Hausa novels

Ruwan Zuma Page 44 Hausa Novel

(44) A idon Mas’ud Laila ta fad’i ta suma, cikin sauri ya iso gurinta ya durk’usa yana kiran sunanta. Madu daya biyo bayansu don ya yiwa Laila magana ya zo ya samesu a haka, tare suka cicci6i Laila suka shigar da ita cikin gidan. A falon Ummii suka kwantar da ita, su Ammi na tambayar meya sameta cikin tashin hankali. Ruwa aka yayyafa mata ta farfad’o tana kallon mutane ta fara zubar da hawaye zuciyarta na mata zafi. “Shima ya tafi Ammi, ya gudu kuma ya sakeni.” Ta fad’i hakan tana rufe fuskarta da dukkan hannayenta. Salati Ummii ta saka cikin fargaba tana tambayarta abunda ya faru, kafin ta bada amsa Madu ya fita daga falon kai tsaye kuma ya shiga motarshi ya fita daga gidan gaba d’aya. “Sai ki fad’a musu laifin da kika mishi har ya sakeki Kalti.” Mas’ud ya fad’a cikin sanyin murya don jikinshi ya mutu da yaji Haydar ya saki yayarsa. “Laifin me ta mishi Mas’ud?” Ummii ce tayi tambayar ganin Laila ta kasa bada amsa sai hawaye kawai take yi tana girgiza kai. Ammi kuma tuni ta matsa gefe tana kiran wayar Haydar cikin tsoron abunda zai aikata, addu’a take yi a ranta kar ya gudu ya barta bayan ya gama jin labarin k’azamin rayuwarta. Wa zai so ya gane cewa uwarsa karuwa ce kuma kowa ya sani? “Cikinshi ta zubar saboda wai ta tsufa da haihuwa. Bata ji kunyar kwanciya dashi ba sai kunyar yawo da cikinshi take yi.” Mas’ud ya bawa Ummii amsa kamar ya kaiwa Laila duka. “Waye ya fad’a maka na zubar? Yana jikina ban zubar ba, shi kuma bai tsaya muka yi magana ba balle in fad’a mishi cewa ban aikata ba. Mas’ud ka nemoshi kar yayi nisa don Allah.” Ta fad’i hakan wasu hawayen na sauk’a a k’uncinta. “Ke kika fad’a mishi zaki zubar da cikin?” Ummii ta yiwa Laila tambayar cikin takaici. “Eh amma wallahi daga baya ban iya na aikata ba Ummii.” Laila ta furta cikin tsoron fad’an Ummii don bata so taji labarin ba kwata-kwata. “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un. Laila wani irin zama kike yi da yaron nan? Ina fatan ba ke kika zama mijin a auren naku ba don kinga kin fishi shekaru? Ashe zaki iya bud’e bakinki ki furta mishi zaki zubar da ciki bakya jin tsoron Allah da kuma kunyarsa? Ashe baki da mutunci baki san mutum mai miki halacci ba Laila?” Ummii fad’a take yi ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, Ammi ce kad’ai ta dawo kusa dasu tana bata hak’uri amma hankalinta na kan Haydar wanda ta kira wayarsa taji a kashe take. Mas’ud kuwa tuni ya fice daga gidan neman Haydar tunda yaji abunda Laila ta fad’a. Gidansu ya fara zuwa ya tambayi maigadi ko Haydar yana ciki, maigadi yace masa yanzu ya fita da jakan matafiya bai yi ko minti biyu ba. Cikin tsoro Mas’ud ya isa bakin titi ko zai hango Haydar a hanya amma bai ganshi ba, haka yayi ta yawo a tashoshin mota yana dubawa ko zai ganshi amma bai ga alamarshi ba. K’arshe dole ya hak’ura ya dawo gida jikinshi a sanyaye ya samu Laila da Ummii a falo suna zaune zugum-zugum basa magana. “Ina Ammi?” Shine tambayar daya fara don bai ganta ba. “Tana d’aki tana ta gwada wayar Haydar. D’azu ya turowa Laila sak’on sakinta da yayi sannan yace a bawa mamanshi hak’uri ya tafi kar asha wahalar nemanshi.” Ummii ta bashi amsa tana hararar Laila kamar zata bugeta. “Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun.” Shine abunda Mas’ud ya furta yana jin zuciyarshi na mishi zafi kamar yayi hawaye. Wannan wani irin abu ne yake faruwa a zuriyarsu? Daga wannan ya 6ace sai wannan shima ya 6ace? Meyasa baza su zauna as one big happy family ba? Meyasa suke tunanin 