Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 41 Complete Novel

…*ASM Bk2041*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

 

 

……..Sai dae ko kafin ya kai har ta kulle kopar, knocking ya fara yi yana kiran sunanta shiru har bayan wani lokaci tak’i ta bud’e hakan yasa ya koma cikin parlon ya zauna had’i da had’e hannuwan shi ya d’aura beard d’in shi, shi dama initially hakanan zuwa binciken lafiyar bai kwanta mashi ba kawai don ta matsa ne yasanta sarai da k’wallafa rai akan abu in bai goya mata baya ba haka za tay ta damuwa yanzu kuma ga wata damuwar data fi wancan, tunanin yadda akai tana da wannan problem d’in amman ko ita bata gane ba a matsayin ta na likita ya shiga yi daga baya kuma ya tuna in Allah yaso ya 6oye Al’amari dama ba lalle a gane ba yana ta zaune can ya mik’e ya koma kan 3 seater ya d’auki wayar shi ya fara kokarin kiran Hajiya tana fara ringing ta d’auka suka gaisa ta tambayi ya Fanan jin ya d’an yi shiru dama ta ji yanayin voice d’in shi kaman yana cikin damuwa, tambayar shi tayi lafiya taji kaman yana cikin damuwa saida ya d’an nisa sannan cikin natsuwa ya fara mata bayanin komae to itama dae Hajiyar ta girgiza da jin bayanin matsalar tabbas itama haka tay ta fama da lalurar yawan 6ari wani lokacin sai cikin yayi kaman zai tsaya sai kuma ya zube ko kuma bayan ta haife ya koma saidae kuma tayi mamakin jin Fanan nada irin matsalar ba tare da an ta6a fuskantar wata babbar alama ba, cikin tashin hankali ta tambaye shi tana ina yace mata tayi locking kanta acikin d’akin tace bari ta kira wayar ta ya sanar da ita wayan na nan parlor, cike da damuwa tace dole ta shiga mawuyacin hali ba kamar yadda take da son ta haihu, ce mashi tay ya samu ya lalla6a ta ta bud’e kar wani abun ya sameta ba kamar da yake rarraunar zuciya gareta ya rarrasheta sosae itama zata kira suyi Magana ya amsa mata da Ok, mik’ewa yay walking slowly ya sake komawa bakin kopar yana knocking had’i da kiran sunanta shiru bata bud’e ba hakan yasa shi fara tunanin kar wani abu ya sameta nan take ya yanke zuwa yasa azo a 6alle kopan yana shirin juyawa yaji tana bud’e wa da sauri ya dakata ya kai idon shi jikin kopar yasa hannu ya tura, a tsaye ya ganta har saida gabanshi ya fad’i ganin yadda cikin kankanin lokaci duk ta yamutse ga hancinta duk alamun jini da alama nose bleeding tay dama yasan tana hakan tun tana k’arama in ranta ya 6aci ko ta buge sai tayi ha6o, hannunta ya kama suka koma cikin d’akin ya zaunar da ita gefen gado shima ya zauna idon shi a Kanta sai faman ajiyar zuciya take saukewa still yana ruk’e da hannunta guda slowly ya furta “Fanan” kaman bazata amsa ba sai kuma a hankali tace “Na’am” cigaba yay “Why all dis? Do you want to harm your self?” Shiru tay bata ce komae ba ya cigaba “I know how u’r feeling but kiyi hakuri muyi Addu’a Allah ya yaye matsalan yakamata ba damuwa ba tunda is curable kowane lokaci zaki iya samun lafiya” a hankali ta d’ago da rinannun idanunta ta kalle shi cikin disasshiyar murya tace “Babe ina tsoron ace bazan haihu ba bansan ya zaman mu zai kasance ba” ta k’arasa kwalla na zubo mata ya kai hannu ya jawo ta jikin shi yay mata side hug ya d’aura ha6ar shi a saman gashin ta gently yace “In sha Allah zaki haihu and nothing will change tsakanin mu ko kin haihu ko baki haihu ba ina son wife ena itama tana sona hakan ya wadatar