Hausa novels

Halysaah Page 96 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 96…Mami ta kwantar da murya tace “Tun da ka nace kai sai ka auri bazawara, naji zaka aureta Jawwad amma ga sharadi na, duk da a farko nace shawara amma yanxu zan maida shi sharadi a maimakon shawara, yanda tayi aurenta na farko to haka kai ma zaka yi auren ka na fari kafin ka aureta, abun nufi shi ne ko zaka aureta sai bayan akalla wata hudu zuwa biyar da auren ka da Hadiyah, idan yaso sai kaje kayi ta auren nata ni bazan hanaka ba tunda kace kaji ka gani” Jay ya dinga kallon Mami babu ko kiftawa, Mami tace “Ko baka fahimci abinda nake nufi bane?” Shiru yayi bai ce komai ba har sannan yana kallonta, Mami ta gyara zama tace “Ina ga kamar baka fahimci zance na ba, Jawwad cewa nayi in har zaka auri bazawara to sai bayan wata hudu zuwa biyar da auren ka na fari, wato auren ka da Hadiyah, in wata biyar ya cika sai kaje can ka auro bazawarar ka, amma fa bazan taɓa sonta ba bari in gaya maka zance na gaskiya, kuma don bana sonta ba shi ke nufin zan musguna mata ba a matsayin surkata, kawai dai a raina nasan bana son ta kuma bazan taɓa son ta ba, amma tunda kai kana sonta sai ka je ka aureta ka zauna daga kai sai ita cause u will never expect ur family to like her also don Hadiyah ce ta mu, ba lallai ma sai na dinga haduwa da ita ba ko kuma ta zo inda nake duk na yafe wannan, ko ince duk mun yafe wannan a family” Jay ya sauke idonsa cikin sanyin murya yace “But Mami wata biyar sun yi yawa, plss reconsider this Mami, don Allah ki duba, lokacin yayi tsayi….” Da mamaki Mami ke kallonsa, can tace “Ikon Allah, wato wata biyar sun maka yawa? Wannan wani irin tsinannen asiri yarinyar nan da iyayenta suka yi maka ne Jawwad? Shi wata biyar din ne yayi maka yawa saboda a kage kake ka auri guzumar ko?” Jay ya ɗan hade rai yace “Ni babu asirin da aka min, ni na ganta nace ina so ba ita ta gan ni tace tana so ba, beside she is just 20 years, kema kuma nasan zaki so ta idan na aureta kika ga qualities dinta, daga ita har iyayenta babu me matsala ko kananan magana, ita Hadiyar da kike ganin baza a samu matsala ba ina me tabbatar maki da ita za a samu matsalar, kin fi kowa sanin wacece Mahaifiyarta and how she behaves, ki bar ganin tana maki biyayya tana bin ki sau da kafa, ita kanta yarinyar idan na fara lissafo maki flaws dinta you will be greatly shock, yarinyar da take sangartacciya….” A fusace Mami ta dakatar da shi tace “Rufe min baki, saboda buzaye sun baka ka ci ka sha shi ne har kake da bakin kushe Hadiyah da uwarta yau? Ita Kanwar mahaifin taka ce kake kushe akan wata yarinya yau? To ai da ka hada har ni ka kushe akan buzuwa sai in san da gaske kake, wallahi idan baka bi ni a sannu ba Ahmad ko magana ya sake haɗaka da yarinyar nan zan iya yi maka Allah ya isa, akan me za a nemi rabani da kai bayan kai kadai Allah ya bani, meye laifina don nace bazaka auri bazawara daga wata kabilar ba? Yau da ina da wasu ‘ya yan da ba sai dai in kyaleka in zuba maka ido ba kayi duk abinda kaga dama tun da baka jin maganata, in ma baka min biyayya ba ai yan uwanka za su min, to amma kai kadai Allah ya bani