Ruwan Zuma Page 3 Hausa Novel
(03) A nan Aliyu ya bawa Laila labarin duk abunda ya faru a majalisarsu har ta kai ga ya fara zuwa nemanta zuwa rana mai kamar ta yau. “Sai dai Laila bazan miki k’arya ba, tun ranar da na fara arba da ke zuciyata ta kamu da sonki bana wasa ba, na zo ne da niyyar gwadaki amma sai na fad’a sonki ba tare da na shiryawa hakan ko kuma hakan nayi niyya ba. Sati na sama nake da niyyar turo magabatana amma sai Abdul ya gane halin da ake ciki har hakan ya faru. Ki sa a ranki ba yaudaranki nayi ba, wallahi duk wata kalma da kuma nuni da na miki na soyayya Laila gaskiya ce ba yaudara ba. Wallahi Ina sonki da dukkan zuciyata kuma ina shirin aurenki Laila.�? Share hawayenta tayi cikin takaici da zogin zuciya ta ce, “Wannan son ba zai yi amfani a yanzu ba Aliyu, kayi wasa da damarka domin Babana ya samu labarin kudirinka a kaina, bana tunanin Idan ya gane cewa kaine Aliyu zai barka haka balle har ya baka aurena. Nagode da soyayyar da kake mini kuma bazan rik’eka a zuciya da abunda ka mini ba. Allah ya sadamu da alkhairinsa.�? Da haka ta juya zata koma cikin gida. “Idan kuma kika ji cewa tun jiya naje gurin Baba yau kuma magabatana na zuwa da dare fa?�? Aliyu ya fad’a fuskarshi d’auke da murmushi alamar zancen gaskiya yake fad’a. Wani wawan juyi Laila ta yi tana kallonshi da tsantsar mamaki a fuskarta. “Wasa kake yi ko gaskiya? Ko kuma dai har yanzu baka gaji da wasan kwallo da zuciyata bace?�? “Babu k’arya a maganata Laila. Jiya bayan na bar gurinki can shagon Baba na je, na fad’a masa komai na kuma rok’i gafararsa da kuma neman aurenki Idan ya amince. Ki shirya biki nan da wata d’aya ko biyu masu zuwa in Allah ya yarda.�? Ya k’arishe maganan yana murmushi mai k’ayatarwa. Laila da tsantsar farin ciki ya lullu6eta ta shige gidansu da gudu tana rufe fuska, Aliyu ya bi bayanta da kallo yana dariya. Abdul ya so ya tada k’ayar baya kan aurensu, domin har cewa yayi sai ya nak’asta Aliyu ya kuma auri Laila. Sai da Baban Laila ya samu Babanshi ya tsawatar mishi sannan ya saduda ba don ya so ba. Daga baya ma sai ji suka yi wai an fitar dashi k’asar waje ya bar Nigeria gabad’aya. “Yanzu kam tunda babu Abdul hankalinki ya kwanta ko?�? Cewar Aliyu a wata yammaci da ya zo zance gurin Laila bayan an saka ranar aurensu sati biyu masu zuwa. “Hankalina ne bai kwanta dashi ba domin yana da zuciya sosai, Ina tsoron kar yaje ya maka illah.�? “Bai isa ba Laila, ko kin manta cewa nima namiji ne kamar sa? Tunda nace naji na gani ina sonki to ki sani ko a doke babu wani saurayin da zai dokeni balle har ya rabani da ke. KI SA A RANKI ALIYU YANA SONKI NE DA DUKKAN ZUCIYARSA.�? Umman Aliyu ta so ta hana wannan aure amma ganin Aliyu ya nace yasa ta barshi ba don ranta ya so ba. “Umma Ina ji a jikina zaki so Laila da zarar na kawota cikin gidan nan a matsayin matata, duk abunda ya faru bata da laifi domin nine ma na mata laifi da naje k’ofar gidansu da niyyar yaudaranta. Umma ki sassauto da zuciyarki ki barni in auri wacce nake so don Allah.�?