Hausa novels

Mejo Najeeb Page 11 By Autar Alheri

“Wani irin zabura takomayi batareda takowaiwayi abinda takauraba balle tasan minene Hakan tasake kwasa aguje tanufi jirgin tana ihu tana ƙarawa, sosai take tura jirgin kamar wani abun wanda zata iya turewa sedai ko gizau beyiba amma takasa fahimtar ba’abunda zata iya awurin…..shikuwa najeeb yakasa koda ƙwaƙƙwaran motsi sakamakon ruwa naƙara ta’azzara ciwonshi Hakan yasa yafara fita hayyacinshi sedai dudda wannan halin da yake ciki Hakan behanashi hangotaba yadda taketa haƙilon son ture jirgin.General aliyu ne yafito asukwane shida captain Jameel sakamakon tsinkayo faɗuwarsu dasukayi kuma sunga yarinyar tatashi amma shi komotsi beyiba, suna ƙarasowa general aliyu yaɗagoshi yana faɗar subahanallah mejo miyasameka Hakan badai dama bakada lpy ba? Yafaɗa Aɗan rikice..”yasalam wlh rashin lafiyarshi ne tamotsa inaga akwai abinda yaɓata mishiraine, cewar captain Jameel. Ɗan shiru yayi kafin yakoma cewa “innalillahi wa’inna ilaihiraji’un yanzu yazamiyi dashi acikin wannan ruwan wanda koda agida muke baya buƙatar likita balle anan. “Yanzu dai duk ba wannanba kamashi mufiddashi daga cikin ruwan tukunnah semusan abunyi, cewar general aliyu Haidar. Hakan kuwa suka kamashi aka fitar dashi daga cikin ruwan inda suka samu wurinda sukaga shimfiɗar Isseta suka kwantardashi batareda sunsan me shimfiɗar ba…baki general aliyu yabuɗe zeyi magana kenan yahangota tana tsalle tana duka jirgin ruwan cikin matsanancin kuka. Ido yazaro yana faɗar “tofa itakuwa waccan yarinyar wacece ko’acikin jirgin tafitone? Takasa komawa? Yatambayi kanshi, kamun yace to Amma fa kamar kuka takeyi baradai muga yafaɗa yana nufar wurinta kaitsaye.Isarshi keda wuya yaji tana faɗar “nashiga ukku wlh Allah bazan yaddaba kunkashemun mahaifiyata kunrabanida farin cikina wlh Allah seya sakamun innalillahi wa’inna ilaihiraji’un maahhh dan Allah kitashi kuɗaga jirgin maahh tafito kundanneta wayyooo maahh sunkasheki..Hakan kawai Isseta kefaɗa cikin kuka da muryar matsanancin tashin hankali atareda ita.”Innalillahi badai mutum jirginnan yatakaba shine dalilin tsayuwarshi? To inba mutin yatakaba mezetsaidashi anan? Wani gefe naxuciyarshi yabashi amsa, ya salam shine abunda yafito daga bakinshi kafin yanufeta cikin sauri ganin tana ƙoƙarin nutsawa acikin ruwan, cikin zafinsu na sojoji yadamƙota tareda ɗagata cak yafita cikin ruwan da ita…sosai take wutsil wutsil daƙafafuwanta tana dukanshi amma besauketaba seda yafita ruwan. Aiko yana ajiyeta takoma zabura zata komawa tana gunjin kuka tanufi Dede hanyar tsakiyar gulbin, Shima cikin azama yaƙara rufamata baya sabida ganin zata hallaka kanta, tana gabda shiga ruwan yamiƙa hannu yariƙeta akuma Dede wannan lokacinne ruwan sukayi wani irin toroƙo suna tsartuwa asama tare jelar kifin maah sekawai ta bayyana gaba ɗayanta…amugun tsorace general aliyu yaja baya yana zaro manyan idanuwanshi, dagashi har captain Jameel dake bayansu yana kallon duk abinda ke faruwa acikin ruwan…itako Isseta wani irin ihun murna ta buga tareda rugawa aguje tana