Hausa novels

Halysaah Page 168 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 168…Ajay yace “A bar ta dai Kanon tayi kwana biyu tukun Hajja” Hajja tace “Sam hakan ba me yiwuwa bane, dama yanxu Jawwad ke ce min uwarsa na kano, zuwa anjima zan sa ayi min kiran Mai martaba in ce ya kirata ya sanar mata taje gidansu Jiddah ta daukota ta dawo da ita masarauta tayi jinyar jinjirin cikin jikinta, idan ya so daga nan sai a tura Hajiya Sumayyah ta tafi Kanon ta sameta su je gidan iyayen Jiddan tare su taho da ita” Ajay yace “To ai bata da lafıyan da zata iya bin hanya yanxu” Nenne tace “Babu jirgi ne daga kanon zuwa Bauchi? Idan ma ba a samu jirgi ba su bi jirgin Abuja kawai, daga Abujan su biyo jirgin da zai dawo garin nan ba shikenan ba” Ajay dai kallonta kawai yake, tace “Ai da kayi shawara da mu bazaka fara barin ta a gida wai don bata da lafıya ba, haka kawai baza ka yanke hukunci kanka tsaye kamar baka da mafada ba, balle a irin babban gidan nan da komai ke da ka’ida kuma bama wasa da al’ada, you are making it look as though we are not capable of looking after her, this is big slap to the Emirate as a whole” Ajay bai sake ce mata komai ba, kamar tasan tunanin dake ransa tace “Idan ma kana fargaban zamanta gidan sarki ne sai a sauketa a nan ga dakuna nan sai wanda na zaba za a ajiyeta, za kuma ta zauna babu takura, sannan ga masu aiki da za su kula da ita kwarai da gaske, nima kuma zan saka mata ido sosai….” Ajay felt that is okay for him, amma bai san yanda za a kwashe da Nenne ba tunda ta nemi alfarman ya bar masu Khaleesat har ta ji sauki ya kuma amince mata, yanxu kuma gashi za a aika daga masarauta aje a daukota, Hajja tace “Kayi shiru? Ko tsarin nawa bai maka bane kafi son a bar ta can masarauta?” Ya daga ido ya kalleta yace “Bai fi tayi sati biyu fa a Kanon, bayan sati biyun ba sai aje a taho da ita ba” Hajja ta hade rai tace “To bamu lamunta da hakan ba, kuma bamu amince ba, zan je har gidan sarki da kaina in sanar masa ya aika mutane su je su taho da ita, yaushe aka haifeka da har zaka canza mana tsarin gidan sarauta?” Ajay ya tabe baki ya mike ya koma kan kujera yace “To ki je ki daukota da kanki mana” Hajja zata yi magana Hadiyah ta shigo parlon da sallama, sai baza kamshi take ga make up ta sha a fuska, cire gyalenta tayi da takalma, ta jefa jakan hannunta kan kujera tana yatsine fuska tace “Shegen driver din nan kullum idan na fita sai na dinga kiransa ya zo ya daukeni kamar bai san aikinsa ba, dama amfaninsa ba ya zauna ya jirani ko awa nawa zan yi ba ya dauko ni? Gaskiya canza min shi za ayi bazan iya surutu ba” Hajja na kallonta tace “Na dai raba ki da fita ki kai dare haka da aurenki Hadiyah, me yasa baki jin maganata ne? Kuma kina ganin kirana kika ki dauka” Hadiyah ta dan kalli Ajay, da kamar bazata ce komai ba sai kuma kamar dole tace “Ina wuni” Ba tare da ya kalleta ba a takaice yace “Lafiya” Fita tayi daga parlon zata tafi dakinta, Ajay ya kalli Hajja yace “Yanxu da auren kike bari tana fita har ta kai dare Hajja?” Hajja tayi kasa da murya tace “To ya zan mata tunda tana son fita Junaid? kuma naga babu inda take zuwa sai wajen cousin sisters dinta sai wasu kawayenta dake garin nan, ai ba nisa take yi ba, kuma kai fisabilillahi baza ka ma dan uwanka magana ya ajiye wannan tsinannen fushin