Uncategorized

Ta tabbata an canza Nafisa Abdullahi da Fati Washa a cikin shirin Labarina shiga kaga cikakken bayani

 LABARINA.


MARUBUCI:  Nasir S. Gwangwazo.

Gwangwazo kat! Ne a duniyar rubutu. Tababas! Mun ga aikin ƙwaƙwalwa wajen jan zaren labarin ta hanyar ɓadda bami. Wato duk lokacin da lissafin ya yi Gabas, sai mu tsinci amsa ta bayyana a Yamma.

UMARNI: Shirin ya samu sanya hannun fasihin mai ba da umarni a duniyar finafinan Hausa. Malam Aminu Saira, gwani ne na yankan shakku.

KAMFANI: Saira Movies.

TAURARI:

  • Sarkin Waka
  • Lukman
  • Rukayya
  • Ummi
  • Umma
  • Baba Dan’audu
  • Al-Amin Buhari
  • Iya
  • Atete
  • Kabir
  • Umar
  • Jagwado
  • Eze.
  • Baba Rabiu

1. An sanya kalaman barkwanci da suka sanya masu kallo darawa, musamman kalaman Eze da Jagwado. Haka nan arangamar Baba Ɗan’audu da Baba Rabiu a gidan yari.

Also Read: Shin ko kunsan dalilin yin kidnapping din Sumayya a cikin shirin Labarina kuwa?

2. An sanya gurbi na tinatarwa dangane da muhimmancin imani da damƙa lamura ga mahalicci. Tatatunawar Ummi da Lukman ta zo da salo mai burgewa.

Lukman: Ina jin kamar Sumayya ba za ta dawo ba.

Ummi: Me yasa kace haka?

Lukman: Idan ana faɗa mini kalaman nan, sai na ga masu faɗi kamar suna nuna mini cewa Sumayya ba za ta dawo ba ne.

Ummi: Idan ba tinatar da kai Allah yanzu ba, sai yaushe? Ba ka zo duniya domin Sumayya ba, ba kuma za ka mutu dominta ba. Babu mamaki Allah ya mayar maka da wadda ta fi Sumayya.

Lukman: Toh! Tunda Allah aka ce, ba zan yi musu ba.

Ummi ta mike za ta fi ta.

 Lukman: Ina kuma zaki?

Ummi: Ba zan iya zama ina sauraren wadannan kalaman naka ba, zaka iya irga kwanakin da na yi a gidan nan?

Lukman: A’a

Ummi: Na dawo gidan nan ne saboda ina so ka, ka sani Allah ba zai taba baka abin da ba naka ba. Ya kamata ka sanya wannan a ranka.

3. Zuwan Baba Dan’audu da haɗuwarsa da Baba Rabiu a gidan Yari, wata ilhama marubucin ya yi mana na warwarewar ƙullin da muka daɗe muna dako.

ƘORAFI: Mintoci bakwai cif ake kwashewa a farkon shirin ana yin talla, musamman ma e-nairan nan da kuma tallan jihar Kano. Ya kamata a duba mana, hakan akwai yawan tallace-tallace da suke ɗaukar lokaci, da har sai nasu kallo sun ƙosa.

Kalli cikakken shirin 

Akwai sauran kallo a labarin nan!

MAI SHARHI

     Mubarak Abubakar Saulawa

                      

Back to top button