Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 104 By Ayshercool

104Miƙewa Nabila ta yi tsaye, tana tunanin kamar ba ta ji sosai ba.”Wane irin wasan banza ne haka sumayya take yi mini?” Tayi maganar tana mamaki.Wayar Sumayyan ta hau kira, amma wayarta a kashe, jikinta na rawa ta fito falo, amma ta tarar kowa ya kwanta, ko ina a rufe.Ta koma ta hau kiran Umman Sumayya, amma ita ma ta ta wayar a kashe.Ta saka wa zuciyarta zolaya ce kawai Sumayya take yi mata, dan tun da aka yi musu lallae take cewa tayi kyau kamar ranar tarewa a gidan Viper.Sai dai wannan ya wuce wasa, ta rasa meyakamata tayi, ta din ga fatan Allah ya sa mafarki ne ba gaske ba.Gaba ɗaya ta kasa bacci, sai dai yadda ta kasa baccin nan, haka Nasir ya kasa, da yayi juyi ya kalli invitation ɗin auren Nabila, sai gabansa yayi wata irin mummunar faɗuwa, cike da baƙin ciki da damuwa.Ya so Nabila tun tana ‘yar ƙarama, tun tana yawo ba riga, ba ta san ciwon kanta ba, yana matuƙar tausayinta, yana taya major ƙaunarta, saboda maraicinta, ga rashin lafiya ga kuma ƙiyayyar da mutanen gida suke yi mata.Wahalarta babu wadda bai sha ba, kaita makaranta, yawon visiting kaita Asibiti idan Major baya nan, duk wata gudunmawa da ya san zai iya bayarwa domin ta ji daɗi yana yin su.Duk rashin jin ta da karaɗinta baya damunsa, babban burnsa ya ganta tana cikin faranciki, mussaman idan yayi la’akari da hadisan Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, da suka yi magana a kan kula da maraya, idan ya tuna mamanta ta rasu, ba ta san waye babanta ba, sai matsanancin tausayinsa ya ƙara shigarta.Bayan Major ba ta da wasu da yadda da su take ƙaunar su, sama da shi da Sumayya, koma Yaya Nasir ko Sumayya, duk wata wauta da taɓara da zata yi, baya gajiya, da hakan matsanancin son ta ya shiga ransa, sai dai mama ta riga tayi masa kandagarki da Allah ya isa a kan Nabila, tsawon lokacin nan baya iya kula kowacce mace, saboda Nabila, sai dai duk wannan son da yake yi mata, lokaci ɗaya kuɗi suka rufe masa ido, ya tafka mummunan kuskuren da ya rushe waccan kyakkyawar alaƙar da take tsakaninsu, har ta kai tana yi masa kallon maƙiyinta a yanzu.Da Asuba Viper ya nufo Kano, Abbu ya kira shi a waya, suka gaisa ya ce “Ka taho ɗin ne, zaka halarci ɗaurin auren?””Eh in sha Allah Abbu, ai ina hanya ma, na biyo sojoji mun taho””Akwai kuɗi a wurinka ne?”Viper ya ce “Eh, amma kamar nawa?”Abbu ya ce “Dubu ɗari biyu””Eh ba za a rasa ba””To da ka dawo ka taho gida da kuɗin, ina son ganinka””To in sha Allah, ina nan tafe””Allah ya kawo mini kai lafiya”Viper ya yi murmushi ya ajiye wayar.Sai dai babu daɗewa Walid ma ya kira shi, ya ɗaga ya ce “Mazaje ya ne?”Walid ya ce “Mai zamani””Mai laya?””Za ka zo ɗaurin auren yayar Nabila ne?””Eh in sha Allah”Walid ya ce “To ka yi sauri””Me zaka bani, ba sai bayan juma’a ne ɗaurin auren ba?””Eh kawai dai ka yi sauri”Viper ya ce “To aiko mini da fuka-fukai na tashi sama”Walid ya yi dariya ya ce “To in dai zaka yi sauri ai shikenan”*****Wayewar garin Allah, Ana idar da sallar