shi yasa kake bani wahala yanda ka so” Jay ya sauke kansa bai ce komai ba, he wish zai iya hakura da Halysaah ko don saboda Maminsa, amma xuciyarsa bazata iya daukar rabuwa da ita ba, shi kansa bai san wani irin so ne wannan yake mata ba, bai taɓa zaton har zai so Halysaah ba duba da yanda suka dade a apartment daya tare amma ko sau daya bai taɓa jin komai a ransa game da ita ba, kallon just his sister in Islam yake mata during all that period, bai san me yasa so yayi masa haka farat daya ba, he can’t even tell when he deeply fell in love with her, ya dai san ba a tsohon apartment dinsu bane, Mami dai sai studying dinsa take tana kallonsa, har cikin ranta da gaske ta tsani ganinsa cikin damuwa ko wani iri ne, saboda shi taki aure tun rasuwan Babansa don definitely in tayi aure dole zata bar rikonsa gaba daya ya koma wajen kanin Mahaifinsa ne kuma tana ganin irin rayuwar da Junaid ke yi a gidan a lokacin saboda rashin uwa, so tari ma ita ke jawo Junaid din jiki in kuma ta tuna wasu abubuwa sai ta dake zuciyarta ta kyalesa ya karata can hannun matar ubansa, sannan tana tsoron tayi aure ta tafi gidan mijin tare da Jawwad a dinga yi masa kallon agola bayan da gatansa kaca kaca, duk wannan yasa ta sadaukar da komai nata akan farin cikin tilon ɗan ta, yanda zai rayu gabanta bai yi kewar mahaifinsa ba balle uwarsa sannan ba a hantaresa ko an kyare sa ba, Mami ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya tace “Kamar yanda nace maka Jawwad tun da ka nace sai ka auri yarinyar nan ni bazan hanaka ba, amma sai bayan auren ka da wata biyar, wannan shi ne sharadi na kawai” Girgiza mata kai Jay yayi a hankali yace “Lokacin da kika diba yayi yawa Mami, kiyi hakuri ki rage” Da mamaki Mami ke kallonsa, murya can kasa yace “Ina laifin ki ce sati biyu zuwa uku” Tsabar mamaki Mami ta ma rasa abinda zata ce masa, after some minutes ta mike ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita. Wajen karfe goma Mami ta tafi bangaren Aunty ta sameta zaune da ɗan ta Walid, suna ganinta suka yi shiru kamar ba magana suke kasa kasa ba, Aunty tace “Kin tashi lafiya Fulani?” Mami ta karasa cikin parlon tace “Barkan mu da Safiya” Gaishe da Mami Walid yayi sannan ya mike ya fita daga parlon, Mami ta bi sa da kallo sannan ta zauna tana kallon Aunty tace “Ashe Walid na gari” Aunty tace “Eh jiya ya dawo….” Mami tace “Ikon Allah, daga UK din yake ko dama yana Nigeria tuntuni…” Tuni Aunty ta kawar da zancen ba tare da ta ba Mami amsa ba tace “Yanxu ya ake ciki ne Fulani, kin samu Jawwad din kuwa kin fito masa a mutum dinki? Jibi ne juma’an nan fa, kinsan halin Mai martaba a sanda yaga mun tubure bama son abu to a sannan yake daukar abun nan da muhimmanci” Mami ta sauke wani ajiyar zuciya tace “Ana idar da Sallah daxu na tafi bangaren Jawwad din Fulani, kinsan tun da nayi wannan magana a wajen meeting ban kara saka sa a idona ba sai yau da naje har bangarensa na jira ya dawo daga masallaci, in takaice maki dai daure ni da jijiyoyina kawai Jawwad yayi daxu da asuba, wai ai shi bai san zancen da nayi na cewa bana son auren ba tunda shi ba haka nace masa ba kuma shi yana nan a kan