Halysaah Page 105 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 105Khaleesat na komawa cikin gidan Hajja ta tarar da Hajja zaune parlor da Jay tana masa magana cikin kwantar da murya, Hajja ta daga kai ta kalleta da mamaki, Jay dai sau daya ya kalleta ya dauke idonsa, Hajja tace “Halan kin yi mantuwa ne Jiddah?” Khaleesat ta kasa kallonta ta gyada mata kai kawai, Hajja tace “To je dakin ki duba….” Hanyar parlon Hajja ta nufa tana tafiya a hankali, tana shiga parlon hawaye ya gangaro fuskarta ta juya tana kallon entrance din parlon kamar tana jiran taga ya shigo, she stood for almost 3 minutes a parlon daga karshe ta goge idonta kawai ta fita ganin ba shigowa zai yi ba, she was so heartbroken and sad, da kyar ta koma main parlor tana kokarin ganin hawaye bai zubo mata ba, Hajja tace “Kin gani?” Ta gyada mata kai ba tare da tace komai ba don tana iya fashewa da kuka, bata ga Jay a parlon ba, a haka tayi ma Hajja sallama da kyar ta fita, Har suka koma masarauta Ajay bai kalli direction dinta ba ita ma haka, sai goge hawayen da yaki tsaya mata take, suna isa bangaren sa taga ya bude daya daga rooms din dake bangaren ya shiga a maimakon part dinsa, ita dai tana tafiya a hankali ta shiga parlonsa ta zauna kan kujera wasu sabbin hawaye na zuba idonta, sai kuma ta kwantar da kanta kan kujeran tana kuka a hankali, Har aka yi Magrib Ajay bai shiga part din nasa ba, at this point, the whole situation is beginning to get him very angry, why is he even to be blamed? Shi adalci aka masa with this marriage? Yarinyar da is nothing but a burden to anybody around her….. Khaleesat na zaune parlor bayan ta idar da sallah kana ganinta kasan tana cikin damuwa sosai, tayi nisa tunanin da take taji an kwankwasa kofar parlon, a hankali ta juya daga inda take zaune tana kallon kofar bata dai amsa ba, bayan few seconds aka bude kofar Yakumbo ta shigo da sallama ta tsaya nan bakin kofar tana gaida Khaleesat cikin ladabi, Khaleesat ta sauke idonta ta gaisheta ita ma cikin sanyin murya, Yakumbo tace “Abinci ne za a shigo da shi ranki shi dade idan babu damuwa” Khaleesat ta gyada mata kai tace “To” Sai a sannan Yakumbo tayi ma ma’aikatan dake bayanta izinin shigowa parlorn with trays of different food a hannunsu, su ma duk suka gaisheta da ladabi sannan suka ajiye duk abincin har da kayan marmari bayan sun fita Yakumbo ta kara kwantar da murya tace “Babu wani damuwa dai ko ranki shi dade?” Khaleesat ta girgiza mata kai tace “Ba komai, Nagode” Yakumbo tace “To maa sha Allah, sannan babu wani abu da zaki bukata da za a kawo maki?” Khaleesat tace “Eh ba komai” Yakumbo tayi mata sallama sannan ta nufi kofa ta fita, tsaye taga Ajay bakin kofar dakin da yake ciki don tun da yaji anyi knocking door din parlonsa ya fito don ganin waye a part din nasa, Yakumbo ta risina kai ta gaishesa ya amsa sannan yace “Idan kin gama ayyukan da kike zaki kwana nan bangaren tare da ita, akwai ɗan aikin da zan yi can anjima da daddare….” Da ladabi Yakumbo tace “To in sha Allah ranka shi dade” Juyawa yayi ya koma cikin dakin ya kulle kofa. Ana idar da sallahn Asuba Ajay ya shirya ya tafi gidan Hajja don tun ma ba ayi sallah ba kiranta ya shigo wayarsa don ta tunatar masa tana jiransa bayan anyi sallah, yana isa gidan bayan yayi parking ya fi minti goma zaune cikin motar daga karshe ya kashe ya sauka ya shiga gidan, direct ya nufi parlon Hajja ya sameta zaune tare da Jay, zaunawa yayi ya gaisheta calmly, Hajja ta amsa tana kallonsa, bayan kusan minti biyu tace “Ban ga ka gaisa da ɗan uwan naka ba Junaid” Ajay yaki ce mata komai kuma bai fasa kallonta ba, Hajja ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Jay dake danna wayarsa kawai, can ta sake kallon Ajay speaking with calmness tace “Junaid, you