faɗar maaahhh tanufeta…cikin tashin hankali general aliyu daya ƙame wuri ɗaya sabida ganin wannan halittar Afili wadda betaɓa ganiba arayuwarshi se a tv dominshi bema yadda da akwaita azahiriba se yanzu dayaganta, wannan dalilinne yasa tashin hankalinshi yakasa ɓoyuwa, tofa cikin wannan tashin hankalinne yaje taro Isseta gudun kartaje gareta ta hallakata..amma ina yamakaro domin tuni Isseta ta isa gareta harta faɗa jikinta tareda ƙanƙame jelar kifinta domin tayi mata tsawo bazatakaiga jikintaba. itako tashiga shafa kanta tana murmushi cikin farin cikin ganin tsananin soyayyar ta agun ƴartata tana kallonsu general aliyu…seda Taga Isseta tasamu mutsuwa tukunnah takamo hannunta suka fito inda takoma mutun ɗinta gaba ɗaya domin tasamu damar takowa daƙafarta tafito waje.Shidai general aliyu yana’nan aƙame kamar ruwa yacinyeshi sabida mamaki da tsoro ga tsintsar al’ajabi..suna zuwa wurin su maah tayi murmushi tana ƙara riƙe Isseta dake maƙale ajikinta tadubi general aliyu tace “ɗan saurayi miyakawoku wannan wurin har kuka fito daga jirginku? Bakusan wurinnan nada haɗarin gaskeba? Yatambaya tana zuba mishi ido…ajiyar zuciya general aliyu yasauke cikin alamun gaskiya da gaskiya yace “dan Allah kiyi haƙuri wlh jirginne yatsaya munacikin tafiya bamada nufin tsayawa anan sam amma segaya ƙaddara tatsayardamu bayan tsayuwar jirginne brother na yafito domin bayada lpy sekuma sukayi karo da wannan yarinyar shinefa dalilin fitowarmu kuma wlh Allah ƴarki dana riƙa wlh bansan ba mutin bace shiyasa Nazo temakonta Allah shine shaidata banada nufin cutarwa agareta. Yaƙarasa zancen cikin jaddada gaskiyarshi….murmushi maah tayi kana tace “duk nasan wannan itama bayin kanta bane ganitayi kunbi takaina da jirginku shine abunda yatada mata hankali Batasan cewar baku ganni bane saɓanin itadatake ganina, zancen ƴata Kuma dakace bakasan cewar bamutun bace ita tokasani mutunce kamar kai nicedai ba mutinba kamar yadda idonka yagane maka domin ban’isa na ɓoyema wannan ba tinda karigada magani. Ko wannan wurin dakuka tsaya sabida kun bigenine domin maryama ce kawai keda damar shigowa wurinnan tafita lpy sekuma wanda takawo sabida Hakan kukoma jirginku kubar wurinnan domin yanzu jirgin zetashi da izinin Allah.”Wata ajiyar zuciyar General aliyu yaƙara saukewa Yana yiwa Allah godiya da yasa wannan me imanince suka kaɗe da watace datuni tayi watandarsu acikin ruwan nan, cikin jin dad’in karancinta agaresu yace mungode sosai Allah yasaka da alkhairi baramudauko brother na dabashida lpy dan Allah mungode sosai.. murmushi taƙarayi kawai batareda tace komaiba hakama Isseta dake jikinta tinɗazu itama batayi maganaba. shikuwa general aliyu yajuya kenan zetafi yajiyo muryar captain Jameel yana kiranshi daƙarfi muryarshi abirkice. Wani irin tsinkewa zuciyarshi tayi cikin mugun fargaba yanufi wurinsu…duk wannan tashin hankalin dayashiga lokaci ɗaya maah na kallonshi Hakan yasa tabi bayanshi domin Hakan kawai taji yaron yakwanta mata arai….koda suka isa atare general aliyu yaɗago mejo najeeb daketa karkarwa idonshi na