Halysaah Page 121 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 121…Har karfe biyu da rabi na dare Ajay na parlonsa, duk da ba kallo yake ba amma haka nan ya kunna TV din parlon, ya canza position from sitting to lying down yafi a kirga a parlon, kuma ko minti biyar bai iya yi a each position din, da ya kwanta zai mike zaune, after some minutes kuma ya sake komawa ya kwanta haka yake ta yi tun daxu, mikewa zaune yayi ya dau sauran coke din gwangwani da ya ajiye kan Centre table ya shanye making it the second Canned coke he is drinking, sake bude wani coke din dake kan table din yayi ya ci gaba da sipping a hankali, after a while ya dau remote din AC ya kunna Ac din parlon jin ya daina jin sanyin da yake ji duk da Jacket ne a jikinsa, karfe uku saura minti goma ya ajiye Gwangwanin coke din hannunsa bayan ya shanye, ya mike tsaye ya saka hulan Jacket din jikinsa trudging towards the door kamar ana tilasta sa, tun daxu yake son zuwa dakin Khaleesat just to check on her after what happened amma bai je ba, yana isa kofar dakin ya bude gently sannan ya kai hannu ya kunna wuta yana kallon saman gadon, baccinta take sai dai bata rufa da duvet ba don AC din dakin a kashe yake, ya kusa minti daya tsaye bakin kofar kafin ya karasa ciki har zuwa kusa da gadon, kallo daya yayi ma laps dinta dake bude gaba daya ya dauke kai kamar bai gani ba, can kuma dai ya juya ya fita daga dakin kawai bayan ya kashe wutan ba tare da ya duba abinda ya kawo sa ba. Tun da gari ya waye Khaleesat ta kasa sauka downstairs gashi she is very hungry don karfe goma sha daya yayi, duk da ranan asabar ce taso zuwa school amma da ta kira Sophie sai tace mata cramps take bazata je school din ba ita, wannan ne yasa ta fasa tafiya makarantar amma da tun da sassafe zata bar gidan, ganin zaman dakin bazai fissheta ba yasa ta sauka daga saman gado a hankali ta dau Hijab dinta ta saka, slowly ta tura kofa ta fita daga dakin, tana sauka downstairs ta gansa zaune study area dake parlon yana danna laptop dinsa, suna hada ido duk suka dauke kai lokaci daya kamar hadin baki, tana tafiya a hankali ta nufi kitchen ta shiga ta kulle kofar, Noodles ta dafa bayan ta gama ta dau ruwan gora a fridge ta fito daga kitchen din, ko by mistake bata yarda ta kalli direction dinsa ba ta wuce sama, sai a sannan ya bi ta da kallo. Ajay ya ajiye wayarsa bayan sun gama magana da Mai martaba ya kalli agogon wrist dinsa dake nuni da karfe bakwai dai dai, yasan definitely jirginsu ya kusa sauka yanxu tunda da rana suka taso, duk da baya jin dadi tun safe ga ciwon kai da yake yi haka nan ya mike daga zaunen da yake ya dau sauran coke dake kan table ya sha ya tafi kitchen yayi disposing gwangwanin sannan ya wuce sama, ɓangarensa ya nufa ya dau over coat dinsa ya saka sannan ya fito, ya bude kofar dakin da Khaleesat take ciki, tana zaune saman darduma ta idar da sallah hannunta rike da wayarta tana karatun Alqur’ani a zuciyarta, tun da ta daga kai suka hada ido ta mayar da kanta kasa still looking at her phone screen, a takaice yace “Take all what you will need and put them inside that box….” Khaleesat ta sake daga kai ta kallesa, ganin ya juya zai fita tace “Kamar yaya?” Ya juyo ya kalleta fuska daure yace “Kamar yanda nace, and I am giving you just 10 mins, idan kin gama ki sauko downstairs with the box, do not waste my time” Yana fadin haka ya bar bakin kofar dakin, Khaleesat tayi shiru tana nazarin abinda yace, to ina kuma za su je da daddaren nan da zai ce ta hada kaya? Can dai ta taɓe baki ta mike ta fara yin abinda yace tayi, tana gama hada abinda tasan zata bukata ta dau akwatin ta sauka downstairs ta ajiye tana kallonsa a parlon, without looking at her yace “Ki je mota ki jirani” Tace “Ina zamu je?” Still not looking at her, calmly yace “Ban sani ba” Hade rai tayi ta dau akwatin ta fita zuwa parking space ta rungume hannu ta jingina jikin