owe Jawwad an apology even though you are not at fault but for peace to reign you have to do that, don in batun gaskiya za a bi ba a kyauta ma Jawwad ba, things were never supposed to be done this way in an zurfafa tunani, bana son zumuncin ku ya taɓu akan mace, a ajiye duk wani circumstances da yayi leading to all this amma yana da kyau ku fahimci juna da ɗan uwanka, come to think of ur bond together, this is so pathetic….” Ajay dake ta kallonta yace “Apology for what in particular Hajja? Why is he trying to play the victim whereas nima tauye ni aka yi tunda ban bude baki nace ina so ba don ban hango future na tare da yarinyar ba, why is he playing the victim in this situation? Ni nace a aura min yarinyar?” Jay ya ɗaga kai ya kallesa calmly yace “That is a lie, idan da baka so babu ta yanda zaka yi accepting auren, stop fooling your self Man” Ajay ya mike yace “Then you do ur worst Jawwad, you think yanda ka nuna ma Mai martaba ba shi da 100% say akan ka sai yanda Mamin ka tace kana tunanin nima zan nuna masa haka, You think I can also disappoint him and make him look foolish in the eyes of people? Beside stick this to ur brain Jawwad… Abba bai yi shawara da ni kafin ya yanke wannan hukuncin da ya yanke ba tunda yasan ni ya isa da ni dari bisa dari” Mikewa Jay yayi ya nufesa yana kallonsa direct in the eyes carefully yace “Watch ur tongue, do not let me voice out all what is in my mind Junaid, do not push me” Ajay yace “So? Ya wuce kace idan naka Dad din ne bazai yi maka haka ba, ina ce iya abinda zaka fada kenan, wannan kuma ba ni zaka gaya ma ba kaje ka samu Mai martaba and tell him that, go meet him” Hajja ta hade rai ta mike ita ma tace “Bana son sake jin bakin kowa a cikin ku, ba wannan ne dalilin da yasa na hada ku a nan ba, what is all this nonsense???” A hankali Jawwad yace “There is nothing that will be said to me here da zai yi convincing dina or change my perspective of this whole thing Hajja, don haka kar ma ace min komai i am not interested, bana bukatar jin komai” Hajja ta saki baki tana kallonsa, zai fita daga parlon tace “Jawwad” Tsayawa yayi amma bai juyo ba, Ajay ya karasa har inda yake tsaye ya zaga gabansa yana kallonsa yace “Halysaah ko? Take a chill pill, she is urs…. It’s just a matter of time, i am giving you my words” Yana kai wa nan ya fice daga parlon without turning back, Jay ya bi sa da kallo, Hajja was totally speechless a inda take tsaye baki bude, bayan few seconds tace “Allah ya sauwake, Allah ya tsare mu da wannan taɓara sai kace a garin gaɓa gaɓa, shi Jawwad din mahaukaci ne me kuma zai yi da matar da aka aura maka, ko kuma ita Halysaar er gwal ce? meye ma amfanin auro irinta cikin zuri’a tunda ta dalilinta gashi zumunci na neman samun tangarda, sam ni yarinyar ma bata min ba saboda abubuwan nan da ke faruwa babu kan gado, shi Jawwad din bashi da hankali ne? Me kuma zai yi da matar ka?” Jay ya juya ya kalli Hajja. Khaleesat ta fito daga Bedroom wajen karfe goma na safe jin sallaman Yakumbo a parlor, cikin kwantar da murya Yakumbo tace “Ranki shi dade yanxu Yarima ya kirani yace a sanar maki ki shirya za ku yi tafiya yau, ina fatan kin sani” Khaleesat tayi shiru tana kallonta, can tace “To” juyawa tayi ta koma Bedroom din, rabonta da ganinsa tun jiya da suka dawo gidan Hajja da yamma, ta zauna kan kujera tayi tagumi tana kallon babban plasma din dakin, ko baccin kirki bata yi ba daren jiya saboda damuwa gashi har ta fara jin kirjinta na ciwo, tana ta zaune har bayan minti talatin ta ji an bude kofar dakin ta daga kai da sauri, bai ko kalli inda take zaune ba har ya shigo cikin dakin, ta bi sa da kallo har ya dau abubuwan da zai dauka zai fita daga dakin ta hade rai tace “Ina za mu je?” Ba tare da ya kalleta ba yace “Ban sani ba” Daga haka yayi ficewarsa daga dakin, ta taɓe baki ta dauke kanta, bayan fitarsa babu dadewa sai ga Yakumbo ta zo sanar mata ta fito Yarima na jiranta, Khaleesat ta ɗan hade rai tace “To ai ni ban hada kayan ba” Yakumbo ta ɗan yi murmushi tace “To ranki shi dade idan babu damuwa ki bani izinin in hada maki, Sai ki dinga nuna min duk abinda zaki bukata” Khaleesat tace “A’a kar ki damu Mama zan hada yanxu” Daga haka ta juya ta koma dakin, sai da Khaleesat ta ɓata kusan minti talatin kafin ta hada duk abubuwan da tasan zata bukata a akwati, gaba daya jikinta a sanyaye yake duk da tafi zargin Maryland za su koma, But will she cope there without Jay?? tunanin hakan yasa hawaye ya fara sauka idonta, a haka ta fito daga dakin, Yakumbo ta fita da akwatin nata waje Khaleesat na biye da ita kamar warce aka zare ma laka, Mikewa Ajay dake zaune daya daga parlor din part din yana jiransu yayi, yana kallon Yakumbo yace “Ki bar akwatin a nan za a shigo a dauka” Da ladabi tace “To ranka shi dade” Ita dai Khaleesat sau daya ta kallesa ta sunkuyar da kanta, babu yabo babu fallasa yace “Mu je” Bin bayansa tayi fuskarta babu fara’a suka tafi har parlon Mai martaba don yi masa sallama, Mai martaba na kallon Ajay yace “Flight din karfe nawa ne?” Ajay yayi kasa da murya yace “Na dare ne ranka shi dade” Mai martaba yace “Toh Allah ya kai ku lafiya, idan kun koma sai ka fara mata processing visa din UK, kasan akwai occasion da za ku yi attending a can, if there is anything concerning the Visa processing you let me know” Ajay yace “To in sha Allah ranka shi dade” Ita dai Khaleesat kanta na kasa tun da suka shigo parlon, Mai martaba ya sa masu albarka suka bar parlon bayan yayi instructing Ajay yaje su ma Aunty sallama. Bayan sun fito bangaren Sarki Ajay ya nufi part din Aunty duk da bai so ba but he have no choice, ita dai Khaleesat na biye da shi tana jan kafa, Aunty na zaune parlonta tare da Walid sai Maryam warce bazata wuce 25 years ba Ajay ya shigo parlon tare da Khaleesat, duk suka daga kai suna kallonsu, sosai gaban Khaleesat ya fadi bayan sun hada ido da Aunty, ta zauna kasan carpet ta gaidata a hankali sannan ta gaida Walid da Maryam, Walid ne kadai ya amsa gaisuwar nata yana kallonta, Maryam kuwa sai danna wayarta take ta toshe kunnenta da Ear pod, Ajay ya zauna kan kujera ya gaida Aunty without looking at her, a takaice yace “We are leaving for Maryland…” Da mamaki Aunty tace “You are leaving for Maryland?dama ka saba zuwa yi min sallama ne idan zaka tafi ko kuma rashin kunya ka shigo yi min ka nuna min ai an maka aure?” Ajay yace “Mai martaba ne yayi instructing dina mu shigo mu yi maki sallama so i have no option than to obey his instructions….” Maryam ta kalli uwarta tace “Wai Aunty wannan ce Bazawarar matar da ake cewa dama? Na ganta gidan Hajja jiya na zata irin masu zuwa kawo kukan su suna neman taimako ne” Ajay ya daga kai ya kalleta, tana ganin haka ta mike daga inda take zaune tana yamutse fuska sanin sai ya iya wanke ta da mari, Aunty ta daure fuska tace “Ina zaki? Ai ba karya kika yi ba Bazawarar ce er matsiyata, sai ma kin ji history din ubanta…” Ita dai Maryam taki tsayawa a parlon ta nufi kofar wani daki tace “Tabbb wa yaga kwamacala, lallai akwai aiki babba, wai er matsiyata a gidan sarauta, how is that even possible” Daga haka ta shige cikin daki har da sa makulli, Aunty tace “To karen hauka ya sha da zai taɓa ki, meye na shigewa daki kuma, ubanki ne shi da zaki ji tsoronsa?” Walid dai kallon Khaleesat da ta sunkuyar da kanta kawai yake yi kamar ya samu TV, Ajay ya mike yana kallonta a takaice yace “Tashi mu je” Sai a sannan ta daga kanta hawayen da ya fara taruwa idonta ya gangaro ta mike tana kallonsa, bai kara second biyar a parlon ba