Karfe A Wuta Chapter 83 By Ayshercool
“Ban gane aikinku ku ke yi ba, wane irin aiki ne babu evidence, kawai ku kama mutum ku rufe shi?””Distinguish, na sanar maka yaron nan fa muna da evidence a kansa, ciki har da videon da CCTV camera ta ɗauka, lokacin da yaje gidan, dan haka musu ba naka bane ba. Babbar shawarar da zan baka bai wuce ka je ka nema masa manyan lauyoyi da zasu tsaya masa ba” gaba ɗaya jikin Indabo yayi sanyi ƙalau, cikin mamaki da tsantsar tashin hankali ya ce “Ka ce kana da videonsa lokacin da ya shiga gidan?””Ƙwarai kuwa, da cikakkiyar hujja da aka bamu muka kama shi, kuma wadda ya aikatawa abin, tana tare da hukuma, kuma ta tabattar da hakan da bakinta, dan haka zamu gurfanar da shi a gaban kotu kamar yadda kotun ta buƙata”Indabo ya cire hular kansa da ya ji gumi na barazanar ture ta daga kansa, ya shafi shimfiɗaɗen sanƙon da gwagwarmaya ta raba tsakanin gashin kansa, yana sauke numfashi yayin da bugun zuciyar sa ke ƙara hauhawa tamkar ta tsaga ƙirjinsa ta fito.”Ina Abdul ɗin yake?”Jami’in ya ce “Mu je na kai ka ka ganshi” yayi wa indabo jagora, har zuwa in da aka rufe Abdul, yana ta tangaɗi, sai da ba iya mayen yake yi ba, har da magagin ciwon da yake sakaɗarsa, sai dai mayen da yake yi ya hana shi gane takamaimai abin da yake danunsa.”Abdul yasar” Indabo ya kira sunansa cikin tashin hankali, ganin a wurin da aka ajiye shi, ɗan ƙut a takure, duk wurin babu tsafta, har gari prison ɗin da ɗan uwansa yake a ƙasar waje, a kan wurin nan da aka ajiye Abdul.Abdul na jin muryar Indabo ya taso, cikin maye ya ce “Daddy dan Allah ka fito mini da ramma, kar na mutu ban ganta ba, ban ga ɗa na ba, akwai ɗa na a cikin ta, dan Allah ka yi mini rai, ka dawo mini da ita rahama rayuwata ce””Dalla rufe mini baki, soko bita zaizai yarinyar da ta tona maka asiri, ta tabattar da kai ka yi mata fyaɗe ka ke nema, saboda baka da hankali, ita tayi silar shigarka wannan halin da ka ke ciki”Abdul ya ɗaga idanunsa da kyar, ya ce “Rahaman? Ta fara so na fa, kai wannan zance ne, rahama ba zata taɓa yin haka ba, kai ka saceta kawai ka fito da ita, tun kan na faɗi komai, a bani mata ta kawai mu bar garin nan, kan na fasa ƙwai mai wari” yayi maganar yana zamewa a hankali ya faɗi ƙasa, saboda ciwon cikin da ya murɗe shi.Indabo ya ce “Abdul, kai Abdul anya yaron nan lafiyarsa ƙalau ku fito da shi a san abin yi”.”Lafiyarsa ƙalau a cikin maye yake, zai miƙe ya ware ne, kar ka damu”Indabo ya ja jami’in suka koma gefe, ya ce “Officer babu yadda za ayi ne? Zan bayar da ko nawa ne, ku sakar mini shi dan Allah””Am so sorry sir, hakan ba zai taɓa yiwuwa ba, ana sane da duk wani motsinmu, kayi haƙuri lauyoyin dai yakamata ka ɗaukar masa” Indabo yayi shiru bai sake cewa komai ba, ya fice ya bar wurin.Yana komawa gida mahaifiyar Abdul ta tare shi cikin damuwa da tashin hankali ta ce “Yaya ake ciki? Ina Abdul ɗin yake?”Ya girgiza mata kai ya ce “Da gaske an kama shi, wannan karon bana tunanin kuɗi da sanayya za su yi amfani, kuma wannan duk munafuncin kankarofi ne, da ni yake zancen”Hannu ta ɗora a ka, ta fara kurma ihu “Na shiga uku naga ta kaina, shikenan gaba ɗaya yaran rayuwarsu ta tarwatse, babu wanda zan mora? Wannan wane irin abu ne?”Indabo ya ce “Kiyi haƙuri mana, ai matsalar Abdul da sauƙi, nan gida Nigeria ne, komai zai zo da sauƙi da yardar Allah, ki yi haƙuri ki daina wannan kukan” da kyar ya din ga rarrashinta, gaba ɗaya hankalinta ya tashi.