motarsa, after some minutes sai gashi rike da makullin mota coming towards the parking lot, bude motar yayi ya shiga yayi igniting motar, ta bude back seat ta ajiye box dinta don bazata iya kai wa booth ba, can tace “To ni ban dauko wayata ba ai” Yace “Kin ga idan kika bari na koma cikin gidan nan you will have to carry ur cross all alone” Bata ce masa komai ba ta juya ta koma cikin gidan tana cika tana batsewa, sama ta tafi ta shiga cikin daki ta dau wayarta da Charger har da laptop dinta da Chargern sa, sannan ta dau handbag ta fita, tana komawa parking space ta bude back seat duk ta ajiye kayan hannunta sannan ta rufe ta shiga gaban motar, tun da suka fita daga gidan take zuba ido taga inda zai kai ta da daddaren nan, after almost a 35 minutes ride ta ga apartment dinta ya kawota, juyawa tayi ta kallesa, bayan yayi parking a garage ya bude motar ya sauka stretching himself, ita dai kallonsa kawai take don he doesn’t look alright, lokaci daya ta tuna Hajja tace su Aunty za su zo Maryland, to ko suna hanya ne, bata san sanda ta sauke wani ajiyar relieve ba, and she felt really grateful, bude motar tayi ta sauka still looking at him ganin ya nufi kofar apartment din ta bude back seat ta fiddo akwatinta tabi bayansa zuwa gidan, ita duk tunaninta an saki gidan ne da yake tambayarta ko tana da kudin haya kwanaki da tace ya maidota apartment dinta, yana dusting kujera ta samesa a parlon, ta koma ta dauko sauran kayanta a motar bayan ta ajiye kan Centre table din da yayi dusting tace “Na gama dauko kayan” Don ya kulle motarsa ne yasa ta gaya masa amma bai tanka ta ba, ta dau akwatinta ta wuce sama tana tafiya a hankali zuwa dakinta. Bayan ta yi gyare gyare a dakin ta shimfida bedsheet ta fito tana leka downstairs taga baya nan, sauka tayi ta dau laptop dinta da handbag ta koma sama, ta bude bandakin dake Bedroom din ta shiga ta wanke tas sannan tayi wanka ta dauro alwala ta fito, a ranta ta dinga fatan Allah ya sa ta dawo apartment din nata kenan, don ta tsani zaman gidan nan nasu tafi samun freedom dinta ita kadai bama sai ta zauna da kowa ba, bayan ta idar da sallah ta yi shafe shafenta ta saka kayan bacci sannan ta dora Hijab a kai, tana zaune gefen gadon tana danna wayarta har kusan karfe tara, daga karshe ta mike ta bude kofar dakin, sai da ta leka downstairs taga ba kowa sai ledoji dake ajiye sannan ta sauka, bude ledan tayi taga shopping din kayan shayi ne da bread with butter, ta bude wani ledan taga cookies iri iri da biscuits sai Chocolate, wani ledan kuma taga fresh fruits, sai ledan takeaway din abinci kusan hudu da ta gani, ga kuma pack din bottle water, daya bayan daya take bude takeaway din abincin taga Jollof rice and peppered turkey, white rice and stew with chicken, sai fried rice shi ma da peppered turkey, takeaway din karshe taga shi ma white rice and stew din da beef, tana ta kallon abincin kafin daga karshe ta dau takeaway uku ta kai freezer a kitchen ta ajiye su, nan taga har ya gyara kitchen din ko ina fes kamar yanda yayi ma parlor, ta koma parlor sauran kayan da ya siyo duk suma ta kai kitchen ta ajiye su sannan ta dawo parlon ta zauna ta dau rice and stew din ta fara ci, tana zaune parlon har karfe goma sha daya, can dai ta kalli kofar parlon, mikewa tayi ta tafi ta murda taji a kulle, ta window ta leka garage taga motarsa na nan, ta dawo parlon sai a sannan ta lura da spare key da ya ajiye mata kan kujera, kawai ta juya tayi wucewarta daki. Ajay na ƙishingiɗe parlor a gida yana shan grapes yana kallon football, bacci yake ji sosai amma still yana zaune parlon, yasan baccin da bai yi jiya bane ke damunsa, Walid ma na zaune parlorn har ya gaji da wara ido yana jiran yaga ta ina Khaleesat zata fito amma bai ga haka ba, don har cikin dakinta sai da yasan yanda yayi ya shiga amma bai ganta ciki ba har da duba bandaki, Gimbiya Firdausi ce ta sauko downstairs tana kallon