ƙayataccen murmushi tasaki kamin tace Masha Allah, sekuma ta kalli umaima tace naso nazauna da ƴata Kodan naji ɗiminta ataredani amma Zaki ɗauketa to idan kika ɗauketa se yoshe Zaki maidamin ita??? Tatambaya tana murmushin…Itama umaima murmushi tayi kana tace bazan iya ɗauke maryama daga garekiba har abada domin jini baya ƙarya maryama babu wanda isa yaraba jini ɗaya se Allah sabida Hakan Karki damu duk lokacinda gimbiya laweesat tace nakawo Miki ƴarki ashirye nake dana kawota gareki…..ido Ammi taɗan waro kaɗan sekuma tace “baiwar Allah a’ina kikasan sunana maryama?? Tatambaya da mamaki. Dariya umaima tayi kana tace Karki wani damu dasanin wannan maryama domin kuwa Allah nabamu iKon sanin abinda baku saniba wanda ya yardar muna da musani sabida Hakan sanin sunanki bawani abin bane agareni balle ma gakida Sunan ƴar lelen gimbiya laweesat… murmushi sukayi dukkansu kafin waninsu yaƙara magana sukaga babu umaima babu dalilinta koda suka waiwaya kuma babu Isseta…murmushi kawai Innar halima tayi kana tace barana haɗa Miki ruwa kiyi wanka maryama mesunan ƴata sekizo muci abinci..daga Hakan tamiƙe batareda tajira cewar Ammi ba..inda tabarsu itada halima tana ƙara bata labarin Isseta dakuma yadda take shan wahala wurin kulada ita…wannan labari da halima kebawa Ammi kuwa baƙaramin ƙara sanya soyayyar Isseta yakeyi azuciyar Ammi ba.LagosUmaima bata ajiye Isseta ko inaba se bedroom ɗin Mejo Najeeb inda ta ɗauketa,tayi tafiyarta….ɗakin tabi da kallo tana tuna mejin nata ayanayinda suka kasance jiya, agefe ɗaya kuma tana tuna amminta dataji ashema sunansu ɗaya maybe hadda Hakan yasa takeson matar sosai aranta, murmushi tasaki kamin tamiƙe tashiga bathroom tayi wanka tare da alwala tafito, tayi sallar azzahar tukunnah taje gun mirror Tayi shafe shafenta, kana taɗauko kayanta da umaima taɗauko mata ɗazu buɗewa tayi taɗauki wata abaya ash color me rashin baƙi atasaka tayi rolling ɗin mayafinta, Masha Allah sosai tayita kyau matuƙa domin dama can Isseta kyakkyawar macece ajin farko….kayan taɗauka tashiga jerasu acikin widrop ɗinshi seda Tagama tsab tukunnah tashiga gyara ɗakin bayan Tagama tadawo perlor tanacikin gyaran perlor ne Hajiya mama tashigo part ɗin domin Taga kotadawo…cikin girmamawa dajin kunya tace mama inawuni. “Lpy qalau Maryam kintashi tashi Ashe? Cewar mama tayi mata kamar batasan bata gidanba. “Eh Natashi mama, tafaɗa kanta aƙasa…..”to shikenan idan kingama kisauko muci abinci gaba ɗaya ko akawo Miki naki ananne?? “ah,ah mama zanzo yanzu in sha Allah..to shikenan sekin fito, Hajiya mama tafaɗa tana barin pert ɗin.Tunda Ummi takai anty hawwa pert ɗin Hajiya mama Basu haɗu da juwaira ba se yanzu dakowa yafito cin abinci domin koda sukaje part ɗin juwaira na bedroom ɗin Ummi itako anty hawwa a perlor suka zauna itada ummi dudda bafira sukeyiba amma suna zamansu atare suna kallo…yanzu ma Ummi ce takira juwaira akan tazo suyi lunch domin ƙa’idar gidance idai kowa yana’nan to a general parlor akecin abinci, sedai idan bakajin yunwa seka bari seka buƙata amma muddin alokacin zakaci to atare za’acishi…….juwaira na fitowa idonta yasauka akan anty hawwa dake zaune tana kallo, zuwa tayi zata wuce kawai anty hawwa tace “ke juwaira bakiganni bane? Zaki wuce bako magana? Tukunnah ma miyazaunar dake bakibi su zubaida ba? Tatambeta cikin isa adoli ita babbace….wani wulakaccen kallo juwaira tajefa mata kamin tace “au zamanki nakeyi dazakice miyasa bantafiba? Ke kanki dakike taƙamar waike amarya Anan kika sameni kuma kibari har idan kinsamu wurin zama agidan tukunnah kiyi yunƙurin korar wani, tana gama faɗar Hakan taficewarta…baki anty hawwa tasaki tana kallon ƙanwar tata cikin mamakin furucinta kamin tasamu damar yin magana Hajiya mama tashigo perlor cikin mamakin ganinta zaune sakeda baki tace”hawwa’u miyasa bakifita gun lunch ba?? Kefa ba