***Ramma na kwance, jikinta ya ɗauki zafi, ga tarin damuwa, mama sai faɗa take yi mata, tana kiranta mara hankali, saboda furucin da tayi, a kan kar a zubar mata da ciki.Mama ta cigaba da jaddada mata abin da baban Abdul ya yi wa Nura tana kuka, wanda hakan ba ƙaramin taɓa zuciyar ramma yake yi ba. Haka nan ta ji ta kasa hukunta Abdul da laifin da babansa ya aikata, ita burinta ɗaya a hukunta shi a kan ci mata zarafi da yayi, shi ma ƙasan zuciyarta tana fatan a sassauta masa, mussaman ta ɓangaren alkhairin da ya yi wa garinsu, da kuma yafiyarta da ya din ga nema babu yau babu gobe. Ta din ga tunanin ko yana cikin wani hali yanzu oho.Sai dai duk da haka, abin da aka yi wa yayan nata ya daketa, ya taɓa zuciyarta nesa ba kusa ba.***Gaba ɗaya Abba ya tashi hankalin sojojin nan, a kan lallai su nemo masa yar sa a take, ba sai bayan wani lokaci ba.Lallai su kir wannan ɗan daban, ya dawo masa da yarinyar sa.Nasir kuwa gefe ya koma yayi shiru yana nazari tare da takaicin daɗewar da aka yi Nabila tana raina masa hankali.Ya kama liti, aka sake shi, ya yi target ɗin Walid, kwatsam ya daina zuwa wurin saida shayi, yayi target ɗin ɗan mama shi ma ya suɓuce masa, yanzu ya ƙara tabattar da Nabila shigo-shigo babu zurfi tayi masa, ta din ga rusa masa aiki, ashe mama son sa take yi, da take ta ankarar da shi a kan Nabila, amma ya kasa ganewa. Sai dai duk da haka, ya kasa tsayawa ya ji haushinta sosai, sai haushin Viper. Ya tsane shi ta kowace fuska, saboda yadda yake tozarta masa careersa ta aiki, kuma ya yi imani da cewa shi ne yake ziga Nabila yake yaudararta da wannan hotunan da daɗin baki, take kare shi, saboda ya ga yana da makamin yin hakan.Nabila a hanya suka ɗauki liti da kuma Walid, Nabila ta ce “Oga walid ina kwana?””Lafiya ƙalau, ya aiki?””Alhamdilillah”Viper ya kalli yadda ba su kula juna da ita da liti ba, yayi gyaran murya ya ce “Kin yi wa Abdallah fa laifi”Ta ce “Waye hakan?” Ya ce “Liti mana””Nayi masa me?”Ya ce “Kin saka an kama masa ɗan mama, kasa bacci yayi jiya, gashi dama shi ma kin taɓa sakawa an kama shi. Kin saka sa da suka je CID suka kai masa abinci, suka zo in da muka haɗu”Cikin tsiwa Nabila ta ce “Ni na matsi bakin ɗan maman na ce yayi magana, to ya fashe ya huta mana””Viper ka daina haɗa ni da yarinyar nan, zan iya karairayata ba ta da kunya”Viper ya ce “Easy mutumina, a din ga yi wa ‘yar madara kara mana””Dan Allah ka daina haɗata da waliyiyyar baiwa, babu haɗi kashi da fura”.”Waye kashin waye furar?”Daga gaban motar ya waiwayo a fusace ya ce “Ke ce kashin, ke kin isa ma na haɗa ki da jauhar, mutuniyar