Ajay tace “Kai Junaid ita matar taka isasshiyar wace gari ce da har yanxu bata shigo inda muke ta gaishe mu ba kusan awan mu biyu da sauka gidan nan kenan? Ko dai bata da hankali ne??” Ajay ya daga kai ya kalleta, bayan ya gyara zamansa cikin nutsuwa yace “Ai bata gidan, they are having exams on Monday so bata yi karatu ba saboda tafiyar da muka yi, shi ne ta tafi hostel wajen kawarta za su yi group reading da Coursemates dinta, so she is in school, shi yasa ma na yi maku takeaway din abinci ai” Yana gama fadin haka ya ci gaba da shan grapes dinsa, Walid dai ya juya yana kallon Ajay kamar wanda ya ji mummunan labari, Gimbiya Firdausi ma ta dinga kallon sa for almost 30 seconds sannan ta juya ta koma sama, Ajay ya bi ta da kallon gefen ido yana shan grapes dinsa a hankali, Gimbiya Firdausi na shiga dakin da suka sauka ta kalli Aunty tace “Wai kinji tana makaranta Fulani….” Aunty tace “Karya yake munafuki, ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba tana ɓangarensa, ai ya riga ya nuna mata bamu da daraja kar ta mutunta mu, kin ga yanda ya raina mu baya ganin mu da daraja to bari ita ma ya dorata akan wannan layin, amma tana gidan nan babu inda taje, ai ɗan iska ne, ba dai wata biyu ya rage mata ta gama karatun ba kuma dole masarauta zata dawo mu zauna don ubanta, to ina nan ina jiran wannan lokacin….” Shahuda dake zaune dakin tace “Wallahi Aunty sai kin ga irin kallon rainin da ta dinga yi ma mutane a England yanda kika san Ubanta wani ne a kasar nan, sai daddaga kai take tana flaunting designers a gabanmu” Gimbiya Firdausi na kallon Aunty tace “Ina bangaren nasa yake Fulani?” Mikewa Aunty tayi suka fita tare Shahuda na biye da su, Aunty tayi leading dinsu har zuwa part din Ajay, suka wuce parlor suka karasa har Bedroom dinsa Aunty ta bude kofa, babu kowa dakin that was very neat and cool, Shahuda sai bin dakin take kallo, su Aunty da Gimbiya Firdausi suka fito, sai da Gimbiya Firdausi ta bari suka koma daki ta kulle kofa ta zauna gefen gado tana kallon Aunty tace “Fulani meye shawarar ki akan wannan shegiyar buzuwar da Sarki ya aura ma Yarima?” Aunty ta sauke wani ajiyar zuciya tace “To ni kuwa me zan ce Gimbiya, ai ni i am not against aurensu tunda kinga ba don dubaran nan da sarki yayi ya maida auren kan Yarima ba Fulani Aseeyah so tayi tayi ruining reputation dinsa a idon jama’a, duk abinda zai taɓa reputation din sarki kuwa ai kinga baza mu so ba, don haka i am not against the marriage, kawai babban damuwata yanda ya raina ni haka yake son daura yarinyar akan layi, don har suka yi kwanakin da suka yi a masarauta suka taho Amurka wallahi bata taɓa zuwa ta gaisheni ba a gidan nan, to ni shi ne haushi na, amma bayan nan babu komai a raina sai fatan alkhairi” Gimbiya Firdausi bata sake cewa komai ba jin abinda Aunty tace, don taga bai ma kamata ta sake wani magana da Aunty akan Khaleesat ba, Aunty dai sai kallonta take ta gefen ido, Gimbiya Firdausi tace “Allah ya sa mu dace” Aunty ta sauke wani ajiyar zuciya tace “Ameen Gimbiyah” Da asuba bayan Khaleesat tayi sallah ta sauko downstairs taga still parlon babu kowa, ta leka garage taga his car is still there, nan ta gane cewar a can gida ya kwana, bayan ta gyara ko ina na gidan ta goge ta koma sama ta kwanta, wajen karfe tara ta tashi bacci tayi wanka ta shirya sannan ta sauko downstairs ta hada breakfast, tana gamawa ta dau wayarta…. text ta tura ma Ajay cewar zata je gidansu Safiyyah bata da lafiya har da Please dinta a karshe, ta ajiye wayarta hoping he will let her go, after some minutes sai ga text dinsa ya shigo, turo baki tayi tana hararan wayar don ta ma san cewa zai yi a’a, tana duba reply dinsa taga yasa “Ok” sosai taji dadi ta tashi ta tafi sama ta shirya sannan tayi order din Lyft, ko gaya ma Safiyyah tana zuwa bata yi ba ta kama hanyar gidansu.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence 07087865788*