dani” lumshe ido tay koba komae taji dad’in Maganar shi kuma tasan har cikin ranshi gaskiya ya fad’a mata shiru tay tana cigaba da shak’ar daddadan k’amshin da jikinshi ke fitarwa tana jin wata irin natsuwa na shigar ta, Allah ne shaida tana matuk’ar son Haisam tana jin tamkar da son shi aka halicce ta tabbas tasan rasashi babbar barazana ce ga rayuwarta tana wannan tunanin wata zuciyar ta ayyana mata wani abu da yasa gabanta fad’uwa ba shiri ta d’ago da kanta ta kalle shi shima ita yake kallo ganin kaman tana son yin Magana yasa ya tambayeta akwae wani abu ta d’aga mashi kai alamar eh yace ta fad’a mashi miye d’an jimm tay kafin tace “pls Ya Haisam I want a Favour from you” jinjina mata kai yay alamar to k’ara yin shiru tay tama rasa ta ina zata fara ya lura da ta kasa fad’i mashi Alfarmar da take son yay matan ya kai hannuwan shi ya kama duka hannuwanta yace kar ta ji komai ta fad’a mashi zai yi iyakar kokarin shi yay mata abunda take so in dai zai sakata farin ciki kuma ta daina damuwa haka, jin wannan batun nashi yasa ta samu k’warin gwuiwa ta fara magana cikin d’an rawar murya tace “I…. i want u to promise me dat you’ll not marry another wife” bin ta kawai yay da ido bai ta6a zaton abunda zata fad’i ba kenan don bai ga dalilin da zata fad’i hakan ba, kaman ta san tunanin da yake ta had’iya abu kafin tace “ina nufin koda ban haihu ba don Allah ya Haisam kai man Alk’awarin bazaka k’ara aure ba tunda akwae hanyoyin da zamu iya samun yara zamu iya adopting ma in muna so” still kallon ta kawai yake hakanan ya kasa ce mata komai ganin kallon da yake Matan yasa taci gaba “isn’t dat am trying to be selfish kawai ban son rasa ka ne babe in ya kasance ban haihu ba ka auro wata ta zo ta haihu zata rink’a man gori tana kirana juya k’arshe ma ta raba ni da kai hakan ya sha faruwa wllh and I can’t survive without u” ta k’arasa kwalla na shararo mata taci gaba da tabbatar mashi da hakan zai faru in dae ya k’ara aure rayuwarta na cikin had’ari ya taimaketa su ci gaba da zaman su tare, gaba d’aya ya rasa mi zai ce mata bawai bazai iya yi mata alk’awarin bane amman yasan ta dama can tana da kishi ko ba don wannan matsalar ba tana yawan rok’on shi kan kada yay mata kishiya don bazata iya sharing nashi da wata ba da dai sauran maganganu, ganin yak’i yace komae yasa ta k’ara sautin kukan ta tana fad’in ya taimaketa yay mata alk’awari hakan ne kawae zai sa ta samu natsuwa a cikin zuciyarta da yanzu take mata rad’ad’i sauke ajiyar zuciya yay ya d’an yi jimm kafin calmly yace mata shikenan yayi mata alk’awarin hakan tun kan ya rufe baki ta fad’a jikin shi ta wani k’ank’ame shi tanata mashi godiya had’i da d’agowa tana yi mashi kiss a dukkan side d’in fuskar shi d’an murmushi kawai yay can yace ta tashi tay wanka zata fi jin dad’in jikinta tace to suyi tare mana yace mata zai d’an yi wani abu yanzu taje tayi yana zuwa ya fara kokarin mik’ewa yana ruk’e da hannunta ya d’agata saida ya kaita har cikin toilet d’in sannan ya fito, Bedroom d’in shi ya nufa yana shiga bayan ya rufe kopar ya nufi bakin gadon shi ya zauna, had’e dukkan hannuwan shi yay ya d’aura ha6arshi hakanan yake jin kaman bai yi daidai ba da yace yayi mata alk’awarin to amman yasan in har ba yayi mata yadda take son ba bazata ta6a natsuwa tabar damuwa ba ya d’an d’auki lokaci a haka yanata sak’e sak’e kafin can