Uncategorized

An Kama Wasu Mata A Bisa Zargin Wulakanta Alqur’ani Da Jinin Biƙi Tare Da Taka Wani Ɓangare Nasa.

 

A Garin Zamfara: An kama wasu mata a bisa zargin jika Alqur’ani da jinin biki, sannan suka jefar da shi a cikin masai. Rahoton DailyTrust. Masu rahotonni su ka ce babbar shedar su ita ce ganin daya daga cikin littafan mai tsarki jike da jini a yayin da ake gudanar da shari’a a gaban kotu. Da kuma sirinjin jinin biki har guda saba’in da bakwai (77) da aka dauka bayan gama haifuwa, sai kuma wata karamar takarda mai dauke da sunan wata daga cikin wadan da ake zargi. Da kuma wasu kayan mallaman tsibbu da wani boka mai suna Tukur ya basu. Lauyan hukuma ya bayyana cewa suna sihirin ne domin neman kudi. Alkali ya dage zaman Shari’ar zuwa ranar uku 3 ga watan maris.

         KARANTA WASU LABARAN

 Kotu ta yanke wa wani dan kano hukuncin Kisa saboda cin mutuncin Annabi da yayi

  AlhamduLillahi Anyi sulhu tsakanin Naziru Sarkin Waƙa da Abubakar Maishadda

  Amfanin Dabino Ajikin Ɗan Adam

 Hanyoyin sace zuciyar budurwa cikin sauƙi

A Garin Kano: Yan sanda sun kama wani matashin mai gadi a bisa zargin yaga Alqur’ani da kuma take wani bangare nashi. Wani matashin mai gadi wanda har yanzu ba a bayyana  sunansa ba yana hannun hukumar yan sanda akan zargin da ake masa na yaga Alkur’ani tare da take wani sashe nashi. Jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin kuɓutar da shi daga hannun jama’ar yankin na Kuntau dake birnin Kano da suka yi kokarin ƙona shi da ransa. Sai dai hukumar Hisba sun yi ƙoƙarin kwantar wa jama’ar yankin hankali da cewa su bari doka ta yi aikinta.

Back to top button