Mejo Najeeb Page 15 By Autar Alheri
“Tana gama jerasu tashiga bathroom tayi wanka taƙara gasa jikinta bayan tafito tashafa mayukanda yasiya mata tayi simple makeup dama gata gwanar son kwalliya seta fito asalin maryamarta,,,kayan tabuɗe taɗauko wata doguwar riga milk color daratsin golden ajikinta sosai rigar tayimata ɗass kamar angwada a jikinta,, ribbon tasaka takama jular gashinta data sauko har gadon bayanta kana taɗaura mayafin abayar akanta.Ahakan tafito perlorn ta tana ƙarewa tsarinshi kallo sosai yabirgeta Hakan yasa tashiga saukowa ƙasa cikin sanɗa gudun karta ganshi a general parlor harta sauko kobataga kowaba babuma alamun akwai mutun agidan,,nan tashiga zagayen perlor har kitchen da sauran bedrooms din ƙasa seda tashiga takashewa kanta ƙwarƙwatar ido🤩sosai tsarin gidan yabirgeta Masha allah tazaga ko ina seda tagama zagayen kana Takoma kitchen domin samawa kanta abunda zataci jin cikinta yafara Kiran chiroma 😅kayan abincinda ya’ajiye mata tashiga dubawa babu abinda babu aciki duk wani abinda zata buƙata na abinci da anfanin kitchen akwaishi aciki. Ajiyar zuciya tasauke bayan tagama duba kayan taɗauko indomie kawai taɗora tare da ruwan tea seda tagama girkin kana tagyara kitchen ɗin tsab kamar ba’ayi komai acikiba sa’annan taficewarta ɗakinta acewarta karyazo yasameta anan tinda dai tagama buƙatarta.Acan tazauna seda tagama cin abuncinta taƙoshi kana tamiƙe tashiga gyaran ɗakin dudda bawata datti yayiba amma kasancewar anjima ba kowa agidan yasa yayi ƴar ƙura aiko sosai Isseta tazage tagyara ko ina agidan tindaga bedroom ɗinta har zuwa nashi bedroom ɗin wanda batamasan nashi bane seda tagama gyaran tazo wanke banɗaki ananne Taga boxes ɗinshi daya cire lokacinda yayi wanka, ɗauka tayi tawanke mishi komai batareda damuwaba tinda tasaba wankin nasu ya balah, seda tagama gyaran part ɗin nashi tasaka mishi tirare kana tarufe kamar yadda taganshi tukunnah tasauko ƙasa seda tagyara ko ina agidan kana takoma bedroom ɗinta izuwa wannan lokacin anyi sallar azzahar banɗaki kawai tafaɗa tare da sakeyin wanka da alwala tafito tayi sallar azahar bayan ta idar tayi kwanciyarta se bacci..GombeTafiya takeyi cikin sauri ita kaɗai akan hanya batada burin daya wuce taganta agaban aminiyar tata abakin tekun ta tsaya tana waige waige ganin bakomai awurin kamar anyi shara gaya kuma bataga ko motsin aminiyar tataba yasata tabuɗe baki ahankali tace “maahh tafaɗa cikin fargaba domin yanzu taɗanji tsoro saɓanin ɗazu datake kan hanyar zuwa….tanatsaye awurin kuwa Sega jilar kifin maah tabayyana daganan Itama tafito gaba ɗaya, kallon halima tayi cikin murmushi domin dajin Kiran tagane itace..cikin sauri halima tagaidata.”Murmushi maah taƙarayi bayan ta amsa mata tace “ƙawarki kikazo ganiko halima?? Tatambeta da kulawa. “Kanta a ƙasa tace “Eh maah nazo nagantane.Jinjina kai maah tayi kamin tafito daga cikin ruwan takamo hannun halimar suka zauna bakin tekun tace “halima..”na,am ta’amsa gabanta na faɗuwa. Sarai maah taganota amma seta share taci