ya mik’e da k’yar don duk jin jikin shi yake ba dad’i ya nufi toilet, sosae taji dad’in jikinta da ta fito daga wankan duk da da sauran damuwa da kuma fargaba a cikin ranta na ko zata warke ta haihu ko bazata warke ba press ta nufa ta ciro wata yar riga iya gwuiwa tasa ta nufi gaban dressing mirror iya turare da roll on kawae ta sa ko mai bata shafa ba ta nufi Parlor don ta d’aukko wayarta, bayan ta dawo a bakin gadon ta zauna ta kira Momynta gaisawa suka fara yi tace ya taji muryarta ta canza bata lafiya ne aikuwa kaman tana jira ta saka mata kuka nan fa Hajiya Maryam ta rud’e ta hau tambayarta abunda ya faru cikin kuka ta shiga fad’i mata komae sosae itama ta girgiza ta hau yin salati harda ce mata ta tabbatar an yi aune aunen daidai kuwa tace mata eh kwararran likita ne suka gani sosae ta shiga damuwa amman Saboda kada ta k’ara tada ma Fanan d’in hankali sai ta hau rarrashinta tana nuna mata kada ta damu in sha Allahu zata samu lafiya tunda ana warkewa tambayar ta tay mi Haisam d’in yace da yaji zancen matsalar tace hakuri yake ta bata yana rarrashinta sam bai damu ba yama yi mata Alk’awarin koda bata haihu ba bazai k’ara aure ba zasu cigaba da zama a haka sosae Hajiya Maryam taji dad’i tace mata in sha Allahu ma zata haihu bama d’a guda ba yanzun dae ta tabbatar ta kwantar da hankalinta tunda Haisam d’in ma bai damu ba dama shine abun ji daga baya ta tambaye ta ta fad’a ma Daddy d’in su ne tace a’a Hajiya maryam d’in tace to ta bari yanzu zata kira ta sanar mashi tasan zai kirata tace to ta tambayeta su Farha da sauran yan’uwanta daga baya sukae sallama tana niyyar aje wayar kan gadon sai ga kiran Hajiya ya shigo bayan tay picking suka gaisa ta hau jajanta lamarin kafin ta shiga kwantar mata da hankali sosae tana mata nasiha daga baya sukai sallama ta aje wayar ta kwanta tana facing ceiling ba tunanin kowa take ba face Haisam ita tasan ta gama yin dacen miji ba k’aramar baiwa Allah yay mata da samun shi ba slowly ta lumshe ido wani irin son shi na ratsa zuciyarta tana haka wayarta ta sake yin ringing ta kai hannu ta d’aukko sunan Dad d’in ta ne ya bayyana kan screen d’in da sauri ta yunk’ura ta tashi zaune, bayan tay picking ta gaishe dashi shima dai rarrashin ta ya shiga yi yana kwantar mata da hankali yace kada ta damu za’ai iya bakin k’ok’ari ay treating problem din yana nan zuwa ma sosae taji dad’i harda su murmushi bayan sun gama wayar ne ta tuna da basu ci lunch ba gashi har yamma tayi sosae da sauri ta mik’e ta fita daga d’akin ta nufi Bedroom d’in Haisam tana shiga ta iske shi saman gado a kwance jikin shi sanye da jallabiya don yana fitowa ita kawae ya zura ya kwanta da alama dae wani abun na damun shi ko kuwa alk’awarin da ya daukan ne Allah masani, tana isa bakin gadon ta zauna ta kwantar da kanta a saman chest d’in shi can ta d’ago suka had’a ido ganin yanayin shi yasa da sauri ta tambaye shi mike damun shi ne slowly yace mata ba komae ya gaji ne tace tasan harda yunwa yay hak’uri bata bashi Abinci ba har yamma yayi sosai ya taso suje table ta mik’e tana kokarin d’aga shi ta hanyar kama hannun shi, baida yadda zai yi dole ya tashin ya zuro da k’afafun shi amman yafi buk’atar kwanciyar ya ji shi shiru, a daren ranar sosae Fanan ta faranta mashi duk da damuwar da take ciki da alama tukuicin Alk’awari ne aka bashi, Allah dai yasa a wanye lpy.