asuba, Nabila ta tafi ɗakin Abba, ta tarar bai ma dawo daga masallaci ba, ta samu wuri ta zauna tana jiran dawowarsa.Yana yin sallama ta tashi tsaye, ta ce “Abba, ina kwana?””Lafiya ƙalau, kin tashi lafiya?””Abba ni fa ban yi bacci ba, Sumayya ce ta yi mini wani wasan banza da ya ɗaga mini hankali, wallahi ido biyu na kwana cikin zullumi da fargaba, na zata mafarki ne ma zan farka, amma dai na ga gaske ne”Ya zauna yana faɗin “Subhanallah, wane irin wasa ne haka, da ya hana barrister bacci?””Ɗaurin auren hafsa ta sanar, kuma sai na ji ta faɗi sunana da na Viper, wai za a ɗaura mana aure”Major ya ce “Ikon Allah, kuma kin kira wayarta?”Ta ce “N kirata wayar a kashe, na kira ta Umma ma, amma ba ta shiga duka”Abba ya jinjina kai ya ce “Abin da mamaki gaskiya, bai kamata ta yi miki wannan wasan ba gaskiya, amma ki je ki samu ki yi bacci, na san da wasa take yi miki, wurin ƙarfe goma sai ki shirya ki tafi can gidan naku wurin bikin, na ji Antynki da su Magajiya duk suma za su je”Ta ce “To Abba” sai ta ji ƙwarin gwiwa, ta je ta nemi wuri ta kwanta, sai ta samu bacci ya ɗauke ta.Tana farkawa, Sumayya ta fara kira, wayar ta shiga amma Sumayya taƙi ɗagawa, hakan ya ƙara fusata ta.Ta fita kitchen, tana gaya wa baba magajiya abin da tayi mata cike da takaici.Baba magajiya ta ce “Kun fi kusa, ina fatan Allah ya tabattar mana da alkhairi””Ba amin ba, ba da shi ba alkhairin”Baba magajiya ta ce “Au zaki ga ba da shi ba, ni dai ina yin sa, duk da ya ce kar na gaya miki, ranar da suka zo, dubu goma ya bani, ya ce na sha lemo, a samarinki waye ya taɓa saurarata”A shagwaɓe ta ce “Ni fa ba saurayina ba ne ba””Oho miki dai, ni dai Allah ya zaɓa abin da ya fi alkhairi”Nabila ba ta sake cewa komai ba, ta hau bubbuɗe kwanuka, ta buɗe fridge ta ɗauki gasarar alkama, ta dama kunu da ita, ta ɗebi doya ta dafa ta ɗebi miya ta koma ɗaki.Ta fara karyawa, ta shiga facebook, saboda tana buɗe data, notifications suka din ga shigowa ba ƙaƙƙautawa.Ai tana shiga da invitation ɗin ta fara cin karo, ana ta yi mata Allah ya sanya alkhairi, ba ta san lokacin da ture kofin kunun ba, ta tashi da sauri, har tana tuntuɓe, ta shiga ɗakin major tana zazzare ido.Ta tarar da shi tare da telansa, ta ce “Abba ka ga fa” tayi maganar tana haska masa fuskar wayarta.Ya sallami telan sannan ya ce “Zauna mu yi magana”Ta zauna jikinta yana tsumar rashin sanin abin yi.”Nabilatul arfa, tun da mahaifiyarki ta rasu ta bar mini ke, nake kula da ke cikin ikon Allah, tamkar ita nake kallo, ban taɓa yi miki wani abu da zai cutar da ratuwarki ba. Kuma na daɗe ina baki dama na aikata duk abin da ki ke so, muddin ba gani nayi zai cutar da ke ba, babu irin ƙalubale da bamu fuskanta ba daga ni har ke, amma na toshe kunnuwana, domin ganin kin rayu cikin farin ciki da jin daɗi.Wannan hukuncin mahaifinki ne ya yanke shi, duk yadda na kai ga nuna miki so da ƙauna, ya fi ni iko da ke, ko da a gaban shari’a ne, na ce ya bani dama na tattauna da ke a kan yaron nan, ya bani amma ki ka nuna ke fafur ba kya son sa.Kafin na amince