kirki, yar aljanna, ai wallahi an cuci yar madara idan na ana haɗata da ke, shi kansa Vipern ƙular da ni yake yi, yadda yake kula ki. Kamar nayi muku dukan tsiya, ai wallahi an ci amanar ‘yar madara. Kuma ba zai aure ki ba, sai dai ki je can ki auri wannan suɗaɗɗen yayan naki, tun da an ce sonki yake yi. Yar madara an yi an gama, kuma ba za a sake ba wallahi””Aikuwa sai dai baƙin ciki ya kasheka, Allah a saki Anas, a kama ka”Walid ya ce “Dan Allah liti kayi haƙuri, kai a duniya kamar kuturu saboda naci da nanata magana””Kaga ka ƙyaleni na yi mita ta, ina raye ana cin amanar yar madara mai bani taliya da cincin ga ladabi sama da ƙasa, kawai sai wasu abubuwa yake yi yana sakarwa wannan fuska. Ni wallahi idan aka dame ni, na fasa kai ku wurin, ku je ku nemi wurin da kanku”Walid ya ce “Allah ya baka haƙuri, Allah ya huci zuciyar ka””Eh naji Amin, yarinya sai taurin kai da nacin tsiya, itakaɗai a cikin maza, zaratan ‘yan daba, kamar ba mace ba. Yar madara da ko haɗa hanya ba ta iya yi da maza””Ni yakamata ka gaya wa haka Abdallah ba Nabila ba, idan ka ci zarafinta kamar juhar ka yi wa, ni kuma taɓa jauhar taɓa ni ne kai tsaye yakamata ka kiyaye”Liti ya ce “Easy maza, tuba nake ba zan sake ba in sha Allah”Nabila kuwa tuni ta fara kuka, ta ji haushin maganganun da liti ya gaya mata, Walid ya din ga bata haƙuri, liti yayi musu banza. Viper sai ya tsinci kansa da kasa bata haƙuri, maganganun liti suka yi tasiri a zuciyarsa, ya ga tamkar cin amanar jauhar yake yi. Sai dai kuma yana tsananin tausayin Nabila, so take yi masa da gaske ba na wasa ba.Wayarsa ce ta fara ringing, ya ciro ya ɗaga.”Viper kana ina ne?””Na je wani wuri ne””Maza maza ka dawo, idan ka san kana tare da yarinyar nan barrister ka dawo da ita, mahaufinta ya zo yana ɗaga mana hankali”Viper ya ce “Muna tare, amma mun yi nisa gaskiya, zan turo muku, address ɗin da muke, a bashi””Viper” sojan ya kira sunansa da ƙarfi.”Am sorry sir, am ready to face the consequences of my actions, ba zan iya dawowa yanzu ba” ya ajiye wayar. Nabila ba ta kula shi ba, balle ta ji da wa yake waya.Sai dai yana gama wayar, ta ta wayar ma ta fara ringing, ya miƙa mata, ta ɗaga.Cikin girmamawa suka gaisa da mai kiran wayar ta ce “Eh muna tare bari na bashi”Ta miƙa wa Viper wayar.Ya kalleta yana jiran jin ba’asin waye.”Ka karɓa mana” tayi maganar tana kallonsa.Ya saka hannu ya karɓa, ya saka a kunnensa ya ce “Salamu alaikum”Cikin matsananciyar rawar murya ya ce “Aminu, Al’amin ni ne, Al’amin ka yi mini magana dan Allah” sauke wayar yayi, yana yi wa Nabila wani irin kallo, take ta sha jinin jikinta, wani fitsarin tsoro ya cika mata mara, wani irin kallo yake yi mata mai cike da tuhuma da kuma tambayoyi.”Ban gargaɗe ki a kan abin da ki ka aikata ba?”Walid ya ce “Menene kuma?””Dan me, meyasa ki ke da taurin kai, mutumin da ya ce baya buƙatar ɗan ta’adda a cikin rayuwarsa zaki haɗa ni da shi, ban gargaɗe ki ba?” A take Walid ya fuskanci in da zancen ya dosa.”Ba magana nake yi miki ba” Viper ya