baƙuwa bace kinzama ƴar gida tashi mana kije cikin ƴan uwanki kici abinci kinjiko…”okay kawai anty hawwa tace kana tamiƙe tafita…da kallo kawai Hajiya mama tabita kafin tagirgiza kanta Itama Takoma perlor.Zaune suke dukkansu akan dining table, Hajiya Umma, Hajiya mama yah munir, yah sajad, mansura, auta siyana, ummi, juwaira, anty hawwa. Dukkansu suna zaune Hajiya mama nayin saving ɗinsu yah munir se tsokanar auta siyana yakeyi yana faɗar “ƴar lelen yah najeeb yatafi yarshi ko sallama basuyiba😜 yanayi yana mata gwalo cikin tsokana yace yanzudai mungano yah najeeb yadenaji dake siyana se haƙuri….kuka siyana tasaka tana rigima tare da faɗawa jin mahaifiyarta tana faɗar “umma kinji yah munir ko? wai yah najeeb bayasona. Taƙarasa zancen tana sake sakin kuka.. faɗa Hajiya Umma tafara yiwa Munir tana faɗar yadena tsokanar mata yarinya…Hakan yasa yace to “shikenan yi haƙuri nadena barama nakira mikishi kiganshi..yana gama faɗar Hakan yashiga WhatsApp tareda Kiran mejo video call domin yaganshi a online…seda takusan tsinkewa kana yaɗaga yana kwance akan makeken bed ɗin hotel room ɗin dasuka sauka, yanasanyeda ƙaramar riga red color Kuma buɗaɗɗiya agaba duk sumar ƙirjinshi awaje takwanta tayi lufff kamar abarda yakeyiwa shampoo 🥳 buɗe blue eyes ɗinshi yayi dasuke a lumshe sabida jin muryar autar tasu, tana faɗar “yah najeeb na..bece mata komaiba se kallonta dayakeyi da wannan rikitattun idanuwan nashi, ga dukkan alamu ƴan miskilancin nataredashi ayau…jin yayi shiru kuwa yasa auta siyana sakin kukan shagwaɓa tana faɗar”yah najeeb dagaske kadena Sonako? Shi yasa kaƙiyin magana Taƙarasa zancen tana sakin kuka ga dukkan alamu dai mejo yasangarta siyana sosai. “Ahankali yabude baki cikin cool voice ɗinshi mekashewa ƴanmata jiki yace “ohh my god angel stop crying please kinji. Wayace Miki nadena sanki? Yafaɗa akasalance domin gabaki ɗaya tunanin sahibarshi maryama ne cikin ranshi koda Munir yakirashi. Tunda mejo Najeeb yafara magana wurin yayi taittt bakajin komai awurin se sautin daddaɗar muryarshi….cikin shagwaɓa siyana tace yah munir ne.. “Humm yace ahankali kafin yacigabada faɗar “bagaskiya bane kirabidashi kinji idan nadawo zamuje yawo ko? “Eh yah najeeb na I love you my lovely bro….”love you too my angel, bawa munir wayar yafaɗa agajiye…miƙawa yah munir wayar tayi tanata munar yah najeeb ɗinta bedena jida itaba….”yah najeeb kunsauka lafiya?? Cewar Munir….harara yafallawa Munir ɗin kafin yace “banasan shashanci fa Munir zaka saka yarinya agaba dashirme? “I’m sorry bro, Munir yafaɗa yana dariya..”Humm kaga Maryam ayau ɗinnan? Yafaɗa yana lumshe blue eyes ɗinshi. “Wacece Maryam ya najeeb? Munir yatambaya cikin mamaki…kafin najeeb yabashi amsa Isseta tasauko perlor cikin tafiyarta mejan hankali, “gatanan zuwa nan wurin yah munir cewar Ummi tana nuna mishi ita. “Wow Masha allah shine abinda ya fito daga bakin Munir Yanabin Isseta da kallo domin tayi kyau sosai awannan shigar tata…ido mejo yabuɗe sosai yana kallon yadda ƙanen nashi yasaki baki da hanci yana kallon wani abun wanda yanada tabbacin Maryam ɗin ce dayaji Ummi tanuna masa, atake yaji wani mugun takaici yarufeshi, domin yanzuma Yanajin muryarta tana gaisarda su hajiya Umma.Sajad kuma nagaidata…cikin tsawa yace “wai wannan wanne irin iskanci ne Munir inama magana Kanacan kana kallon yarinyar mutane ? Kallon mata kakomayi yanzu? Yafaɗa ahasale. Se alokacin Munir yadawo nutsuwar cikin jin kunya yace “I’m very sorry please bro wlh banjika bane, yafaɗa kanshi aƙasa…tsaki najeeb yayi kana yace aibazaka jiniba dama kabata wayarka zankirata kuma anjima kaje kasiyo mata waya, yana gama faɗar Hakan yayanke wayar kuma duk abinda yake faɗa duk wanda ke wurin yaji shi..”Anty Maryam barkada fitowa? Cewar sajad.. murmushi Isseta tayi kana tace “yawwa barka Ina wuni, tafaɗa cikin sexy voice ɗinta