ya fice Khaleesat na biye da shi, Aunty ta bi su da wani kallo me cike da tsantsan tsana. Hawaye kawai Khaleesat take bayan sun bar masarautan, Ajay dai bai ce mata komai ba a bayan motar cause he was also deep in his thought, bayan tafiyar kusan minti talatin driver din yayi horn bakin gate din wani gida bayan an bude gate din ya shiga yayi parking, Ajay ya bude motar ya sauka, Khaleesat ta bi sa da kallo kafin ita ma ta bude motar ta sauka tana goge idonta, building din gidan taga ya nufa yana making phone call, ta bi bayansa tana tafiya a hankali, suna shiga parlon gidan bayan few minutes sai ga Hajiya Shafa’atu ta sauko downstairs ta karaso cikin parlon da fara’a tana masu sannu da zuwa Khaleesat ta zamo kasa daga kan kujera ta gaisheta cikin sanyin murya, Hajiya Shafa’atu ta ɗagota ta zaunar da ita kan kujera kusa da ita tana amsa gaisuwarta da murmushi tace “Sannu da zuwa amarya” Sai kuma ta kalli Ajay tace “Ni fa duk tunanina za ku yi few weeks kafin ku koma Amurka, ko dai za ku zauna Abuja ne for sometimes before traveling?” Ajay yace “A’a, Flight din na karfe sha dayan dare ne yau in sha Allah” Hajiya Shafa’atu tace “Ikon Allah, yanxu baza ku jira ayi Walimar Jawwad da Hadiyah ba? It’s taking place in few weeks time fa, Ina ga ya kamata ace kuna nan za ayi” Khaleesat dai sai kallon Hajiya Shafa’atu take babu ko kiftawa jin abinda tace, Ajay yace “She is resuming school this Monday, kuma final semester ne” Hajiya Shafa’atu tace “Gaskiya kuma ya kamata ku koma saboda wannan, to Allah Ubangiji ya kai ku lafiya nima nan da few weeks za mu je Canada idan an gama Waliman an kawo amarya, kaga in mun koma ko weekend sai ka dinga kawota tayi tunda daga Maryland zuwa Toronto ba nisa sosai garemu ba, Visa kawai zaka fara nema mata tun yanxu” Ajay yace “Haka ne” Wajen karfe uku suka isa garin Kano, Khaleesat taji ina ma ya kai ta gidansu taga Ummanta ko zata ɗan samu relieve din abubuwan dake damunta suka tunkushe mata a rai, tun da yayi lodging dinta a wani babban hotel sannan aka kawo mata lafiyayyen lunch bata sake ganinsa ba har sai karfe shidda da rabi na yamma da yayi knocking, Bayan ta bude kofar yana kallonta a takaice yace “Where are your Traveling document?” Khaleesat ta jingina da kofa tana kallon different direction kamar bazata ce komai ba sai kuma tace “Gidanmu” Yace “And you were quiet all this while, da hancinki zaki koma US din ashe” Ta wani kallesa tace “To ai ba a tambayeni ba, don har nayi zaton an fara tafiya haka ne babu document” Yace “I will give you a dirty slap, ni kike gaya ma haka?” Tura baki tayi ta juya ta bar wajen ta koma cikin dakin ta zauna gefen gado ta rungume hannunta, kullo kofar dakin taga yayi, ta harari kofar, tana ta baza ido ya dawo yace mata ta fito su tafi can gidan nasu ta dauko document din ko ba komai dai zata ga Umma amma shiru shiru bata ga ya dawo ba, sai karfe takwas saura ya dawo dakin yace “If you feel like leaving sai ki taso ki bar masu dakinsu” Da ido ta bi sa har ya fita sannan ta taɓe baki ta mike ta bi bayansa, yana zaune gaban mota sai drivern da zai kai su airport wanda dama shi yayi driving dinsu daga Bauchi, tana bude back seat ta shiga taga traveling document din nata a kan kujera har da wayarta da Charger da ta bari a gida sanda za a kai ta Bauchi, lkci daya hawaye ya cika idonta ta daga kai tana kallonsa a gaban motar, shi ne bai tafi da ita gidan ba taga Ummanta, a haka suka bar hotel din tana jin hawaye na sauka idonta wani mugun haushinsa ya cika zuciyarta kuma bata fasa masa wani irin kallo ba wanda bai ma san tana yi ba a bayan motar.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah ur evidence via 07087865788*Thanks so much for prayers and patience, I am better now, nagode sosai.