da maganar Al’amin, na yi bincike a kansa fiye da yadda ki ke tunani, wurin aikinsa, wurin mahaifinsa, duk wani motsi na rashin jin sa sai da aka bani labari. Na zauna da abokansa, sun bani labarin yadda ki ka shiga rayuwar sa, da duk abin da ki ka din ga yi, rayuwarsa da yar uwakki, wanda shi kansa bai sani ba.Irin rayuwar da ya yi da ‘yar uwakki, duk na bincika, gefe guda babansa na ta bi na yana yi mini magiyar a shawo kanki, Allah ma’aiki kar ya koma rayuwarsa ta baya.Honorable Mu’azzam Wada kankarofi, shi ma bai ɓoye mini komai ba, shi ya ƙara ƙarfafa lallai ayi auren nan, zaku zauna yana sonki kina sonsa, ke kuma naga gaba ɗaya shirme ne a kanki da wauta, dan haka muka yanke wannan hukunci.Sumayya ba wasa ta faɗa ba, katin aurenki ne, kuma ina fatan zaki yi mana biyayya baki ɗaya”Ƙurawa Abba ido ta yi, ji take kamar almara, kawai kuma ta fashe da kuka “Abba ka fa ce ba zaka yi mini auren dole ba, haba Abba””Wannan ai ba na dolen bane ba””Haba Abba, na dole ne mana, ba sai an tambayi mutum yana so ko ba ya so ba, kuma ka tambayeni na ce a’a kawai kuma sai a ɗaura”Ya ce “Eh gaskiya ne, ban kyauta ba, za’a kai ƙarata kenan, na taɓa masu shari’a”Yanayin yadda yayi maganar ya sanya ta gane zolayarta ma yake yi, bai ɗauki hakan serious ba. Hakan ya saka ta ƙara sautin kukanta har da sheshsheƙa.Abba ya ce “Maza yi ta yi, in dai kukan banza ne, dama tun kina zanin goyo halinki ne, idan ki ka isheni kuma, na zane miki jikinki””Abba ba na son shi fa, gaba ɗaya baya so na, ai an baka labarinsa da Jauhar, ya ce duk duniya itakaɗai ce mace, ba fa ya so na ko kaɗan, Wannan auren dole ne Abba””To Arfa a kaini gaban me Shari’a a tuhume ni da laifin child abuse, na yi wa barrister auren dole, amma sai ki haɗa da ni da ubanki duk ki kaimu ƙara. Kai waye a nan wurin ku kira mini magajiya ta zo ta ɗauki yarinyar nan daga gabana, kafin na casata a wurin nan”Ƙarshe ya tashi ya bar ta a wurin, tana ta gursheƙen kuka, kamar an sanar da ita mutuwar tsohuwarta.****Ƙarfe sha ɗaya Viper ya shiga gida, Abbu ya ce “Dama tuntuni kai nake jira, ka ƙaraso mu karya”Viper ya yi murmushi, yana jin daɗin tattalin nan da Abbun yake yi masa.Ya ce “Abbu ya su Walid kuma?”Abbu ya ce “Yaran kirki, Abdallah babansa ya kai shi kasuwa, wurin sayar da sarƙoƙi da kayan shafe-shafen mata, ya ce a kama masa shago, idan ya gane kan harkar sosai, yaƙi zama muna tare da shi a kasuwarmu, wai shi ba ɗan daudu ba, me zai yi da wani kayan shafe-shafen mata. Na daɗe ban ga rigimammen mutum kamarsa ba, yanzu haka ma suna kasuwa ne kayanmu zasu iso, daga nan za su yi mini wani aiki, da yanzu ka gansu a nan. Na je gida mun yi magana da mahaifinsa na ce yayi haƙuri ya ƙyale shi, tun da ga in da hankalinsa ya karkata”.Viper ya ce “Liti akwai rigima, wanda bai san halinsa ba ba zai iya zama da shi ba”Abbu ya ce “Ai naga alama, akwai barkwanci””Idan yana yin mutum kena ba, amma ga wanda bai san shi ba, goga ne, a lokacin muna mazaje, muna ji da rashin ji, ya fi Walid karsashi, ‘yan daba idan sun