 

 

A daidai kopar gidansu Keke Napep d’in ta tsaya Fatuu ta fito jikinta sanye da fararen Uniform d’inta ta biya shi kud’in shi ya ja ya tafi tana juyawa zata nufi gida taje da d’an k’arfi ance mata “wait!” da sauri ta juyo idanunta suka sauka akan wanda yay Maganar Matashi ne kaman tsaran Kawu Amadu ko ya d’an girme mashi yana sanye da manyan kayan shadda blue harda hula tsaye tay tana kallon shi ya nufo ta a gabanta ya tsaya yana mata murmushi ita kuma ta k’ura mashi ido gani take tasan mai fuskar amman tana kokonton in shine d’in don ya canza mata sosae ganin irin kallon da take mashi ne yasa shi cewa “halan baki gane ni ba, ko sai nace Aljana sannan” waro ido Fatuu tay baki bud’e da tsananin mamaki tace “GAYE!” d’an d’aure fuska yay yana mata wani kallo yace “Point of correction, ba wannan sunan yanzu Ashiru zaki ce ko kice Malam Ashiru” k’ara bud’a baki Fatuu tay tasa hannu ta rufe baki mamaki ya gama kasheta abunda bata ta6a zaton gani ba ne take gani a gabanta shi kuwa sai faman murmushi yake don ya fahimci Al’ajabi ya hanata magana can yace tunda bazata tay mashi Magana ba bari ya tafi da sauri tace “to ai ni Gaye wllh mamaki yama hana ni yin magana wai don Allah da gaske kaine?” Yar harara ya wurga mata yace “ba nace maki ba wannan sunan ba yanzu ko so kike ki zubda ma Malam Mutunci ne” Fatuu kau mi zatay in ba Dariya harda tafa hannu ta ruk’e ha6a bin ta da kallo yay daga sama har k’asa yace “Oh su Aljana an girma nayi k’ok’ari ma dana gane ki koda yake d’azun da safe naga Amadu na tambaye shike ke yace man kina makaranta shiyasa yanzu ina ganin ki na gane kece a ina kike karatu ne?” ta fad’i mashi still da mamaki akan fuskar tata don gaba d’aya ya canza Maganar ma cikin natsuwa yake yin ta irin ta masu hankali, tambayar shi tay wai ina ya tafi ne ta daina ganinshi yace mata yana Jos,

 

“Kaci gaba da karatu ne?” ta tambaya yace “Eh mana, ke da ban cigaba ba Kya ganni haka na gama Nce” bud’a ido Fatuu tay tace “inyee yayi kyau gay….au Malam Ashiru, mi ka karanta ne?”

 

“Islamic studies kinsan d’an Malam ne ni nayi gado” Fatuu na murmushi tace da kyau ta taya shi murna Allah yasa Alkhairi ya amsa mata da Amin tace “ina Abokan ka su goga” wani kallo yay mata irin baiso tambayarba tay yar dariya tace don Allah suna ina yace duk sun yi laifi suna gidan yari Fatuu ta zaro ido tace “kace saida dai suka je gidan yarin saura kai kenan” cike da zolaya tay Maganar aikuwa ya galla mata harara yace “amman gaskiya ke mak’iyata ce yanzu Malam d’in kike ma fatan zuwa gidan yari Saboda rashin Mutunci” sosae Fatuu ke dariya tana fad’in ashe har yanzu bai daina tsoron zuwa gidan yari ba yakamata ya d’an je ko don yaci gabza shima dariyar yake yace wannan ai tata ce ita yakamata ta ci ta koda sau d’aya ne,

 

“Sai Mutumin ki yay aure” tambayar shi tay wa yace “Yaya Haisam na gidan Hajiya mana ai nayi zaton ke zai aura” yanayin murmushin fuskarta ne ya d’an canza tace waya fad’a mashi son ta yake da zai aureta yace “kawae yanayin yadda naga yana kula ki ya damu dake acan baya yasa nay tunanin ko yana ciki ne” d’an ta6e baki tay bata ce komai ba yace “da kin aure shi da kin more miji wllh ni tunda nike a rayuwa ta ko a labari ban taba jin mutum mai kirki irin nashi ba don kirkin nashi har ya yi yawa kinsan fa shine ya d’auki nauyin karatun da nayi bayan daya sa aka yafe mana laifin nan…..” Nan ya kwashe komai tun daga ranar da suka je da mahaifin shi yin godiya ya fad’a mata yace yanzu ma da ya dawo nan aikin teaching za’a samar mashi har ma yasa ya kai ma Hajiyar Sanata takardun shi gyad’a kai Fatuu tay tace mashi ai yasan mijin wata bai auren matar wani kowa da wanda Allah ya kaddaro zai aura yace tabbas hakane tace shi yaushe zai auren ne yana dariya yace “ai bani da budurwa saidae ko in ke zaki taimaka ki aure ni” wata muguwar harara ta watsa mashi kafin tay dariya tace ai ni nafi k’arfin ka gaye ko da can ma saidai ka zama driver na sosae yake dariya yana fad’in yanzun Malam d’in ne zai zama drivern ta, ganin kaman ta gaji yace ta shiga gida ya tsayar da ita kuma yasan ta kwaso gajiya da yunwa ta tambaye shi sai yaushe yace ai ya dawo kenan don haka zai zo su sha hira tace to sai yazo yace ta gaida mashi gwaggo daga haka suka rabu,tana shiga gidan bayan ta shiga toilet ta fito ta nufi d’akin gwaggo tana zaune bata dad’e da gama cin Abinci ba don ko plate d’in bata kaiga d’aukewa ba, zama Fatuu tay akan kujera ta gaishe da ita tana murmushi ta amsa tay mata an dawo tace eh nan ta hau bata labarin Gaye cike da mamaki gwaggon tace ai ba abu mamaki ba ne Allah yana shiryar da bawan shi a lokacin da yaso duk mun munin abunda yake aikatawa da Allah yasa yana da rabon shiryuwa sai kaga ya bari shiyasa ba’a so aita hantarar mutum ana aibata shi in yana aikata ba daidai ba an fi so aja shi a jiki da fad’a da nasiha in da rabo sai kaga ya bari ya dawo kan daidai daga k’arshe ta hau yabon Haisam da Hajiya had’i da yi masu Addu’oi Fatun na amsawa tace taje ta zubo Abinci ta amsa da to saida ta d’auki plate d’in da gwaggo tay amfani ta fita.