abinda na fada masa da farko, wallahi Fulani kasa aiwatar da abinda ya kai ni dakinsa nayi, bana son duk wani abu da zai damesa ko ya ɗaga masa hankali….” Aunty ta saki baki tana kallonta da mamaki, can ta gyada kai tace “Tabdi, ai kuwa nan gaba sai kin gwammace dama kin bata masa ran kin masa kaca kaca an wuce wajen da dai abinda zaki fuskanta nan gaba, don wallahi wallahi kinji rantsuwar musulmi fulani zai kai ya kawo ke da Jawwad sai gani sai hange daga nesa, ke kinsan su waye buzaye kuwa? Naga kamar kina ɗaukar wannan issue din sakwa sakwa fa, wallahi in zaki cire kulafucin yaron nan a ranki Kiyi abinda ya kamata to ki cire, su fa Buzayen nan ko Nijar din ma an san ba can ne asalinsu ba, nomads ne fa da suka yada zango a Nijar sai kuma suka ki tafiya suka yi kaka gida a can, wallahi in har kika yi kuskuren zuba ma Jawwad ido ya auri yarinyar nan a sunan kina tausayinsa sai kin yi da kin sanin da baki taɓa yin irinsa ba a rayuwarki, zaki san su kika haifa ma ɗa, yanxun ma ai kin fara ganin haka tunda gashi gida me tsada ya cire miliyoyin kudi babu sanin ki ya siya masu, Jawwad ya taɓa yin abu da makudan kudi bai sanar maki ba? Ai tun daga wannan action din nasa ya kamata ki gagara bacci da daddare kuma” Mami ta dafe kai tace “Na rasa ta inda zan billo ma lamarin nan Fulani, yanxu fa saboda gudun bacin ransa har ce masa nayi ya bari ya auri Hadiyah zuwa nan da wata biyar sannan sai ya auri ita buzuwar, wai fa nan duk dubara ce nake masa, nasan yana auren Hadiyah suka tare zai manta da wata bazawara can, kuma tunda sun gama Phd din nasu ko Amurkan ma bazan bari ya koma ba ta yanda bazai ganta ko by mistake ba tunda a Bauchi zai zauna da Hadiyah ai, to amma kinsan me yaron nan yace min? Wallahi ba kunya ya kalli idona yace min shi wata biyar sun masa yawa in rage in mayar sati biyu ko uku, a sannan na kara shan jinin jikina da yaron nan Fulani” Aunty tayi wani dariya tace “Kin ji ko? Ai sun shanyesa sai abinda kika gani, to ki bar sa a lokacin da yace din tunda tsoronsa kike” Mami tace “Ban gane tsoronsa nake ba” Aunty tace “To haka ne mana Fulani, ka haifi yaro amma kana tsoron tunkarar sa da magana, da nayi niyyar kawai in zuba maki ido tunda ke in an kawo maki shawarar da zai amfane ki sai ki yi fatali da shi ki gwale mutum, to bari zan fito maki a mutum yanxu Fulani in dai ba ta karkashin kasa kika bi ma Jawwad ba to kina gaff da shiga uku wallahi, kin ji kina gani mace zata rabaki da tilon ɗan ki, yanxun ma me ya rage? Jawwad da na sani mai kawaici da gudun bacin ranki har ya tsaya yana ja in ja dake yace shi lallai sai yayi abinda bakya so, tun farkon lamarin nan nake nuna maki hanya kina kaucewa, ga abu har yayi nisa yanda bama zato, ta yanda suka bi suka juya hankalinsa mu ma ta nan din dai za mu bi mu dawo da hankalin nasa, ai ba wajen boka nace zan kai ki ba Fulani balle kiyi ta tsoron kauce hanya don nasan abinda kike tsoro kenan, da ilimina nima fa kin sani, to don me zan yi abinda zan kauce hanya, in dai zaki ji ta nawa ki yi shiru ki bar sa a sati ukun da yace idan ya so sai a daura auren nasa da Hadiyah wannan Juma’an tunda haka Mai martaba ya