Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 59 Hausa Novel

A gaban gidan ta tsaya ta ƙura mishi idanu kaman yanzu ne komai ke faruwa da ita, tana tuna baƙar wuyar da ta ci daki-daki cikin wannan gida, hawaye ne suka cika mata idanu shaidan na raya mata ta juya ta koma kawai don basu chanchacanci duk wata alfarma daga gareta ba, da kyar ta hadiye wani abu da ya tsaya mata a wuya tana tuna ni’imomin Allah a gareta sai ta furta Alhamdulillah don ko daga fasalin gidan zaka san cewa rayuwa ya ƙara taɓarɓare musu wane wane don daga inda take tana kallon har kofofin dakunan gidan saboda rushewar ginin ƙasan dake zagaye da gidan, yunkura wa tayi zata shiga sai ta ga Fitowar wani dattijo a yanayin shiga da fuskarshi ya nuna kamilalle ne wanda kai tsaye bata kawo ko kusa Kawu Labaran bane sai da suka haɗa idanu, Chakk ya tsaya yana ƙare mata kallo kaman yadda ita ma take ƙare mishi kallo.Sanye yake da jallabiya baƙa har da hula taɓani ka ji hadisi da chasbi riƙe a hannunshi sai wani littafi da ya nuna mata na addini ne, ya rame kam gabaɗaya ya lalace, shi karan kanshi bai gane ta ba sai da yaga kallon da take mishi da hawayen dake zuba mata don kaman an yi mata wankin inji ne, kaman bata taɓa sanin menene wahala ba a rayuwarta, muryarta na rawa tace “Ka..kawu”Tana tuna ranar da ta zo da Saleem yayi mata kora irin ta miyagun aljannu da kayan tsubbu da komai.”Af…Afee..fah??? Ke ce Afeefah? Da gaske ke c..e?”Cikin wani irin karyayyen murya yake maganan, ta ɗaga kai sai gani tayi ya iso gabanta ya zube gwiwowinshi ƙasa da sauri itama ta durkusa yadda yayi suka saki kuka a tare, nata dai bata san me take ji ba don abubuwa ne suka haɗe mata shaidan na tuno mata duk wani minti da tayi a gidan cikin azabtarwa yana tuna mata irin muggan kalaman kawu a kanta da rayuwarta yana nuna mata basu chanchanci komai na alkhairi daga gareta ba ta wani ɓangaren tana jin babu daaɗin yadda ta zo ta ga inda suke rayuwa da kuma lalacewar da kawun yayi kaman kuɗin guzuri.Shi kuwa nadama ce, nadama da kunyar kasa riƙe amana da zumuncin ɗan uwanshi yake yi wa kuka, kunya mai tsanani da ba zai iya cewa ya taɓa jin irin shi ba yake ji na ɗiyar cikinshi.”Afeefah idan na ce ki yafe min na so kaina dayawa, na san na yi miki abubuwa masu yawa na zalunce ki, na ci amanar zumunci, na cutar da rayuwarki fiye da ƙima, na wargaza natsuwarki har ya kai na kore ki da kaina daga kusa na bisa tarin jahilci da baƙar zuciyata… Ina kallo matana kowacce take abinda ta so da rayuwarki ana gara ki kaman kwallo, na dauke ki da kaina na jefawa hukuma ke don kawai ina ganin kin zame min Ƙashin kifi, an zo neman aurenki har nan na lalata komai saboda kawai wani zargi wanda babu wanda ya tabbatar, saboda son zuciya irin tamu… A ƙarshe na aurar dake ba tare da na ko yi binciken wanene za ki aura ba, mecece sana’ar shi, su waye danginshi don kawai sun cika ni da kuɗi sun kuma nemi auren kawai suke so, tun bayan aurenki da kaddara ta faɗa min bisa neman zuwa wurin ki da nayi na ci arziki na faɗa hannun ‘yan shan jini a ranar na san cewa ke ba Mayya ba ce yadda muke faɗa, a ranar na tabbatar harkar shan jini da maita ya fi