6acewarsu zai magance halin da suke ciki? Meyasa Haydar ya tafi alhali dashi ake k’ok’arin dawo da hankalin Abul gida? Meyasa kullum a kwanan rayuwarsu sai sun had’u da wani tashin hankali? Shima guri ya samu ya zauna ya dubesu yace, “Shikenan shima ya gudu, don nima na nemeshi ban sameshi ba.” Wannan magana yasa Laila tayi dana sanin furta cewa zata zubar da ciki, me amfanin rayuwarta babu Haydar a ciki? Meyasa ma tun farko ta kasa hak’ura ta raini cikinta albarkar aurenta da Haydar? D’aura hannu tayi a cikinta tana jin tausayin kanta da duk abunda yake ciki idan har ya tashi babu uba a kusa dashi. A makeken falon Alhaji Abdul aka yiwa Madu iso ya samu guri ya zauna yana jiran maigidan ya fito. Minti biyar da haka Alhaji Abdul ya fito yana takawa d’ai-d’ai ya zauna a kujera mai fuskantar Madu cikin izza da isa yace, “Ya aka yi?” “Albishir na taho maka dashi Alhaji.” Madu ya fad’a yana washe baki. “Na me kenan?” Alhaji Abdul ya tambaya without any interest. “Yaron nan ya saki Laila sannan an gano mahaifiyarshi ‘yar uwarmu ce data gudu ta bar gida.” Da sauri Alhaji Abdul ya gyara zamanshi cikin tsananin farin ciki yana godewa Allah da wannan kyakkyawan labarin. “Da gaske kake yi?” “Kwarai da gaske, a gabana aka yi komai kuma nayi recording duk abunda ya faru na tura maka.” Ya bashi amsa yana jin kamar yayi abun kwarai. Alhaji Abdul kasa zaune ko tsaye yayi sai safa da marwa yake yi a falon yana fad’in irin farin cikin da yake ciki duk da cewa yasan kafin Laila ta amshi soyayyarsa sai ya jima, amma zai jirata ko da zuwa tsufansu ne. Kyauta mai tsoka ya yiwa Madu kana ya koma cikin d’akinsa inda ya bar matar daya kwana tare da ita a kan gado. Yana shigowa ta farka tayi mik’a sannan ta dubeshi taga yanayin da yake ciki wato na murna. A zatonta duk a dalilinta ne irin bajintar data mishi jiya, hakan yasa tayi k’asa da murya tace, “Baby murnar me kake yi?” Bai ko kalli inda take ba ya zauna kan sofa dake can k’uryar d’akin yace, “Haydar ya saki Laila.” Kana ya fara bud’e wayarsa don nemo wannan recoding d’in da Madu ya turo masa. D’iff annurin fuskarta ta d’auke tana jin mugun kishi a ranta dalilin tsanar Laila da tayi domin ita take son Alhaji Abdul ba Laila ba. A kan son da take yi mishi yasa ta auri Madu yayan Laila don kawai ta juya hankalinshi ya tilastawa k’anwarshi auren Alhaji Abdul duk da cewa a ranta bata so hakan ba. A kanshi ta kasa zaman aurenta ta kuma k’i haihuwa da Madu duk don ko watarana idan ya samu auren Laila zai tausaya mata itama ya aureta. Saboda sonshi da take yi yasa take yawan neman izinin zuwa garinsu gurin mahaifanta na k’arya duk don ta kasance da Alhaji Abdul, wanda yau kwananta biyu kenan tare dashi kuma sati biyu tace zata yi a garin nasu. A kan sonshi ta dinga fad’in k’arya akan Laila duk don ta rasa manema Alhaji Abdul ya aureta kamar yanda suka tsara tun farko. Sai dai a lokacin da Laila tayi aure zuciyar Jamila ta samu salama har tana tunanin zai nemi aurenta, a lokacin kuma taso ta kashe aurenta amma ya hanata yace ta jira akwai abunda yake son kullawa kuma yana buk’atar ta kasance a cikinsu don aikin ya tafi daidai. A tunaninta Laila ta mishi nisa shiyasa ta hak’ura ta zauna a gidan Madu zuwa lokacin da Alhaji Abdul ya karaya ya gane cewa ta ku6uce mishi sai ta kashe aurenta ta aureshi. Ashe hak’anta ba zai cimma ruwa ba, domin yanzu wani sabon zaman za’a sake kafin Laila ta waiwayi Alhaji Abdul tunda a wancan karon ma sai da tayi shekara ashirin kafin ta yarda zata aureshi, sai dai wannan karon Jamila bata jin zata iya