Hausa novels

Halysaah Page 150 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 150…Bangaren Mami Jay ya nufa yana tafiya kamar wanda bai son tafiyar, ya bude kofar parlon yana kallon ciki, Mami dake zaune cikin parlon ta daga kai tana kallonsa, ya karasa ciki ya zauna kan kujera kansa a kasa, Mami dai sai kallonsa take cause he doesn’t look okay, A hankali ya gaisheta, Mami ta sauke idonta daga kallonsa tace “Lafiya lau, ya jikin nakw?” Yare “Na ji sauki” Mami tace “Ina son zan je wajen Mai martaba na jirana yanxu, sai dai zuwa anjima idan na dawo” Noor ce ta shigo Parlon da sallama tana rike da warmer din zogale da Mami ta bata ta kai ma Hajja, warmer biyu Mami ta bata daya na Hajja, daya na Khaleesat sai gashi ta dawo da na Hajja, ta duka kusa da Mami tace “Wai Hajja tace ita ta koshi bazata ci ba” Mami tayi shiru tana kallon warmer din, don tasan Zogale is among Hajja’s favourite, bata taba yi mata tace bazata ci ba sai yau, Mami tace “To shikenan, ki kai kitchen ki ajiye” Noor ta daga kai ta gaida Jay da ya maida dubansa kan TV, har ta mike ta tafi zata kai Warmer din kitchen bai amsa gaisuwar ba kamar dai bai ji ba, sai da ta shiga kitchen Mami tace “Jawwad gaisheka fa tayi?” Bai kalli Mami ba a takaice yace “Ban ji ba” Mami dai kallonsa kawal take babu ko kiftawa, after few seconds yace “Mai aikin ki ta tafi ne?” Mami tace “Me zata maka?” Yace “Mai martaba ke kiran Junaid, in tana nan ki aiketa ta sanar masa” Mami tace “Ita Mai martaba ya aika kenan?” Jay yayi shiru bai ce komal ba, a hankali Mami tace “Yaushe ka zama haka Jawwad?” Jay ya kalli Mami jin abinda tace, Mami tace “Sarki ya aike ka shine zaka zo aikan wani? is this proper?” Jay dai bai ce komal ba ya sauke idonsa kasa, Mami bata sake ce masa komal ba saboda Noor da ta fito daga kitchen, Noor tace “Mami zan koma can” Mami tace “Baza ki kwana nan ba Noor?” Dan murmushi tayi tana wasa da hijab dinta tayi shiru, Mami dake ta Kallonta tace “To shikenan, ki tafi sal da safe” Noor ta gyada mata kal tara “Nanorda” Mana haka ta luva ta fita lana……..kofar parlonsa bayan tafiyar Yakumbo da ta zo sanar masa sakon da Jay ya bata na cewar Mai martaba na kiransa, mamakin dalilin kiran ya dinga yi, haka dai ya juya ya koma cikin parlonsa still pondering on why the king sent for him, after some minutes ya fito ya nufi sashin sarki cikin rashin kuzari, rabon shi da zuwa side din sarki tun ranan da yayi prohibiting dinsa from doing so, yana kusa da part din Sarki ya ga Jay tsaye ya jingina da bango yana danna wayarsa, Ajay ya dauke idonsa har ya wucesa, sal da ya dan yi nisa yayi noticing Jay na biye da shi a baya from a reasonable distance. Ajay ya shiga parlon Mai martaba kansa a kasa, walking slowly ya tafi ya zauna favourite position dinsa a Parlon ya kasa hada ido da Sarki, sal ga Jay ma ya shigo shi ma ya tafi ya zauna inda ya saba zama, Cikin ladabi Ajay ya gaida Mai martaba har sannan bal dago kansa ba… Mai martaba yayi shiru na wani dan lokaci yana kallonsu kafin yace “Ina son kowannen ku ya fada min dalilin gaban da yake yi da dan uwansa, starting from you Junaid” Ajay was quiet bayan yaji abinda Mai