Ruwan Zuma Page 7 Hausa Novel
(07) Laila sake baki tayi tana kallon Mas’ud wanda ya tsaya gem fuskarsa babu alamun wasa. Numfashi ta sauk’e sannan ta jawo akwatin ta ajiyeshi a gefe ta fara mishi magana, “Batun gudu wani gari bai taso ba Mas’ud, domin bamu san halin da zamu fad’a ba daga ni har kai. Sannan Ina zamu je? Gurin waye? Kana tunanin zamu iya rayuwa mu kad’ai babu iyaye da danginmu? Sannan wani hali zamu saka su Ummii Idan a yau suka samu labarin ni da kai tare da jikokinsu biyu sun shiga duniya? Wani lokacin dolene muyi hak’uri da abunda muke so don gudun halin da zamu saka na kusa damu.” Mas’ud dai bai daddara ba amma ya share zancen suka nemi Nurse d’in da zata d’aurawa Abul ruwa, ko minti goma ba’ayi da saka masa ba ya kwanta bacci mai nauyi. Suna zaune har azahar sannan ruwan ya k’are aka cire masa. Laila ta bawa Mas’ud kud’i akan in yayi sallah ya sayo musu abinci sannan da kunu wanda zata bawa Abul. Laila ta rok’i wata mata wacce gadonsu ke kusa ta bata aron buta da sallaya tayi sallah. Bayan ta idar ta mayar mata sannan ta mata godiya, kana ta zauna tana bawa Sabrin nono wacce ke ta6a Abul da k’afarta cikin wasa. Mas’ud yana dawowa suka ci abincin sannan suka zauna jiran lokacin da Abul zai farka. K’arfe uku da mintuna ya farka ya fara kuka, ganin Mamanshi kusa dashi tana shafa kanshi tana lallashinsa yasa yayi shiru ya mannu da jikinta yana sauk’e ajiyar zuciya. “Ina ga ya d’auka har yanzu a gidan wancan matan yake.” Cewar Mas’ud wanda abun yaso ya bashi dariya. Hararanshi Laila tayi sannan ta bud’e ledan kunun ta fara bawa Abul a baki, yana sha a hankali har ya k’are. Kwantar dashi ta yi tana kallonshi shima ya zuba mata ido yana rik’e da mayafinta kamar mai tsoron zata gudu. “Babu inda zan je Abul, Ina nan tare da kai har k’arshen rayuwata.” Magana d’aya ya gane duk cikin zancen nata wato ‘babu in da zan je’ don haka ya gyad’a mata kai ya rufe idonsa. “Mas’ud yaron nan bacci ya sake yi fa, anya lafiyanshi kuwa?” Ta tambayi k’anin nata cikin kad’uwa da tsantsar damuwa. Tuni kuwa fuskarta ta kwaye alamar zata yi kuka. Ganin hakan yasa Mas’ud ya mik’e da sauri yana cewa, “Bari in kira Nurse ta dubashi.” Da haka ya tafi zuwa kwanan Nurses d’in sannan ya dawo tare da wacce ta d’aurawa Abul ruwa. “Me ya samu yaron?” Ta tambayi Laila wacce ke rik’e da hannun Abul gam. “Tun da kika saka masa ruwa bacci yake yi, d’azu ya tashi na bashi kunu da magani ya sake kwantawa yayi bacci. Ko dai wata cutar ce gareshi?” “Bana tunanin cuta ce ta sakashi bacci, hutu kawai yake buk’ata, ku barshi har sai ya tashi da kanshi.” Tace dasu sannan ta tafi bayan ta ta6a jikin Abul wanda babu zazza6i yanzu. Abul bai tashi ba sai gab da magriba, yana tashi kuwa ya fara wasa da Sabrin wacce tun d’azu take son d’alewa kanshi amma mamanta na hanata. Ai kuwa yana fara mata tafi da hannayensa ta fara kyalkyalewa da dariya tana shilla k’afa. Farin ciki Laila taji mara misaltuwa da taga ‘yayanta guri d’aya suna wasa kamar yanda suka saba. Mas’ud wanda tun d’azu magiya yake yiwa yayarsa kan su gudu yanzu ma ya cigaba. “Kalti baki ce komai ba, ki yarda da shawarata don Allah.” Jakarshi ta mik’a mishi tare da akwatin sannan ta goyi Sabrin ta d’auki Abul a hannunta wanda bashi da takalmi tana cewa, “Mu koma gida tukunna muga hukuncin da zasu yanke, Idan sun rabani da Abul zamu gudu kamar yanda kace d’in.” Tace dashi don kawai ya bar maganan guduwa wacce a gurinta bata ma taso ba. Da haka suka fita daga asibitin bayan an basu sallama, wannan karon ma Taxi suka k’ara hawa wanda ya sauk’esu a k’ofar gidansu. Suna fita mai motan ya juya su kuma suka tsaya cirko-cirko suna kallon-kallon tsakaninsu da Baba da Madu. Madu ya kallesu daga sama har k’asa, sannan ya dubi jaka da akwatinsu wanda bayan dawowanshi daga kasuwa aka lura basa nan, a nan suka gane cewa Mas’ud k’arya