gabada faɗar”ina mematuƙar baki haƙuri akan hukuncin danayanke akan ƙawarki sedai inaso kisani bayin kaina bane ƙaddarartace tazo ahakan kuma In sha allah komai zezama labari. Nisawa tayi kamin tacigabada magana kamar Hakan “kisani maryama tana garin Lagos ayanzu….ido halima tazaro cikin kaɗuwa take duban maah idonta suncika tabb da ƙwallah…kai maah tajinjina mata alamar tabbatarwa kana tace “kiyi haƙuri halima zuwan maryama Lagos bayana nufin rabuwarku bane sedai yana nufin faruwar wani al’amari megirma abunda nakeso dake ayanzu shine kisaka aranki cewar kinatareda maryama aduk inda kike kuma maryama Matana taredake, sa’annan kizamewa maryama abokiyar gwagwar mayarayuwa akowanne hali kinjiko halima…kai Hakima yaɗaga tana me haɗiye kukanta…murmushi maah Tayi kana tace yawwa ƴar albarka kikwantarda hankalinki kuma aduk lokacinda kikesan wani temako daga gareni kizo kawai kinji ƴata in sha Allah nidakaina zansa akaiki gun maryama Kona kawo Miki ita idan baki ɗaga hankalinkiba…ajiyar zuciya halima tasauke kana tace “toh maah in sha Allah zanyi Hakan ngd sosai…yawwa ƴar albarka yanzu maza kije gida gasaƙo can kiɗauka, Tana gama faɗar Hakan Takoma cikin ruwa…. miƙewa halima tayi jikibaƙwari tanufi wurin dutsen nan da suke zuwa itada Isseta aiko tasamu maƙodan kuɗaɗe awurin kamar yadda suka saba gani inatada Isseta hawayen idonta tashare kana tasaka hannu taɗauka tabar wurin….tana shiga cikin gari takalli tulin kuɗin hannunta atake tatunada abinda Isseta keyi da kuɗin idan takarɓo aiko babu ɓata lokaci tanufi majalisar su yaya shamsu…yana ganinta tafe yataso cikin sakin fuska suka gaisa anan yayi mata jajen ɓatan Isseta kamar yadda aka yaɗa agari…murmushin da yafi kuka ciwo halima tayi kana tace mishi bakomai ai ƙaddara ce domin tayiwa maah alƙawarin bawanda zeji Isseta nanan lpy,,,daganan tace mishi zuwa tayi suje asibiti gun mamin Isseta…murmushin yaya shamsu yayi kana yace “to shikenan halima kicedai Zaki ƙarasa aikin ladanda aminiyarki taɗauko kenan? To ai Hakan akeso Allah yabamu iKon yin abinda yadace…Ameen y rabbi kawai halima tace daganan suka sami adedeta yaɗauke su zuwa asibitinKoda sukaje alhmdllh sunsamu mamin Isseta yadda sukesan ganinta domin atsabtace take sabida tanasamun kyakkyawar kulawa komai sedai suce Masha allah abu ɗaya ne ya gagara samuwa shine lafiya amma Itama dassanu zatashiga ciwone kesamuwa lokaci ɗaya….godiya Sosai sukayiwa ma’aikatan wurin suka ƙara biyan wasu kuɗaɗen koda za’abuƙaci wani abu tare da yiwa ma’aikatan alheri suka tafi suna masuyiwa mamin Isseta addu’ar samun lafiya..AbujaJirginsu nasauka kaitsaye suka wuce babbar hidikwatar sojoji dake garin Abuja inda suka samu duk wasu manyan jami’an soja da’akeji dasu a Nigeria suna wurin hadda general faruk sojan ƙasar Niger shima datawagarshi duk suna wurin zuwansu kawai ake jira ashiga meeting Shima sabida general faruk yace bazeyi maganar komaiba harse jami’an sojojin dasukayi nasarar kama ƴan ta’addan sunzone sabida sune sukasamu information