martaba yace, bai taba zaton maganar da Mai martaba zaiushbai yi zaton dalilin kiran Mai martaba kenan ba, Sarki dai kallonsu kawal yake patiently yana jiran amsan tambayar da yayi masu, Bayan few seconds Ajay ya dago da kyar ya kalli Mai martaba cikin calm voice yace “Allah ya kara maka lafiya, ni ba gaba nake yi da shi ba” Sarki ya gyada kai sannan ya kalli Jay yace “Kai kuma fa Jawwad?” Jay ya girgiza kai yace “Ba gaba nake yi da shi ba ranka shi dade” Sarki yace “Ohk, space ku ka ba juna kenan?” Kusan a tare suka gyada masa kai, Mai martaba yace “Good, starting from you Junaid, Ina sauraron dalilin space din da ka basa” Ajay ya kasa cewa komal at first, ganin kallonsa sarki yake yana jiran amsa, yayi kasa da murya yace “Naga yana ignoring dina ne shi yasa i decided give him space Sarki yace “How did you understand he is ignoring you?” Ajay ya sauke idonsa a hankali yace “He doesn’t want to speak to me tun bayan da ka daura mana aure da Jeeddah, May be he is thinking ni ne na bukaci a daura mana aure da ita, fun daga wannan lokacin yake avoiding dina, I tried speaking to him twice yana ignoring dina” Mai martaba yayi shiru bayan yaji abinda Ajay yace, can ya kalli Jay yace “Jawwad meye dalilin ka na ignoring dinsa, or let me put it this way, why are giving him space?” Jay ya kasa cewa komal kansa a kasa, hawaye ya ji ya kawo idonsa ya kai hannu yana share hawayen, Ajay dake kallonsa ya sauke idanuwansa a hankali, Mai martaba dai sai kallon Jay yake babu ko kiftawa, Jay ya girgiza masa kai kawai don ya kasa…………..hankali yace “Jawwad…” Jay ya daura goshinsa a kan Knee din sarki wasu hawayen na sauka idonsa, sosai jikin Mai martaba yayi sanyi, and he became speechless, ya dinga kallonsa, after almost a minute a hankali Mai martaba ya dafa shoulder dinsa yace “Nayi hurting dinka ko Jawwad?” Jay ya girgiza masa kal har sannan bai cire kansa a Knee dinsa ba, Mai martaba ya daga kai ya kalli Ajay, hawaye ya gani a nasa idon shi ma alamar he couldn’t stand seeing his brother crying, Ajay ya sauke idonsa a hankali, Mai martaba bal taba tunanin things will turn out this way ba, bai taba zaton things will get to this extent ba, abinda ya kara masa kwarin gwiwan aura ma Ajay Khaleesat bayan abubuwan da Mami ta dinga yi duk a zatonsa Jay was only covering for Ajay at the beginning don ya saba ya dauki laifin Ajay ya dora ma kansa komin girman laifin, tun suna yara haka suke, ya kuma yi la’akari da cewar duk zuwan da yayi America bai taba ganin Jay tare da Khaleesat ba sai dai Ajay, har cikin dakinsa da baya barin kowa ya shigar masa ya ga Khaleesat a kwance, Mai martaba ya sauke ido yana kallon Jay calmly yace “Gaya min yanda kake son ayi Jawwad….. Feel free and tell me what you want, ka gaya min abinda ke zuciyar ka, I ask for it” Jay ya girgiza masa kai har sannan bai dago kansa ba cikin breaking voice yace “Ina neman alfarman ka bari in koma UK in samu aiki a can ranka shi dade, i will prefer staying there, bana son zaman gidan nan kuma” Sarki ya dinga kallonsa jin abinda………gathering muen courage ya kaili Mai martaba yace “in ka yarje min ranka shi dade ni zan İya sakin Jeeddah, i