yi mata tsawa cikin maɗaukakiyar murya.Fashewa tayi da matsanancin kuka, ta takure a jikin ƙofra motar tana kiran suna. Abba cikin matsanancin razani da tashin hankali. Ƙoƙarin buɗe ƙofar ta din ga yi, dan gara ta buɗe ta dungura tayi waje, da wannan tashin hankalin da yake yi mata.”Viper zata fita fa ka hanata” liti yayi maganar cikin tashin hankali.Sojan da yake jan su, ko a jikinsa ko kallonsu bai yi ba, balle ya saka musu baki.Allah ya sa an yi locking motar.”Hey stop here, let’s reverse, take us back to barrack””A’a ba zamu koma ba, abin da zai saka mu koma, ka sake mayar da mu baya, abin da tayi dai-dai ne, ka yi haƙuri kawai malam”.”Mai laya, dan me zata nemi lambar mahaifina ta haɗa ni da shi, kin je kin haɗu da shi kenan ko?” Ta girgiza kai cikin tsoro tana kuka.Walid ya ce “Mai zamani, dan Allah ka nutsu, ka yi haƙuri, mutumin nan zai yi reverse fa, ka hana shi dan Allah da kyar ya shawo kan Viper, suka cigaba da tafiya.Abbu kuwa miƙewa yayi a razane, yana ta tsuma, yana sake kiran layin Nabila, amma ya ji an kashe wayar.Bai gaji ba ya cigaba da trying, amma shiru ba ta shiga, Ihun rahila ya jiyo a waje, ya fito da saurin gaske, ya tarar da Abba a buge, yana ta ball da ita a tsakar gida.Shahida ta maƙale a bango, sai ihu take yi tana neman ɗauki, da sauri Abbu ya ƙaraso, ya hankaɗe Abba gefe, sai dai tuni Rahila ta riga ta suma, saboda yadda ya din ga dukanta da ƙafarsa.Abbu ya ce “kai yanzu kana son ka gama da duniya lafiya, uwar taka ka ke duka saboda lalacewa?”Shahida ta ce “Wai kayansa ta kwashe masa, shi ne yake daketa”Kururuwar da maƙwabta suka jiyo, tuni suka fara shigowa, aka kwasheta aka tafi da ita Asibiti.***Tafiya suke Nasir na ta fafara gudu, amma Abba mita yake yi, gani yake kamar Nasir baya sauri. Yayi shiru ya kashingiɗa, ya tafi tunani.JALINGON JIHAR TARABA. can cikin wani jeji, da ke ƙarƙashin ƙauyen gamyel.Ƙatuwar harabar gida ce, mai da sashe sashe ne a cikin gidan. Mai ɗauke da bukkoki.Akwai tarin turaku da ke ɗaure da shanu, a wasu sassa na gidan, daga wani sashe na gidan, matashiyar yarinye ce, ‘yar shekara goma sha biyu, take surfa gero, ɗaya ɓangaren kuma wata matashiyar mace ce take iza wuta.Cikin harshen fulatanci ta ce “Chubaɗo, kina ganin har na gama tuwon nan, mu yi aikin furar nan da daddare?”Matashiyar yarinyar da take fara tas, da siririn billenta na fulani, ta ce “Eh mana, bari ma ki ga na ƙara sauri” sai kuma ta ɗan yi jimm ta ce “Dada, kamar kukan karsana nake ji, ko dai haihuwa za ta yi, bari na je na ga meyafaru””Kul kar ki kuskura, kin san baffanki ya hanaki shiga turken shanu ko? Sai kin je makarai sun sake make ki a turken nan ko? Hanzarta ki gama, na san idan Habibu na nan, zai je ya duba”.Ta cigaba da dakan geron, sallamar da aka yi ya sanya duk suka tsaya suna amsawa.Chubaɗo ta risuna ta ce “Baffa sannu da zuwa””Yauwwa chubaɗo, aiki ake yi ne?””Eh baffa”Ya ce “Sannu, ramata sannu da aiki”Matar ta ce “Yauwwa, sannu da zuwa” tayi maganar tana ƙoƙarin ɗaukko tabarma ta