Fentin Zina Page 22 Hausa Novel
*****Shirin kayanta takeyi a cikin akwatinta mai girma ta sanya komai nata a ciki kama daga kaya, takalma, hijabai, harma da kudaden ta data ajiye ta dauka a boye ta ajiye a can kasan kayanta bata son kowa ya gani domin bata so wani karin zargi ya shiga tsakaninta da mutanen gidan a karo na biyu.Fateema ta dago labulen ta shigo da sallama ta zauna a gefen Ameena tace adda zanyi kewarki sosai zanso da baba malam zai bani izini mu tafi tare dake inyaso sai in dawo kafin a fara jarabawar fitan mu.Jan zip din Jakar Ameena tayi tace ki gwada sa’a sai kiga ya barki din.Hum nasan zai barni amma tsoron tambayar sa nike ji.Kedai ki gwada mana me zai miki?.Tam shikenan adda zan gwada Allah yasa ya yarda.Haka suka ta hira jefi jefi har ta gama adana komai a guri daya.*****Cikin ikon Allah fateema ta tambayi baba malam kuma ya amince mata akan ya bata sati biyu ta dawo, murna a wurinsu ba’a magana tun bama Ameena ba don tana jin zafin rabuwa da iyayen nata da kuma tilon kanwarta don haka ta samu kanta cikin farin ciki daya kasance tare zasu tafi da fateema.Yau ta kama ranar da zasu tafi JOS baba malam ya kira su cikin dakin shi yayi musu nasiha mai bin jijiyoyin jiki tare da fada sosai kan au kula, kuka sukeyi sosai har dai ya soma karaya dukda shima karfin hali kawai yake yi amma kasan zuciyar shi yana jin kunar rabuwa da ‘ya’yan shi musamman Ameena wacce kaddara ta zana mata sabon layi da babin rayuwa kuma zata dauketa tayi nesa da ita duk cikin ‘ya’yan shi baya jin akwai wacce yake so sama da Ameena tun tasowan ta yarinya ce mai ladabi da biyayya mai bin dukkan umurnin da zasu gindaya mai kuma addini da kokarin kiyaye dokokin ubangiji shiyasa ta shiga ranshi sosai, a yanzu da jarabawa ta fada mata ya karbi kaddara ya mata uzuri domin yazo a ingantaccen hadisi cikin arba’una hadith cewar tun mutum na ciki ake rubuta dukkan ayyukansa arzikinsa ajalinsa da kuma makomarsa “ma’ana dai shi tababbe ne ko mai rabo ne” wannan dalilin ne ya sanya shi bai tsaurara da yawa gameda lamarin ba domin ya tabbata ba halin Ameena bane illa yazo a babin kaddara wacce babu wanda ya isa ya canja.Hawaye yaji suna taruwa a idanun shi yayi kokarin cijewa ya mayar dasu don baya so su fahimci raunin shi.Sosai ya musu nasiha kana ya dauko kudi masu dan dama ya mikawa Ameena yace kudin motar kune harda na dawowar fateema sauran canjin kuma ki bari a wurin ki koda zaki bukaci wani abu, roko na har kullum a gareki shine wannan abun da ya faru inaso ya zame miki darasi mai girma ki kara kiyaye addu’ah sosai, karatun Qur’ani kada kiyi wasa da shi, ki tsare kanki da mutumcin ki sannan ki zauna da mamar taku lafiya kiyi mata biyayya daidai yadda zaki mana, Allah ya muku albarka.Suka hada baki wajen cewa Ameen baba, sannan Ameena tace kwalla na zubo mata baba nagode Allah ya saka da alkhairi Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana mai albarka inna har yanzu taki ta saurare ni baba dan Allah ka tayani bata hakuri wallahi nayi nadama ban san taya zansa ta gasgata ni ba.Kiyi shiru Ameenatu zata fahimta ki bata lokaci, sannan abu na gaba ban yadda ko kofar gida ku leka ba idan ba tare da dalili mai karfi ba, bana kallon ku kuma bazan kasance a gefen ku ba don haka nikeso ku daukar mun alkawarin kiyaye dokata!.Insha Allah baba mun dauki alkawarin bin umurnin ka, suka hada baki wajen fada.