ya musu, kuma d’azun yazo ne don ya kwashi kayansu su gudu. A zuciye ya isa gurin Laila ya kwasheta da mari har tana k’ok’arin fad’uwa dalilin k’arfin marin sannan ga yaranta biyu duk a jikinta. “Kai Madu, Madu kar ka sake ta6ata.” Shine abunda Baba yake cewa yana mai zuwa gurinsu cikin sauri. Amma ina! Kafin ya iso Madu ya k’ara d’aga hannu ya watsawa Laila mari, wannan karon ta zube k’asa da yaran duka. Madu ya finciko Abul daga jikinta yana cewa, “Idan akan yaron kike wannan haukan sai na mayar dashi gun kakarsa na rabaki dashi har abada wallahi.” Mas’ud da yake kusa da ita ya jefar da jakarsa ya kama hannun Abul yana kiciniyar kwaceshi a hannun Madu yana cewa, “Ka bata d’anta, ka sakeshi mugu kawai azzalumi!” Daidai nan Baba ya iso wanda bai yi wata-wata ba shima ya d’auke Madu da mari wacce sai da unguwar ta amsa. A firgice Madu ya juyo yana duban Baba wanda fuskarsa take nuna tsananin 6acin ran da yake ciki yace, “Sakar mata d’anta.” Ai kuwa Madu ya sakeshi a take Abul dake kuka ya koma hannun Mas’ud, da sauri Mas’ud ya mik’awa Laila hannu wacce ke dar6ashe a k’asa tana kuka. Hannu d’aya ta mik’a masa ya jawota ta tashi tsaye tana kuka tana cewa, “Dubamin Sabrin Mas’ud kar na karyata ban sani ba.” “Tana bacci bata ko farka ba.” Ya bata amsa bayan ya duba Sabrin d’in. Hakan yasa hankalinta ya d’an kwanta amma bata manta da cewa wannan kad’an ta gani daga hukuncin laifin da ta aikata ba. Babanta ne ke kallonta cike da tausayawa yace, “Laila Ina kika shiga muna ta nemanku? Dama zaki iya gudu ki bar iyayenki don ‘yayanki? Haba Laila! Maza ku shigo cikin gida ki huta.” Da haka ya k’ar6i Abul daga hannun Mas’ud sannan ya sakata a gaba suka shige cikin gida. Madu da tun da aka mareshi yake dafe da k’uncinsa kansa kuma na k’asa ya juyo yana duban Mas’ud wanda shima kallonshi yake yi cike da haushi da kuma dad’in marin da yasha. “Uwar me ka tsaya kake gani? Zaka 6ace mini da gani ko sai na baka naka?” Ya fad’a cikin 6acin rai har yana kumfar baki. Ganin haka yasa Mas’ud ya rufawa kanshi asiri ya d’auki kayansu yabi bayan su Laila. A cikin gida Ummii ce ta fashe da kuka bayan tayi ido hud’u da Laila, sai dai cikin 6acin rai ta yiwo kan Laila zata daketa Baba ya dakatar da ita yana cewa, “Kul, kar ki kuskura ki ta6ata, Idan baza ki godewa Allah da yasa ta dawo ba to baza ki daketa ba. Laila shiga d’akinki, yanzu za’a kawo miki abinci kici. Kai, amma me ya samu yaron nan ne ya rame ya lalace haka?” Ya tambayeta yana mai d’aga Abul sama kamar kara. A daa yana cikin masu tsokanan Abul wai ya cika k’iba, shi ba zai iya d’aukansa ba wai ya cika nauyi, wasa dai irin ta Kaka da Jika. Amma wannan karon zai iya cewa Sabrin ta fishi nauyi da kuma k’iba. Laila dake kallon Ummii cikin tsoro ta fara bashi labarin abunda ya faru a gidan Umma har da kaishi asibitin da tayi, sai dai bata fad’a mishi cewa Mas’ud ne ya ta’azzara su gudu ba. “Baba a cikin kashi na sameshi muryarshi bata fita ga zazza6i rau a jikinshi, amma kuma tana gefenshi tana bacci bata ma jin kukan da yake yi. Don girman Allah Baba wannan karon karka rabani da ‘yayana, kuyi hak’uri ku yafe mini amma kar kuce zaku kasa mini yarana.” “Babu mai rabaki da yaranki Laila, ki kwantar da hankalinki. Amma karki sake batun gudu wani guri, wannan ba tarbiyyar da muka baki bane. Yanzu dai ba wannan ba, maza shiga ki zauna a kawo muku abinci ki ci ki huta. Maza shiga, Falmata kawo mata abinci.” Ya fad’a yana yin gaba zuwa d’akin Laila na daa. Bayan sun ci abinci sun huta Baba yayi kiranta falonsa, nasiha ya fara mata tare da lallashi sannan ya k’are da fad’a yana nuna mata matakin da ta d’auka sam bai yi ba. Hak’uri Laila ta bashi sannan ta k’ara rok’on alfarmar a bar mata Abul a wajenta ya girma a hannunta. “Gobe zan je gidan nata muyi magana sosai. Ki tashi ki tafi, Allah ya bashi lafiya.” “Amin