know it’s taking him long to heal saboda ganinmu da yake yi tare, ni kuma i will never chose her over Jawwad, na kuma san ko na saketa ba lallai ya aureta ba, but if she is far away from us duk za mu mance komai, ta haka ne komai zai wuce kamar ba ayi ba” Jay ya daga kal yana kallon Ajay jin abinda yace, Sarki ma kallonsa kawal yake babu ko kiftawa, Mukhtar ne ya shigo parlon da sallama Sarki ya daga kai yana kallonsa ya amsa sallamansa, zaunawa yayi kan Carpet yace “Allah ya taimake ka, tun daxu kayi wasu baki biyu sun ce ka san da zuwan su, suna kuma kiran wayarka basu same ka ba” Mai martaba ya sauke ajiyar zuciya yace “Ehh nasan da zuwansu Mukhtar, wayar tana wancan parion ne…” Mal martaba ya kalli Jay da Ajay a hankali yace “Za mu yi magana da asuba in sha Allah….” Daga haka ya mike ya nufi second parlor dinsa duk jikinsa a sanyaye, sal yanxu ya fahimci kalman da Hajja tayi masa 6 months ago da tace ya bar baya da kura, bal taba yin abu ya dawo yaji da bai yi abun ba sal wannan lokaci, he just realized the harm is more than the good. Har Ajay ya isa part dinsa bai san ya isa ba duk da dishi dishin da ya dinga gani a hanya, ya zauna kan kujera a parlornsa ya dau remote din AC ya kunna don wani irin zafi yake ji a jikinsa, ya dafe kansa da yaji yayi masa nauyi sosal, yafi minti goma a haka yana sauke numfashi a hankali kafin ya a mike mike ya shiga bandakiya………..Mamınsa, Mami na zaune kasan carpet kanta a kasa hawaye na zuba idonta, Hajja kuma na zaune kan kujera a parlon ta inda take shiga ba ta nan take fita ba kamar zata ari baki, Ummi dai na can zaune gefe ta daure fuska sal jefa ma Mami harara take, ga Hadiyah zaune kusa da ita tana matsar kwalla har da shessheka, Hajja na kallon Mami a fusace ta ci gaba da magana don kukan da Hadiyah take kara tafarfasa mata zuciya yake, tace “Ke haka na maki a sanda kike auren da na? Ko kin taba ganin na sa ido a sabgarki da Ahmadu Allah ya kai haske kabarinsa, wani irin mulki ne baki zuba ba a gidan nan Aseeyah na taba ce maki don me? Sai jikata ce zaki sako gaba da tsana da tsangwama ki hanata zaman lafiya ki hanata walwala tare da mijinta? Ko kin mance ni na haifi uwarta? A kanki kadai aka fara haihuwar da dava a………duniya da zaki ce lallai lallai sai kin saka masa ido kin hanasa rawan gaban hantsi da matarsa? To wallahi tun wuri ki shiga hankalinki, banda akwal abinda kika kulla a ranki sau da nawa sau da nawa kike zaman gidan sarki? Ke da sai kiyi wata da watanni baki zauna a gidan nan ba amma saboda mugun nufin ki na saka jikata a gaba shi ne kika tattaro kika dawo masarauta kika tare gaba daya, to kuwa za su bar maki gidan ko kuma su bar maki kasar ma gaba dayan ta” Mami taji wani abu ya tokareta a zuciya banda hawayen bakin ciki babu abinda take yi, wai Hajja ta rasa gaban warce zata mata wannan cin mutuncin sai gaban Hadiyah, bata taba da ta sani irin wannan da take yi ba a kaf rayuwarta, tayi da ta sani babu lyaka, ina ma zata iya maida hannun agogo baya, ina ma ta varda sha…………Da, date kanta tayı nawaye masu zati na zuba iconta, ko ba komal in bata ji dadi ta wajen Hadiyah ba zata ji ta wajen Khaleesat, sosai tayi