kai goma, zai ratsasu shikaɗai ba ya tsoro ba kuma ya san wargi”Abbu ya rausayar da kai ya ce “Na so ace tuntuni na farga, na ja ku a jiki ku duka, da kai ɗin da su, na riƙe ku na kula da iliminku, na kaiku kasuwa, da yanzu Allah kaɗai ya san me zaku zama, su waɗanda nake kallon su ne shiryayyun na ɗauki ɗawainiyar su, gashi a ƙarshe ba wanda ya more su, na yarda da ɗa da dukiya ba a yi musu mugunta, yanzu gashi ku ɗin da ake kallon marasa ji, yanzu al’umma sun fara amfanar ku, ba zan manta da honorable wada kankarofi ba, bawan Allahn nan ɗan halak ne, gashi ka zama soja kana aikinka, Allah ya ƙara dafa muku”Viper ya ce “Amin”Abbu ya ce “Amma ya aka yi ka ke da kuɗi tsakiyar wata, ai ni da na ce ka taho da 200k da idan ka ce babu, zan ƙara nuna maka amfanin haɗa kasuwanci da aiki ne, an ce albashin naku, ba shi da yawa”.Viper ya yi wata irin dariya ya ce “Ko a cikin sojoji, irin aikinmu na musamman ne, kuma mai hatsarin gaske, ina da salary mai kyau, zan zaɓi garin da nake so a bani gida, kuma za a bani abin hawa, ba a buƙatar rashin gskiya ko a samu irinmu da halin cin amanar ƙasa, idan aka kama mu da haka, babu shari’a kisan kai ne kawai. Shiyasa irinmu a sojoji ba su da yawa ko kaɗan”Cikin mamaki Abbu ya ce “Wai bayan fitowar ka har ka yi training ɗin ko kuwa? Kuma wane iri ne aikin naku a sojoji?””Ina gaya maka kashe ni za ayi, ba a faɗa kawai dai ka saka a zuciyarka ɗanka soja ne, mai muhimmancin gaske ga ƙasarsa, kuma a kowane lokaci zaka iya rasa shi, dan haka ka yi mini addu’a kawai”Abbu ya ce “In sha Allah sai ka yi retire da kanka daga aiki, ba za a kashe ka ba” haka Abbu ya din ga jan sa da hira, har lokacin salla ya ƙarato.Abbu ya ɗaukko masa sababin kayan kar, dark blue ɗin shadda, riga da wando, da hula. Ga sabon agogo da takalmi.Ya ce “Wannan fa?”Abbu ya ce “Wurin ɗaurin aure zamu je, ba na son yawon da ku ke yi da ƙanan kayan nan, kamar ba yaran hausawa ba, dan haka su zaka saka”Shafa kayan ya yi, yana tuna abar ƙaunarsa, Jauhar, a lokacin da ta bashi kyautar kaya ranar sallar idin ƙaramar salla.Su Walid ne suka yi sallama a waje, Abbu ya ce ace su shigo, suka shigo sanye da fararen kaya, liti ya riƙo hularsa a hannu.Abbu ya ce “Abdallah, ya ka cire hular ka ga yadda ka yi kyau a cikin kayan kuwa?”Ya ce “Abbu, hular ce ta ɗame mini ƙeya nake ta gumi shi ne na cire””Ai fa rashin sabo ne””Mai zamani, Abbu ne fa ya ɗinka mana kaya” liti yayi maganar yana nuna masa kayan jikinsa.Walid ya ce “Mai zamani haka ka ke kyakykyawa, rabon da ka yi kyau kamar haka, tun ranar aurenka da marigayyiya”Abbu ya gyarawa Walid zaman tasa hular, ya ce “Yauwwa ko ku fa ‘yan samari, Allah ya nuna mini aurenku duka” suka kasa cewa Amin.Wani farinciki ne ya mamaye zuciyar Viper, ganin yadda Abbu yake nuna wa su Liti ƙauna, wanda ya san duk dan saboda shi ne, shi yanzu a duniya abin da zaka yi masa, ka saka shi farinciki, ka so mutanen nan uku kamar yadda yake ƙaunar su, ya san a duniya ba shi da abin biyansu.Haka suka ɗinguma a mota, suka tafi masallaci, domin