nasa ba yarinyar nan ta koma dakinta haka nan, duk an zuba masa ido an rasa me yi masa magana a kaf masarauta, yan uba sai murna da hakan suke tunda ba wai suna son ci gaban mu bane, ni sai naga ma kamar sarki tsoron Jawwad yake, to banda haka na ce yayi masa magana ya kai sau uku sai dai Sarki yace za ayi masa abu ya doshi sati uku yanxu, shi yanxu Mai martaba yafı son yanda Hadiyar ke zaune gabana kenan? wannan abun kunya har ina?” Ajay yace “Ke me ya hanaki yi ma Jawwad din magana?” Hajja tace “Sau nawa kuma? Na masa magana yayi sau goma in ma bai fi ba, har kiransa nayi a waya wallahi, yanxu ma da yaya na samu ya taho gidan nan? Tun safe nake kiransa ya baro Kanon nan ina son ganinsa, Ni ban ma san kuna tare a Kanon ba, wajen karfe biyar na sake kiransa daxu bayan kun dawo sai ce min yayi shi ya gaji bazai iya zuwa ba, na cire rai kawai sai gashi kamar an jefosa, tuni nayi ta kiran yarinyar nan ta dawo kar yaga bata nan amma taki daga wayata, ya shigo kenan sai ga ka” Ajay yace “Ni dai nasan daga ke har ita sai Allah ya kama ku, tunda da aurenta kike supporting dinta ta fita gantali har da kai wa dare” Hajja ta hade rai tana kallonsa tace “Ni kake gaya ma wannan magana Junaid?” Ya mike yace “Ai ke dama baki son gaskiya, hanyar gaskiya daban hanyar da kika bi daban, yarinya na misbehaving har yanxu shi ne ake son ta koma dakinta ba a dau hanyar seta mata zama ba” Hajja tace “Kaga fita ka ban waje kar raina ya baci Junaid, uwar me tayi da za a seta mata zama, akwai macen da take perfect dari bisa dari a dakinta ne dama?” Ajay yace “Oho dai, zaman da take a gida ne bai isheku ba shi yasa kike ganin she is not suppose to be perfect….. Yana kai wa nan ya fice daga parlon, Hajja tace “Munafukan banza kawai, dama ai duk bakin ku daya kai da Jawwad din gantalallu, kuma idan Jawwad bazai dena wannan kuturun zuciyar ba zai yi ta samun matsala ne a rayuwarsa, a haka za a basa rikon masarauta mutum baya kauda kai akan abubuwa komai sai ya hau dokin fushi, kai ba gashi kana zaune da matarka lafıya ba babu me jin kanku duk shakiyancin da ta dinga yi maka bayan aure me yasa baka korata gidansu ba ita da take ba er kowa ba ma, akan idona na sha ganin yanda take nuna kai ba zabinta bane tana wasu abubuwa marasa kan gado amma haka ka hakura baka taba kai ma kowa kararta ba….” Mikewa Hajja tayi ta fita zuwa Main parlor cikin bacin rai, tana kallon Jay dake zaune dinning tace “Dama ashe zuga ķa ake shi yasa ka bar min yarinya kamar wata mara galihu a gabana har yanxu?” Ajay dai na zaune parlon yana kallon TV bayan yayi changing channel zuwa na football, Jay yaki ce ma Hajja komai, sai ga Hadiyah ta shigo parlon tana wani yatsine yatsine tace “Da galihuna wallahi Hajja, kar ma kice an bar ni a nan kamar mara galihu, da gatana kaca kaca, banda kaddara ma ni me zai sa in auri wanda uwarsa ke controlling duk abinda zai yi a gidansa, hatta kudinsa ita ke controlling kamar wani karamin yaro, shi yasa ake kin biya min bukata ta….” Jay ya daga kai ya kalleta yace “Kee, Watch ur tongue” Ta masa wani kallon banza tace “To karya nayi? Ba baabarka bace ke controlling din ka? Ko zaka hanani fadin gaskiya ne, da ta hanaka zama da ni ai sai ta jika ka ta shanye mu ga” Mikewa yayi yace “To ki je na sake ki, sannan duk wani abu da yake naki a bangarena ku kwashe su kar in sa a fitar min da su Daga haka ya figi wayoyinsa ya nufi hanyar fita daga parlon, ba Hajja da Hadiyah ba har Ajay dake zaune parlon sai da yayi shock, Hajja ta fashe da kuka jiki na rawa tace “Ko dai Jawwad ya fara hauka ne? Ko dai shaye shaye yake? Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, me ya samu Jawwad haka” Ajay ya mike ya bi bayansa yana kiran sa, har ya isa compound Ajay ya cim masa, ya fixgosa yace “Are you on ur right senses Jay? Sakinta fa kayi?” Jay yace “Eh sakinta nayi, in kuma zaka hada da ita ne ga ka ga ta ai….” Ajay ya dinga kallonsa babu ko kiftawa, barin sa yayi wajen a tsaye ya nufi motarsa ya shiga within seconds yayi zoom off daga gidan. Wajen karfe goma da rabi na dare Ajay na zaune parlon Mai martaba ta dalilin kiransa da Sarki yayi, shi kadai ne zaune parlon yana jiran fitowar sarki daga parlornsa na ciki, Jay ne ya shigo parlon suna hada ido da Ajay ya sauke idonśa har ya karaso cikin parlon ya zauna, shi dai Ajay inda yake kallo daban a parlon, after some minutes Jay yace “I apologize for my outburst earlier this night Junaid” Without looking at him Ajay yace “It’s fine” Babu wanda ya sake cewa komai a parlon sai ga Sarki ya fito, kusan a tare suka mike, har ya karaso cikin parlon ya zauna sannan suka zauna, Ajay ya fara yi masa barka da dare sannan Jay ma yayi haka, Sarki ya amsa, after a while yace “Akwai abinda ke damunka ne Jawwad that you are not telling us? Tell me what ur problem is” Jay ya sauke kansa kasa a hankali yace “Allah ya huci zuciyar Mai martaba, babu abinda yake damuna, a gafarce ni….” Sarki yayi shiru yana kallonsa, can ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace “Wa yace maka ana saki a gidan nan? Me yasa zaka yi creating room na kananun zance a masarautar nan?” Jay yace “Tuba nake Mai martaba” Sarki yace “Tun maganar nan bai fita ba ka maida Hadiyah dakinta, na san tayi learning lessons dinta yanxu dai Jay yayi shiru at first, sai kuma a hankali yace “A gafarce ni ranka shi dade, amma….” Kasa ci gaba yayi, Sarki yace “Amma me?” Yayi kasa da murya yace “Ina son a bani lokaci Mai martaba, bana son ya kasance ba da son raina na maidata ba tursasa ni aka yi nayi hakan…. Sarki dai kallonsa kawai yake, sam baya son forcing Jawwad on anything yanxu, duk abinda yake so in dai bai saba addini ba ya dau alwashin barin sa yayi abun nan without hindrance, Sarki ya sauke ajiyar zuciya yace “Take ur time, but ka duba zumunci Jawwad, kar ka mance Hadiyah er uwarka ce ta kusa, it’s a big slap to this Emirate ace maganar abin nan da ya faru ya fita….” Jay dai bai ce komai ba kansa a kasa, Sarki yace “Sai ka toshe kunnen ka da duk wani magana da zai biyo baya most especially from ur Grandmother” Jay ya gyada masa kai kawai don shi kam sai dai su masa duk abinda za su yi babu niyyar maida Hadiyah a zuciyarsa, dama last week Mai martaba yace masa zai je Nijar to check on his new company, yana zuwa kasar zamansa zai yi a can har sai ta fita iddah sannan ya dawo, Mai martaba ya kalli Ajay yace “Jeeddah kuma gobe za aje daukota a dawo da ita gidan nan, don mun yi maganar hakan da Hajja, Allah ubangiji ya bata lafıya” Ajay ya sauke idonsa yayi shiru, Walid ne ya shigo parlon da sallama, ya zauna kasan carpet ya gaida Mai martaba, Sarki