Hausa novels

Mejo Najeeb Page 33 By Autar Alheri

“Sunjima suna kallon juna kamin kowacce tanufi abin gabanta, Hajiya Umma tanufi bedroom ɗinta yayinda Hajiya mama tanufi na Dady…tana shiga tasamu yafito daga wanka yana zaune bakin bed ɗinshi zama tayi itama kusanshi kamin yace “har kingama haɗa breakfast ɗinne? “Eh nagama alhaji. “Okay kawai yace kana yaci gabada shafar manshi. Ɗagowa tayi Taganshi babu wata damuwar ataredashi tukunnah tafara mishi magana domin tasan idan rashin a ɓace yake sam baze fahimcetaba. “Alhaji nace yoshene zakuje garinsu yarannan domin kawo ƙarshen komai? Ɗan nisawa yayi kana yace “yau in sha Allah zamu tafi domin kinsan bazamu ajiye mutane musharesu ba doline musan abunyi…”hakane gaskiya amma fa Alhaji inaga da anbar tafiyarnan zuwa next week domin Najeeb bayanan ɗazu yazo yasameni akan cewa nasanar maka zeyi tafiya zuwa South Africa aikine na gaggawa yataso musu yazo yasanar dakai amma baka tashi daga bacciba Hakan yasa yace nagayama please Alhaji Abar tafiyar haryadawo tunda kaga aikinsu kamar haɓo yake zuwa kawai yakeyi bada sanarwaba, taƙarasa zancen cikin rarrashi….acijiyar zuciya Dady yasauke bayan yagama jin bayananta kamin yace “to Amma ita waccan ɗaya amaryar yazamuyi da ita? Tunda bazama zeyi da itaba muna ajiye ƴar mutane???”Ah,ah Alhaji amma aikuma bawani abin bane tunda mako ɗaya ne kawai mize hana amayarda family nata iyaso ita abarta anan idan yadawo sekuje dukanku koya kagani?? “Eh to badamuwa Hakan yayi kigaya musu sushirya anjima se amaidasu ɗin amma kar wanda yayi musu zancen komai acikinku.. “shikenan in sha Allah Hakan za’ayi bawanda zemusu wani zancen. “Yayi kyau Hakan cewar Dady daga Hakan yaci gaba da shirinshi.Hajiya mama nafita kuwa tawuce pert ɗin baƙi inda tasamu Mamansu yah balah da jimmala cikin mutunci suka gaisa tare da yimusu yabaƙunci tukunnah tagaya musu saƙon Dady tafice warta…bayan fitarta su jimmala suka shiga haɗa kayan su dudda basuso barin gidanba amma ba yadda zasuyi domin kuwa doline sutafi tunda amarya suka kawo…..anty hawwa kuwa dataji labarin Zasu tafi baƙaramin baƙin ciki tajiba domin bataso aɗauke mata anty bilki amma ba yadda zatayi doline tabari sutafi sedai wlh datazaunu tazama ƴar gida zata ɗauko anty bilki tadawonan dazama suɗora daga inda suka tsaya🤔Misalin ƙarfe 10:00am zaune suke dukkansu a general parlor gidan tawagar kawo amarya sukazo yimusu sallama…sosai su Hajiya Umma da Dady sukayimusu alkhairi na ban mamaki mamansu yah balah hadda kukanta sabida farin ciki kana suka yi musu sallama suka tafi anty bilki da anty hawwa daƙyar aka raba su kowace se kuka taketeyi,,,sudai mutanen gidan nabinsu da kallo kawai harsuka tafi, inda dady yasaka sojojin dasuka ɗaukosu sumaidasu.Bayan suntafine kowa yawatse Hajiya mama tacewa Ummi takai anty hawwa part ɗinta tunda juwaira nacan sunzauna tare su ukku. 