Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 48 Hausa Novel

Ta zame ta koma ta kwanta; tabbas ba kuskure tayi ba ciki ne da Naja, ko da kuwa bai kai sati shida ba. Kuma tabbas ta san ba ita Mustapha yayi niyyar biyawa Hajji ba, Najan ya so biyawa. Kawai dai cikin ya zo masa ne a matsayin uzuri da kariya. Ya wanke kansa daga zargi. A hankali ta zame ta gyara kwanciyarta ta janyo abun rufa ta rufe jikinta sannan ta rufe idonta kamar mai bacci; haka ta kwana zuciyarta tana kuna.Me Mustapha ya mayar da ita ne; shikenan idan dai abun karuwa ne ba zai iya sakata a ciki ba sai bayan ya saka Naja amma idan dai wahala ce itace a kan gaba? Yanzu yana nufin yace da matarsa zai tafi aikin Hajji; wadda itama cikin ne da ita sannan ita kuma ya barta ta kular masa da yara da gida duk da itama cikin ne da ita. Zata iya wahalar kula da gida amma ba zata iya wahalar ibada ba kenan? Sai yau ta gane girman rainin da Mustapha yayi mata da kuma yanda ya dauketa.Tun ranar da Mustapha ya sanar da ita zai tafi Saudiyya da Naja taso ta je gida wajen Mommy, amma saboda kada abun yayi kama da zata yi reporting dinsa sai ta hakura.Tun dare ta sanar da shi zata je gida kuma ya bata izini, don haka gari yana wayewa da yake ba itace da girki ba ta shirya. Hafsa ta kama hannun Hammad suka sauko, suka fice tsakar gida suna jiranta yayinda ita kuma take rufo part dinta. Ta saba duk lokacin da zata fita idan Naja tana nan sai ta leka ta sanar da ita ta fita, don haka yau din ma tana saukowa ta shige parlor din Naja.Tun kafin ta hango fuskokinsu ta dauki muryar Yaya Jidda, bata yi mamaki ba tunda yanzu sun saba zuwa gidan su wuni a wajen Naja idan bata sauko ba babu mai hawa nemanta kuma ko yara ba za a tura ace ta zo ba. Ta karasa ta zauna a kan hannun kujera ta gaida Yaya Jidda cike da girmamawa sannan suka gaisa da Naja. Har ta mike zata fice Yaya Jidda ce ‘Sai muka ji abun arziki kuma, Mustapha yace da shi da Naja zasu je aikin Hajji.’Ta dan koma ta zauna tana murmushi tace ‘Eh, haka yace.’‘To Allah ya sa suje a sa’a, muma ‘yan baya Allah ya kirawo mu.’‘Amin ya Allah.’ Ta amsa sannan ta mike tayi musu sallama ta fice.Har taje gida abun yana yi mata ciwo a rai; wato harma ya gayawa ‘yan uwansa da Naja zai tafi Hajji kenan an fara zuwar mata murna ta kuma ana yi mata Allah ya kaow na ‘yan baya. Kuma wannan ganin da ta yiwa Naja ya kara tabbatar mata da cewa Najan tana dauke da ciki domin yawu ne a bakinta irin wanda masu ciki suke tarawa.Tun da ta shiga gidan Mommy ta san da matsala, amma dai bata tambayeta ba saboda bata son ganin kukanta. Ta san yanzu da ta tambayeta damuwarta sai tayi kuka mai isarta sannan zata gaya mata damuwar.Sun zaune a parlor din Mommy bayan sun gama cin abincin rana suna hira yayinda Hammad yake ta kaiwa da kawowarsa, Mommy ta dubeta tace ‘Ki bar min Hammad a nan ya kwana biyu ki samu ki dan huta, naga duk kin yi wani zuru-zuru.’Tayi gajeran murmushi tace ‘Gashi nan Mommy an bar miki, idan na shirya sai Ahmad ya mayar da ni gida ya karbo masa kayansa.’Tayi dariya ‘Dama neman kai ake da shi.’Jimawa kadan tace ‘Momy wai Abbansu ne zai tafi Hajji shi da Naja.’Nan da nan fara’arta ta karu, tace ‘Kai ma sha Allahu, Allah ya amsa ibada.’ Ta kalli Khadijan suka hadu kuma kamar wadda aka tunawa wni abu tace ‘Ah, to ke me yasa ba za a hada dake ba ko kuma a fara kaiki, ko kinyi halin naki ne ya bata miki rai kin ce ba kya son kujerar?’Ta sa yatsanta ta goge kwallar da ta fado a kwarmin idonta, ta kawar da kai sannan tace ‘Haka ya zaba ya fara tafiya da ita.’Da mamaki ta zaro ido tana tambaya ‘To ke me kika yi masa, tunda dai ai kece babba ke ya kamata ya fara tafiya dake ko kuma ya tafi daku dukanku a lokaci guda.’