ya amsa sannan ya kalli Jay yace “Da Walid za ku tafi Nijar sati me zuwa, kafin nan ina son kai da Junaid za ku fara zuwa Calabar….. Ko numfasawa Sarki bai yi ba Walid yayi saurin gyara zama yace “Zan bi su can din ma ranka shi dade, ai yanxu duk wani harkar kasuwanci ina son a dinga yi da ni saboda in samu experience ta yanda zan tafiyar da wanda zaka dora ni a kai smoothly Ajay ya daga kai ya kalli Walid, Walid ya jefa masa wani kallon tsana ya murtuke fuska, Mai martaba yace “You have a point Walid, sai ka shirya ka bi su ku je gaba daya….. Dan murmushi Walid yayi, sai kuma yayi ma Sarki sai da safe ya mike ya fita daga parlon yana murmushi…. Aunty na kallon Walid dake zaune dakinta tayi kasa da murya tace “To ni ka ki gaya min menene shirin naka Walid, wallahi ina fargaban kar a kamaka duk da nasan you are very wise, amma Junaid is brave and smart gashi da shi kace za ayi tafiyar, kar ya zargeka shi ne damuwata….” Walid yayi wani murmushi yace “Momy ni fa ba sabon abu bane wannan a wajena, ko kin taba jin an zargeni ko kuma an kama ni akan wani laifı makamancin haka? Ai sai dai kawai ace an kamani da kwaya, kuma ba wai bana manyan lefukan bane amma nasan move dina don da kwararru nake aiki, Ba ruwana da wani dan iskan Junaid can, na yi farin cikin da za aje Calaban nan don hanyar nan ne dai dai wajen aiwatar da duk abinda mutum ke so Aunty tayi tagumi tayi shiru, can tace “Ko dai kawai a kirkiro wani abu da zai hana tafiyar nan da Junaid, don gaskiya tsoron yaron nan nake” Da sauri Walid yace “A’a ba wani a hanasa tafiya Momy, dole ma da shi za aje ne, ki kwantar da hankalinki na fa san ta kan aikina” A hankali Aunty tace “To shikenan, ka ji kuma ya saki Hadiyar ma daxu ko? Tun fa da aka nadasa Yariman nan yake wani ji da kansa ya dau girman kai da iskanci ya dora ma kansa a gidan nan, baya saurara ma kowa, har gwara Junaid yanxu a kansa, don munafurci uwarsa ta tattara ta bar gidan dama munafurcin ne yasa ta dawo take zaman gidan ai, i can’t wait all this to come to an end wallahi, idan na fara lissafo maka kamfanonin Mahaifinku wanda Jawwad ke jagoranta a kasar nan sai kayi mamaki, wasu ma ban san su ba sai dai a kawo min tsegumi, ku da ubanku amma duk yayi kane kane kan abinda ku ya kamata a dora a kai, ga dukiyar ubansa da ya mutu ya bar masa shi da uwarsa suna yanda suka so suna facaka da shi sai zuba uban investment suke basa shawara da kowa, ace kuma Mai martaba shima idan ya tashi sai ya dorasa kan nasa dukiyoyin saboda neman suna da son a sani, kai da Junaid da kuke ‘ya yansa kuma ko oho” Walid na huci yace “Wai yaushe kika fara tsaya ma wannan shegen Junaid din ne komai kice ni da Junaid, meye hadinmu da shi ne? Ko kin mance abinda yayi min ne ko gama warkewa ban yi ba?” Aunty tace “Ban manta ba Walid, amma a yanxu kam Jawwad ne babban kalubalen gabanmu ba Junaid ba, Junaid din da ba wani damuwa da shi da lamarinsa ake yi ba a masarautar nan kana gani saboda rashin gata kwace title dinsa aka yi babu wanda ya iya convincing sarki ya maida masa har ita Hajja, sai kace ba dan sa ba, ai Jawwad ne babban challenge dinmu a yanxu” Walid ya mike yana tabe baki yace “Ke kike ganin haka” Daga haka ya nufi kofa yace “Ni zan je mu ci gaba da shirin da muke da mutane na” Aunty tace “To kayi ta addu’a dai