Baba, nagode.” Da haka ta tashi ta shige d’akinta, tana mai kallon k’ofar d’akin Ummii wacce tun shigowarta har yanzu bata mata magana ba. Washegari Baba ya je gidan Umma kamar yanda yayi alk’awari. Tun da ya fara magana Umma ta 6ata rai da ta fahimci maganar daya zo da ita. “Ina neman alfarmar ki bar mata yaron tunda ta nuna tana son hakan, wannan alfarma nake nema mata a matsayina na mahaifinta ba don mun fiki iko dashi ba.” Kuka ta fara tana matsar kwalla tana cewa, “Alhaji ba musu zan yi da kai ba, amma tun farko na nuna Ina son rik’e yaron nan, amma ‘yar nan ta shigo har cikin gidana ta d’aukeshi tamkar satarshi nayi ba nice uwar mahaifinshi ba. Abun ya mini zafi, akan d’an Aliyu aka mini haka! Kaico.” Ta goge hawaye da zaninta. “Nima ban ji dad’in abunda Lailan ta yi ba kuma na mata fad’a sosai, ina mai baki hak’urin abunda ta aikata kuma itama zata zo da kanta ta baki hak’uri, ai ko ba komai ke uwa ce a gurinta.” Musun dai Umma ta k’ara yi domin a bata Abul, ganin haka yasa Baba ya ce, “To tunda abun ya kai ga haka zan ce miki ko a musulunce rik’on Abul a gurin uwarsa take har sai an ga cewa baza ta iya ba, shine za’a kar6eshi a baku. Ni zan tafi.” Umma bata so hakan ba amma tasan ko kotu ta kai k’ara baza’a bata rik’onshi ba, gashi shi Baba da take ganin zai bi bayanta ma ya nuna ‘yarsa ce zata rik’e Abul. Haka Baba ya tafi dukkansu rai babu dad’i. Washe gari sai ga Laila tayi sallama ta shigo gidan, a tsakar gida ta samu Umma da Muna suna zaune. Suna ganinta suka tamke fuska kamar sun ga babbar mak’iyarsu. Basu amsa sallamarta ba, haka kuma basu amsa gaisuwar da take musu ba suna shiru tamkar ma bata gurin. Laila taji haushin hakan sosai amma bata isa ta mata rashin kunya ba, domin ko bata haifi mijinta marigayi Aliyu ba ta girmeta. “Dama nazo ne don na baki hak’uri kan abunda ya faru. Don Allah kiyi hak’uri.” Ko kala Umma bata ce sai ma wani harara da take watsa mata wanda ke nuna bata yi hak’urin ba. Mik’ewa tsaye Laila tayi tana cewa, “Na barku lafiya.” Har ta je bakin k’ofa ta jiyo muryar Umma cikin kaushi tana cewa, “Kin yi nasara a yanzu amma ki saka a ranki cewa duk ranar da kika tashi aure wallahi tallahi ni Nafisatu sai na kar6i Abul, kuma ko kotu zan shiga dake kuma a k’arshe a bani shi. Wallahi d’an Aliyu ba zai yi agolanci a gidan wani ba….” Zuciyar Laila ce ta buga da k’arfi har bata ji sauran maganganun Umma ba, bata k’ara sakanni biyar ba ta fice daga gidan cikin sauri. Dama ita d’aya ta zo, ko Sabrin bata d’auka ba gudun kar Umma ta kwaceta duk dama ta nuna bata sonta Abul kawai take so. “Bazan yi aure ba har abada. Zan zauna tare da ‘yayana, su kad’ai sun isheni farinciki. Bana buk’atar kowanne namiji a rayuwata.” Shine abunda take ta maimaitawa cikin bushewar zuciya da kuma kafiya a kan maganarta. Laila ce zaune a falon Babanta kai a k’asa ko numfashin kirki bata yi. “Na kiraki ne don naji amsarki.” Cewar Baba yana mai kafeta da ido fuskarsa babu alamun wasa. “Baba a yi hak’uri a kara mini lokaci domin har yau bani da wanda nake jin zan iya aure cikinsu. Baba nikam da kun barni a haka domin wallahi banida sha’awar aure ko kad’an.” “Bana son shashanci Laila, ke kad’ai ce wacce mijinta ya ta6a mutuwa? A haka dubu irinki suka yi aure ba don sun manta da mazajensu ko kuma sun ci amanarsu ba. Shekara hud’u kenan da rasuwansa, kina tunanin mutane basa magana ne kan zamanki a gida a matsayin bazawara? Kinsan da cewa duk in da kika ratsa wasu zarginki suke yi, yayinda wasu ke bibiyarki domin su ga wani abun kaico a tattare dake su yad’a? Laila ba zan yarda da zamanki haka babu aure ba, ki sake lale. Na k’ara miki sati biyu kiyi za6i ke da kanki akan masu neman aurenki wato Nazifi (Yayan Aliyu) Dr Zubair (Likitan da ya duba Abul) da kuma Abdul wanda dama a baya kunyi nema k’addara tasa bai zama mijinki ba. Na sallameki.”
Mum Fateey👌