“Aliyu rashin sanin ciwon kai yasa kake son auren yarinyar da aka kusa yankaka a kanta, ni mahaifiyarka na fika son karan kanka. Wallahi daa ba don ka mini shigar sauri ka tura Baffanunka gurin iyayen yarinyar nan ba daa babu abunda zai sa ka aureta. Kai, kai Aliyu baka kyauta mini ba, bana son yarinyar nan ko kad’an.�? A haka aka yi auren ba tare da tana so ba a bisa dalilinta d’aya, saboda akan Laila an kusa kashe mata d’anta, wanda duk bayanin da Aliyu ya mata na cewa babu laifin Laila a cikin wannan al’amari Umma bata gane ba. Koktel kad’ai aka yi a bikin dalilin Baba ya hana a koma Maiduguri su yi bikinsu na al’ada. Amarya, Ango tare da abokansu da ‘yan uwa sun taru a wani babban d’akin makarantar sakandire dake nan kusa da gidansu Laila. An yi jolof d’in shinkafa, alale da kuma cincin sai kuma ruwan lemu na kwalba wanda aka bud’e aka tura abun zuk’a a ciki, duk aka jera a kan teburi kowa ya d’auka da kansa. An ci, an sha, an yi shagali sannan da dare aka d’auki Amarya aka kaita gidan mijinta wato gidan da mahaifiyar Aliyu take zaune da kuma yayansa Nazifi da matarsa Muna. Bayan an gama biki kowa ya watse Ango ya shigo d’akin Amaryarsa bakinshi d’auke da sallama. Ganin Laila yayi zaune akan gado tana lullu6eta da mayafi da ita da d’akin nata duk kamshi suke yi kamar an yi 6arin turare. Daga nan gurin Umma yace su je domin tana kiransu. Ba musu Laila ta tashi suka fita zuwa d’akin Umma wanda ke kallon d’akinsu ita da Muna. A k’asa ta zauna ta gaishe da Umman wacce daga jin yanda ta amsa zuciyarta ta fara bugawa. Tun da aka fara bikin dama danginta na rad’i-rad’in cewa wai uwar Angon kamar bata son auren. “Na aika ne aka yi kiranki saboda ja miki kunne akan rayuwar gidana da kika shigo cikinta, bana son tara samari domin yanzu ke matar aure ce..?�? Da sauri Aliyu ya d’ago kanshi cikin mamaki yana cewa, “Umma wannan wani irin magana ce? Ya za’a yi da aurenta ta kawo saurayi k’ofar gidan nan?�? “Hali ai zanen dutse, da take tare da wancan d’an iskan saurayin nata wanda ya so ya kasheka ai bai hana ta k’i tsayawa da kai ba. Aliyu kar ka k’ara saka mini baki cikin maganata domin da kai da ita duk a k’arkashin ikona kuke, Idan kuma so kake ka nuna mata cewa ban isa da kai ba balle ita sai ka cigaba da tsayar dani.�? Yanda Umma take maganan cikin 6acin rai yasa Aliyu ya sadda kanshi k’asa yace, “Kiyi hak’uri Umma, bazan sake ba.�? “Tunda ka nace anyi auren ni kuma dole ta bi dukkan sharud’d’ana muddin tana son zama da kai.�? Laila kuwa tun furucin Umma na farko zuciyarta ta karye ta fara hawaye. Ashe a haka zata rayu cikin tsangwaman uwar miji? Ta d’auka Idan ta auri Aliyu tayi bakwana kenan da duk wani tashin hankali, tana tunanin cewa zasu yi zaman aurensu cikin kwanciyar hankali da jindadi, ashe akwai wani tashin hankalin a gaba. “Bayan haka, ke da Muna ce zaku dinga mana girki domin ‘yayana basu da k’arfin da za’a yi tukunya biyu a gidan mutum bakwai kacal. Tunda Allah ya kawoki, wankin kayana da sharan d’akina zai dawo kanki tunda kece k’arama. Sannan ki girmama manyanki, kamar yanda Nazifi yake yaya ga Aliyu to haka matarsa Muna take gaba dake. Ina ga shikenan maganan da zan fad’a, idan kuma na tuna wani abun zan sanar dake tunda yanzu aka fara zama. Zaku iya tafiya.