karfin kwakwalwarki nadama mai yawa ya rufe ni a kullum Adu’a ta shi ne yadda zan ganki kafin ƙasa ya rufe min idanu Afeefah….”Sossai yake kuka ta mayar da kanta ƙasa tana cigaba da hawaye, hatta Aisha da Abeeha hawaye suke shi kuwa Rayyan kanshi ya kawar yana jin zuciyarshi na jagulewa.”Ashe za ki zo inda muke Afeefah? Ashe za ki neme mu?”Zuwa lokacin makota duk ana maƙale ana kallon me ke wakana Larai da Asabe da ma wasu yaransu dake gida duk sun fito sai dai ita bata kai hankalinta kansu ba yayinda duk suke kuka.Hannun kawu ta riƙe tana jin yadda zuciyarta ke kakkaryewa tace “Dole na nemeku kawu dole duk inda zan shiga ku ne nawa, ko me za ku yi min ku ne dole na duk duniya ba ni da waenda suka fi ku. Tsoro nake ji… Tsoro nake ji kar ku ƙi karɓa ta..””Ko a ya kika zo Afeefah wallahi ba zan ki karbarki ba a yanzu, na tuba na yi nadama mai tarin yawa, na roki Allah a salloli dayawa akan ya waiwayo mana dake ya sa ki tuna da mu. Don Allah, Don darajar Allah ki dubi girman shi ki yafe min Afeefah ki yafe min don Allah”Kai take gyaɗa wa ta kai hannu ta share mishi fuska “Na yafe maka kawu wlh duk na yafe muku Allah ya yafe mana gabaɗaya”Inna Asabe ta rarrafo “Afeefah don Allah ki yafe mana don Allah”Ta kallesu sai ta ga inna Larai na ja da duwawu kafa ɗaya kam babu gabaɗaya kuma ba sanda bare wheelchair zubewa tayi tana neman yafiyarta duk ta yafe musu, Rayyan da ya gaji da kukan ya taho ya ɗaga ta tsaye yana kallon cikin idanunta ya fidda hanky fari tas mai cike da kamshi ya fara ɗauke mata hawayen fuskarshi babu ɗigon walwala.”Am sorry”Ta faɗa a hankali.Iso aka yi musu sai dai duk gidan an rasa ma taburma mai haske da za’a iya shimfida musu su zauna, Rayyan take kallo ta juya ta kalli kawu ta sake kallon Rayyan.”Ko za ka tafi mota ka zauna Ya Saraki?”Ya harareta ya samu wani dutse ya zauna a kai ta mayar da kanta ƙasa ko wannan kaɗai ya isa ta yafe musu, wa zai ce Rayyan zai iya zama a irin wurin nan saboda ita? Saboda kawai tana wurin idan ba don haka ba me haɗin kifi da kaska?Rayuwar mutanen gidan sossai ya chanza mata ko da ta ji irin neman ilimin da kawu ke yi tun daga sanadiyar yan shan jini da suka kama shi Allah ya nufe shi da shiriya ta tabbatar da gidan sun rabauta don ilimi shi ne ginshikin rayuwa, yaranshi duk sun dawo kan hanya sai talauci da yayi musu matuƙar yawa don Allah ya jarabcesu da babu tun bayan tuban shi abinda za’a ci ma wahala yake sai dai basu daina neman ilimi ba kuma dayake tuban gaskiya suka yi yana iya yinshi ya ga an ci wani abu ko da sau ɗaya ne a yini, tayi kuka har sai da Rayyan ya fara yi mata faɗa ganin da gaske ranshi ya ɓaci ya sa ta daina, ta basu labarin duk abinda ya faru da ita har kawo yau “Allahu Akbar… Allahu Akbar kabiran lallai shi mahakurci mawadaci ne kuma mai haƙuri shi yake dafa dutse… Yanzu Afeefah har ‘ya’yan sarki mai tarin daraja biyu ne a gidana ta sanadiyar ki? Ashe ke ce kike gina wannan tamfatsatsen gini da masallacin juma’ar da babu irinshi a wannan gari? Allah mai girma Allah mai yadda ya so”Kawu ke magana cikin hawaye da tabbatar da girman zatin ubangiji.Kallon Inna Larai tayi tace “Kawu me ya sameta?””Maciji