nadama tayi regretting action dinta gashi ta jefa kanta a damuwa sannan ta jefa dan ta ma a damuwar da ya kasa healing har yanxu, banda ita me zai yi da wata Hadiyah?? babban bakin cikinta yanda Hajja ta sakata gaban Hadiyar da uwarta tana gaggaya mata maganganu marasu dadi wanda duk ba haka bane sharri kawal Hadiyah tayi mata, tun da Hadiyah ta tare a masarautar nan zata iya kirga sau nawa taje bangaren Jay balle ace ta takura su ta hanasu rawan gaban hantsi, bata taba hanasa yi ma Hadiyah komai ba na kyautatawa, wani lokacin ma idan taga wani abu ita ke nuna masa ya siya mata, ita kanta ta sha siya mata duk wani abu da tasan na gyaran mace ne, bata taba yi ma Hadiyah ko da kallon banza ba tun da ta tare a bangaren Jay, kwatsam rana daya Hadiyah ta dena gaisheta a gidan ko kuma in ta ganta sai tayi maza ta canza hanya, sai dai ta tafi can wajensu Hajiya A’isha ko ta tafi bangaren Aunty, idan kuwa ta kira Jay ko tana bukatar yayi mata wani abu sai Hadiyah ta daga tace yana bacci ko kuma tayi ta saka mata kiran a busy,…………sakayyan, Jay da yayi tsaye bakin kofa duk yana jin abinda Hajja ke cewa Mami ya karasa cikin parlon yace “Hajja akan Hadiyah zaki sa Mamina a gaba kina duk wa ennan maganganun?” Hajja tace “An sa ta gaban, ita haka nayi mata? Da haka nayi mata ai da bata kai war haka a gidan nan ba, ita ba abun kunya bane ace ta hana er kanwar marigayi zaman lafiya a gidan mijinta?” Mami ta daga kai da kyar tana kallon Jay hawaye na zuba idonta tace “Kayi tafiyarka kawai Jawwad” Juyawa Jay yayi ya fice daga parlon, Ummi tace “To ai ba iya wannan ba Hajja, ta yaya zata dinga fifita bare akan Hadiyah a gidan nan? Kullum bata da aiki sai dora ma Hadiyah laifi duk ta bata ta wajen Mai martaba” Hajja tace “Wacece bare?” A fusace Ummi tace “Matar Junaid mana….” Hajja tace “A’a ba bare bace, kar ki sake ce mata bare a gidan nan, tunda har jikana ke aurenta to babu ta yanda ta zama bare Maimuna, kawai dai don ta cusa ma Hadiyah bakin ciki take yin haka, whereas ita bakin cikin zai kashe don babu yanda zata yi da auren Hadiyah da Jawwad….” Hajja na kai wa nan ta mike tana cewa “Ke ba a tsangwame ki ba duk mulki da isan da kika zuba a gidan nan shi ne zaki takura jikata, akan wani dalili? To wannan na daga cikin dalilin zuwana garin nan, babu wanda zai taba min jikoki in kyale” Tana kai wa nan ta nufi kofa Hadiyah ta mike ta bi bayanta da sauri suka fita tare, Ummi ta tabe baki ko kallon Mami bata yi ba ta mike ta bi bayan uwarta da er ta, Mami ta hi to do ballo bouque Juho idants hoto toho………….sillyu wa zuill Sund bangarenta ta shiga dakin da Khaleesat take tare da Noor, zuwa yanxu kam Khaleesat is getting much better, don kula sosai take samu wajen Hajja da Likitan dake dubata sai Mami, Hajja ta zauna kan kujera tana kallon Khaleesat tace “Zuwa gobe sai ki koma can bangaren mijinki ya ci gaba da kula dake ko Jeeddah?” Khaleesat ta sunkuyar da kanta don sai da gabanta ya fadi jin abinda Hajja tace, Hajja ta kalli Noor tace “Kin ci abincin kuwa takwara?” Noor ta gyada mata kai tace “Na ci” Bude kofar dakin aka yi duk suka juya, Hajja taga Hadiyah ce tsaye bakin kofar, ta wani daure