shimfiɗa masa.Yasar da taɓaryar hannunta tayi, ta fyalla waje da gudu, jin an kira sunan maitama a wajen.Tana fitowa, maitama ya saki akwatin hannunsa, ya ƙarasa ya rungumeta yana murmushi.Cak yaran da suke murnar ganinsa suka tsaya, ba su ba har da manyan da suke wurin, ganin abin kunyar da jibo ya aikata wato maitama.Ita kanta Chubaɗo sai ta ga abun wani iri, tayi sukuri da kai tana sunkuyar wa.Ya ce “Masha Allah, mairamu kin girma, ya ki ke””Lafiya ƙalau hamma, ya birni?””Birni Lafiya ƙalau tana gaishe ki” ta ɗauki jakarsa ɗaya, shi ma ya ɗauki ɗaya, ya riƙe hannunta suka shiga gida.Baffa da yake shan fura, ya ɗago ya kalle su, ya mayar da kansa ya sunkuyar ya cigaba da shan fura.Jibo ya ƙarasa gaban baffa, ya durƙusa ya ce “Sannu Baffa na dawo”Baffa ya ce “Sannu””Yauwwa”Ramata ta ce “Jibo sannu da zuwa”Ya ce “Yauwwa sannu”Chubaɗo ta shiga ɗaki ta shimfiɗa masa tabarma, ta ce “Ka zauna, bari na sake gyara maka ɗakinka, nayi ta mafarkinka, ashe ka kusa dawowa” yayi murmushi ya zauna, ta ɗebo masa ruwan randa, ta kawo masa, ta buɗe bukkarsa da shekara guda kenan, rabonsa da ita tana sake gyara masa.Babu wanda ya kuma kula shi, shi kuma ko a jikinsa, ya cigaba da hira da chubaɗo.Ta ɗauki ƙoƙo, ta tafi gidansu Habibu, da kanta ta shiga tsakanin shanu, ta tatso masa madara, mai ɗumi ta kawo masa, sai rawar kai take yi.Baffa yana fita aka sanar da shi abin kunyar da jibo ya tafka, na rungume chubaɗo. Hakan ba ƙaramin ƙona wa Baffa rai yayi ba, ya zubar masa da ɗan ragowar mutuncin daga dawowarsa, bayan wanda ya zubar masa a baya, yazo ya fara gwada yahudanci da baƙar ɗabi’ar da ya koyo.A fusace ya dawo gida, ya sake tarar da Jibo, yana ta hira da chubaɗo kamar wata sa’arsa. Yana yi mata tambayoyi a kan abubuwan da ya koya mata a baya, dangane da karatun boko da na addini, cikin ikon Allah bata manta ba, har sunanta da nasa, da haɗa baƙi duk bata manta ba.Sosai yake murna, kan ya jiyo muryar Baffa yana faɗa “Maitama, dama abin da ka je ka aikata kenan daga dawowarka, saboda yahudanci a gaban mutane ka rimbaci chubaɗo, saboda rashin mutunci”Jibo ya ce “Baffa chubaɗo fa ƙanwata ce ciki ɗaya, shekara guda rabona da ita, menene laifi a cikin hakan? Kuma naga ai ba wani girma ne da ita ba””Zaka rufe mini baki, ko sai na rushe maka kai da sandar nan? Tashi kema daga kusa da shi, kana naɗa miki duka. Ka tashi mu je arɗo yana son ganinka yanzun nan, har labarin zuwanka da abin da aikata ya je masa. Kalle ka har ka fara tsufa, sa’aninka duk sun yi aure, sun kusa ma fara aurar da ‘ya’ya kai kuma kana nan kana gararanba, kana shashanci”Jibo ko a jikinsa, ya ce “Nima dawowata yanzu har da maganar auren na dawo””A ina zaka yi auren?””A can in da nake ne”Baffa ya ce “To bayahudiyar zaka aura kenan, masu bawali a tsaye, to sai su yi maka waliccin auren, tashi mu tafi” tashi yayi ya bi baffa, ko da suka je fadar arɗo, tuni wasu manya a rigar sun taru suna jiran su.Aka hau jibo da faɗa, da jaddada kiransa da bayahude, kuma suka ce lallai ya