Hausa novels

Ajiya A Duhu Book 1 Page 12 Complete Novel

🅿️➖1️⃣2️⃣______________Abubuwan da nake saidawa Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumesNumbers 0803446968108135142610Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuriesTikTok username @ummu_mahnoor_luxuriesFacebook ummu_mahnoor_luxuries__________…….Yau kwanakin Maanal biyu a KK HOSPITAL. Zamu iya cewa Alhamdullahi abubuwa sun fara dai-daita, duk da dai har zuwa yau ba’a barin kowa shiga inda take sai doctors kawai. Tun a jiya su Ammie suka iso suma ita da Daddy. Tsabar munafunci na Hajiya Basariyya sai ta ce zata biyosu taga jikin Maanal ɗin. Dan a waccan ranar da Daddy ya dawo tunda ya koma gida ya rufesu da faɗa ita da Hajiya Yaya akan ƙin zuwansu asibiti, sai dai faɗan nasa yafi tsamari akan Hajiya Yaya data zama itace sanadin komai, dan yama sanar mata ya haramtawa Sabuwa zuwa masa gida, idan kuma tai gigin zuwa ALLAH sai ya saka jami’an tsaro sun kamata. Itama kuma ta jira hukuncinsa bayan Maanal ta warke dan yanzu baida lokacinta. Tofa wannan abu da Hajiya Basariyya dake laɓe taji yasa ta dawo ta lallaɓa Daddyn ta bashi haƙuri akan nata laifin daya faɗa naƙin zuwa asibiti kawai, ta kumaji duk halin da ake ciki akan maida Maanal Abuja shine ta maƙale itama zata bisu. Ammie bata san da batun ba sai da suka fito zasu wuce taga Hajiya Basariyyan. Sosai ta sake jinjina makircin matar a ranta, dan ta jima da gane wacece Basariyya, sai dai bata taɓa nuna mata ba ta barta da halinta. A lokacin ma murmushi kawai tai batace komai ba, hakan kuma sai ya ƙonama Hajiya Basariyyan rai, ta rasa wacece Ammie, ta rasa ta inda zata kamo lagon matar, ta rasa ta inda zata shiga jikinta kamar yanda take shiga jikin Hajiya Yaya tasan sirrinta. Amma ba komai, idan tasan wata ai bata san wata ba.     Anan Abujan itama ta kwana dan Daddyn nada gida anan ɗin dan yana harkar sayen gidaje da sayarwa ne. Kasancewar komai akwai a gidan yasa sauka kawai sukai anan ɗin. A yanzu ma haka tana a asibitin tare da su. A ɗakin da aka kwantar da Maanal ɗin ɗakine na musamman kamar palor da bedroom, dan haka duk suna a palor ɗin zaune itama Maanal na daga ciki babu mai shiga sai dai su leƙata ta jikin ƙofar glass ɗin. Shahidah da Amal suka iso ɗauke da abinci, bayan duk sun gaishesu suna ƙoƙarin zama Daddy da RK suka shigo ɗakin sai wani ba’indiyen likita da shine akan case ɗin Manaal ɗin ma. Gaishe da Daddy su Shahidah sukayi, sannan suka gaisa da su RK da suma suke gaida su Ammie. Su RK na ƙoƙarin barin wajen kamar daga sama sai Hajiya Basariyya cewa tai, “Nikam likitan nan kamar na sanka”. Yanda tai maganar idonta akan RK ya sakashi fahimtar da shi take, kallonta ya ɗan yi sai kuma ya rissinar da kansa tunda bai san matsayinta ba a garesu ya ce, “Mommy zata iya yiwuwa. Sai dai ban san a ina kika sanni ba”.    Batare data damu da kallon harara da Daddy ke mata ba ta ce, “A zaria gidan Alhaji Saminu Ashafa”.     Cikin jinjina kai RK ya bata amsa da, “Ni ƙanin amaryarsa ne Majdiya”.    