Education

An Bude Shafin Karbar Bashin Dalibai A Yau Kowane Dalibi Zai Iya Shiga Domin Cin Bashin

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani kan sabuwar dokar bai wa dalibai rance a Najeriya.

A karshe kudirin bai wa daliban Najeriya na manyan makarantu rancen kudi na 2024 domin yin karatu ya zama doka, bayan da a ranar Laraba shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya rattaba masa hannu.

A watan Yunin 2023 ne dai shugaban ya fara rattabawa kudirin hannu to amma sakamakon wasu kurakurai da aka gano, ya sa ba a iya fara aiwatar da tsarin ba, inda shugaban ya sake mayarwa majalisa domin yin kwaskwarima.

Abubuwa 10 game da sabuwar dokar rance

  • Za a kafa asusu na musamman wanda zai kula da bayar da rancen ga daliban da suka cancanta
  • Dalibai za su iya karbar rancen domin biyan duk wasu nau’in kudaden makaranta ko kuma kudaden kula da kai a yayin karatun nasu a manyan makarantun da suka hada da na koyon sana’o’im sabanin abin da yake a dokar 2023 da aka yi wa kwaskwarima.
  • Sabuwar dokar ba ta kayyade yawan samun daliban ko iyalansu ba kamar yadda tsohuwar dokar ta 2023 ta tanada ba wadda ta nuna cewa bashin ga ‘ya’yan talakawa ne kawai.
  • Sabanin a tsohuwar doka, babu bukatar samar da wasu mutane da za su tsayawa dalibi kafin ya cancanci karbar rancen. A dokar 2023 dai sai dalibi ya gabatar da mutum biyu da suka hada da ma’aikacin gwamnatin tarayya mai mataki na 12 ko sama da kuma lauya wanda ya kwashe shekaru 10 yana aiki.
  • Yanzu asusun bayar da rancen ne gindaya ka’idoji dangane da dalibin da ya cancanci ya ci gajiyar tsarin.
  • Babu abin da ya hada bashin da ake bin iyalan dalibi da wanda asusu zai ba shi domin karatu, sabanin abin da tsohuwar dokar 2023 ta ce idan ana bin iyalan dalibi ba shi to ba zai ci gajiyar wannan ba.
  • Asusu ba zai fara batun dalibi ya biya bashin da aka ba shi har sai bayan shekaru biyu da kammala yi wa kasa hidima.
  • Wanda ya ci gajiyar yana da damar gamsar da asusun cewa ba shi da kudin biyan bashin kasancewar bai fara aiki ba kuma babu abin da yake shiga aljihunsa. Za a yi hakan ne ta hanyar nuna shedar rantsuwar kotu.
  • Dokar ta tanadi tuhumar cin amanar kasa tare da hukuncin daurin shekaru uku a gidan maza ga duk wanda ya yaudari asusun ta hanyar bayar da bayanan bogi.
  • Harwayau, sabuwar dokar ta tanadi yiwuwar yafe bashin ga wadanda suka rasu kafin su biya ko kuma suka samu jarrabawar talaucin da ba zai yiwu su iya biya ba.

‘Akwai sauran runa a kaba’

Masana a fannin ilimi da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum dai sun fara tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan sabuwar doka ta bai wa daliban manyan makarantu rance kudin domin gudanar da karatu ta 2024.

Wannan abu ne mai kyau kuma abin a yaba wa shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa la’akari da yadda ya saka hannu a kan dokar farko amma sakamakon rashin amincewa daga ‘yan kasa y asake mayar da ita majalisa domin yin kwaskwarima. Kuma ka ga yanzu ya sake saka mata hannu.” In ji wani masani da ba ya son a ambaci sunansa.

Ya kara da cewa ” shugaban ya fahimci irin illar da ke tattare da dumbin matasan Najeriya da suka kammala sakandare amma sun kasa ci gaba saboda talauci.”

To sai dai masanin ya bayyana fargaba guda daya da ya ce ita ce za ta iya lalata tsarin idan dai har ba a sa idanu sosai ba.

“Ka ga matsalar alfarma da kuma bayar da na goro kafin a yi maka abu a Najeriya ita ce za ta iya tarwatsa tsarin nan musamman idan gwamnati ba ta irin mutanen da suka kamata ba a jagorancin shi asusun bayar da rancen ba. Ka ga kenan akwai sauran runa a kaba”

 

Domin Cin Bashin Kaitsaye Sai Ku Danna Link Din Da Ke Kasa 👇👇👇

 

Back to top button