‘Yace wai ciki ne da ni don haka ba zai tafi da ni ba sai dai ko wata shekarar zuwa lokacin na haihu.’Ta kalli cikinta sannan ta kalli fuskarta ‘Ciki? To ai karami ne kuma naga har yanzu ana zuwa da masu ciki sai dai idan basu da lafiya. Ni ban ma san kina da cikin ba ai.’‘Nima bai fi last week na gane ba, ban ma sa rai da shi ba kawai na ganshi.’Mommy ta dafa hannunta tace ‘To ai shikenan tunda ya zo sai muce Allah ya raya, amma dai masu ciki suna zuwa aikin Hajji har yanzu. Ana ta dai cewa za a hana amma ba a hana din ba tukunna. Kawai da yace bai so zuwa dake ba.’Ta sake share kwalla tace ‘Tabbas Mommy bai so ba, don itama Najan ai ciki ne da ita. Kawai dai ya zata ban san tana da cikin bane shi yasa yake so ya raina min hankali kamar yanda ya saba.’‘Ikon Allah.’Suka yi shiru na dan lokaci; itama Mommy abun ya daure mata kai. Duk gidajen da ta sani na mata biyu ko sama to idan irin wannan damar ta samu babba ake fara kaiwa. Tabbas abun ya sosa mata rai to amma babu yanda zata yi. Ta dafa hannun Khadeejan wadda itama tayi nisa a nata tunanin tace ‘Kuma baki gaya masa Najan ma ciki ne da ita ba?’‘Ban gaya masa ba Mommy, kuma ba zan gaya masa ba. Yana sane da abinda yake yi Mommy, tsaf ya san tana da ciki. Ita da take tara yawu idan tana laulayi, kuma ko yau ma da na shiga wajenta da yawuna bakinta. Kawai dai da ita yayi niyyar zuwa, ko na gaya masa kuma ba canzawa zai yi ba sai dai kawai yayi ta kawo hujjoji.’‘Uhm, to ai shikenan. Kin ga dama shi Hajji kiran Allah ne, kema in sha Allahu Allah zai kirawoki nan ba da dadewa ba ta hanyar da ya so. Kada ki sa wata damuwa a ranki balle ki illata dan da yake cikinki.’Suka yi sshiru na dan lokaci, jimawa kadan ta gyara zama tace ‘Wallahi ni Mommy na ma gaji da auren nasa gaba daya. Tabbas ko shekara nawa zan yi da Mustapha ba zai taba canzawa ba, ba zai iya yi min adalci ba. Watakila ya daina so na, watakila kuma iya son da yake min kenan. Amma dai gaskiya na gaji Mommy.’Ta dafa hannunta cike da kulawa tace ‘To ai hakuri zaki yi, dama shi aure ya gaji haka kuma ribar aure ta me hakuri ce. Baki sani ba ko ita abokiyar zaman naki wani abun take yi na biye-biyen malamai, ai duka ana yi.’Tayi murmushin yake tace ‘Ai wallahi babu wani biye-biye Mommy, a hayyacinsa yake yi. Kawai dai idan hidima za ayi masa to ya fi so ni ya saka ni aiki, idan kuma morewa zai yi da harkar soyayya to wannan ita ta iya. Amma babu wani asiri haka ya tsarawa kansa.’Ta sake kama hannunta tarike tana kallon fuskarta tace ‘Ki dai yi hakurin, in sha Allahu zaki ga ribarsa. Kuma idan dai Hajji ne da izinin Allah kema zai kirawoki.’‘Uhm.’Nan suka dauki lokaci Mommy tana bata baki. Can zuwa yamma ta shirya Ahmad ya mayar da ita gida ta barwa Mommy Hammad.——–Shirye-shiryen tafiya aikin Hajji sun kankama domin ana maganar saura sati uku alhazai su fara tashi. Duk wani abu da suke bukata na kula da gida Mustapha ya tanada ya kawo musu, kuma yayi mata bayanin abokinsa wanda dama ta san shi; shine zai kawo musu raguna kuma ya tsaya a yanka.Yanzu kullum sai yamma tayi sai ya dauki Najan a mota su fice wai sun tafi bita, haka ta zuba musu ido tana ta bawa kanta hakuri.Gaba daya maganar tafiyar ta fita daga ran Khadeeja, kuma Mustaphan ma gaba daya ya fice mata daga rai; ji take yi kamar matsayinta a wajensa bai wuce na mai aiki ba. Zuwa yanzu ta san wanda ma bai san halin da suke ciki ba ya san Naja tana da ciki domin tara yawunta ya karu kuma tayi fari tas irin na masu ciki. Sai dai har yanzu ita Khadeejan bata sanar da Mustapha cewa ta san Najan tana da ciki ba. Sai shirye-shiryensa yake yi yana zuwa sallama da mutane domin Hajia ta gama gayawa kaf dangi Mustapha zai tafi Hajji da matarsa. Danginsa da na Naja sai zuwa suke sallama, duk wanda ya zo sai ya cewa Khadeeja Alah ya kirawo ‘yan baya. Wannan kalmar ba karamin bata mata rai take yi ba, amma haka ta share ta kawar da kai…

Back to top button