ne ya sare ta mun yi gargajiya har mun gaji kafan ya rube dole muka nemi taimako dai da kyar muka hada kudi aka yanke kafar sai dai babu kudin ko sanda ne bare kujeran guragu a dole take yawo a haka da ja da duwawu”Lokaci Ryan ya kalla ya mata umurnin su tafi ana jiran su wurin taron da suka gayyata, kawu da iyalan shi duk suka tafi dasu wurin taron kusan duka jama’ar garin suna ɗakin taron barin ma fankoki dake kaɗa su ya sa sai nishadi suke.Mai gari ne ya fara yin bayani da kuma godiya ga wacce ta dubi garin ta zaɓi inganta rayuwarsu ta hanyar ba su ilimi wanda ta wannan hanyar ta riga ta gama musu komai, da ya zo wurin kiran suna sai ya ce “Wannan ɗin ba kowa ba ce illa mata ga Ciroma Sameer, Ciroma mai jiran gado kuma Yariman Matasa na ƙasar Fombina Afeefa..h Afeefah kamal??”Sai yayi saurin kallon matar da ake cewa ita ce Afeefahn, duk yan garin ido suka zuba mata suna mamaki da ikon Allah, wasu kunya na rufe su a yayinda tayi murmushi ta miƙe ta haura podium ɗin ta karɓi mic “Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbataga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa dagasharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu.Wanda Allah ya shiryar babu mai ɓatar dashi, wanda kuma ya ɓatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bautada gaskiya sai Allah, shi kaɗai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad bawansa ne manzonsane. Bayan nan ina yi mana Sallama irin ta addinin musulunci shi ne Assalamu Alaikum warahmatullah”Duk suka amsa, ta ɗan sauke numfashi “Ba gixo ba kuma ba mafarki ba haƙiƙa ni din ce Afeefah kamal wacce kuka fi sani da Annoba ko kuma Mayya a wannan gari, haƙiƙa na jure abubuwa dayawa daga gare ku ‘yan uwana, yayyena, Ƙannene na da kuma iyayena. A baya na zama mujiya cikin tsuntsaye Abar kyamata da gudu. Abar tozarta wa da wulaƙanta wa, Abar muzantawa a cikin al’umma saɓanin a yanzu da nake da miji nagartacce nake kuma da surakan girma waenda suka taka rawar gani bisa inganta rayuwata daga Wacce ta sallamar da farin ciki ta sallamar da jin daaɗi zuwa wacce ta zama mai cike da buri da alfahari. Da na zauna nayi nazari da tunanin Meyasa nawa iyalan kuma dangina suka yi min abinda suka yi a baya sai na fahimci babu wani abunda ke damun ahalin wannan gari na mu sai rashin ilimi da sanin daidai. Na fahimci mun samu tawaya da koma baya a wannan ɓangaren iyayen babu bare su tarbiyatar da yara akan daidai, a sadda na sake zurfafa tunanin me zan yi na taimaki al’ummata sai na ga babu abinda ya fi dacewa irin in wayar mana da kai in taka rawa wurin ganin mun samu ilimi har ma muna aiki dashi, in ga cewa wata mace ko wani yaro bai ɗanɗani irin ɗacin da na ɗanɗana ba, in ga cewa yadda rayuwata ta inganta kowa ma a yankina rayuwarshi ta inganta gobenmu mu samu tsatson da za mu yi alfahari da su daga wannan gari namu.Ya ku ‘yan uwana musulmai ku sani cewaaddinin musulunci addini ne na ilimi. Umarnida neman ilimi shi ne farkon abin da AllahMaɗaukakin Sarki ya umarci Annabinsa(S.A.W) da shi, yayin da ya saukar masa dafaɗinsa :اقْرَاْ بِاسْمٍ رَبِّكَ الَّذِي خَلَقَ! خَلَقَ الْإِنْسَانَ مِنْ)عَلَقٍ 2 اقْرَاْ وَرَبُّكَ الْأَكْرَمُ 3 الَّذِي عَلَّمَ بِالْقَلَمِ 4 عَلَمَ.