yin salla da halartar ɗaurin Alhaji mu’azzam.A sahu ɗaya suka yi salla da Alhaji mu’zzam, suna ta yi masa Allah ya sanya alkhairi.Bayan an idar da salla, babban abin da ya ba wa Viper mamaki, bai wuce ganin abokan Abbu da yawa a wurin ba, da kuma wasu daga cikin ‘yan uwansa, bai kawo komai a ransa ba, suka gaggaisa, suna taya shi murnar wanke shi da kotu tayi, wasu kuma na zuzuta kyan da yayi, wasu kuma suna yi masa Allah ya sanya alkhairi, shi dai duk bai gane kan abin ba, ana ta ɗaura aure, aka zo kan na Alhaji mu’azzam, aka ɗaura aurensa da Hafsa.Bayan an kammala na su, aka nemi waliyayyan Al’amin, saroro yayi yana kallonsu, ganin Baba yana kallonsa yana murmushi, haka Major.Ya waiwaya, har da su doctor Muktar, da Abdul yasar a wurin.Sai da aka ɗaura aurensa da Nabila, sannan ya fuskanci abin da yake faruwa.Walid ya cire hular Viper, ya shafa kansa ya ce “Angon Nabila ka sha ƙamshi, yau dai Allah ya yi Allah ya sanya alkhairi”Yayi saroro yana kallonsu, liti ya ce “Mun iya Suprise ko? Sai ka bamu tukuci yasin, idan ka cire kayan nan ni zaka bawa, in saka ranar auren Walidi, ko Allah ya sakani a damshinku””Mai laya yaushe aka shirya wannan abin, ita Nabilan ta amince ne?”Liti ya ce “Oho muku, mu dai an haɗa kai da mu, an ƙulla sunnar ma’aiki, ai yanzu rumfar shayi har da banner dalilin aure zan saka. Idan aka biye muku, wahalar da mu kawai zaku yi ta yi, yanzu sai ku ƙarata ku sasanta kanku”Aka fito daga masallaci, Viper sai jin sa yake tamkar ba shi ba, abin kamar almara.Alhaji mu’azzam ya ƙarasa ya miƙa wa Viper hannu ya ce “Na haƙura na janye, na kuma yarda Jauhar taka ce, Nabila ma taka ce, ba a takara da kai Viper, duk da ka fuskanci ƙalubalen rayuwa da yawa, amma ina da yaƙinin Allah yana sonka, yadda yake tafiyar da lamuran rayuwarka. Ina yi maka fatan alkhairi, Allah ya baku zaman lafiya mai ɗorewa”Viper ya riƙe hannun Alhaji mu’azzam, amma ya kasa magana sam.Major ma zagayo wa yayi, ya dafa kafaɗar Viper, ya ce “Yadda na samu labarin ka riƙe Jauhar amana, dan Allah ga ‘yar uwatta nan ma, Allah shi ya san dalilin da ya sanya ya karɓi jauhar a lokacin da ka ke matsanancin son ta, ya musanya maka da ‘yar uwatta, wataƙila da bai ɗauke Jauhar ba, babu yadda za ayi Nabila ta ga mahaifinta, komai sila ne, kuma duk abin da Allah ya yi dai-dai ne, ba a tambayarsa dan me? Allah ya baku zaman lafiya”Viper ya risunar da kai ya ce “In sha Allah Abba, na gode sosai”Abbu ma ƙarasowa yayi, ya ce “Al’amin, a karo na biyu na sake nema maka auren ‘ya, kuma Alhaji Bashir ya sake bamu, a rana mai kamar irin ta yau aka ɗaura maka aure da jauhar, yau ba ta raye, an sake ɗaura maka aure da Nabila, dan Allah Al’amin ka riƙe musu ‘ya da mutunci da amana”Kawai ya fara zubar da hawaye, duk da yayi iya ƙoƙarin sa wurin mayar da hawayen, amma abu ya gagara, kawai ya lumshe idanunsa ya basu damar su zuba.Major ne ya ce “Ya haka kuma? Amare ke kuka ba angwaye ba, dan Allah kar ka bayar da mazaje mana, soja ne fa kai”.Jiki a sanyaye Walid ya ce “Ai a duk lokacin