jiranshi dalilin tsufan data fara, duk bleaching creme ya k’ona mata fata bata da wani mamora sai gayyan tsufa da tarin zunubai. “Yanzu ni ya zaka yi dani? Wani abu ka tanadar mini a gaba?” Ta tambayeshi tana tashi tsaye ta fara mayar da kayan jikinta. Wani wawan kallo yayi mata yana ganin surar jikinta yanda ya fara jemewa, in ba don yana son zamanta tare da Madu ba bai ga abun so a jikinta ba da har zai ji sha’awarta. Tunani yayi cewa ya kamata ya rabu da ita don ya lura she’s obsessed with him, kar ta kawo mishi cikas a gaba. Ajiye wayar hannunshi yayi kana ya dubeta da kyau yace, “Lokaci yayi da zamu daina huld’a tsakaninmu domin bana son Laila ta gano ina kwanciya dake matar yayanta. Yanzu ma bani da daraja a idonta kuma bana son abun ya wuce haka. Ina so daga yau karki sake ki nuna kin sanni, idan kina son cigaba da zaman aurenki babu ruwana kuma bazan hanaki ba amma ki nisanceni. Zan tura miki million goma a matsayin tukuicin k’ok’arin ki a gareni, zaki iya tafiya.” Tashin hankali ya hango k’arara a fuskar Jamila wacce ta sukwano ta durk’ushe a gabanshi tana cewa, “Don Allah Abdul karka mini haka, a kanka babu wahalar da ban yi ba duk don ka samu farin cikinka ko nima zaka tausaya mini daga baya. Na rok’eka don son da kake yiwa Laila kar ka raba tsakanina da kai don kai nake so ba kud’inka ba.” Shiru yayi yana kallonta tana mishi magiya har kuka take yi da idanunta, a maimakon yaji tausayinta sai yaji haushin dalilin da yasa duk tsawon wannan lokacin meyasa bai rabu da ita ba? A yanzu da yake son ya nitsu yaji labarin uwar Haydar baya son takura da kuma ihun da Jamila take mishi. Hakan yasa ya d’auki wayarsa yayi danne-danne kana ya dubeta yace, “Na tura miki kud’in. Sannan na baki minti biyar ki fita mini a gida kafin in saka securities suyi waje dake.” Tana jin hakan ta share hawayen fuskarta a zuciye ta dubeshi tace, “Ka jira kaga ni kuma me zan yi.” “Ni kike fad’awa haka? Uban me zaki yi? Wallahi kika kuskura kika 6ata mini plan sai na saka an shafe babinki a doron k’asa kuma kin san zan aikata. Don haka zan baki shawara ki 6ace a garin nan gaba d’aya kar in sake jin d’uriyarki, aurenki da Madun ma ya k’are dama ni na had’aku. In kuma kika mini shirme wallahi tallahi zaki gwammace baki had’u dani ba.” Ya k’arisa maganan yana nuna ta da yatsa tamkar zai kifeta da mari. Amma kuma a zuciyarsa yana fargaba yana kuma addu’an Allah yasa taji tsoro ta fita a harkarsa gaba d’aya. Jamila bata ce komai ba bayan nan ta had’a kayanta ta fice daga gidan Alhaji Abdul cikin bushewar zuciya da kuma alk’awarin lalata mishi rayuwa kamar yanda ya 6ata mata lokaci a rayuwarta. Bayan tafiyarta Alhaji Abdul ya saka aka bita a baya akan idan tayi yunk’urin tona mishi asiri a mata lahanin da zai hanata magana ba tare da an kasheta ba tunda bai ta6a sawa a kashe mutum ba. Gyara zamanshi yayi ya kunna recording d’in yana ji zuwa can annurin fuskarsa ta d’auke ya daskare a gurin yana cewa, “No way!!!” Da k’arfi. Fitan Jamila daga gidan Alhaji Abdul banki taje ta kwashe duk kud’inta dake cikin account d’inta sannan ta koma gidan Madu. A tsakar gidansu ta had’u da yaran kishiyarta suna kallonta da mamaki domin kwana biyu kenan da tafiyarta garinsu amma shine har ta dawo? Nan k’aramin cikinsu mai shekara biyar ya gudu d’akin mamanshi yana fad’a mata. Hannatu (Hajja) uwargidan Madu bata saurari yaron ba illa kwa6anshi da tayi tana cewa bata son gulma, kana taci gaba da harkar gabanta domin halin Jamila babu wanda bata sani ba illa zaman hak’urin da take yi da ita. Daga