[العلق: ٥ – ١] (الْإِنْسَانَ مَا لَمْ يَعْلَمْ 5Ma’ana : (Ka yi karatu da sunan Ubangijinkada ya yi halitta. Wanda ya halicci mutum daga gudan jini. Ka yi karatu kuma Ubangijinka shi ne mafi karamci. Wanda ya sanar da alqalami. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba). (Alaq : 1 – 5)Addinin musulunci ya kwaɗaitar da mabiyansa akan neman ilimi, domin ba zai yiwu mutum ya bauta wa Allah ba sai da ilimi. Allah madaukakin Sarki yana cewa :فاطر:] (إِنَّمَا يَخْشَى اللَّ مِنْ عِبَادِهِ الْعُلَمَاءُ28)TA].Ma’ana : (Kaɗai waɗanda suke jin tsoron Allah daga cikin bayinsa su ne masu ilimi) Idan na ce zan kawo muku faɗar Allah da kuma hadisan da suka yi magana akan ilimi da amfaninsa gare mu za mu kwana bamu ƙare ba amma tabbas da akwai ilimi da duk ban fuskanci abinda ya faru da ni a wannan kauyen namu ba, Ajalin mahaifina ya same shi ba tare da na zo duniya ba, mahaifiyata ta rasu bisa rashin kula da rashin zuwa asibiti a yayin daukar ciki zuwa haihuwan gida, kakata shekarun ta ya ja ƙwarai wacce dole a yi mata tsammanin mutuwa a sadda ta tafi haka Goggona ta tafi bisa sakaci da zaman jahilci da dabbanci da ake yi a cikin gidanta, bamu san kan mu ba bare mu nemi sanin hakkoƙin da suka rataya mana, hakkoƙin matayenmu, hakkoƙin iyayenmu bare hakkoƙin ‘ya’yayenmu wanda duka sai ta hanyar ilimi za mu sani, na koma wurin Aunty zainabu ta gamu da postpertum wanda ciwo ne da ake samun shi bayan haihuwa duba da bata taɓa ba ga yawan shekaru babu wanda ya fahimci hakan sai da lokaci ya ƙure ta tafi duk ba mu dubi ajalin su ne yayi ba, mun manta Allah ya ce ba zai taɓa jinkirta ajalin dayanmu ba idan ya zo dole za mu tafi. ku sani na yafewa kowannenku da wanda yayi min na sani da wanda ban sani ba duk na yafe muku, a wannan gidauniya tawa tafiyar duk na neman ilimi ne da kuma tsayuwa akan kafafunmu don Allah ina roƙon mazaje da ku bar matayenku da ma ku karan kanku ku nemi ilimi don Allah ba ya ƙarbar uzurin bawa akan rashin sani saboda ya mana umurnin nema. Akwai ma’aikata da za su koyar da sana’o’i ga yara da matayenku su ma ku bar su don zai amfani wannan al’umma tamu, duk lokacin yaye ɗalibai idan yayi zan zo kuma idan Allah ya amince za mu dinga raba kyaututtuka da suka shafi sana’ar da mutum ya koya don ya cigaba daga inda ya tsaya ina Fatan ganin chanji daga gare mu bakidaya na gode”Wasu hawaye suke yi suna tuna abinda suka mata amma dayake tana da zuciya mai kyau dubi Alkhairin da ta nufe su dashi, kawu ta miƙawa mic ɗin don ya taso yana son yin magana, a gaban tarin al’ummar yana kuka ya ba da duk labarin abinda yayi mata da wanda aka mishi ta sanadiyar son zuciyarshi da yadda ilimi ya sauya shi daga mummuna zuwa kyakyawa har ya kara da “An karɓo daga Kasir ɗan Qaisi ya ce, inazaune tare da Abud Darda’i a masallacinDimashqa, sai wani mutum ya zo wajensa ya ce masa, Ya Abud Darda’ i na zo wajenka ne daga Madinar Manzon Allah (S.A. W) sabodawani hadisi da aka ce min kana faɗa daga Manzon Allah (S.A. W), kuma babu wata buqata da ta kawo ni nan sai wannan. (wato jin wannan hadisin) Sai Abud Dar’ da’i ya ce,”Na ji