😱GombeAbakin kogiIsseta nahango rungume da maah ɗinta se shagwaɓa take zubawa yayinda Maah keta doka murmushi tana kaɗa jelar kifinta..Cikin taushin murya tace “wai yoshene Maryama zata girmane? Tunda harna aurarda ita bata girmaba amma inaga laifin najeebullah ne nidakaina zan bashi shawarar yasakaki kigirma Hakan maybe kyadena taɓara, taƙarasa zancen tana shafa fuskar Isseta…baki tatura gaba kamar yadda tasaba tace”Allah ni maah nagirma bakigaba nazama ƙatuwa, tafaɗa tana ɗago hannun rigarta….kafin maah tayi magana umaima dake gefe tana kallon diramar uwa da ƴarta tace “iko se Allah maah kisako muna ƴar taki Hakan domin halima tuni takai asibiti tana jiran ƙawar tata…..murmushi maah tayi kana tace “shikenan umaima barana sallami maryama domin daga asibiti idan kungama abinda yadace karku dawonan kemaidata gidan mijinta. “To shikenan in sha Allah Hakan za’ayi. Cewar umaima.Wani abun maah tamiƙawa Isseta ahannu kamar ƙololon daimon..seda Isseta takarɓa tariƙe shi sosai kana tace “maryama lokaci yayi da amminki zata samu lafiya biqudiratillah dama nasan haukarta bana asibiti bane amma alokacinda akakaita asibitin canne yafi dacewa da tazauna domin tasamu kyakkyawar kulawa shiyasa nabari kikakaita amma ayanzu inaso tadawo cikin hayya cinta kamar kowa sabida Hakan kijeda wannan idan kukaje asibitin kunemi asallameta daganan kukaita gun innar halima in sha Allah bazaku samu matsala da itaba…bayan kunkaita gidansu halima sekisamu zam zam kisaka wannan aciki idan yanarke ko bata tasha sauran kishafa mata akanta zuwa fuskarta in sha Allah itada hauka har ibada..wani irin waro ido Isseta tayi cikin mugun farin ciki tace “maah ammina zata warke? Dagaske zata dawo lafiya qalau kamar kowa?? Wayyoo Allahna maahhhh tafaɗa daƙarfi cikin ɗauki tarungume maahh ɗin tata…..Itama rungumetan tayi sosai kamin tacigaba faɗar sekuma abu na biyu maryama akwai wani labari daze riskeki acikin kwana kinan dan Allah duk lokacinda yasameki Karki ɗaga hankalinki kinji ƴata kisani duk abinda kijaji gaskiya ne Karkiyi kokwanto aciki….ahankali taɗago tana kallon maah ɗin tata kana tace “wanne irin labari ne wannan maah?? Tatambaya cikin mamaki…Zaki sani maryama duk ranarda kika haɗu da mamarki bintu yanzu dai kuyi sauri kuje kar halima tagaji dajiranku kinjiko…zatakomayin magana kawai Taganta bakin get ɗin shiga asibitin mahaukatan…ido tazaro atsorace tana waige waige idonta yasauka akan umaima dake tsaye tana murmushi..fuska takwaɓe kamar zata saki kuka domin tagano ɗauketa ne umaima tayi dankarta ƙara yiwa maah ɗinta wata tambayar…umaima kuwa bata batadamar yin maganaba tanuna mata halima dake can nesa dasu zaune tana bin mutanen dake wucewa wurin da kallo, ai aguje Isseta takwasa tana tunkarar halima cikin farin cikin ganintaHalima kuwa nacan zaune kamar ance taɗago kanta aiko tayi ido huɗu da Isseta wani irin waro ido tayi tare da daka tsallen Itama tanufo Isseta ɗin cikin matsanancin farin cikin ganinta, gudusukeyi amma ganisuke kamar basa kaiwaga juna sabida tazararda ke tsakaninsu….gabaki ɗaya ma’aikatan dake harabar asibitin baki suka saki da hanci suna kallonsu…wani irin rungume juna sukayi atare suna sauke ajiyar zuciya lokacinda suka haɗu wuri ɗaya shakka babu waƴannan aminan sunyi matukar kewar junansu bakaɗanba dubada yanayinsu ayanzu…sunjima maƙale dajuna seda umaima Taga abin nasu banaƙare bane tazo kusadasu