�? Aliyu ne ya fara mik’ewa sannan itama Laila ta tashi tana goge hawayenta da mayafinta, “Na shiga uku ni Nafisatu, Aliyu me na yiwa matarka take kuka? Ke Lamla me aka miki?�? “Umma watak’ila kukan rabuwa da iyayenta take yi har yanzu, ba wai don kun mata wani abu ba.�? Aliyu yayi saurin fad’a don baya fatan a sake wani zaman akan wanda aka yi. Laila dake tsaye tace, “Sai da safe Umma.�? Sannan ta juya ta fita. “Kai Aliyu zauna ina son magana da kai.�? Cewar Umma tana mai kishingid’a. Aliyu ya koma ya zauna yana jin hiran Ummansa wanda bai ga abun sauri ciki ba. Sai da ta gaji don kanta sannan ta sallameshi ya tafi, wai ta yi hakan ne don ta nunawa Laila tana da iko da Aliyu. Ko da ya koma dak’insu ya samu Laila ta kwanta, ga kazar da ya shigo musu da itama har ta yi sanyi. Zuciyarsa ba dad’i ya zauna akan gadon nasu ya dafe kanshi yana tunanin mafita. Ya so ya nemi gidan haya a gefe amma Umma ta hanashi k’ememe, wai tafi son su zauna a gida d’aya su saba da juna, kwata-kwata gidan kuma d’akuna uku ne in ka cire guda d’aya da yake cikin zaure wanda k’annen Aliyu, Najib da Naziru suke kwana a ciki. Gida ne k’arami wanda kana shigowa zaka fara cin karo da d’akin Umma wanda a daa d’akin Abban su Aliyu ne, bayan rasuwarsa ta dawo ciki da zama. Sai wasu d’akuna biyu wanda sune nata kuma a ciki Nazifi da matarsa suke ciki, da auren Aliyu ya zo ne Umma ta yi kane-kane tasa aka toshe k’ofar tsakanin falo da d’akin, wato kowannensu ya tsira da d’aki d’aya. “Aliyu.�? Yana tsaka da tunani ya jiyo Laila tayi kiransa, sautin muryarta kamar ana busa sarewa. Juyowa yayi yana kallonta yana jin bak’in cikinshi na yayewa, “Amaryar Aliyu. Dama baki yi bacci bane?�? “Uhm, ban yi ba.�? Ta bashi amsa tana mai wasa da mayafinta wanda dashi dama ta kwanta. “Ki sauk’o mu ci abinci sai ki samu kiyi bacci don naga alama kamar kin gaji da yawa.�? Da haka yasa ta sauk’o suka ci kazar sannan ta koma ta kwanta shima ya hau kan gadon yana tunani har bacci ya d’aukeshi. Washe gari tun bayan sallan asuba Umma ta fito tsakar gida ta shimfid’a tabarma tana jin labarai a rediyo, a kan idanunta Aliyu da Laila suka fito suka yi alwala sannan suka koma cikin d’akinsu dalilin basu da band’aki a ciki. Suna idar da sallah Aliyu ya nemi ya kwanta da matarsa amma suka jiyo Umma na kiranta daga tsakar gida. Laila ce ta fara fita bayan ta mayar da kayan jikinta sannan shima Aliyu ya fito ya gaishe da mahaifiyarsa. Yana gaisheta ya koma d’aki yayin da ita kuma Laila ta shiga d’akin Umma don mata shara kamar yanda ta umarceta. Tana gama sharan Umma tace ta d’aura musu dumamen tuwo ta kuma dama kunu. Tana cikin dama kunun Muna ta fito tana mik’a sannan ta nufo wajenta. “Ina kwana?