Manzon Allah (S.A. W) yana cewa :”Duk wanda ya bi wata hanya yana neman ilimi a cikinta, to Allah zai sanya shi akan hanya daga cikin hanyoyin Aljannah, kuma haqiqa Mala’iku suna sanya fika – fikansu ga ɗaliban ilimi, don yarda da abin da yake nema, sannan duk wanda yake sama da qasa yana nema wa malami gafara, har ma dakifayen da suke cikin ruwa. Falalar malami akan mai bauta kamar falalar wata ne a darengoma sha hudu a kan sauran taurari, kuma haqiqa malamai magada Annabawa ne,Annabawa kuwa ba su bar gadon dinari ko dirhami ba, kaɗai sun bar gadon ilimi ne don haka don Allah kar mu raja’a akan boko don shi iya na duniya ne mu nemi lahira kuma mu koyar komin kankartarsa, ko uwa malama ce akan yayanta kar mu saka finafinai ko waƙa gaba mu ta rawa da nishadi da yara mu koya musu abinda zai amfanesu a gaba. Ni a karan kaina misali ne kuma Aya ne ubangiji ya nuna min akan Afeefah”Duk jikin mutanen wurin yayi sanyi kuma sun gamsu ɗari bisa ɗari da lallai suna da nakasu ta wannan fannin dole rayuwarsu ya tafi a jiɓance, Afeefah da manyan gari a gefenta mijinta ne da ya bata support ɗari bisa dari suka zaga wurin tassss ta yabi kyau da tsarin komai na wurin kuma duk abin bukata akwai.Kawu ta damƙawa wurin ta ce ta bashi amana ya riƙe mata ya kula da komai yadda ya kamata bisa tsari shi dai babu bakin magana don ya rasa me zai ce.Cikin jami’an tsaro masu kula da taron kawai idanunta ya sauƙa kanshi, da sauri ta nufe shi tana kallonshi shima ita yake kallo a hankali ta nuna shi “Sa’adu? Sa’adu Rabi’u kai ne?”Kai ya gyaɗa yana murmushi ya gane ta amma bai zaci zata nuna ta sanshi ba ta juya ta kalli Rayyan ya matso “Ka tuna shi Ya Saraki?””Wannan police da ya ceceki daga sharrin gurbatattun ‘yan uwansa”Za Ta cire zobenta na gwal ya miƙa hannu ya riƙe nata, ya zari kati daga aljihunshi ya miƙa mishi “Ka ƙira ni in shaa Allah kyautarka ya fi karfin kuɗi za’a mayar da kai cikin Kaduna da matsayi mai kyau”Hawayen murna ya fara yana godiya.Ko da aka watse taron suka koma gidan Kawu akan za’a saka date na fara daukar ɗaliban da suka kamata za kuma ta turo waenda za su taimaka mishi wurin fahimtar komai da komai kan a sakar mishi, a tsakar gidan suka samu an jibge kayan abinci babu abinda babu wanda za su iya ma watanni goma zuwa ashirin basu nemi kayan abinci ba, a gefe crouches ne da wheelchair na inna Larai Afeefah tayi saurin kallon Rayyan ya girgiza mata kai yana dan ɗage kafada sai ya juya ya fice ta bi bayanshiZa tayi magana jiri ya ɗan dibeta da sauri ya riƙo ta “Boɗɗi menene? Ba kin ga illar kukan da kika dinga yi ba duk yau kin tarawa kanki damuwa! Kan na ciwo ne?”Ya kai tafin hannunshi yana dafe goshinta hawayen ta sake farawa “Ban san da wani baki zan fara maka godiya ba Ya Saraki… Ko baka faɗa ba na san aikinka ne Allah ya biya ka ya saka maka da alkhairi ka yi min komai Ya Sa…”Hannunshi ya sa ya rufe mata baki yana dan ɗauke hawayen da take zubarwa yace “Kin chanchanci fiye da haka a gareni Afeefah don haka ba komai ba ne, na so ko gidan haya ne mu kama a gyara wannan amma bai samu ba idan ba damuwa za su dan koma Kaduna ko ma su je ganin ɗakin ki a Fombina kan su dawo sai