 

Haisam ya fasa zuwa sakamakon d’aga bikin da zai zo da akai aka maida shi sai cikin farkon sabuwar shekara wato bayan Christmas da new year kamar yadda ya sanar da Fatuu da suna waya tace mashi Allah ya kaimu lokacin, a cikin lokacin su Fatuu sukai jarabawar kammala aji d’aya suka shiga aji biyu. Hajiya zaune a Parlor ta tasa Saude dake zaune akan Carpet gaba tun bayan data sanar mata cewa Officer ya mata Maganar yana son aurenta ta sunnar da kai ba tare da ta ce komae ba,

 

“Saude kin k’i cewa komae ko bakya son shi ne?” a hankali ta d’ago da alamun damuwa akan fuskar ta tace “Hajiya ba wai ban son shi bane ni gaskiya nafi son in ci gaba da aiki na” d’an murmushi Hajiya tay tace “amman Saudatu ai yin auren yafi ko kyata zama ne gashi da sauran yarintar ki ba wani tsufa kikai ba ki dai duba kema in kika yi ai Kya fi samun natsuwa” d’an mommotsa baki ta shiga yi tana kikkafta idanu Hajiya tace indai bata son shi ne karta ji komai ta fad’a mata ita tasan yadda zatai in kuma har tana son shi to tafi son ta amince mashi suyi Auren kawae sai gani Hajiya tay ta fashe mata da kuka da mamaki take kallonta tace to miye na kuka kuma ba tace in bata son shi ba ta fad’i sai ta kama kuka kaman wata k’aramar yarinya girgiza kai ta fara yi cikin kukan take fad’in “Hajiya ba wai auren shi ke banson yi ba nasan aure rufin asirin mace ne ni kawae har ga Allah ban son rabuwa da ke ne shiyasa tun farko da yay man Maganar tun ba yanzu ba na nuna mashi yay hakuri kawae tunda nasan k’arshen ta garinsu zai kai ni ya had’a ni da d’ayar matar shi” yar dariyar jin dad’i Hajiya tay tace “nima ba don dole ba Saude ai bazan so rabuwa dake ba to amman hakan bazai sa in so kaina ba in hana ki yin abunda yakamata ba kuma shi Officern ma yace ke a nan zai sama maki gida ya ajiye ki wannan sai ya daina damun ki” cikin muryar kuka tace “to aikin fa zan ci gaba ko?” dariyar dai Hajiya ke yi ta lura dae da gaske bata son barin gidan can taji tace “to ko ku zauna anan?” Ba shiri da sauri Saude ta kalleta don bata tsammaci jin hakan ba Hajiya taci gaba “in dai kuna so tunda ga d’akuna nan biyu a kusa da na Tukur sai kuyi amfani da su kawae” Saude tace “to Hajiya ba matsala kuwa?” tana dariya tace “Wace matsala kuma ba wata matsala in dae wurin yayi maku ai sai kuyi zaman ku kici gaba da zama da Hajiya kafin mai rabawa kuma ta raba” shiru Sauden tay don Maganar Hajiyar ta k’arshe ta kashe mata jiki kuma dai abune da ya zama dole ko ba dad’e ko ba jima saidae fatan dacewar Ubangiji, ganin tayi shiru yasa Hajiyar cewa shikenan ko tace mashi ya tura Daura Sauden ta jinjina mata kai had’i da sadda shi k’asa alamar kunya Hajiya nata dariya tana fad’in to miye abun jin kunya…..

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button