tsara, ana daura auren mu kuma muna abinda ya kamata a gefe, wallahi wallahi sai kinyi mamakin yanda Jawwad zai mance da wata buzuwar bazawara can, wai ke baki yi mamakin yanda Walid ya nutsu ba ya dena abubuwan nan da yake har da su ɗaga kwalba? Bazan boye maki ba taimako ake ta nema masa shi yasa kika ga Walid a haka yanxu, don haka shi ma Jawwad taimakon za mu nema masa don wannan halaka yake son fadawa Fulani” Mami dai tayi shiru ta rasa abinda zata ce, amma da alama maganar Aunty ya fara tasiri a zuciyarta, Aunty tace “Don haka in ma ke kina dar a zuciyarki har yanxu to kawai ki bar min wuka da nama, kawai magana ce ta kudi kuma in sha Allahu sai kin gode min wallahi, sati daya yayi yawa zaki ga aiki da cikawa” Mami ta sauke wani ajiyar zuciya tace “Ni fa na zata maganganun da na gaya ma Mai martaba zai yi zuciya ya aura ma ɗan sa bazawarar sai naga ba haka ba kuma, wallahi da ni muguwa ce tsaf zan san yanda zanyi in juya auren ya koma kan Junaid shi ya auri bazawaran dama ai kince tare kika ganta da Junaid din a Amurka” Aunty ta ɗan bude ido jin abinda Mami tace, da sauri tace “A’a ba sai an kai ga haka ba Fulani, kin ga wannan ai babban magana zai zama a masarautar nan da ma garin Bauchi baki daya, mu dai bakinmu alekum mu yi abinda ya kamata hankalin Jawwad ya dawo jikinsa ya mance da wata bazawara” Mami tace “To shikenan Fulani, Nagode kwarai da gaske” Aunty tace “Haba ai yi ma kai ne, banda ma yan zugi sun shiga tsakaninmu a masarautar nan ai ke din mutuniyata ce a shekarun baya, yanxu dai ki nuna ma Jawwad kin ji kin amince sati ukun da yace sai yaje yayi ma ubansa Mai martaba magana a ɗaga auren” Mami tace “Zan sanar masa in sha Allah, bari in je ko breakfast ban yi ba” Daga haka Mami ta mike ta nufi kofa ta fita, Aunty ta kyabe baki murya can kasa tace “In bari a juya aure kan Junaid? Ashe ina ma son sa da alkhairi in har na bari aka yi haka, ai sai dai in sa a aura masa warce zata zamo ajalinsa in ma na bari yayi auren kenan….” Shiru Mai martaba yayi yana kallon Jawwad bayan ya gama sauraronsa, after a while ya sauke ajiyar zuciya yace “Fulani ce tayi maka wannan tsarin ko?” Jay ya sauke idonsa yayi shiru don bayan sun gama magana da Mami few hours ago sai da ta jaddada masa kar ma yace ma Mai martaba yayi magana da ita, Mai martaba yace “Nasan duk tsarinta ne wannan, so kana nufin yanxu in sake turawa a sanar masu na canza maganar da nayi shekaranjiya kenan?” A hankali Jay yace “Ai ba sai an tura ba ranka shi dade, ta waya ma idan aka sanar masu ina ga ya wadatar” Mai martaba dai yayi shiru yana kallonsa, bayan wasu mintoci yace “Baza a ɗaga daurin auren nan ba Jawwad, ranan Juma’ah kamar yanda na tsara za a daura auren, nothing is going to change that” Jay ya daga kai yana kallonsa a sanyaye bai iya yace komai ba…. Ko da ya koma bangaren Mami ya sanar mata yanda suka yi da Mai martaba kuka ta sakar masa tace “Ni kuma in dai ba nan da sati hudun da muka shirya da kai ba wallahi Ahmad kayi aure ne ba da yawu na ba, ba kuma da amincewata ba, kuma bazan taɓa saka maka albarka a wannan aure ba” Sosai jikin Jay yayi sanyi yace “Don Allah Mami ki