Gargadar So Chapter 28 By M Shakur
Baccin ma dataso tayi batayishi ba yaki zuwa, wajajen 4 ta tashi ta chanza kaya zuwa abaya tadauki car key tafito Baba na zaune a tsakar gida yana wanke kaji shi kadai gaban pampo ganinta yasa yace “ina zaki ya jikin”? Ahankali tace “bari nadan sayo magani Baba” da dan damuwa ya gyadamata kai yace “toh shikenan kije karki jima” gyadamai kai tayi tafice shiga mota tayi ta tada tawuce gidansu Ni’ima babu wani nisa sosai daga layinsu shiga layin tayi har zuwa gaban gidan tai parking tafito tashiga da sallamanta, Mama na zaune a tsakar gida tana gyara wake itada yar makotansu da aka aiko yaranta duka sunyi aure yar aikin ta kuma ta aiketa tana ganin Hawwa tai dan murmushi tace “ahh yau su Hawwa ne agidan” shigowa ciki Hawwa tayi cike da girmamawa tace “Mama ina yini” murmushi Mama tayi tace “lafiya lau ya kike Hawwa yasu wajen Baban naki” ahankali Hawwa tace “lpy lau” tazauna awajen tai shiru takasa magana kaman wata marainiya, Mama ta kalleta sosai tabata tausayi dan tausayi duktai wani iri, yarinyar dake zaune Mama ta kalla tace “tafi Husna ki gaida Mamanki kice mata zan shigo anjima” tashi yarinyar tayi tafita, Mama ta kalli Hawwa tace “sabida Ni’ima kikazo ko?” Gyadamata kai Hawwa tayi, Mama tasauke ijiyan zuciya tace “Hawwa dagake har Ni’ima ba yara bane, tariga ta sanar dani komi dake faruwa, she’s just trying to protect her home so I think is best idan kinyi respecting decision nata and give her space datake so, idan tanaso kudawo da kawancen zata nemeki, don’t blame her rayuwa yazama abin tsoro, sai ana sara ana duban bakin gatari fa, kibarta and move on ba dole Hawwa, tunda abu yakai ga haka kifita daga rayuwanta kinji” sosai Hawwa ke kallon Mama dake maganan irin ko ajikinta dinnan, wani iri Hawwa taji hawaye na taruwaa idanunta, Mama tace “kidena nacin nan dan Allah antaba kawance dole? Yo amintan dole ne? Idan kuma kin nace sai kinyi to kema Hawwa ki yarda da mijin da Baba yamiki mana Malam Kabiru kiyi auren kowama yahuta kinayi nasan Ni’ima zata dawo gareki, kinji kiyi tunani akan abinda na fadamiki” Hawwa takarayin shiru zaune awajen akasan simenti, Mama tace “tashi to kitafi” ko motsi Hawwa takasa yi, Mama ta tabe baki tace “Allah kyauta, tashi kije dan Allah nima kada ki sake zuwan gida, wacce ta hadamu tace batayi, kowa nasa yasani aduniyan nan ba’a kuma dole, just don’t take it personal, Ni’ima is protecting her space ibada take, a musulunce miji yafi kawa sau dubu ko nine mijina zan zaba bawata kawaba ana zaune lafiya, yanda kikeda wayau da ilimin nan ko kece a situation din Ni’ima haka zakiyi wlh put yourself in her shoe, y’ata ta samu gidan hutu yo idan kawa zata mata summun bukumun basai aja mata layi ba kowa yayi takansa? Kingani saida safe bari nahadama Malam abincin dare” tawuce kitchen abinta, Hawwa kawai tafashe da kuka da kyar ta dafa bango ta mike bayanta har yanzu ciwo yakemata fita tayi ta shiga motanta, taja ahankali tabar unguwan takoma gida.Baba bayanan but tana shiga dakinta taga ya ijiye mata kula zama tayi ahankali tabude kulan kaza ce ta soyu ansaka kulikuli da yaji gasu cabbage, tana ganin girkin tasan Baba yadafa mata dama yace dayana saurayi yayi sana’an balangu da su gasassun kaji, hannu takai ahankali tadauki daya takai bakinta daidai nan Baba yayi sallama ya shigo yana rikeda leda ganinta zaune gaban kulan yasa yayi murmushi yace “yauwa Hawwa gashinan naje bakin hanya na sayomiki chivita na grape mai sanyi, ranan nan na dandanashi yamin dadi zakiso shi”Yazo yazauna kusada ita yana ijiye karafunan a gefe lumshe idanu Hawwa tayi jin Baba ya zauna kusada ita tabude su tana ganin yanda duk yadamu yana bude mata juice din, this is the first time takejinta so vulnerable she’s tired of being a strong girl, komima na duniya yamata ahankali tadaura kanta jikin hannun Baba gently tasaka hannunta takama hannunshi ta kankame sosai a kirjinta tafashe da kuka mai tsuma zuciya, bala’in tashi hankalin Baba yayi dasauri yajuyo yace “Hawwa, ke, Hawwana? Me akamiki mesa kike kuka haka? Hawwa” sheshekan kuka take jikinta har rawa yake tarike Baba sosai takasa magana dasauri Baba yadago kanta saikuma yajuyo da kyau idanunshi sunyi jaa yace “zonan Hawwa zo” yajawota yasata a kirjinshi tai hugging Baba so tight this is abinda bata tabayiba hugging Baba saidai maybe datana yarinya, bayanta Baba yashiga bubbugawa yace “ya isa Hawwa ya isa, zakisa hankalina yatashi, koma menene ke damunki baifi karfin Allah ba, ya isa Jiddalo na, ya isa, yi shiru yi hakuri kinji, kinada matsala awajen aikinki ne?” Girgixamai kai tayi alamun a’a tana tsagaita kukan tana sauke ijiyan zuciya ba kakkautawa a kirjin Baba, ahankali yace “to menene ke damunki”? Murya chan kasa tace “Baba aure nakeso nayi nagaji da yanda kowa keyi dani sabida banyi aureba” ahankali Baba na buga bayanta yace “karki damu zaki aure, anmini kwatancen wani Malami na Islamic chemist ranan asabar tunda ba aiki zan kaiki muje muji ko aljanu gareki dake hanaki aure, kokice baki sonsu kosu sugudu zamuji dalili kidena damun kanki namiki alkawari bazan kara takura miki ba, lafiyanki yafi komi mahimmanci agareni Hawwa na, kiyakuri kinji yarinyana yar albarka kiyakuri da rayuwa, komi tsari ne na ubangiji kizama mai juriya da hakuri akwai Allah Hauwa’u kinji” gyadamai kai Hawwa tayi, Baba yayi shiru chan yadago ta daga jikinshi yace “zafin jikinki ya baci kinsha magani kuwa?” Gyadamai kai tayi ahankali Baba yace “to zai sauka, sha lemon kici naman bari naje masallaci, kada kuma kisake kuka kinajina” gyadamai kai tayi yadafa gadonta yana mikewa daukan crutches din tayi tabashi ya karba yafice tabishi da kallo saikuma ta kalli abincin bata iyaci, wayanta ne yahau ringing da mugun sauri takai hannunta ta dauki wayan Ammi tagani a screen sanyi jikinta yayi tadauki wayan Ammi ma sake kwantar mata da hankali tayi sun sade suna waya ahaka bacci yayi gaba da ita koda Baba yadawo ganin tayi bacci yawuce yana jawo mata kofa duk ya damu ganin bataci abinci ba. <This message was edited>