da za ayi wani abu da zai tuna masa da Jauhar duk taurin zuciyar sa da ƙarfin halinsa sai ya yi kuka, haryanzu ya kasa jurewa, duk yadda za a bayar da labarin yadda suka rayu, idan ba wanda ya gani ba ba zai gane ba”Major ya ja shi ya bashi handkerchief ɗin sa, yana duddukan kafaɗarsa yana rarrashinsa, Abbu ya ce “Al’amin dole fa ka yi haƙuri, kayi haƙuri, duk lokacin da ka tuna Jauhar ka yi mata addu’a. Sannan dole ka koyi danne zuciyarka, idan ba haka ba, zaka iya sanya wa Nabila kishin ‘yar uwatta, zuciya ba ta da ƙashi”.Kallonsu kawai yake yi, idan ya ce ba ya murna da farincikin wannan auren, ƙarya yake yi, amma zuciyarsa ta tsinke, da yaga yana sake ɗaura wani auren, Jauhar ɗin sa ba ta duniya, a lokacin da yake tare da ita, gani yake duk wani leƙe-leƙe da ake faɗa na namiji a kan mace, itakaɗai ta ishe shi rayuwa.Suka kewaye shi suna ta rarrashin sa, abin da ya ƙara yi masa daɗi da sanya shi farinciki, bai wuce yadda shi da ake ƙyama a da, amma aka tara wannan mutanen saboda shi, kuma duk suka kewaye shi, kowa yana ƙoƙarin rarashin sa, lallai babu abin da ya fi zama mutum na gari.Alhaji mu’azzam ya ce “Ko sai mun dangana da wurin amaryar za ta rarrashe shi? Dan naga tafi kowa iya shawo kansa”Major ya ce “A’a bar amaryar nan, ka san ba ta san da bikin ba sai jiya da sumayya ta sanar da daddare, can na baro ta a falo tana kuka, fushi ma take da ni, ina ga ranar Litinin za a kawo mini sammaci daga kotu, na taɓa masu ƙasa na yi wa barrister auren dole, amma na gaya mata ni da kai zata kama, tun da tare muka yi laifin” yayi maganar yana nuna Alhaji Bashir .Suka yi dariya baki ɗaya. Duk da a ƙurarren lokaci Sumayya ta sanar da ɗaurin auren Nabila, Auren ya samu hakarta ɗaruruwan jama’a, manya da ƙananan mutane, mussaman waɗanda suke supporting ayyukanta, har da wakilai daga gidan gwamnati, manyan lauyoyi da baristoci, har da kwamishinan shari’a, da alƙalin alƙalai na jiha. Da yawa saura kwana biyu uku suka samu invitation ɗin, kuma an halarta sosai da sosai.Ba ƙaramin daɗ Major ya ji ba, ganin irin jama’ar da Nabila ta tara, a ransa yayi mata addu’a Allah ya sa yadda ta riƙe gaskiya a kan aikinta, da ta tara wannan jama’ar, Allah ya sa ranar mutuwarta ta tara fiye da haka.Shi kansa Babanta ya yi farinciki, mussman yadda ake ta yabonta, da jinjinawa yadda ta zamo matashiyar yarinya, mara tsoro da jajircewa a aiki.Nabila kuwa har Abba ya tashi ya shiga bedroom ɗin sa, yayi wankansa ya shirya tafiya ɗaurin aure, tana bayan kujera a zaune tana kuka.Gaba ɗaya shi dariya ma take bashi, dan haryanzu kallon yarinya ƙarama sosai yake yi wa Nabila.Baba magajiya ta je tana rangaɗa mata guɗa a ka, amma tana guɗa Nabila ranta na ƙara ɓaci, baba magajiya har da rawa, da yi mata waƙoƙin amare irin na da.Nabila ta koma ɗakinta, sai ga kiran Sumayya, ta ɗaga wayar, Sumayya ta kwashe da dariya tana amarya ba kya laifi.”Da ke aka haɗa baki aka yi mini haka ko Sumayya, ki je kanki ki ka yi wa” Sumayya dariya har da tuntsurawa ta san a rina, rigima da daru, za a sha su akan abin da aka yi wa Nabila.