Walid, nima zan dinga taya ka a nan, Allah yasa komai ya tafi yanda aka tsara Walid yayi wani murmushi kawai ya fita daga dakin a ransa yace “You don’t know nothing Mom” Har ya kagu ranan da za su yi tafiyar nan ya iso, this is a day he have been waiting for, kusan wata daya da sati biyu kenan yake neman privilege irin wannan sai gashi ya samu cikin ruwan sanyi… Da safe Hajja ta taho masarauta da kanta don ko baccin kirki bata yi ba daren jiya saboda bakin ciki, haka ma Hadiyah da ta kwana tana kuka, tun a jiya Hajja ta sa Ummi ta kira Mami ta gaggaya mata bakaken maganganu masu zafı, bayan sarki yaje har parlonta ya gaisheta tace “Yusuf zuwa nayi inji yanda aka kwana da yaron nan Jawwad, ya maida auren ko bai maida ba har yanxu?” Sarki yayi shiru, can ya kwantar da murya yace “Mun yi magana da shi Hajja, kuma zai maidata in sha Allah” A fusace Hajja tace “Ohh ba umartarsa kayi ba kenan dama Yusuf? Ni da na kira na sanar maka abinda ke faruwa dama ce maka nayi ka zaunar da shi ku yi wata magana da ta wuce kayi masa umarnin maida auren nan cikin gaggawa ba tare da kowa yaji ba?” Sarki ya dan yi murmushi yace “Hajja, ki kwantar da hankalin ki, zai yi hakan in sha Allahu Hajja tace “Allah wadaran Aseeyah, Allah ya kwashe mata, in sha Allahu sai taga irin karshen da zata yi, dai dai da rana daya ban taba takurata ba a sanda uban Jawwad ke da rai suke zaman auren, shi ne a yanxu zata takura jikata ta hanata zaman aure saboda son zuciya, to wallahi koran kare zan mata duk ranan da tayi kuskuren dawowa gidan nan, sannan in ma ka kirata akan taje gidansu Jiddah to maza ka kirata ka gaya mata ba a bukata, don har nayi waya a Kano za aje da motoci gidansu Jiddah a daukota, mu da muke da alfarma ta ko ina a kasar nan” Shi dai Mai martaba yayi shiru yana ta sauraron Hajja…. A fusace Nenne ta shiga dakin Umma tana cewa “A kira min Junaidun ta waya, haka muka yi da shi? Rimi rimi mu yi magana ya amince sai kuma daga baya su turo motoci har uku a dau Khaleesat sai kace har mu za a kwashe? to a kai ta ina tana fama da jikinta, haka suke a masarautar tasu dama?” Mikewa Aunty Farida tayi ta fita daga dakin, Umma tayi kasa da murya tace “Nenne don Allah tunda suka aiko kiyi hakuri kawai ki bari ta tafi” Nenne tace “To da mu da su sai mu ga wa yafi iko da ita, ni da na haifi ubanta Ali nace bazata bi su ba maganata kuma tamkar ta Ali ce” Umma tayi shiru bata sake cewa komai ba a dakin, Aunty Farida na fita dama dakin Nenne ta tafi, tana kallon Khaleesat dake kwance tayi kasa da murya tace “To Nenne na shigowa yanxu ki bude baki da kanki ki ce mata zaki bi dangin mijinki da suka zo daukar ki, ko zaman me zaki mana a nan bayan duk abinda za mu yi maki a can ma mijinki zai maki?” Khaleesat tayi shiru, don ko Aunty Farida bata gaya mata haka ba dama jira take Nenne ta shigo ta gaya mata ita zata bi su, don taji gaba daya zaman gidan ya isheta ta rasa dalili, ji take kamar akan kaya take a gidan tun daga jiya har yau, Aunty Farida na fita Nenne ta shigo dakin tana huci tace “Mu za a gaya ma sarauta, bayan kakana nima yayi Sarkin pawa….” Mikewa zaune Khaleesat tayi tana kallon Nenne, sai kuma tayi kasa da kai a hankali tace “Ni zan bi su Nenne, ai can din ma zai kula da ni….” Nenne ta saki baki tana kallonta babu ko kiftawa.

Back to top button