yi hakuri, ni nasan yanda zan yi convincing Mai martaba zuwa lokacin da kika ce kina son ayi auren” Cikin kuka Mami tace “Da dai yafi maka, duk da bana son auren nan haka na kai zuciya nesa na amince amma nace ga yanda nake son ayi min a matsayina na mahaifiyarka nan ma sai a tauye ni a nuna ban isa ba?” A hankali Jay yace “Kiyi hakuri, yanda kike so in sha Allah haka za ayi” Ba karamin Courage Jay yayi gathering ba ya sake komawa gun Mai martaba bayan Magrib, ya risina kai cikin ladabi yace “Ka gafarce ni ranka shi dade, i don’t mean to disobey or disagree with you in any way, amma kayi hakuri ranka shi dade ka ɗaga wannan aure zuwa nan da wata daya kafin nan nayi shirye shiryen da zan yi a tsanake” Mai martaba ya ɗan yi murmushi ya jinjina kai bai dai ce masa komai ba, shigowar Aunty Parlon yasa Mai martaba yace “Zaka iya tafiya Ahmad, I’ve heard you” Jawwad ya mike yayi ma Aunty barka da yamma sannan ya fita daga parlon. Wajen karfe tara Ajay ya shiga Bedroom din Jay yana kallonsa yace “Don me zaka samu Mai martaba kace a ɗaga auren?” Jay yace “I have no Choice Ajay, haka Mami tace take so” Ajay yace “Must you listen to everything?” Calmly Jay yace “C’mon Ajay, she is my mother, ta yaya zan yi aure babu blessings dinta? Yanxu ba cewa tayi bata son auren kwata kwata ba kamar yanda tace few days ago, kawai so take sai na fara auren Hadiyah da 4 weeks sannan in auri Halysaah, idan ina son ganin dai dai ai abinda tace take so shi zan yi” Ajay ya girgiza kai yace “Ina me tabbatar maka wannan wani plan ne nasu suka hada ita da Aunty cause ita ke zugata….” Jay yace “What ever, ni dai nasan wata dayan da tace bazai cika ba ta canza min magana, shi yasa ban damu ba” Ajay ya sauke ajiyar zuciya yace “Abba isn’t happy with this, he wasn’t expecting this from you, considering the fact that he supported you from the onset…” Jay yace “I have no choice kamar yanda nace maka Ajay, Mami ce ta sa inyi haka and I did that for peace to reign” Ajay ya ɗan yi murmushi yace “At the end ina ga fa sai dai tayi hakuri ta saka albarkan nan da tace bazata saka ba daga baya cause I am assuring you come Friday sai Abba yayi abinda ya tsara, saboda wani reason mara ma’ana bazai canza maganarsa ba a maida shi karamin mutum, come Friday you will be groom to 2 bride….” Jay na kallonsa da damuwa yace “Haka Abba yace maka?” Ajay ya ɗaga kafada bai ce komai ba ya juya ya fita daga dakin, Jay ya rasa ma me zai yi ko kadan bai son bacin ran Maminsa gashi har da kuka tayi saboda shi, nazarin maganganun da zai sake samun Mai martaba da shi ya fara yi, ya fi minti ashirin pondering on what to say to the king for the third time, daga karshe ya mike ya fita with the hope that wannan karan Sarki zai janye batun auren zuwa nan da wata daya. Karfe goma saura Jay ya tafi bangaren Ajay, a parlor ya samesa yana kallon kwallo, Jay ya sauke ajiyar zuciya ya zauna yana kallonsa yace “Daga wajen Mai martaba nake” Ajay ya ɗan kallesa, sai kuma yace “Ya ku ka yi da shi?” Jay yace “I am just hoping he consider all what I said”*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*07087865788

Back to top button