*****Tashar maraban jos suka nufa, anan suka samu motar ta kusa cika suka shiga ba jimawa sauran mutanen suka samu, daga nan suka daga zuwa birnin PLATEAU JOS.Kasancewar basu tashi da wuri ba hakan yasa sai yamma lis suka isa, a tasha suka sauka, fateema ta kira mama rabi a waya tace su tari mai napep su hadata dashi zata mai kwatancen inda zai kawo su.Hakan sukayi, mai napep suka samu suka hadasu, ya fada musu 1k zai kaisu, basu tsaya ciniki ba suka shiga ciki yaja suka tafi.Tun akan napep din baccin gajiya ya soma fisgar Ameena daidai wata kasuwa taga mai atille da ciyo(mogolop) kusan a tare da sauri baccin ya washe tace mai napep dan tsaya in siya abun can, ta fada tana nuna shi da hannu.Mai napep yadan juyo da rabin fuskar shi yace hajiya bafa a tsayuwa a nan kame akeyi kuma gashi yamma tayi amma indon wancan ne unguwar da zan kaiku ma ana saidawa da safe zaki samu.Hadiye miyau tayi wanda sautin shi yadan fito gwat tace babu komai.Har kofar gidan ya saukesu bisa kwatancen da mama rabi ta mai ya parka ya juyo yace ku kirata a waya kuce gamu a inda tace.Fateema ta kirata ta shaida mata sai tace gata nan zuwa.Ba’a dau lokaci ba ta fito suna ganinta suka hau rige rigen sauka.Fateema ce ta riga isa gareta ta rungumeta kana ta saketa, daidai Ameena tana karasowa gurin ta fada jikinta ta saki wani marayan kuka, mama rabi ta hau bubbuga bayanta tana cewa haba Ameenatu kiyi shiru kinji komai zaiyi daidai, ki daina kuka kada mutanen layi su farga.Janye jikinta tayi, mai napep ne ya dauko musu akwatunan su yana fadin, na barku lafiya hajiya.Mun gode Allah ya saka da alkhairi, cewar mama rabi kenan.Ta dauki babban akwatin, fateema ta dauki karamin, Ameena kuma ta dau jakar hannu suka shiga ciki.Gidansu mama rabi gida ne mai fadin gaske don hatta karamin lambu akwai a ciki an kewayeshi da guntuwar katanga sai flats guda uku na mama rabi dana mamar mijinta sai na mijin.Sai da takaiwa Ameena ruwa mai zafi sosai tace da ita ta tafi taje tayi wanka.Ilai kuwa Ameena taji dadin ruwan domin sosai ta gasa jikinta kafin ta fito, fateema ma ta shiga tayi wankan, lokacin magriba tayi don har ana kiran sallah.Dama sunyi alwala daga sanda sukayi wanka don haka sallah sukayi, mama rabi ta gabatar musu da abinci jellof rice ce taji dankalin turawa wato Irish sosai Ameena taci abincin don ba karamin dadi ya mata ba har mama rabi tana cewa ko a kara mata ne? Tace a’a ya ishe ta hakanan.Mama rabi ta nisa tace bari muyi sallahr isha sai muje ku gaida dada kafin muyi laifi don abun magana bayi mata kadan.Toh mama! Inji fateema, kishingida Ameena tayi tana cewa wash na gaji wallahi kamar idan na fara bacci kada a tasheni inyi ma’ishi kafin in tashi.Ai ko dai sai ki jira sai munje mun gaida wancan tsohuwar domin bazan iya da jarabar ta ba.*****Jerawa sukayi su uku sukayi sallama a part din dada mama rabice a gaba suna biye da ita.Dattijuwa ce ba sosai dinnan ba kanta cike da furfura tana taunar goro kallo daya ta musu ta mayar da kanta ga TV.Suka karasa ciki a kasan carpet suka zauna har ita mama rabin, suka shiga gaisheta ta shiga amsa musu cikin gyatsine fuska, ta kalli bangaren da Ameena ke zaune tace wannan ce tayo abun kunyar ko? Meyasa bata ci gaba da zama a gidan su ba?…….. *EESHERT ADAMU* *MATAR MAJEEDADI* ✍️