****Maman ramma kuwa ta tattara ramma da Abdul ta saka musu ido, dan ta fara jin nauyin sa, irin yadda yake hidima da rammar, a da tayi zaton ƙoƙarin sayeta yake son yi da abin duniya, amma sai taga ba haka ba, zunzurutun soyayyar kawai yake yi wa ramman.Yau daga wurin ɗaurin auren Viper, gidansu ramman ya wuce.Tsayawa ramma tayi tana ƙare masa kallo ta ce “Ka ga yadda ka yi kyau kuwa?””Daga wurin ɗaurin auren yayanki nake”Ramma ta ce “Haka mama take gaya mini, ai shekaranjiya babansa ya zo, ya daɗe a gidan nan suna hira da mama, yake gaya mata halin da ake ciki, yau za a ɗaura musu aure, amma daga ita har shi ba wanda ya sani, na ce ikon Allah kamar film””Wallahi rahama ya bani tausayi, kin san duk wannan muzuran da yake yi, da shan ƙamshi, amma ya din ga kuka a wurin ɗaurin auren nan, kamar yaro ƙarami, wai ashe wadda ta rasun ya tuna, wallahi sai da na yi masa kuka, muktar ya ce mini duk yadda nake sonki, da nuna miki kulawa, ba zai kai kwatantkwacin son da yake yi mata ba, da na tuna mahaifina ne sila, wallahi sai na rasa in da zan saka raina. Ya ma yi ƙoƙari yake ɗan iya kula ni a ‘yan kwanakin nan, dan hau har gaisawa muka yi”Ramma ta ce “Yaya zamu yi, ai ƙaddara ta rigayi fata sai addu’a”Sai da aka yi sati guda, sannan Alhaji mu’azzam tare da hafsa suka ɗaga zuwa babban birnin tarayya Abuja.Gidan Hafsat na Abuja mai kyawun gaske, ya fi wanda ta zauna da ita da uwargidansa a can Kano, sai dai taƙi sakin jiki da shi.Jirgin yamma suka bi, gefin magariba suka sauka.Da ya ɗan matsa kusa da ita, sai ta maze ta matsa tana haɗe rai, dan haka ya rabu da ita.Da daddare da kyar ta yadda ta ci abinci, shi ma ba da yawa ba.Ya riƙo hannunta zata ƙwace, ya riƙe gam, ya ce “Haba hafsatuna, ni ne fa, ki yi haƙuri dan Allah, ki bani dama na gyara kuskuren da nayi miki a baya, Please” tayi shiru, ba ta ce masa komai ba, saboda ta kasa manta mummunan halin da ta faɗa a wancan karon a dalilin aurensa.Da kyar ya lallaɓata, kamar budurwar da ba ta san komai ba, sai dai a wannan karon ita kanta ta san da banbanci, dan a wacan karon, banda tsabar kayan tsubbu, da abubuwan da ba ta san ko na menene ba, da su aka yi mata gyaran jikinta.A wannan karon kuwa, ta san da banbanci, domin kuwa maman dr. Ta kankarota ta kankaro martabarta a idon mijinta, dan a wancan karon ko maganin sanyi ba ta yi amfani da shi ba, sai kayan tsubbu da abubuwan da ƙawaye suka din ga ba ta shawara a kai.Shi kansa yadda ya yi appreciating ɗin ta a wannan karon, ya sha bamban da lokacin da tana budurwa.(07069711327 ga masu buƙatar kayanta, su na iya tuntuɓarta kai tsaye, she’s always available for you)*****Viper kuwa kimanin sati biyu kenan, tun da Allah ya sa aka ɗaura aurensa da Nabil, babu wanda ya nemi wani daga shi har ita, kuma hakan ya ɓatawa kowannensu rai.Abba ya sanar mata, da babu ita babu yawo, idan ba wurin aiki ba, dole sai da izinin Al’amin.Rashin kiranta da bai yi a waya ba, ya tabbatar mata da sam ba ya ƙaunarta, auren dolen ne dai