tattara ya bar musu gari, kamar yadda aka yi yarjejeniya da shi da farko.Jibo ya gyara zamansa ya ce “Idan har kuna son na bar garin nan, sai dai ku bani mairamu chubaɗo, na tafi da ita, dan ba zan je na rayu nikaɗai ba alhalin ina da ‘yar uwa ba, tun da ku kun sallama ni””Babu wanda zai baka chubaɗo, kuma sai ka bar rigar nan, ai duk zuwa muna gaya maka, bama buƙatar ka tun da abin da ka zaɓawa rayuwarka daban”Ya ce “To shikenan, amma ku sani duk ƙasar nan babu wanda ya bawa wani ikon ya kori wani, muddin ba zaku bani chubaɗo ba, ku bar ni na din ga zuwa ina ganinta, idan kuma kun ƙi, kun san ƙasa nake yi wa aiki, za a aiko yahudawa kuma su kore ku, su kwashe shanunku” sai kuma duk suka yi saroro.Ya ce “Eh idan mun tashi zuwa kiwo, babu wanda yake hanamu shiga duk in da muke so da shanu, muyi kiwo, saboda yan ƙasa ne mu, amma idan ku ka ce zaku kore ni, to fa kuma za a kore ku daga rigar nan, kuma a ƙwace muku shanu”. Gaba ɗaya sai suka sha jinin jikinsu, sai kuma suka koma rarrashin sa da neman sulhu.Maitama wanda suke kira da jibo, cikakken sunansa shi ne Yusuf, mahaifiyar su Allah ya yi mata rasuwa, a ƙalla ta haifi yara tara amma duk mutuwa suke yi, shi ne na huɗu, har an fitar da ran zata sake haihuwa, ta samu ciki ta haifi mairamu ake ce mata chubaɗo.Kowa ya ɗauki son duniya ya ɗorawa chubaɗo, mussaman ma shi.A can yawon kiwon shanu, ya faɗa wani ƙauye, ya tarar ana makaranta, turawa na koyar da yaran garin karatun boko. Abin ya ƙayatar da shi, ya fara shiga cikinsu, ya shiga cikin ɗalibai, kullum ya fito kiwo, sai ya je ƙauyen nan, komai kyauta ake ba su, da kayan rubutu da karatu.Gashi da ƙwazo, ya shafe wata shida yana zuwa ba a gane ba a gida, daga bisani wani a rigarsu ya gano shi, ya je ya faɗa. Ai tamkar za a cinye shi, aka ce kiwon ma ya daina zuwa gaba ɗaya.Baffa ya koma fita da dabbobin da kansa, sai dai yana ficewa, shi ma maitama yake saka ƙafarsa ya fita, ba boko ba har da karatun allo yake koya a garin.Baffa duk son sa da yara, sai da ya saka aka zane masa maitama, amma washegari ya gudu ya koma can ƙauyen ma gaba ɗaya. Yake kwana a masallaci, abin da zai ci ba wahala yake ba shi ba, kullum gidan mai garin ana bayar da abinci sau uku a rana.Innarsu babu irin nasihar da ba ta yi masa ba, da rarrashi, amma yaƙi.Hnakali ya tashi rashin ganin maitama, aka wakilta ƙarti suka tafi ɗaya garin,arɗo ya ce a ɗoro masa Jibo a ka a dawo masa da shi.Sai dai can garin suka hana kama Jibo, abu ya nemi ya zama rigima da fitina, sai da aka shirya zama na musamman tsakanin malaman dagacin ƙauyen, da ƴan rigar su jibo, a kan a samu fahimtar juna, su bar Jibo yayi karatu, su ma idan suna buƙata zasu iya kawo wasu yaran, a cigaba da yi musu karatu, amma suka ƙi suka ce ba sa son yahudanci.Abu sai da jami’an tsaro suka shiga, suka ce sai Jibo yayi karatu, ba tare da an cigaba da tsangwamar sa ba.Da kyar aka samu masalaha, sai dai can a riga suka ce, sai dai ya bar musu rigar su, babar sa ta din ga kuka tana yi musu