baya ‘yarta budurwa mai shekara sha hud’u Hanifa itama ta kai mata gulmar cewa Jamila na kwashe-kwashe a d’akinta, itama kwa6arta tayi tace babu ruwansu suyi harkan gabansu. Duk abunta mai muhimmanci Jamila ta kwashe a gidan Madu kana ta fito da akwatunanta biyar cike da kaya tasa yaron Hajja ya kira mata taxi a waje. Bai yi musu ba ya fita da gudu don dama basu so dawowanta da wuri haka ba. Hajja ce ta fito tana tambayar Jamila ko lafiya don sauk’e hakk’in zaman tare ba don tana son hakan ba. A wulak’ance Jamila ta dubeta tace, “Nisa zan yi. Idan uban yaran ya dawo kice ya duba cikin wardrobe d’ina akwai sak’on shi a ciki.” Da haka tasa sauran yaran suka fitar mata da akwatunan ta bisu a baya Hajja na kallon ikon Allah. Jamila tana shiga Taxi wanda aka aika bibiyarta ya kira Alhaji Abdul ya sanar dashi cewa ta kwashe kayanta ta bar gidan. Shi kuma Alhaji Abdul da yake cikin kid’ima yace, “Ka rabu da ita, sannan kazo zamu tafi Abuja yanzun nan.” Daga gidan Madu airport Jamila ta wuce tana fatan Allah yasa ta samu jirgin zuwa Niger Republic, tana ga lokaci yayi da itama zata waiwayi gida ba tare da Alhaji Abdul yasan ina ta shiga ba har abada. Cikin sa’a ta samu jirgin da zai je Niamey tayi booking ta gama komai, kafin jirginsu ya d’aga ta tura sak’onni a family whatsapp group d’in zuriyar mijinta irin wanda ta barwa Madu a d’akinta. Alhaji Abdul bai samu jirgin zuwa Abuja daga Kano ba, hakan yasa dashi da driver tare da Right hand man d’insa wanda ke aikata duk abunda ya buk’ata suka kama hanyar Abuja da mota wajen k’arfe sha biyu na rana. Basu isa ba sai bayan la’asar wanda babu 6ata lokaci suka yi hanyar gidan Baban Alhaji Abdul, wanda ya koma Abuja da zama cikin tsohon gidanshi bayan ya dank’awa d’anshi ragamar dukiyarsa duka. Suna shiga farfajiyar gidan suka sameshi zaune a veranda yana karatun jarida. Gilashin idanunsa ya cire yana kallon d’anshi da yake fitowa daga mota yace, “I’m not expecting you Abdul sai next week.” Alhaji Abdul ya iso gurinshi yana cewa, “Baba mu shiga ciki muyi magana.” “Na me?” Tsohon ya furta yana kallon Abdul wanda yake son takura mishi. “Mu shiga ciki Baba sai muyi maganan a can don Allah.” Yayi maganar muryarsa cike da rok’o don yasan tsohonsa akwai taurin kai idan ya so. Mik’ewa Baban yayi ya tu6e takalmansa a bakin k’ofar yana cewa, “Kar ka shigo….” “….mini da takalma.” Alhaji Abdul ya k’arisa maganan shima yana tu6e takalminshi. Suna shiga falon ya tsaya kallon gurin kamar yau ya taba shigowa, carpet ne ja malale a falon gaba d’aya sai kujeru k’irar zamanin 19’s masu kafafun katako, sai akwatin tv shima irin na zamanin da tare da set na dinning table da kujerunsu duk na katako. Yanayin tsaruwar falon zai sa kayi tunanin ko kayi amfani da Time traveling machine ne ya mayar da kai shekarun baya. A kujera Baba ya zauna kana ya dubi Alhaji Abdul wanda ya nemi guri a k’asa ya zauna yana kallon baban nashi. “Ina wuni Baba?” Ya gaisheshi cikin girmamawa. “Lafiya kalau, meya kawoka Abuja yau?” “Baba magana ce tafe dani amma ban san tabbatuwarta ba har sai ka tantance, Ina so ka saurari wannan audio d’in don watakila burinka na shirin cika.” Cikin rashin fahimtar inda maganar Alhaji Abdul ya nufa Baba ya tsaya yana kallonshi yayin da shi kuma yake danna wayarsa har ya zo daidai inda Ammi ta fara magana. Hawaye ne ya taru a idon Baba jikinshi ya fara karkarwa ya mik’a hannu ya kar6i wayar ya manna a kunnenshi, lumshe idanunshi yayi hawaye suka zubo a fuskarsa yace, “Muryar Lu’alu’a ce.”

Mum Fateey 👌

Back to top button