a gyare nan ɗin”Rungume shi kawai tayi ya sa hannu yana dan shafa bayanta kan ta ɗago sai ta sake jin jirin yamutsa fuska tayi, ya shiga mota don bai kula ba itama ta zaci ma stress ne don haka ta koma ta musu bayanin za su je Fombina ko sati biyu su yi za’a ɗan gyare nan ɗin kuka kam kawu har ya rasa hawaye ya rasa bakin godiya a haka suka ɗauki duk abinda za su ɗauka aka adana kayan abincinsu a daki guda suka ɗauki duk wani abu mai muhimmanci, yaranshi maza manyan uku da mata shidda na Inna Asabe uku na Inna Larai biyar suka bar garin zuwa Kaduna.Kai tsaye gidan Mammi suka yi masauki jannah ta turo abinci ko da Abeeha ta gaya mata da baƙi suke ta turo daga restuarant, a masaukin baki aka sauke su suna ta mamaki da santin gidan, Ita dai Afeefah su Suhaila ta ja zuwa ɗakinta ta musu wanka ta duba cikin tsarabarsu da ta musu na musamman ta fidda kaya ta saka musu suka haɗe babban parlor aka ci aka sha kan kowa ya nemi makwanci don sun gaji, sai da ta tabbatar sun yi bacci ta watsa ruwa ta shirya cikin wani Red kayan bacci da yayi mata kyau sossai marabarshi da babu kaɗan ne ta nufi ɗakinshi…Yana jingine da gado yana jiranta suna haɗa ido suka Sakarwa juna murmushi mai ƙayatarwa, yanga tayi ta mishi Dukda kunya dake ɗawainiya da ita barin killer looks da yake binta da su har ta iso gadon ya fusgo hannunta ya manna ta kirjinshi yana matse ta a lokaci ɗaya suna sauƙe ajiyar zuciya a tare A kunnenta ya raɗa mata “Kina kashe ni da raina Gimbiyata”Ta ɗan ɗago bai tsammata ba ta haɗe lips ɗinsu kaman jira kuwa ya mirginata kasanshi ya mata rumfa yana bata wasu kisses da suka sake matar da ita a kaunarshi hannunta na yawo bisa bayanshi zuwa keyarshi tana mishi susa, gasping air yayi ya raba lips ɗin suka yi murmushi mai sauti ya sake mayar da lips ɗin yayi mata kyakyawar Kiss Ta raba fuskansu tana shafa kanshi hancinsu haɗe da juna suna musayar numfashi ta ce “Na gode sossai Na gode kwarai haƙiƙa Allah ya wanke min zuciya ya ba ni mijin marainiya, ya ba ni kai ba tare da wayo ko dabara ta ba a koyaushe ba ni da abin faɗa a gareshi sai Alhamdulillah. Ina roƙon Allah akan duk ranar da za ka haɗu da shi, Fuskarka ya zama mai annuri da sheki fiye da yadda yake a yanzu, ya rabautaka da karɓar kyawawan sakamakonka a cikin tafin hannunka na dama sannan ya ce “I am pleased with you” ya haɗa mu gabaɗaya a aljannah madaukakiya ya ba ni dama da ikon Zama shubagar matayenka a aljannah. Ina ƙaunarka Ya Sameer…Ina ƙaunarka Ya Rayyan ina matukar sonka Ya Saraki”Hawayen dake zuba mata yake bi a hankali da harshen shi yana ɗaukewa cikin wani salo zuciyarshi ƙal yayi fixing gaze ɗin shi cikin idanunta “I love you. love you more than anything Afeefah, ban taɓa jin son wani abu yadda nake jin naki ba, I love you more than myself. I will always love you. I will love you till the end of my time. No words can express how much love i have for you. I will alwavs be here for you no matter what kin ji? Babu abinda zan miki da zan ji yayi yawa you are my favorite girl nd my only blessing”Daga nan ta dafa chest dinshi sai ya koma kwance ta dane jikinshi da kanta ta shiga gigitashi abinda bata taɓa sakewa