magiyar kar su korar mata ɗa.Idan bai ga dama ba, idan ya tafi sai juma’a yake dawowa, kan ya dawo innarsu ta ɗan tanadar masa busashshiyar fura, man shanu, nono, ta ce ya tafi da su, kar ya ji yunwa, haka kurum ta ji ita dai tana son abin da yake yi. Ta fuskanci ƙalubale sosai da sosai, ana cewa ita take goya masa baya, duk lokacin da ya zo, idan zai tafi sai chubaɗo tayi ta kuka saboda sun shaƙu.Tana da shekaru huɗu, haka zai zauna da ita, yana koya mata idan baffa ya ƙyalla ido ya ganshi, ya ɗauke chubaɗo yayi ta yi masa masifar kar ya lalata masa yarinya shi dai ya je ya ƙarata.A haka aka zaɓi ɗalibai har da maitama, aka ce za a kai su makarantar kwana.Nan ma an sha gwagwarmaya, kan maitama ya tafi.Chubaɗo na da shekaru shida, Allah ya yi wa mahaifiyar su rasuwa, maitama yana can makaranta. Da ya zo hutu ya sha kuka, ya shiga tashin hankali da kiɗima mai yawan gaske.Da aka nutsa, suka sake ce masa sai dai ya zaɓa, ko boko ko ya dawo yayi aure, amma ya ce boko, suka ce to ya bar musu riga. Bai damu ba, bai kuma daina zuwan ba.Baffa ya auri ramata, ta riƙe mairamu hannu bibbiyu kamar ita ta haife ta. Sai dai tun tana ƙarama, take fama da matsalar numfashi, sai dai ko maganar asibiti ba ayi, sai dai ayi ta banka mata hayaƙi, wai iskokai ne, cike da jahilci. Ga kuma matsalar iskokai da take fama da su.Maitama ya ɗauke ta, ya kaita asibiti babu wanda ya sani, likitoci suka tabattar da athma ce da ita, wanda irin ciwon ne ya kashe mahaifiyar su.Sai da aka kusa ƙaramin yaƙi a zuriyar, saboda kai mairmu Asibiti da yayi.Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, maitama ya yi degree, ya tafi aikin soja, amma duk sunansa Bayahude a wurin mutanen rigar.A yanzun ma haka suka ƙyale shi, bayan yi musu barazanar saka yahudawa su ƙwace musu shanu su kore su daga riga.Har magana yake yi wa mairamu da turanci, kuma tana iya gane wani abun.Ya fara kashe bakinsu, bayan da ya fara basu ‘yar shinkafa kyauta.Lokacin aurensa da kyar suka je masa walicci, sai dai da suka ga birni sun rikice da yawa, ya so a bashi mairamu amma fafur suka hana shi.Shekaru suka cigaba da ja, chubaɗo na da shekaru goma sha uku a duniya, tsantsar kyawunta, ya fara baiyyana, samarin ƙauyen sun fara kawo hari, saboda kyakywar gaske ce, sai dai da yawa suna tsoron larurarta ta matsalar numfashi da suke cewa aljanu ce.Duk lokacin da Maitama ya zo garin, sai ya kawo mata kayan sawa, na kwalliya, wanda babu wata yarinya da ta taɓa amfani da su a rigar. Ya kan bugi cikinta duk wanda ya ji ya nuna yana sonta, sai ya je yayi masa barazanar saka yahudawa su kama shi, su mayar da shi ƙarfe.Ya kan kawo mata litattafai, ya sayo mata radio, ya gaya mata lokutan da ake gabatar da wasu shirye-shirye a radio na yara.Watarana da ta zama ranar mabuɗin sada chubaɗo da ƙaddararta, ta bi ‘yan matasan matan da suke fita can bakin hanya sayar da nono, domin ta je ta ga motoci, ta fita da shanu, ta fake da haka, dan Baffa baya barinta ta je ko ina…..
Ayshercool 08081012143