cikin tsokana tace “to tip da taya kuyi haƙuri Hakan muyi abinda yakawomu kinsan dai maryama nayiwa mijinki alkawarin zanmaidaki dawuri..ido halima tazaro cikin mamaki “Isseta mijifa naji tace dama aure kikayi? Bayan wanda abbanku yayi Miki lokacinda bakyanan? Aure akan aure Isseta? Duk atare halima kejero mata wannan tambayoyin…ɗan murmushi Isseta tayi cikin sexy voice ɗinta tace “duk ba abinda kike tunani bane halima amma zanyi Miki bayanin komai idan mukaje gida yanzudai please Ina ammina? Inamatuƙar so naganta…halima Bata ƙara cewa Isseta komaiba taja hannunta zuwa inda amminta take……baiwar Allah tana zaune kamar yadda tasaba ita kaɗai tana kallon wuri ɗaya…dasauri Isseta taƙarasa gareta tare da rungumeta tace ammina nayi missing ɗinki ammina yajikinki wlh naji daɗin yadda naganki kincanja Ammi bawanda ze kalleki yace bakida hankali Ammi idan bayasaniba, tafaɗa kamar memagana da wadda ke fahimtar abinda take faɗa tana share ƙwallar idonta…itadai Ammin kallonta kawai takeyi tana doka murmushi daya kayara mata kyau dagani kasan cewar taji daɗin ganin Isseta Sedai babu bakin magana.Ɗagowa Isseta tayi tana kallon halima da Itama Ita ɗin take kallo sekawai tarungumeta tare da fashewada kukan farin ciki tana faɗar “ngd ngd sosai aminayata Allah yasaka muki da gidan aljannah tabbas samun ƙawa irinki zeyi wahala aduniya halima kintayani aikin alkhairi danakeyi munyi tare kuma anzo daga baya bana’nan kuma kika ɗora daga inda natsaya yanzu kalli yadda Ammi Takoma Sam bawanda zece batada hankali Inba yasaniba niko ma zanyi Miki aduniya halima? Inba addu’a ba alhmdllh alhmdllh alhmdllh Ina godiya ga Allah ina gode miki Allah yabamu iKon riƙe amintakarmu har mutuwa…Ameen y hayyu y qayyum Isseta Dan Allah kedena wannan zantukan nima Ammi uwace agareni kamar yadda kika ɗauketa nima Hakan naɗauka dudda cewar bamusan ko wacece itaba amma Hakan baze canja mata suna na uwa agaremuba dan Allah kiyi shiru kawai da bakinki.”Gaskiya kam yanzu kuje kusaka asallameta kuzo muje lokaci na tafiya, cewar umaima. “Sallama kuma ainaga haryanzu bawarkeba, halima tafaɗa cikin mamaki…”eh halima Maah ce tace ayi Hakan kuma idan ansallameta akaita gurin inna tazauna. “Inna agidanmu kenan? Halima taƙara tambaya..”eh a can, Isseta tabata amsa atakyaice. Baki halima tawashe cikin farin ciki tace to muje asallametan tafaɗa tanayi gaba domin baƙaramin daɗi tajiba da Isseta tace agidansu Ammi zata zauna….murmushi sukayi kamin sunufi gun amaikatan Ashe Ammi namaƙale da mayafin Isseta tariƙe shi tamau kamar wata me hankali dan karta tafi tabarta,,su Sam Basusan abinda kefaruwa ba seda wata ma’aikaciyar wurin tayi musu magana tukunnah…dasuka juya suka ganta murmushi kawai sukayi dukkansu Isseta tace “ayya ammina yi haƙuri yau ƙafana ƙafarki in sha Allah…daga Hakan suka gayawa ma’aikatan buƙatarsu,,cikin sauƙi kuwa suka amince tunda sunga babu wata matsala dama agun marar lafiyar tasu kawaide dan Batasan abinda takeyibane…ahakan dai suka yi duk wani abinda yadace suka sallami Ammi daga anan umaima taɗaukesu dukkansu bata ajiyesu Ako inaba se gidansu halima…!

Back to top button