akansu..tofa wannan dalilinne yahana ashiga meeting ɗin.Shigowarsuce tasa duk wanda ke wurin hankalinshi komawa kansu inda ƙananun jami’ai damanya keta ribibin sara musu sabida namijin ƙoƙarinda sukayi…cikin mamaki wasu daga cikin manyan jami’an Nigeria ke kallonsu domin Sam basuyi tinanin subane…wasu kuwa sunsan sune sabida sunansu da’akayi posting alhalin su basuma sanda abunba kawai Allah yayi ikonshi akan lamarin shiyasa har suka gani kuma suka yi aikin inda suka samu nasara cikin iyawar uban giji da buwayarsa…..general faruk ne yazo wurinsu kyakkyawan matashin sauri me farar zuciya. Hannu yabawa general aliyu suka yi musabaha tare da jinjinawa namijin ƙoƙarinsu akan wannan al’amarin kana yabawa mejo Najeeb daga baya sabida mutane da suka yaɓeshi suna girmama shi…Shima bayabo ba fallasa yabawa general faruk hannu suka gaisa cikin mutintawa daganan suka samu wuri suka zauna inda kowa yazauna mazaunin shi sedai abin mamaki general faruk yaƙi zama acikin tawagar shi yadawo kusada mejo Najeeb da general aliyu yazauna abin gwanin birgewa. Dudda manyan nasu sunkulada Hakan sedai bawanda yace komai domin sunsan waye mejo Najeeb bayabin ƙa’ida kuma baya sauren zancen magaba dashi balle sukawo mishi wargi ko renin hankalin manyan jami’ai Hakan yasa ko manyan shayinshi sukeji.Sunjima suna tattaunawa akan wannan matsalolin inda general aliyu yace yanaso yasani waye yasaka sunansu amatsayin waƴanda zasuyi attack ɗin amma kuma ba’asanardasuba?shiru wurin yaɗauka kowa natinanin wannan al’amarin tayaya Hakan zatafaru…dagacan wani mejo tanimu yace “wannan wacce irin maganace general aliyu kakeyi Hakan tayaya zakuce ba’asanarda kuba kuma kukayi aikin kenan ku waliyaine dazakuyi abu bayan bakusanda shiba?? “Mikakesan cewa ne abb…beƙarasaba mejo Najeeb yadakatardashi tahanyar riƙo hannunshi yazaunar dashi..aiko yakoma yazauna batareda yaƙara cewa komaiba..duk abinda kefaruwa kowa dake wurin na kallo… miƙewa yayi tsaye cikin cool voice ɗinshi yafara magana kamar babu komai ataredashi amma anan dayake karkaso kaga zuciyarshi yadda take tafasa kamar anhasa mishi wuta. “The game is over but we I’ll going to south Africa next month in sha Allah…yana gama faɗar Hakan yajuya zebar wurin…cikin daga murya wannan mejo tanimun yace “we not understand you najeeb sahabi mizakuyi a south Africa??? Ahasale yajiyo cikin daga murya yace “zamuje ƙarasa aikin da muka farane domin babu shugaban su anan kuma wlh semunje munkamoshi kuma nida brothers na kawai zamuje Bama buƙatar wata rundunar ko temakon wani se allah that’s all.Dukkansu sororo sukayi suna kallonshi…kamin wani dagacikinsu yace “bamugane kaida brothers ɗinka ba kana nufin bada jami’ai zakajeba mejo Najeeb tayaya Hakan zefaru?? Wani mugun kallo mejo yawatsawa mutumin kamun yace “yes of course nida brothers na zamuje kuma haziƙan jami’ai wanda sukasan aikinsu ba karnukan farautar ƴanta addaba masu ɓata mana ƙasa general aliyu Haidar & general Umar faruk Niger sune brothers na kuma sune zamuje dasu