Kafin Hajiya Basariyya ta samu yin magana Ammie da Daddy suka dubeshi. Abinda ya faru a ranar da sukaje ɗaurin aure gidan Alhaji Saminun ya shiga dawo mata a rai. In dai batai kuskuren fahimta ba shine yaron da Hajiya Majdiya ke mata bayanin yana son Maanal kenan. Wani irin sanyi taji a ranta, dan koba komai ita dai yaron ya shiga ranta a lokaci guda, sannan ta samu karɓuwar addu’ar ta akan al’amarin Maanal ɗin da Yazeed tunda ga raba gardama yazo.. Shikam Daddy murmushi yayi cike da nuna mamaki ya ce, “Ikon ALLAH ashe ma kai ɗin na gida ne doctor. Ai nasan Hajiya Majdiya kuwa sosai saboda Alhaji Saminu aminine kuma ɗan uwana ta fanin mahaifiya, zan iya cemaka ma neman auren Majdiya da komai dani akayisa”.      Wani ɗan karen daɗi ne ya ratsa RK har cikin maƙwallaton zuciya. Sai yake jin gaba ɗaya matsakarsa ma shi ta ƙare kenan. Nan take ya ƙara sakewa da Daddy. A karo na farko Daddy ya shiga ɗakin da Maanal ke kwance shi da Ammie da Nene kawai. Sosai tausayin Maanal ya ƙara mamayesu, dan Ammie kasa daurewa tayi sai da tai kuka. Duk wanda yaga Maanal ɗin sai yayi matuƙar tausaya mata. Numfashi ma sai da taimakon na’urori take yinsa. Duk ta sake figewa. Sun mata addu’a suka fito aka bar Nene kawai dan doctor ya buƙaci a ɗan goge mata jiki a canja mata kayan jikinta. Da ance Ammie tayi amma ta nuna bazata iya ba. Sai dai Nene tayi. Tsaf Nene ta gogema Manaal jiki aka canja mata kaya. Doctor da RK suka shigo, hakan yasa Nene fita ta basu waje dan suyi aikinsu. Ta tarar da Hajiya Basariyya cike fam da takaici, wai tana fushine ita ba’ace ta shiga ta duba Maanal ba, shine taima Daddy ƙorafi akan hakan.  Shi kuma yaƙi tanka mata shine ta cika tai fam. Ita dai Ammie haƙuri ta bata, yayinda su Amal ke mamakin abinda Hajiya Basariyyan tayi. Ita kanta Nene abin ya bata mamaki, dan bataga abin wani ƙorafi ba a wajen tunda gasu Shahidah suma ba’a barsu sun ganta ba. Ita kanta dan Ammie tace bazata iya gogema Maanal ɗin jiki bane aka barta ta shigan. A haka Yazeed da yaje Kaduna ya dawo ya samesu, tare da duk yaran gidan yake tafe, amma abin mamaki yau ɗin ma Hajiya Yaya bata zo ba….      Da mamaki Amrah ke kallon RK, har dai ta kasa haƙuri sai da tayi magana. Murmushi yay mata da tambayarta ya gajiyar biki. Hakan data faru tsakanin Amrah da RK sai ya tsayama Yazeed a zuciya har sai da ya kira Amrah ɗin gefe ya binciketa. Kanta tsaye ta sanar masa abinda ta sani. Yayi mamaki ƙwarai da gaske. Haba no wonder yake mamakin yanda RK ɗin ke tsaye very serious akan case ɗin Manaal ɗin. Ya jima yana son haɗa al’amarin a ransa amma ya gaza samun makama, tunda shi dai sun fitone kawai suka samu motar RK ɗin a ƙofar gida, daga wannan taimakon kuma na kawosu asibiti baiyi tunanin cigaba da ganinsa ba amma sai yaga ya tsaya tsayin daka komai anayi da shi, yayi tunanin kawai tausayi da taimakone sai da aka dawo Abujar nan ya ɗan fara zargi a ransa sai kuma dai yay saurin kaudawa tunda bashi da tabbas musamman ganin RK ɗin matsayin likita shima. Ashe kuwa hakanne.        