Halysaah Page 156 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 156…Mikewa Ajay yayi without looking at her ya nufi inda akwatuna suke yace “We are checking out now…” Khaleesat ta bi sa da kallon mamaki, sai kuma tace “Why? Cikin daren nan za mu yi check out? And Isn’t it money you used in paying for the hotel room?” Juyawa yayi ya kalleta yace “Kudin ki ne?” Kallonsa ta dinga yi babu ko kiftawa jin abinda yace, Fuskarsa daure yace “Ohk… I see you are much comfortable here, tunda gashi har an siya maki abinci kin ci happily, har da exchanging pleasantries at the restaurant, what do I even expect aside this from you??” Cikin daga murya ya kare maganar yana kallonta, can ya juya ya nufi kofa kamar zai tashi sama ya fice daga dakin, tsabar yanda Khaleesat ta zama shocked ko motsin kirki bata yi ba a inda take zaune, nan da nan taji hawaye sun cicciko idonta, tafi minti biyu zaune with different thoughts running her mind, daga karshe ta goge hawayen dake zuba idonta ta mike ta bude box dinta ta dau toothbrush da toothpaste ta shiga bandaki, wanka tayi bayan ta wanke bakinta sannan ta fito ta canza kayan jikinta tayi separating box dinta daga nasa, har sannan bata dena hawayen da take ba, kalmarsa na karshe da yace what did he even expect aside this from her yaki barin zuciyarta, wato yana nufin haka take, so he should expect that from her, akwatin nasa take kallo kamar me nazari can ta duka ta bude inda taga ya ajiye dollars ta ciri 4k dollars sannan ta mayar da box din ta rufe ta mike tsaye tana gyara mayafinta ta dau handbag ta saka kudin, kofa ta nufa tana jan trolley dinta zata bude dai dai nan ya bude kofar dakin, ko kallonsa bata yi ba tana kokarin bin gefensa fuskarta daure zata fita ya shigo cikin dakin ya kulle kofar yana kallonta, tana ganin haka ta fashe da kuka sosai tace “Ni wallahi ka bude min kofa inyi tafiyata, bazan zauna a kasar nan ba” Yace “Ai ba ke kika kawo kanki kasar ba da zaki yi deciding ko zaki zauna ko baza ki zauna ba” Jefar da handbag dinta tayi ta hade kanta da bango ta rushe da kuka, yayi wucewarsa ya bar ta wajen tsaye, she stood there for more than 15 minutes crying, daga karshe ta juya ta kalli cikin dakin taga kwanciyarsa yayi bayan ya canza fitilar dakin, ta karasa kusa da kofar ta murda taji sa a kulle, wasu hawaye suka cika idonta, nan kan Carpet din dakin ta kwanta, ta dade kwance kafin bacci ya dauketa bayan ta gama cin kukanta. Baccinta bai yi nisa ba taji an dauketa cak, ta bude ido da sauri kuma a tsorace, lokaci daya ta hade rai ta fara kiciniyar kwace kanta amma ya ki saketa har ya kai ta saman gado ya kwantar da ita middle of the bed ya kwanto kanta yanda bazata iya sauka daga kan gadon ba duk da bai sakar mata weight dinsa ba, ya kai goshinsa kan nata yayi kasa da murya yace “I tot kin canza kin dena kukan banza yarinyar nan” Turasa ta fara yi a fusace tace “Bana so, ka kyaleni….” a hankali yace “Ohk i am sorry Jeeddah, i care much…. That was why I overreacted” Muryarta na rawa tace “Ni ka ɗaga ni, da ka ga ya biya kudin abincin me yasa baka bar abincin a nan ba ka siya min wani? Ina ce kai ne ma ka rike abincin har zuwa dakin nan? Me yasa baka bar masu a can ba if you are not okay with him paying the bill? Sannan wani pleasantries kaga nayi exchanging da shi? Kuma a takaice kana nufin halina ne na saba haka, shi yasa you are not expecting anything aside from what i did…..” Wani kuka ne ya taho mata ta kasa ci gaba, saboda kwanaki da yaga tana magana da Jay shi yasa zai ce he is not expecting anything aside her reaction to Abdul, but me yasa bai yi considering cewar ko gaida Jay yanxu ta dena yi saboda shi ba, kuka ta dinga rera masa kamar er karamar yarinya, shi dai kallonta kawai yake babu ko kiftawa har lkcn bai ɗaga ta ba, cikin kuka tace “Halina ne na saba kula maza, you were suppose to say it straight to my face, ba wai a rufe ba” after a while ya koma gefenta ya jawota kusa da shi a hankali, yayi kasa da murya yace “Alright I am sorry Jiddah, i realized i overreacted, kuma kin san saboda me?” Ita dai kuka kawai take, ya rungumota kirjinsa cikin sanyin murya yace “Because i care so much about you, that guy is ur Ex Husband, you don’t expect me to be happy seeing him, kinsan yanda naji da na gansa kuwa? All