kafewa wuri ɗaya, kuka yasaki sosai shida captain Jameel suna jijjigashi suna salati…itako maah ido ta kafeshi dashi kafin tabud’e baki cikin mamakin ganinshi tace NAJEEBULLAH.Abba Asukwane yafaɗa gidan kamar wanda akajefo cikin tashin hankali daruɗani yake kiran mama bintu..bintu..bintu..bintu babuko ƙaƙƙautawa ko sheɗa bayayi…arazane mama bintu tafito daga ɗakinta agigice tana faɗar lpy dai mlm…bata rufe bakintaba sukayi karo dashi abakin ƙofarta ita zata fito shikuwa ze shiga Hakan yasa suka ɗunguma dukkansu suka koma cikin ɗakin domin zefi nashi sirri tinda ba itakaɗaice matarshiba…..suna shiga matan gidan dake tsaye tsirma’tsirma suka shiga tsegumi domin tun lokacinda mlm Musa yashigo gidan yana famar kiran mama bintu suka bayyana wajen kamar waƴanda aka kirawo…sukuwa suna shiga ciki mama bintu tace “wai mlm lafiya kakemun wannan kiranne? Ko anga maryama ne? “Humm ajiyar zuciyar mlm Musa yasauke tareda koma share guminda yawankemai fuska na babu adadi kana yace “inafa lafiya bintu tabbas naɗebo ruwan dafa kaina. “Innalillahi mikuma yafaru wanzu? Tatambaya cikin fargaba…gumindai yaƙara sharewa still kana yashiga Bata labarin abunda yafaru afadar megari tindaga farko harƙarshe….aitinda yafara magana mama bintu tafaɗi gwajab aƙasa taredayin zaman ƴanbori taɗora duka hannayenta aka tana faɗar “shikenan mlm kagama damu wlh kagama damu domin gara ɓatan maryama so dubu da wannan auren da’aka ɗaura yanzu mikakeso muce mlm? Kuma ma ina zamuga maryama? Innalillahi wa’inna ilaihiraji’un wlh mlm allura nashirin tono galma idan bamu meda hankalinmuba domin wlh inaga garin tone’tonen kaza tanashirin tono wuƙar yankata. “Cikin faɗa mlm Musa yace “haba bintu kiyimuna fatan alkhairi mana tayaya zakizo kina muna mugun fata sokikiye asirinmu yagama tonuwa dukka gari asan abunda yafaru? Kekanki kinsan matan gidannan sabida sunsan sune silar faruwar komai yasa suka rufe ɓatan maryama badan da Hakananba dayanzu sun fallasa kowa yaji, yaƙarasa zancen yana ficewa daga ɗakin domin jiyakeyi kalaman mama bintu nagabda buga mishi zuciya…da kallo mama bintu tabishi harya ɓacewa ganinta aranta tace wai naɗiyar tabarmar kunya dahauka.NigerTinbayan fitarsu mejo najeeb wannan dattijon yake zaune wuri ɗaya yakasa samun cikakkiyar nutsuwa babu abinda ake karo mishi se fuskar yaron gabaki ɗaya tinaninshi yabirkice cikin ƙaƙanin lokaci yalula wani dogon tinanin nadaban kusan awa ɗaya beta ɓuka komaiba ƙarshe dai dayaga babu abinda ze iya sabida wannan tinanin daya gallabi rayuwarshi kawai seya tattara komai ya kira P.A yarufe office d’in shikuwa yafito inda Scott ɗinshi ke zaman jiran fitowarshi, aikuwa suna ganinshi suka miƙe cikin sauri aka buɗe mishi motar yashiga kana suka cillata akwalta tareda ɗaukar hanyar gida.GombeArazane general aliyu da captain Jameel suka kalleta jin ta ambaci sunan mejo najeeb kafin aliyu yabud’e baki danufinyin magana tayi saurin dakatar dashi kana taduƙa kusan najeeb ɗin sekuma tamiƙe tsaye tareda yin wata irin sufa daganan inda take tsayen se acikin ruwa….!

Back to top button