wanda ko acikin mafalki kake indai kasanta kajishi sekasan itace awurin….wani irin jiyowa anty hawwa da Seyanzu tadawo hayya cinta tun lokacinda taji muryar mejo, ido tawaro daƙarfi tace “keeee dama kina raye baki mutuba?? Tafada cikin out of control…dukkansu da mamaki suke kallonta jin wannan furucin nata..amma Banda Isseta dake kallonta kawai tana murmushi,,Itama juwaira ko kallonsu batayiba domin itayanzu tata damuwarce agabanta…..sajad ne daya buɗe baki ze amsawa Isseta gaisuwarda tayi mishi yafasa tare da maida zancen nashi ga anty hawwa yace “kamarya tana’nan bata mutuba jinkikayi ance tamutune?? Wannan wacce irin maganace Hakan?? “Nimadai abinda zance kenan domin ko juwaira ma ɗuzu tambayar datayi mata kenan wai bata mutuba, cewar Ummi Itama cikin mamakin wannan abin.Seyanzu anty hawwa tadawo hayya cinta kaɗan jin kwabawarda tayi cikin harhaɗa magana tace “do doline nace hakan mana wadda tabar gidan wata dawattini tatafi yawonta har ila yau nemanta akeyi doline naganta hankalina yatashi domin duk atinaninmu ɗauketa akayi ko tamutu…”tofa kuma kikace tatafi yawo kuma kince ɗauketa akayi daga ƙarshe kince tamutu wanne zamu ɗauka kenan? Cewar Munir cikin jin haushinta.. “kai banason zancen banza Munir duk abinda suka faɗa ai baƙarya sukayiba domin kuwa da ƙarya sukeyi ai iyayenta ne dakansu Zasu kawota gidan miji bawai yatsintotaba, cewar Hajiya Umma cikin basarwa…..wannan kalami na Hajiya Umma baƙaramin daɗi yayiwa juwaira da mansura ba yayinda yaƙonawa Ummi Hajiya mama dakuma su sajad rai…cikin renin hankali Hajiya mama tace “to komadai yayane ubantane ya Aurar da ita kuma munada buƙatarta ahakan kamar yadda mijinta keda buƙatarta sabida Hakan banason ƙananun zantukan banza wlh…..”Humm kowa yaci abinci dai kema zokizauna kici abinci cewar Hajiya Umma…Isseta kuwa tun lokacinda idonta yasauka akan abincinda aka zuba awurin gabanta yayi wani mummunan faɗuwa sabida abinda idonta kegane mata aciki gabaki ɗaya hankalinta yatashi sam batajin komai awurin Se abinda take gani….zo kici abinci nace Hajiya Umma taƙara faɗa cikin ɗan ɗaga murya ganin Isseta tayi shiru atunaninta ko ɓacinran maganganunsu ne yadameta kuma dama kahan takeso domin itadai bazata so ɗanta yazauna da korarriyaba…aɗan firgice taɗago tana kallonta kamin tasake mayarda idonta akan abincin…”wai tsayuwar me kikeyi anan abinda aka faɗa anrigada anfaɗa bakoma zeyiba domin magana idan tafito bata komawa sabida Hakan garama ki fiddashi aranki kizauna kici abinci,,muryar Hajiya Umma tasake dokar kunen Isseta….Hajiya mama tabuɗe baki zata bawa Hajiya Umma amsa kenan taji Isseta na faɗar “ayya Hajiya aibanmaji abinda aka faɗaba balle yadameni kuma kodama naji baze ayya Hajiya aibanmaji abinda aka faɗaba balle yadameni kuma kodama naji baze dameniba sabida duk abinda za’afaɗa akaina indai nasan abin bahakan yakeba bana damuwa ni wlh tunanin mijinane yatafi dani domin bansan ko awanne hali yakeba ayanzu, taƙarasa zancen kamar zatayi kuka…..gabaki ɗaya ido suka zuba mata baki sake musamman Hajiya Umma dasu anty hawwa…Hajiya mama kallonta kawai takeyi yayinda sajad da munir suka saki murmushi kawai suna duƙarda kansu aƙasa, dukkansu bawanda yasamu zarafin yin magana har kira yashigo wayar yah munir daya miƙewa isseta ɗin….cikin sauri ta kalli wayar ganin my big bro yasa taɗago tana duban munir kamar zatayi kuka tace “ansaka my big bro mijinane ko?? “Eh shine anty maryam shima Abuƙace yake dayaji lafiyar gimbiyar tashi kiɗaga kawai, munir yafaɗa danya ƙara tura musu haushi…”wayyoo Allah my sweet life ina lafiya wlh tana faɗar hakan taɗaga wayar tare da juyawa cikin wata shegiyar tafiya tanufi pert ɗinshi batareda tatsaya cin wannan rikitaccen abincinba…. dukkansu da kallo sukabita cikin mugun mamakinta amma anrasa wanda zece komai hakan suka koma kamar andasasu awurin….!

