Halysaah Page 109 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 109Wajen karfe goma Khaleesat na kwance daki duk da yunwan da take ji taki fita ta zuba abinci saboda fargaban haduwa da Walid, har sannan mamaki da shock da tsoro sun ki barin ta, she couldn’t believe her self, bude kofar dakin taji anyi ta mike zaune da sauri tana kallon kofar gabanta na faduwa, ganin Ajay ne sai da ta sauke boyayyen ajiyar zuciya, ta koma a hankali ta kwanta, ya tsaya daga bakin kofar yana kallonta yace “Have you dish the food for you self ko katti kawai kika yi ma girkin dama?” He asked that question because sau hudu yana ganin Walid na cin abinci daga sanda ta gama girkin zuwa yanxu, ta sauke idonta murya can kasa tace “My waist is aching me, bazan iya zuwa downstairs ba kuma” Yace “To wa zai je maki downstairs din? Ke tsohuwa ce da waist din ki zai maki ciwo” Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, jin bai sake cewa komai ba ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake, ta sauke idonta, juyawa yayi ya fita daga dakin ya kullo kofar, after almost 10 mins sai gashi ya dawo dakin da plate din abinci da bottle water, ko kallonta bai yi ba ya ajiye abincin a gaban mirror ya fita daga dakin, ajiyar zuciya ta sauke ta mike ta tafi ta dau abincin cause she was very hungry, a nan dakin ta bar plate din bayan ta gama cin abincin gudun ta fita da plate zuwa kitchen ta sake haduwa da Walid, ta tafi bandaki ta wanke bakinta don tayi wanka tun sanda tayi isha’i sannan ta dawo, kofar dakin ta nufa tana kallon kofar wishing me makulli ne amma keyless door ne, and she don’t know the Code, kawai ta kashe wutan dakin tayi addu’a ta kwanta tunani iri iri na yawo a ranta, a haka bacci ya dauketa. Ajay na zaune parlor yana danne dannen laptop har kusan karfe sha dayan dare, Walid ma na parlon yana kallon TV ba me cewa kowa komai cikinsu, daga karshe Walid ya kwanta kan 3 sitter ya dora handkerchief dinsa a fuska, har karfe sha biyu da rabi Ajay na parlon, daga karshe ya juya ya kalli Walid don for an hour now same position yake alamar yayi bacci tun daxu, mikewa Ajay yayi ya kashe TV din da wutan parlor ya dau laptop dinsa ya wuce sama, kofar dakin da Khaleesat take ciki ya bude ya shiga ya kunna wutan dakin yana kallon saman gadon, tana kwance ta rufe har kanta da duvet tana bacci, duk da ba frequently suke haduwa a gidan ba amma kusan duk dare idan ya gama abinda yake yi yakan zo dakin ya tsaya daga nan bakin kofa ya dubata, wani lkcn karfe dayan dare wani lokacin biyu, duk ya bude kofar kuma zai ganta kwance ta rufe har kanta tana bacci, kashe wutan dakin yayi ya fita ya jawo kofar ya rufe sannan ya nufi bangarensa. Cikin bacci Khaleesat taji ana kokarin sauke duvet din jikinta, ta bude ido da sauri ta rike duvet din gam ta yunkura ta mike zaune duk da bata ganin koma waye saboda duhun dakin cikin firgici tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” Muryar Walid taji yace “C’mon, why do u have to close ur face while sleeping, do you want to suffocate ur self?” Sosai hankalinta ya tashi ta fara komawa baya tana rike da duvet dinta taki barin ya sauke daga jikinta tace “Don girman Allah ka fitar min a daki, me yasa zaka shigo min daki? Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” Yace “Hum, just to compliment you Halysaah, you’ve got a beautiful glowing skin and a fine body structure…..” in hankalin Khaleesat yayi dubu ya tashi a wannan moment din, muryarta na rawa tace “Don Allah kayi hakuri ka fita plss” Yace “C’mon, meye big deal don na shigo dakin ki? why are you acting like a bush girl warce bata waye ba, sai kace ba a abroad kika yi karatu ba?” Kunna wutan dake kusa da gadon yayi yanda zai dinga kallonta da kyau, da sauri ta fara kokarin komawa daya bangaren gadon tana gyara hularta da ya kusa cirewa daga kanta, ya fixgota ya hau kan gadon yana rike da ita speaking in a low tone yace “Hey