bakuma shawara nake nemaba kojiran umurni noo hukuncine narigada nayanke kuma na tabbatar Sena aikata biqudiratillah.Yana gama faɗar Hakan yaficewarshi cikin takonshi na jaruman maza masuji da izza da dajarunta. miƙewa general aliyu yayi yabi bayanshi batareda yaƙara cewa komaiba hakama general faruk dayayi mutuwar zaune jin mejo Najeeb yakirashida brother ɗinshi tofa Shima ficewarsuce tadawo dashi hankalinshi Hakan yasa yamiƙe cikin sauri Shima yamara musu baya sukabar kowa dakewurin da baki asake..wani mugun ƙololo mejo tanimu ya haɗiye yanajin baƙi cikin yadda wannan yaron ketaka kowa ahukumar soja kuma bame tanka mishi gaskiya doline suyiwa tubkar hanci yaƙarasa zancen yaname barin hold ɗin Shima inda muƙarrabanshi suka takemai baya(hmm nikuwa nace aiki yasameka Alhaji tanimu🤩)Suna fita mota kawai yashiga suma duk suka shiga hadda general faruk suka nufi gidan Mejo ɗin dake cikin garin abuja dukkansu wanka sukayi kana general aliyu yayi musu order abinci online kafin akawone suka shiga tsara yadda zasu ɓullowa lamarin kafin lokacinda mejo ɗin yaɗiba nazuwansu South Africa yayi sunjima a general parlor gidan kafin Mejo yamiƙe yashige warshi bedroom…da kallo general faruk yabishi harya ɓacewa ganinshi kana yasaki murmushi yana girgiza kanshi…taɓoshi general aliyu yayi Shima yana murmushi tare da ɗaga mishi gira ɗaya 🤨alamar yadai…murmushi Shima yaƙarayi yana shafa kwanta ciyar sumar kanshi ta buzayen asali yace “wlh kawai guy ɗin yana birgeni ne yadda yake komai ba tsoro balle fargaba gakuma miskilanci ko acikin maza seya bayyana gaskiya wannan kam mace zatasha fama ataredashi..dariya sosai zancen general faruk yabawa general aliyu Haidar seda yayi me isarshi kana yace “inafa kasani aibakaga komaiba indai najeeb ne iyaganin yau ne kake mamakinshi inaga dashi kake rayuwa? “Humm gaskiya kam abin dai Allah ya kyauta..to Ameen amma tabbas matarshi kam nada aiki zanso ganin yadda zeyi rayuwar auren shi cewar general aliyu..dariya general faruk yayi cikin mamaki yace badai bayada aureba?? “Aikuwadai kam bayadashi kamarni maybe Kaine kawai me mata acikinmu…wata dariyar yaƙarayi yana faɗar “tab dijam niɗin?? humm aiko duk mune sedai Allah yanuna mana munyi.. Ameen y rabbi cewar general aliyu Yana murmushi…abuncinda general aliyu yayi order ne aka kawo musu shine abinda yakatse musu fira, fita yayi yakarɓo abuncin kana yadawo perlor Anan sukaci abincinsu sukabarwa mejo nashi domin ga dukkan alamu bacci yakeyi,,seda suka ƙoshi kana kowannensu yanufi ɗaya bedroom ɗin suka kwanta se bacci..Kwanansu mejo huɗu a Abuja kana kowannensu yanufi garinsu inda suka yi musayar nomber waya suda general faruk domin awannan ƴan kwanakin shaƙuwa me ƙarfice tashiga tsakaninsu Hakan yasa dasuka fito seda suka raka general faruk har airport inda tawagarshi take yashiga jirgin komawa ƙasar shi kana suma suka hau nasu jirgin zuwa Lagos suka rabu cikin kewar junansu kamar suwuce gari ɗaya amma ba damar yin hakan to sedai muce Allah ya saukeku lpy…!