kawai, shi ma ya nemi ya aureta ne kawai saboda mafitarsa.Kasancewar hidimar bikinsa, tare da na Walid za a haɗa, ya sanya yayi delay na komawa aiki, domin sanin shirye-shirye da yakamata yayi.Yana son ya tambayeta, abin da take buƙata na harkar biki, amma ya shareta.Ta koma wurin aikinta, ana ta yi mata Allah ya sanya alkhairi, aka din ga tambayarta meyasa ba ta tafi hutu ba, ta ce ɗaurin aure aka yi, ba ayi biki ba.Aka din ga bata gudunmuwar biki, ta in da ta zata, da in da ba ta ma zata ba.Kawai tana zaune a office taga alert ɗin dubu ɗari biyar, da sunan Al’amin da komai.Sai a lokacin ta kira wayarsa, ya ɗaga amma yayi shiru.”Naga ka turo mini kuɗi””Ki fara sayen abin da ki ke buƙata na lefe, zan sake turo wasu, na san wannan ba za su isa ba”.”Ni bana so” ta faɗa a daƙile.”Menene ba kya son?””Kuɗin, ni ka bani account number na dawo maka da su”Wani malolon takaici ya ƙule masa zuciya ya ce “Bani da lokacinki, ki same ni a gidan su rahama, sai ki dawo mini da kuɗin” ya kashe wayarsa.Ba tare da tunanin komai ba, ta miƙe ta fara harhaɗa kayanta.Da ta isa gidan su ramam, Maman ramma ta ce “Amarya ke da kanki, ina ta cewa Aminun ya zo ya kai ni gidanku, amma haryanzu shiru”Nabila ta ce “Dama baya nan? cewa fa yayi na zo na same shi a nan””A’a ya dai ce zai zo, amma bai ƙaraso ba tukuna” yanayin fuskar Nabila da ta gani babu fara’a, ya sanya ta din ga yi mata nasiha, tayi haƙuri ta rungumi mijinta su zauna lafiya kamar yadda yar uwatta tayi.Ita kuwa Nabila gani take, ba zasu gane ba, ba su san waye Al’amin bane.Ita a tata wautar, da gaske zuwa ta yi ta mayar masa da kuɗinsa, sam bai iya rarrashi ba, ba ta san tarko ya yi mata ba.Awanta guda a gidan, ya zo, kuma yaƙi shigowa cikin falon, ya ce ta je ta same shi a sitting room ɗin harabar gidan.Ta tashi ta ce “Mama ina zuwa” ta fita ta ƙarasa ɗakin.Sai dai tana arba da shi, duk wannan fitsarar da take ji da ita, ta nemeta ta rasa, sai tsoro da fargaba da suka mamayeta. Lallai miji yafi gaban wasa.Ya ɗago ya kalleta, doguwar riga ce a jikinta, sai mayafin rigar. Gaba ɗaya Nabila ba ta da wayo, ko kaɗan, abin da ba ta sani ba, ba wai dawo masa da kuɗi ne ya kawota ba, son ganinsa ne ya kawo ta, ba tare da ta yi lissafin hakan ba.Ya kawar da kansa ya ci gaba da danna wayarsa.”Ka bani account number ɗinka, na mayar maka da kuɗinka, ni bana buƙatar komai daga wurnka, ba zaka taɓa iya bani abin da nake so ba”.Ramma ta yi sallama da ƙaton faranti, shaƙe da kayan abinci, ta gaida Al’amin ya amsa, ta kalli Nabila da ke tsaye ta haɗe rai, ba ta ce komai ba ta fita.Ta fara ƙosawa da tsayuwar da take yi, ya miƙa mata hannunsa, ba tare da ya Kalle ta ba ya ce, “Bani wayarki na saka miki account number ki dawo mini da kuɗina” babu musu ta ƙarasa ta miƙa wayar, ya yi amfani da hakan, ya janyota jikinsa.Wata ƙaramar ƙara ta saki, jikinta ya hau tsuma, ta kalli fuskarsa, babu alamar wasa a tattare da shi, wani irin kallo yake yi mata da ba ta san a yaya zata fassara shi ba.

Ayshercool 08081012143

Back to top button