fuska bayan ta jefa ma Khaleesat harara tace “Wajen ki na zo Hajja” Mikewa Hajja tayi tace “To mu je” Fita tayi daga dakin bayan sun dawo parlor Hajja ta kalli Hadiyah tace “Ya aka yi?” Kamar zata yi kuka tace “Kina ganin ya kulle kofar part dinsa ina ta kwankwasawa yaki budewa ko Hajja” Da mamaki Hajja tace “Shi Jawwad din?” Hadiyah tace “Wallahi, har kiran wayarsa nayi yaki dagawa” Hajja tayi shiru, can dai ta zauna kan kujera ta dau wayarta tayi dialing number Jay, sal da ya kusa katsewa sannan ya daga, Hajja tace “Jawwad akan wani dalili ka kulle ma Hadiyah kofa?” A takaice yace “Ta bi Baabarta kawal su koma Lagos, sai na neme ta” Hajja ta bude baki jin abinda yace, without waiting for her yace “Sal da safe” Daga haka ya katse wayar davon ya saka sa gaba……matsanancin ciwon kal throughout night din sallah yayi tayi, bal taba jin bai son asuba yayi ba a rayuwarsa kamar yau, gaba daya damuwansa na baya suka dawo masa fresh, he was so restless, ya canza position a dakin yafi a kirga, he needs to speak to anybody that will calm him down amma ya rasa wa, a hankali ya jawo wayarsa yayi dialing number Ammi yana fara ringing ta daga, daga daya bangaren tace “Ahmad….” Sauke idonsa yayi a hankali yace “Ammi” Ammi tace “Hope all is well dear?” Ya kasa ce mata komal, tace “Ahmad” Ya gyada kai da kyar yace “Ina ji Ammi” Tace “Tell me, me ya faru?” Ya rasa ta inda zal fara, har sai da ta kara kiran sunansa, cike da karfin hali ya fara gaya ma Ammi duk abinda ya faru a parlon Sarki jiya da daddare, Ammi was speechless jin maganar kamar ta wasan yara, Ya girgiza kai muryarsa na rawa yace “Amma ina jin kamar bazan iya sakinta ba Ammi, saboda… saboda ina sonta” Yana fadin haka yaji hawaye sun kawo idonsa, da kyar ya ci gaba cikin sanyin murya yace “Wallahi ina sonta Ammi, bazan İya sakinta ba, I don’t know what will become of me idan nace zan rabu da ita, ban san yanda zan yi ba Ammi…” Kasa ci gaba yayi ya hade kansa da gadu, cikin kwantar da murya Ammi tace “Baza ka saketa ba Ahmad, ai ba garin gaba gaba ake ba da za ace ka saketa saboda Jawwad, shi ma Mai martaba nasan bazai bari hakan ta faru ba don wannan babban slap ne to the Emirate as a whole babu inda ake haka to calm tunda ba wasan yara bane abun, i want you to Cam down son, ka kwantar da hankalin ka, Khaleesat will remain ur wife for ever, babu ta yanda za ayi Dethroning dinka a basa title din sannan kuma ace ka saki matarka saboda shi, ko da kuwa bazai aureta ba wannan ba abu bane da hankali zai dauka….” Da sauri Ajay ya daga kansa jin anyi knocking kofar parlonsa, sosai gabansa ya fadi, don yasan kilan Mai martaba ne ya aiko ayi kiransa, da kyar yace “Someone is at the door Ammi, I will call you back” Ammi tace “Ohk I am waiting Dear” katse wayar yayi ya mike cike da karfin hali ya nufi kofar dakinsa ya fita, tsaye yayi bakin kofar yana kallon Jay dake zaune parlon nasa ya tallabi chin dinsa da hannu biyu, Ajay ya sauke idonsa ya karasa cikin parlon cikin sanyi jiki, sai a sannan Jay ya daga kai a hankali ya kallesa, Ajay bai yarda su hada ido ba ya zauna kan kujeran dake facing din Jay dake ta kallonsa.

Back to top button