listen to me Halysaah, stop acting like you don’t know where i am headed, this is just between i and you, beside i will even be more active then him ur so called husband, if you don’t co-operate now i promise even without ur co-operation i will get what i want wallahi, balle gwara kiyi co-operating yanxu kawai a wuce wajen, just once, after this I won’t bother you again….” Khaleesat bata san sanda ta kwala kara ba tsabar yanda ta gigice da kalamansa ta gatsa masa cizo da karfi a hannu don har sannan yana rike da ita yana kokarin cire duvet din da taki sakewa, tsabar tashin hankali har wani zufa da zafi take ji duk da Ac dake kunne dakin, lokaci daya ya saketa bayan ta kurma ihun ya mike da sauri ya ciro wata karamar wuka a aljihunsa yana nunata da shi cikin kakkausar murya yace “I will deal with you, kuma na rantse da girman Allah kika ce zaki gaya masa sai na hallaka ki kuma babu abinda zai faru wallahi, kin dai ji na rantse, kuma i will definitely get what I want” Yana fadin haka ya kashe wutan jikin gadon da ya kunna ya nufi kofa da sauri ya fice daga dakin ya kullo kofar in a haste ya sauka downstairs kamar yasan reaction din da zata yi kenan shi yasa sai da yayi wanka ya canza kaya don kar ma dakin ya dau kamshin turarensa sanin how sensitive his step brother can be, Khaleesat kuwa bata fasa ihun da take ba cikin firgici da tashin hankali, bude kofar dakin aka yi lokaci daya aka kunna wutan dakin, ya nufeta da sauri yana kallonta yace “Me ya faru?” Sosai ta fashe da kuka tana sauke numfashi, har lkcin kuma tana rike da duvet din jikinta gam gashi duk ta hada zufa, bai san sanda ya zauna kusa da ita ba yace “Bakya ji na ne? What happened?” Cikin rawan murya tace “I had a dream” Da wani expression yace “Dream? What dream?” Taki cewa komai tana kuka tana sauke ajiyar zuciya, bin dakin ya fara yi da kallo, sai kuma ya kalleta yace “Didn’t you pray before sleeping??” Cikin shesshekan kuka tace “Nayi” Jawo pillow dinta yayi kusa da ita yana kallonta yace “Kwanta….” Ta fashe masa da sabon kuka ta matso kusa da shi kamar zata shige jikinsa muryarta na rawa tace “Ni wallahi bazan iya kwanciya a dakin nan ba” ya dinga kallonta, sai kuma ya cire duvet din jikinta ya mike yace “Come down” Da sauri ta sauka daga kan gadon tana goge hawayen dake sauka idonta, rigar bacci purple ne jikinta ya ɗan wuce gwiwanta, Ajay dai ya kauda kansa daga kallonta yayi shirun kusan minti daya, ita dai tana tsaye kusa da shi tana zare ido, can ya juya ya kalleta yace “Mafarkin me kika yi?” She look so afraid and confused tace “Kamar na manta” Wani kallo ya watsa mata, ta fara wani sabon kukan, yace “Mu je” Da sauri ta nufi kofa yace “Ke, ina hijab din ki?” Ta dawo ta tafi ta dau hijab din sallanta ta saka, kofa ya nufa ta bi bayansa da sauri, ya jira ta fito sannan ya kashe wutan dakin, ko jiransa bata yi ba ta nufi bangarensa shi dai ya bi ta da kallo kafin ya bi bayanta, zaune ya ganta kan kujera a parlor ta hade kanta da gwiwa tana shesshekan kuka, ya karasa har inda take zaune ya zauna, a tsorace ta dago tana komawa baya jin mutum kusa da ita, sai kuma ta fashe da kuka a hankali, yace “Ke, gaya min mafarkin me kika yi?” Cikin rawan murya tana kallonsa tace “Tsoro nake ji” Mikewa yayi yace “Ta shi” ta sauka daga kan kujeran yayi leading dinta har zuwa Bedroom dinsa, tana shiga dakin bata jira yace mata komai ba ta cire hijab dinta ta ajiye kan kujera ta tafi saman gadonsa, dai dai inda yake kwance kafin yaji ihunta ta tafi ta kwanta ta jawo duvet dinsa ta rufa jikinta har kanta da shi, ya ɗan hade rai ya kauda kai, bayan few seconds kawai ya juya ya fita daga dakin ya kullo kofar, Ya tafi kan 3 seater dake parlonsa ya kwanta har sannan fuskarsa a daure, duk da kamshin turarensa da ya cika Khaleesat ta ko ina both kan gadon, pillonsa da bargonsa haka bacci me nauyi ya dauketa.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788*