A ranar su Amrah suka koma Kaduna harda Hajiya Basariyya data wuce bisa tirsasawar Daddy dan kuwa badan taso ba, taso ace sai taga kwal uwar daka. Ta zata da Daddyn zasu tafi sai yace mata shi yana nan har sai yaga yanda hali yayi akan jikin Maanal ɗin. Hakan ya masifar ƙona mata rai, dan ta kalla abunne a sigar rainin hankali irin na maza kawai. A ganinta Daddyn nason holewa da Ammie ne a wannan ƙayataccen gida shine ya fake da ciwon agola. Ita Ammie tsaf ta fahimci manufar Hajiya Basariyya ɗin, amma sai ta basar kawai tama dinga ƙarfafa Daddy ɗin akan yaje suma suna da hakki a kansa, tunda dai Maanal ɗin tana samun dukkan kulawa anan ɗin gasu kuma ga Yazeed shi yaje ya huta gashi ya dawo daga tafiya. Sam Daddy ƙin saurararta yayi, daga ƙarshe ma ya fara fushi da ita dole tai shiru ta zuba masa ido kawai su Hajiya Basariyyan suka wuce…      A ɓangaren Yazeed kuwa ya fara janye jikinsa daga RK. Tun RK ɗin bai fara fahimta ba har ya fahimta. Dan sai wani isa ma Yazeed ke nuna masa akan Maanal ɗin yanzu da gadara. Mamaki hakan ya bama RK, dan shi a zatonsa Yazeed da Maanal uwa ɗaya uba suke ko uba ɗaya dan yana ɗan tantamar Ammie ta isa haihuwar kamar Yazeed ɗin. Bai daiyi magana ba yabar abin a ransa dan ganin iya gudun ruwan Yazeed ɗin. Ana cikin wannan dambarwa a tsakaninsu Hajiya Majdiya yayarsa tazo duba Maanal ita da yaranta tun daga Zaria. Dan shine ya kirata yake sanar mata, aiko baiwar ALLAH sai gata tazo. Ammie tayi mamakin hakan kasancewar batai waya da Hajiya Majdiya ɗin ba akan hakan. Sai Hajiya Majdiyan ke sanar mata, “Sirikinki ne ya kirani yake sanar min ai.”    Murmushi Ammie tai da faɗin, “Haba nayi mamaki fa, sai kuma hankalina bai kawo nan ɗin ba. Ai babu abinda zamuce da Rafeeq sai fatan alkairi. ALLAH yay masa albarka”.        “Amin ya rabbi. Yaya jikin nata yanzu? Dan naga hankalinsa a tashe yake matuƙa yau har cewa yay na nema masa masu saukar Alkur’ani yana son ai mata”.    Ajiyar zuciya Ammie ta sauke. Zuciyarta na sake jin nutsuwa da RK ɗin. “ALLAH sarki, ALLAH ya saka masa da alkairi. To Alhamdullahi zamu ce. Sai dai har yanzu bata san wanda ke kanta ba. Amma dai suna tabbatar mana bugun zuciyarta na dai-daita zuwa yanzu. Kowane lokaci kuma zata iya farfaɗowa cikin hayyacinta.”       “ALLAH ya bata lafiya, yasa ya zama kaffara. Abin tausayi yarinya ƙarama haka da wannan irin babban ciwo mai haɗarin gaske, ALLAH ka bamu ikon cinye jarabawoyinmu. Shiyyasa gata nan sanyi-sanyi ko kuzarin kirki bata da shi. Ban taɓa sanin tana da wannan lalurarba ai da tuni na haɗaku da Rafeeq ɗin dan aikinsa ne. Yanzu haka reshen wannan asibitin suka buɗe acan garin jos shine yaje can da kansa yake riƙe da asibitin kusan shekara ɗaya kenan, anan ne ma ALLAH ya haɗasa da ita”.        