because I care so so much about you” A fusace tace “You care so much about me shi yasa kayi raping dina after still knowing that I am a virgin?? Beside haushin me zaka ji saboda ka ga Abdul bayan kai ne kayi taking pride dina without even pitying me” Ta fashe da wani sabon kukan bayan ta tuna irin azaban da ta sha a ranan da ya rabata budurcinta, abun ya dawo mata sabo a zuciyarta, kasa cewa komai Ajay yayi don lokaci daya ta tayar masa da wani irin shaukinta da yake ji duk sanda ya tuna shi ya fara saninta ya mace, ya kankameta kissing her all over her face muryarsa na rawa yace “I know wife, I know this, i know i took ur pride, but bazan hana kaina kishi idan naga tsohon mijinki ba, because, i… I….” Kasa ci gaba yayi yana rungume da ita kamar za su hade su zama daya, tana jin yanda zuciyarsa ke bugawa da sauri, they were like that for many minutes ya dinga jin wani irin abu game da ita a zuciyarsa that is difficult to understand, a hankali yace “Jeeddah” Khaleesat taki cewa komai, Sai da ya kai zuciyarsa nesa saboda wani azababben kishi da ya turnukesa tun ma bai fadi abinda yake son fadi ba yaji wani abu ya tokaresa a kirji, but just to quench his curiosity forever, da kyar murya can kasa yace “Tell me everything about your marriage life with ur Ex Jeeddah” Khaleesat ta zame kanta daga jikinsa tace “It’s not necessary, it’s my past… so it’s not worth remembering or talking about” Ya sake jawota jikinsa as if murmuring his words yace “I know Jeeddah, but everything seems like a miracle how it was possible for you to come out of his house a virgin… Ko bashi da lafiya ne?” Dariya sosai tambayarsa ya ba Khaleesat duk da haushinsa da yake zuciyarta na abinda yayi mata, tace “Kai da kake da lafiya ba gashi ka cuceni ba har da stitches?” Ya kai bakinsa wuyanta yana lumshe ido kamar me jin bacci yace “To ai ke din ce mutum bazai iya resisting ba idan ya fara….” Sai kuma yayi mata rada a kunnenta, wani iri taji a jikinta duk da kunyan da ya rufeta, amma lokaci daya ta dawo dai dai bayan ta tuna pain din, ta tura baki ta fara kokarin kwace kanta daga rungumar da yayi mata, yaki saketa a hankali yace “Tell me plss Jeeddah, ai ni na tambayeki, kinsan yanda nake ji a zuciyata before gathering courage to ask you this, let me just know now and forever” Ta ɗan kallesa, sai kuma tace “To ka fara bani amsan tambayar da zan maka first kafin in baka naka amsan” Obediently ya kwantar da murya yace “Billah ur wish is my command ur Majesty” Ɗan murmushi tayi tana nanata ur Majesty din da yace a ranta, dagota yayi suka zauna ya jingina da gado ya rungumota between his legs, kanta na saman chest dinsa ya sauke hulan kanta yana wasa da gashinta yayi kasa da murya yace “I am all ears ur Majesty” Tace “Kawai tambayar da zan maka shi ne, ashe dama kana magana haka? I mean lengthily….” Murmushi yayi ya daura forehead dinsa a saman kanta ya lumshe ido as if he never expect the question from her, yafi second talatin a haka don shi kansa yana mamakin maganarsa a yanzu, wanda a baya da Jay kawai yake dogon magana haka, ko Mai martaba baya dogon magana da shi, can ya dago kansa a hankali still smiling, sai kuma ya kai bakinsa kunnenta kamar me rada yace “To bayan kin kai ni sweet paradise dinki what do you expect? Kinsan abinda kika sa naji kuwa” Khaleesat taki cewa komai don dariya da kunya ya bata, ya kara yin kasa da murya yace “A can na samo makullin speech box dina wallahi” Khaleesat tayi murmushi tayi lamo a kirjinsa, hannunsa taji yana kokarin daga rigarta daga kasa, ta hade rai ta buge hannun da sauri tace “Meye haka?” A hankali yace “Nuna maki hanyar inda speech box din yake zan yi mana My Lady” Cike da shagwaba tace “Bana soo” Tuni ta kwance masa daya daga cikin notika uku da suka rage a daure, ya rage masa saura not biyu kacal, yana lumshe ido kamar wanda ya sha wani abu yace “Na dena My Lady” Khaleesat taji gabanta ya fara faduwa ganin ba muryarsa kadai ba hatta yanayinsa ya fara canzawa, zamewa ta fara yi daga jikinsa tana turo baki, yayi saurin rikota pleadingly yace “Plsss mu ci gaba da maganar da muke” Tayi kokarin calming kanta cause her heart was racing so fast tace “Ohk we will talk but on one condition” Ya matso da ita kusa da shi yana kallonta yace “What is ur condition?” ta