Uncategorized

Kungiyoyi shida da Chelsea ta zirawa kwallaye 7 ko sama da haka a gasar Premier ta ƙasar Ingila.

 

Kungiyoyi shida da Chelsea ta zirawa kwallaye 7 ko sama da haka a gasar Premier ta ƙasar Ingila.

 Norwich City ita ce ta zama kungiya ta shida da Chelsea ta zura wa akalla kwallaye 7 a ragar ta wasan da suka yi ranar asabar a gasar Premier kashi na tara.

 Ga kungiyoyi shida da Chelsea ta zirawa kwallaye 7 ko sama da haka a gasar Premier.

 1. Sunderland


 Chelsea 7-2 Sunderland (Janairu 2010)

 Sunderland ta zama kungiya ta farko da Chelsea ta ci kwallaye 7 a ragar ta, a gasar Firimiya yayin da blues ta lallasa su da ci 7-2 a gasar cin kofin gasar 2009/2010 karkashin Koci Carlo Ancelotti.

 Nicolas Anelka (wanda shi ya fara zira ƙwallo) daga nan sai Frank Lampard inda  sun ci ƙwallaye biyu a wasan.  Florent Malouda, Ashley Cole da Michael Ballack sune sauran ‘yan wasan da suka zura kwallaye a raga.  Anelka, Cole da Ballack suma sun samu taimako guda daya a wasan.

2. Aston Villa Chelsea 7-1 Aston Villa (Maris 2010)

 Frank Lampard ya zira kwallaye 4 a raga a wasa guda na Premier League yayin da Aston Villa ta zama kulob na farko danm ta fara nutsewa zuwa relegation a yayin da Chelsea a shekarar ta lashe gasar EPL.

Florent Malouda ya ci kwallayen biyu shima yayin da Salomon Kalou ya ci wa blues ɗin kwallo ɗaya. Inda Yuri Zhrikov ya bayar da taimako Kwallaye 3 a wasan yayin da Lampard da Malouda suma suka ci daya.

 3. Stoke City

 Chelsea 7-0 Stoke (Afrilu 2010)

 Bayan Villa, kulob na gaba a cikin jerin wadanda Chelsea ta murƙushe a wancan lokacin mai ban mamaki na shekarar 2009/2010 su ne Stoke City.

Frank Lampard ne ya fara zura kwallon sa mai ban sha’awa yayi da yaci kwallaye biyu a wasan inda shima Salomon Kalou ya ci ƙwallo.  Didier Drogba, wanda shine jagoran tawagar ta Chelsea shima ya zura kwallaye wanda hakan shi ya baiwa Chelsea daman casa Stock City da ci 7-0.

4. Wigan


 Chelsea 8-0 Wigan (Mayu 2010)

 A dai cikin shekarar ne Chelsea ta ƙara casa Wigan 8-0 a ranar ƙarshe na kakar 2009/2010 PL in da ta dauke gasar ga gagarumin rinjaye.

 Daga karshe Didier Drogba ya shigo yayin da ya ci kwallo a wasan. Tabbas, a wannan lokaci tsohon dan wasan Chelsea Frank Lampard yana kan ganiyarsa. Bafaranshe ya kwace wa kansa ƙwallo daga bugun fanareti. Nicolas Anelka, Salomon Kalou da Ashley Cole sune sauran ‘yan wasan da Chelsea da suka zura kwallaye a ragar Wigan.

 Frank Lampard ya taimaka anci kwallaye 3 a wasan yayin da Joe Cole ya bayar da 2. Chelsea ta kammala kakar wasa cikin nasara inda ta zura kwallaye 103 a cikin kakar PL guda daya.

 5. Aston Villa Chelsea 8-0 Aston Villa (Disamba 2012)

 Aston Villa, a karo na biyu kasa da shekaru uku, Chelsea ta ci su a gasar EPL a kakar 2012/2013. A wannan karon, Chelsea yi  nasara mafi kyau ta hanyar zurawa  Villa ruwan kwallaye 8-0 tare da Rafa Benitez a matsayin manajan blues a wancan lokacin.

Ramires shine kadai dan wasan da ya zira kwallaye fiye da guda daya yayin da yan wasan Chelsea su 6 daban daban suka zura kwallo daidai. Fernando Torres, David Luiz, Branislav Ivanovic, Oscar, Eden Hazard da Frank Lampard da aka fi dogara da shi a wannan lokacin.

 Kyaftin din Chelsea na yanzu, César Azpilicueta ya ba da taimako a bugun farko da Torres ya ci kuma ya kasance shi kadai ne dan wasan da ya buga wannan wasan har yanzu a Chelsea.

 6. Norwich City

 Chelsea ta ci Norwich 7-0 (October2021)

 Wataƙila Frank Lampard ya kafa ɗabi’ar cin ƙwallo a cikin manyan nasarorinsa lokacin da yana murza tamola a Chelsea.

 Mason Mount ne ya zira kwallaye uku rigis (wanda Turawa ke kira da hartrik), daga nan sai dan wasan tsakiya daga baya wato Ben Chilwell, Reece James, Callum Hudson-Odoi yayin da Max Aarons ya kammala inda ya ci gida. 

 Mateo Kovacic ya ba da kwallaye 2 a wasan. Haƙiƙa wasan ya faranta wa duk wani masoyin kwallon kafa ta Chelsea rai, wanda a halin yanzu ita take jan ragamar teburin Firimiya inda ta baiwa Abokiyar hamayarta Livepool Point 1 kacal.

Idan har wannan labari ya burgeka daure ka yi mana sharin

Back to top button