�? Laila ta gaisheta. Wani kallon banza Muna ta bi Lailan dashi sannan ta d’ebi tuwo a kwanon mijinta ta koma in da ta fito. Ido kawai ta bita dashi har ta shige sannan ta maida hankalinta kan abunda take yi. Ko da ta gama kunun ma haka Muna ta k’ara zuwa ta d’iba babu ko sannu. Laila bata koma d’akinta ba sai k’arfe bakwai har da wasu mintuna. A d’aki ta samu Aliyu har ya gama shirin fita gurin aiki a wata kamfanin had’a robobi. “Kaci abincinka kuwa?�? Ta tambayeshi tana mai zama a kan kujeran zaman mutum biyu wanda shi kad’ai ya samu shiga d’akin nata bayan gado da kwabet. “Jiranki nake yi Amarya, ya aiki?�? Ya tambayeta yana mai zama kusa da ita. Sai a lokacin ta fara jin kunyarsa da ta tuno halin da suka kusa fad’awa da safe kafin Umma tayi kiranta. K’asa tayi da kanta sosai tana rufe ido da tafin hannunta, hakan yaso ya bawa Aliyu dariya amma ya dake ya umarceta ta sauk’o su ci abinci gudun kar yayi latti. Bayan tafiyarshi itama ta share d’akinta tare da saka turaren wuta, nan da nan d’akin ya d’auki kamshi. Umma da har lokacin tana tsakar gida ta kwala mata kira, Laila ta fito da sauri ta tsuguna a gefenta. “Lamla kasheni zaki yi daga zuwanki? Aliyu bai fad’a miki ina da Asma bana son k’amshin turare ba? Tafi ki rufe d’akin har sai nace ki bud’e kafin nan kin gama shak’an kayanki.�? Laila ta yi rau rau da ido tana bawa Umma hak’uri tana wallewa. “Wallahi ban san bakya so ba da bazan saka ba, kuma wallahi bai fad’a mini ba, don Allah kiyi hak’uri�? “Ni kam tashi ki tafi kar na jikinki ya mini illa.�? Umma ta fad’a tana toshe hancinta da rigarta. Laila ta tashi da sauri ta koma d’akinta ta rufe k’ofa da windo kamar yanda Umma tace ta yi. Zama ta yi a kan gadonta hawaye ya silalo a idonta guda d’aya ta share tana mai d’aga kanta sama, sai dai tuno da iyayenta da k’annenta da ta yi yasa kuka mai k’arfi ya kwace mata. Har ta gama kukan Umma bata kirata ta fito ba, gashi ko wanka bata yi ba kuma tana buk’atar yin hakan. Awa d’aya biyu har biyar Laila na cikin d’aki tana zaune, tana son fita amma bata son duk wani abu da zata yi da zai 6atawa Umma rai tun da dama ba sonta take yi ba, balle kuma fitanta ya had’u ne da ta6a lafiyar Umman. Ko da aka idar da sallan azahar a nan hankalin Laila ya k’ara tashi domin tana son yin sallah ga kuma fitsari da ya matsa mata. Ta zo bakin k’ofarta sau ba adadi da niyyar bud’ewa, amma da zarar ta tuno da fad’an Umma sai ta koma ta zauna. Daga tsakar gida ta jiyo sallamar Aliyu wanda hakan ba k’aramin dad’i ya mata ba, minti biyu da haka ya turo d’akin ya shigo hannunsa d’auke da kulan abinci amma fuskarsa babu walwala. Dama tun kafin ya shigo ta tashi ta tsaya dalilin fitsarin da ya hanata sakat. “Sannu da dawowa.�? Ta fad’a tana mai goge gumin fuskarta dalilin rashin wadataccen iska a d’akin. “Yauwa.�? Kawai yace da ita ya fara cire jamfar jikinshi ya ajiyeta a kan kujera. Tana son tambayanshi me ya faru ya 6ata rai haka amma fitsarin da ya matsa mata ya hanata aikata hakan. Buta ta d’auka ta fita zuwa band’aki sannan ta had’a da alwala ta fito, akan Idan ta yi sallah sai ta yi wankan. Tana shigowa ta samu Aliyu da kwanon abincin a gabanshi amma bai ko ta6a. “Kiyi sallah zamu yi magana.