marairaice masa tace “Don Allah kar kace zaka min komai, kaga har yanxu ban warke ba wallahi, i am still feeling pain, promise you won’t do anything to me aside from talking” Hawaye ya kawo idonta, ya kwantar da kanta saman kirjinsa yayi shiru, sai kuma ya lumshe ido, hakan yasa muryarta na rawa tace “Kaji plsss?” Ya kwantar da murya yace “Na ji, amma….” Ta ɗago kanta da sauri jin yace amma, ya ɗan yi murmushi ya kai bakinsa kunnenta ya rada mata magana, rufe fuskarta tayi a kirjinsa, murya can kasa yace “Kin ji?” Cike da shagwaba tace “What if you exceed that?” Yace “Kiyi ihu” Dariya ya bata sosai, ta turasa tace “Wanda nayi ranan ya sa ka dena abinda kake yi? Har sai da ka ji min ciwo” Yana murmushi yace “To ai baki yi ihun ba sai da kika ga na dau hanyar paradise, kin ga ai bazan ji ihun ba” Ta fara kokarin barin kusa da shi tace “Kaga bazan yi trusting din ka ba har abada” Yayi saurin rikota yace “To nuna min inda kika ji ciwon, kin ga har yau ban gani ba” Ta daure fuska tace “Ni bana son irin wannan maganar” A hankali yace “Ur command is my priority my queen, I am sorry, mu ci gaba da maganar mu babu abinda zan maki trust me” a hankali ta koma kusa da shi ta kwantar da kanta a kirjinsa ta lumshe ido tana jin wani abu ya mamaye lungu da saƙon zuciyarta, yayi kasa da murya yace “Now answer my previous question, kuma Ina da tambayoyi da yawa da zan maki during our stay in America…..” A hankali Khaleesat tace “Kawai Allah bai nufa yayi min komai ba, let’s leave it that way, now ask you next question” Ajay ya ɗago kanta yana kallonta babu ko kiftawa, slowly ya kai lips dinsa kan nata, ta fara matsawa a hankali don ita dai har yanxu she is afraid of him, tana jin zuciyarta bai yarda da shi ba, ya jawota yana magana kasa kasa yace “Trust me wife, ni fa nace babu abinda zan maki” Sai kuma ya marairaice mata yace “But let me romance you pls, iya shi kadai zanyi i promise” Kamar zata yi kuka tace “Ba daga haka bane kake wucewa, ni wallahi bana so da gaske, why are you wicked bayan nace maka ban warke ba har yanxu” Lokaci daya hawaye suka ciko idonta zuciyarta na bugawa da sauri, ya kwantar da murya yace “To kinsan me zai faru?” Ta daga idanuwanta ta kallesa hawayen dake makale idon suka silalo kasa, ya dora kanta a kirjinsa yana goge mata hawayen idonta a hankali yace “Ba abinda zan maki My Lady trust me, just show me the injury and ko romance din ma bazan maki ba” Turasa tayi tace “Kamar ya? ni bana so” Yace “Da gaske kawai gani zan yi shi kenan, kinga ae har yanxu ban ga injury din ba, have you forgotten i am a doctor, may be in maki prescribing wasu drugs din ma idan na duba” Ta masa wani kallo tace “Doctor me yi ma patient iskanci ba” murmushi yayi yana kallonta kasa kasa yace “Baki ji dadin iskancin ba? Ko kin manta abinda kika yi ranan da Dr din yayi maki iskancin” Da sauri ta rufe fuskarta a jikinsa tana murmushi, kamar me rada yace “Ki yarda dani babu abinda zan maki, ki bari in duba ki plss” Shiru tayi, sai kuma a hankali tace “Ni dai sai dai cikin duhu zaka duba” Da sauri yace “Dama cikin duhun za a duba ai” Yana fadin haka ya kashe wutan dakin kamar jira yake, ji tayi bata yarda da shi ba kwata kwata, ta fara komawa baya tace “Wallahi ni dai ban ji ka rantse ba, ta yaya zan yarda da kai” Dariya ta basa sosai, ya dake yace “Bayan duk oath din da na dauka kafin in zama likita, wani rantsuwa kuma kike son inyi yanxu, ai babu Doctor din da zai yi harming patient dinsa just like that, idan ma yayi sai Allah ya kama sa, at this moment u are my patient and i am ur Doctor, trust me i will not harm my patient” Shiru tayi jin abinda yace, yayi kasa da murya yace “To a cire maki kayan ne ko zaki cire da kanki?” Ta bude ido sosai tace “Ban gane a cire kaya ba kuma?” Da sauri yace “Ohh ashe ɗaga rigar kawai za ayi, na manta ne” Ta tura baki tana kallonsa cikin duhun, jawo pillow yayi ya kwantar da ita, yayi kasa da murya yace “Ko kin zo da Glove so that you will know that I am serious with my Job” Tace “To ka bari sai ka siya Gloves din tukunna….” Da sauri yace “A’a ai ana iya dubawa haka, kuma kinga gobe za mu tafi Zanzibar, gwara a duba yanxu” Bai jira me zata ce ba ya fara daga rigar jikinta da sauri before she could say No, tuni kamshin musk mai tsada da Mami ta bata…