tayi ba ta yi shi a ranar ta goge mishi hadda sai gashi yau ma yana yi mata kuka don ta gama da rayuwarshi in dai ta fannin ne.Washegari sun tashi da mummunan labari don Uncle Usman ya rasu labarin ya kaɗa ta don faɗuwarta kawai suka ji hankalinsu ba karamin tashi yayi ba barin ma Rayyan a hannunshi ya ɗauketa suka tafi asibiti don duk abinda za su yi sun yi matsayin shi na likita ya kasa farkar da ita yana jin panic akan ciwon Mammi amma bai san Meyasa duk abinda ya shafi Afeefah na fitar da ragwantakanshi a fili ba, tsoro da fargaba ya sa ya manta yadda ma ake aikin likitacin sai a asibitin ne aka samu ta farfado nan suke samun labarin tana da shigar ciki kuma razanar da tayi har ya fara barazana ga ɗan cikin nan ya saka aka yi mata allurar bacci don ta huta sossai.’Yan uwanshi sun yi rawan gani da su Sulaiman aka sallaci uncle Usman aka kai shi makwancinshi dogon takarda da ya roki sulaiman rubuta mishi ya ba Rayyan akan idan ta dawo daidai sai a bata.Kwanan ta biyu kan ta dawo cikin hayyacinta tayiwa su Suhail kuka ba na wasa ba don maraici babu daaɗi ta kuma yi alkawarin rike su fiye da ƴaƴan cikinta har illa masha Allah.A kwana na huɗun suka juya Fombina, anan ne Kawu suka san basu ga komai ba baki sake suke bin irin girma, tsaruwa da ma kyaun masarautar irin mulkin da ake shimfidawa ko a mafarki basu taɓa mafarkin halartar irin wannan wuri ba sai gashi wacce suka raina ta zama sanadiyar da ake zube musu, sun yi kuka kaman me don sashe na musamman aka sauke su mai martaba da Ammi suka tura ake musu hidima wane wasu masu kuɗi.Ammi da mai martaba kaman su hadiye Afeefah jin labarin cikinta, soyayyar mijinta kuwa ya ninku fiye da yadda yake jinta a da su Suhail sun zama ‘yan gata don a take aka tsara musu dakunansu Mai martaba ya sa aka cike musu wardrobes da kaya Ammi ma ba’a barta a baya ba don abinda za ta yiwa jikokinta shi take musu har ma sun Fara ƙiran Afeefah da Ammah Ryan kuma Abbu, school na musamman ya saka su masu musu hidima ma daban aka ware don Afeefah laulayi mai wahalarwa take.Satin su Kawu uku suka koma bayan Rayyan ya saya mishi babban waya an hada su da goma sha tara na arziki suka koma, gidan su ya zama daga cikin gidajen da suka fi kowanne kyau a garin ɗan daidai kuma a kayace sai ya tuna akurkin da suka warewa Afeefah take rayuwa lallai Allah ya nuna musu ikonshi sun tuba har sun rasa bakin tuba, a kuma satin da suka koma aka fara gudanar da aikin gidauniyarta.Sai ga kujerar Umura da Rayyan ya biya musu har da su Mai martaba za su tafi da su Abeeha, sun yi murna barin Afeefah da bata taɓa zuwa ba za dai tayi kewan yaranta cikinta na wata huɗu suna gama second semester exams suka chale ƙasa mai tsarki ranar da ta fara ganin ka’aba tayi kukan da sai da tayi zazzabi bata taɓa ganin abu me kyau da natsuwa ba irin shi duk rayuwarta, ta zube wurin ta yiwa iyayenta da yan uwanta da ta rasa Adu’a har sai da miyaun Bakinta ya kafe, sun yi sati uku chan sayayyan baby kuwa kowa yi yake ba Ryan ba ba Ammi ba ba su jannah ba, daga Saudi sun tsaya kaɗan a Turkey sun yi sayan kayan ɗakin su Aisha ana dawowa Nigeria Aka fara hidimar bikin su.

Back to top button