Wani duba na MSN Money da ke kula da hada-hadar kudi da hannayen jari da ƙasidar da lamuni a duniya ya bayyana gine-gine mafi tsada a duniya.
misalin ya fito da gini 30 mafi tsada a duniya, kuma Saudiyya ce kan gaba inda take da gini biyu a Makkah mafi darajar kudi a duniya.
Emmanuel MSN Money da aka keta a 2019 ya nuna cewa, Masallacin Ka’abah na Makkah, wato Masjid al-Haram shi ne gini mafi tsada a faɗin duniya kuma da tazara sosai.
Faɗaɗa masallacin a shekarun ya canza wa ginin masallacin daraja fiye da duk wani gini a duniya, inda MSN Money ya ce darajarsa ta kai dala 100, .
Ginin Abraj Al-Bait a Makkah mai famanshe da otel da ɗakuna na ƙasaita da kantuna shi ne na biyu mafi tsada a duniya inda darajarsa ta kai dala 16.
Babban wurin shaƙatawa a Singapore da ake kira Maina Bay Sands Resorts ne na uku da darajarsa ta kai sama da da dala shida.
Ginin Burj Khalifa, na Dubai a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ne na 30 a jerin gine-gine mafi tsada a duniya, duk da cewa shi ne gini mafi tsawo a duniya.
Gini 10 mafi tsada a duniya
Masallacin Ka’aba, Makkah: Dala biliyan 100
Wuri mafi tsarki a matsayin Islama kuma masallaci mafi girma a duniya Masallacin Ka’abah a Makkah Saudiyya wanda ke matsayin mutum sama da sojojin lokacin aikin Hajji an tsareyasta cewa darajarsa ta kai dala nauyin 100.
Tazarar darajar ciwondin ginin na Mallacin Ka’aba ana ganin da wuya a samu wani ginin da zai kere shi, duk da abubuwa na kayan duniya da kuma cigaba musamman kaɗarori na gine-gine.
Ginin Abraj Al Bait, Makkah: Dala biliyan 16
Dogon ginin Makkah Abraj Al Bait da ke kusa da Masallacin Ka’aba wanda aka gina a 2012 an bayyana cewa darajarsa ta kai dala biliyan 16.
Abraj Al Bait an gina shi kan dala biliyan 15 domin saukar da mahajjata musamman shugabanni da masu hannu da shuni. Baya ga girmansa, ginin shi ke da fuskar agogo mafi girma a duniya.
Ginin Abraj Al Bait shi ne na biyu mafi darajar kuɗi a duniya bayan Masallacin Ka’aba a Makkah.
Wurin shaƙatawa Marina Bay Sands, Singapore: Dala biliyan 6.2
Babban wurin shaƙatawa Marina Bay Sands na Singapore mai ƙunshe da otel da ɗakunan ƙasaita shi ne na uku mafi tsada a duniya wanda darajarsa ta kai dala biliyan 6.2.
Marina Bay Sands wanda aka kammala a 2010 an gina shi ne kan kuɗi biliyan 5.5, kuma yanzu darajarsa ta ƙaru.
Hedikwatar kamfanin Apple, Cupertino: Dala biliyan biyar
Ginin Apple Park, hedikwatar kamfanin Apple da ke Cupertino a California ƙasar Amurka shi ne na huɗu mafi tsada a duniya.
Apple, kamfanin mafi tsada a duniya an bayyana yana da rarar kuɗi fiye da dukiyar da ƙasashe masu tasowa suka mallaka.
Ba abin mamaki ba ne idan kamfanin ya kashe dala biliyan biyar domin gina katafariyar hedikwatarsa.
Ginin Cosmopolitan, Las Vegas: Dala biliyan 4.4
Ginin otel din Cosmopolitan mai yawan ɗaki 3,027 ya laƙume dala biliyan $3.9 wajen gina shi a 2009.
Ginin otel ɗin da ke da babban wurin caca da kuma ɗakin taro mai yawan kujera 3,200 shi ne gini na biyar mafi tsada a duniya.
Sabon ginin cibiyar hada-hadar kasuwanci ta duniya, New York: Dala biliyan 4.1
Sabon dogon ginin cibiyar hada-hadar kasuwanci ta duniya da ke New York mai tsawon ƙafa 1,776 shi ne na shida mafi tsada a duniya, a cewar MSN Money.
Ginin da ake kira One World Trade Center an kammala shi ne a 2012 kan kuɗi dala biliyan 3.8 (£2.7bn), amma darajarsa yanzu ta haura dala biliyan huɗu.
Ginin shi ne mafi girma yanzu a Amurka.
Ginin majalisar Bucharest: Dala biliyan 3.9
Ginin wanda aka fara a 1984 darajarsa yanzu ta kai jimillar kuɗi dala biliyan 3.9. Ginin yana ƙasar Romaniya.
Ginin Otel na Emirates Palace, Abu Dhabi: Dala biliyan 3.8
Ginin na Otel mai kama da fadar sarki a Dubai yana ɗauke da masauki 397 da manyan wuraren shaƙatawa da kantina da wuraren cin abinci na ƙasaita.
Darajar ginin da aka kammala a 2005 an bayyana ta kai dala biliyan 3, yanzu kuma darajarsa ta haura haka.
Wurin shaƙatawa na Wynn Resort, Las Vegas: Dala biliyan 3.4
Yana ɗaya daga cikin kyawawan otel na duniya da ke rukunin manyan gidajen caca na casino a Las Vegas.
A 2005 aka ƙaddamar da wurin shakatawar na Wynn. Kuɗin aikin ginin wannan katafaren gininmai yawan ɗaki 2,716 ya kai dala biliyan 2.7, yanzu darajarsa ta kai fiye da dala biliyan 3.4.
Fadar Sarkin Brunei Istana Nurul Iman: Dala biliyan 3.3
An gina ta a 1984 kan kuɗi dala biliyan 1.4, Fadar Sarkin Brunei ita ce fada mafi girma a duniya kuma har yanzu ginin na nan a matsayin gidan sarauta.
Ginin ne fadar gwamnatin Brunei da ke da yawan ɗakuna 1,788 da kuma katafaren ɗakin taro da ke ɗaukar mutane 5,000.
Sultan na Brunei, Hassanal Bolkiah na cikin manyan attajiran duniya.