Murmushi Ammie tayi tare da jera addu’a ma RK ɗin. Ganin yanda Ammie ta ɗauki zancen da muhimmanci Hajiya Majdiya ta cigaba dama ɗan uwanta campaign wajen Ammie. Yinin gaba ɗaya suna a tare sai bayan Magrib RK ya ɗaukesu ya maida can gidan babbar yayarsu dake nan Abujan zasu kwana anan dan sai gobe idan ALLAH ya kaimu zasu koma Zaria. Sosai Ammie taji daɗin kasancewa da Hajiya Majdiya a wannan rana. Dan zaman ya sake tasirantar da abinda take ji a zuciyarta game da RK da Maanal idan har ALLAH ya tashi kafaɗunta. Bata ɓoyema Nene da su Shahidah ba akan alaƙar Dr Rafeeq ɗin da Maanal. Suma sai abin yay musu daɗi matuƙa, dan suna ganin idan har ALLAH ya baiwa Maanal lafiya wannan itace hanya mafi sauƙi da maganar Yazeed zata janye cikin sauƙi batare da sun ɓata ran Daddy ba kamar yanda duk suke gudu. Dan gwara dai a haƙura da batun Yazeed ɗin nan haka nan tunda dama ita wadda ake dan ita bawai tana sonsa bane. Abu na biyu sudai a haka yanayin Dr RK ya musu hundred percent, dan mutum ne mai sauƙin kai ga girmama na gaba da shi, ga yanda yake ɗawainiya dasu a asibitin nan cike da mutuntawa ma abin a soshi ne. Shi kansa Daddyn sun fahimci RK ɗin ya shiga ransa. Sai dai babbar matsalar sun san ga Yazeed za’a sameta kam. Dan kowa yasan Yazeed na matuƙar son Maanal wannan a bayyane yake. Sannan shi kansa mutumin kirki ne, dan yana da nagartattun halaye masu yawan gaske daya gada ga Daddy, tako ina Yazeed ya cancanci zama mijin Maanal kodan halaccinsa garesu, dan hatta Daddy ya sansu ne a dalilin Yazeed. Sannan kodan Daddy a bama Yazeed auren Maanal, mahaifiyarsa ce kawai matsalar gaskiya, dan Hajiya Yaya sam ba kanwar lasa bace. Bata da kirki ko misƙala zarratin, kanta kawai ta sani, kuma tabbas zata iya aikata komai akan wannan auren kamar yanda take shan faɗa idan har akayisa. ALLAH dai ya bama Maanal ɗin lafiya, zasu cigaba da tayata addu’ar zaɓin alkairi dan duk MAZAJE biyun nan sun matuƙar cancanta da aurenta…      ★ A mota Hajiya Majdiya ke bama RK labarin hirarrakinsu da Ammie, babu abinda yake sai murmushi da ƙara jin ƙaunar ƴar uwar tasa. Sai da ta gama bashi labari tsaf sannan ya jeho mata tambayar abinda ke cimasa zuciya..    “Humm Aunty Alhamdullah na samu karɓuwa wajen Ammie da ƴan uwan Maanal, sai dai ba duka ba”.    “Kamar ya ba duka ba miye matsalar to?”.        “Yazeed Aunty, Yazeed shine matsalar kuma na fahimci yana da ƙarfin faɗa aji akan ƴan uwan nasa. Da farko dai ni da shi normal gaskiya. Amma kwana biyun nan ban san miyyasa ba ko ya fahimci alaƙata da Maanal ɗin sai naga yana jajja baya dani, sannan yana min gadara da al’amarin Maanal ɗin. Dan ma baida yanda zaiyi ne kasancewata ɗaya daga cikin likitocinta shiyyasa. Har abin ya fara bani mamaki dan kamar wani mai kishi da ni. Sai dai nasan ba hakan bane tunda mizai sakashi yin kishi akan wadda suke Uba ɗaya ne ko uwa ɗaya ma ban sani ba”. Ya ƙare maganar cikin damuwa sosai.        Fuskar Hajiya Majdiya cike da damuwa itama ta furta, “To kodai Yazeed ma son Maanal yake?”.    “What?!!!”..  RK ya faɗa a ɗan razane yana taka birki da sauri………✍️🤣Sai ka ɓarar daku malam Rafeequ

Ajiya A Duhu Complete Novel Document Txt

Back to top button