�? Yace da ita yana mai rufe abincin. A hankali ta furta “To�? sannan ta tada kabbara. Ko da ta idar sai ji ta yi Aliyu na cewa, “Laila menene ya faru tsakaninki da Umma yau?�? Yanda yayi maganar zaka san ranshi a 6ace yake. “Na saka turaren wuta ne a d’akina tayi kirana tace baka fad’a mini cewa tana da Asma bane? Tace in shiga d’aki in zauna har sai ta kirani kafin nan turaren ya gama fita. Kuma wallahi ban fita ba, Ina jira ta yi kiran nawa ne shiyasa ko wanka ban yi ba.�? Aliyu runtse idonshi yayi da k’arfi bakinshi na motsi a hankali. Can ya bud’e idon ya sauk’esu a kan Laila wacce daga yanayinta zata gane bata ma san me yake faruwa a wannan lokacin ba, alamar tana cikin duhu akan komai. “Laila kiyi hak’uri har na fara kawo waswasi akanki. Tashi kije kiyi wankan sai mu ci abinci.�? Laila da bata gane komai ba ta ce, “Wani abune nayi? Don Allah ka fad’a mini.�? Girgiza mata kai yayi yace, “Je kiyi wankan kizo mu ci abinci.�? Ba musu ta tashi ta d’ebi ruwa dake cikin randarta dake bakin d’akinta ta shiga wanka ta dawo ta shirya har da yin kwalliya. Sai a lokacin ta ji ta dawo cikin hayyacinta domin tun da take bata ta6a kai har azahar bata yi wanka ba. Suna cin abincin ne yake mata hira cikin barkwanci can kuma yace, “Da yardar Allah bazamu zauna a gidan nan ba, zan nemi aiki a wani gari in d’aukeki mu tafi can domin zaman gidan nan bazai mana dad’i ba Laila.�? Ita dai gyad’a kai kawai ta yi tana saurarenshi. “D’azu da ka dawo naga kamar ranka a 6ace, shin nice na 6ata maka rai?�? Ta tambayeshi domin hakan yana cikin zuciyarta bata manta ba. “Babu komai Laila, babu komai. Kici abincinki kin ji Zinariyata.�? Da haka ya shashantar da zancen suka cigaba da cin abincinsu cikin soyayya da k’aunar juna. Wani abu da Laila bata sani ba shine; Aliyu yana shigowa gida ya fara biyawa d’akin Umma. “Mun sameku lafiya Umma.�? “To lafiya dai za’a ce amma Aliyu ban san me muka yiwa matarka ba ta shige d’aki ta k’ulle ta k’i bud’ewa, su Goggonka Jummatu sun zo ganin d’akin Amarya amma haka suka tafi yarinyar nan tana ciki. A gaban idonka ta nuna tana da ladabi, kana saka k’afa ka fita ta daina yiwa kowa magana shine k’arshe ta kulle kanta a cikin d’aki. Ni banso ma in fad’a maka ba kar kace dama tun can bana son yarinyar har zan fara had’aka da ita. Dama akan yau tare zasu yi girkin rana da Muna to kaga bata fito ba balle har ta ga yanda muke girkinmu. Ga can abincinku a bakin k’ofa ka shigar muku dashi. Kuma ban ce ka mata magana ba, bana son ta kullaceni.�? Ta k’arisa maganan a numfashi d’aya kamar mai wacce tayi haddan maganan. Ran Aliyu ya sosu da ya ji wannan abun da Laila ta aikata shiyasa ya shigo ranshi a 6ace, amma ganinta da yayi cikin zufa babu wanka balle kwalliya yasa ya fara waswasin maganar Ummanshi. Ko da Lailan ta fad’a mishi nata labarin ya gane manufar Umma a kansu. Yana son mahaifiyarsa yana kuma mata hidima, itama hakan yake a gurinta domin har Nazifi na cewa tafi son Aliyu a kanshi, wanda kowa ma ya gane hakan ne. Bai san meyasa wannan karon ta tsani abunda yake so ba, lokacin da yake yaro yana cewa zai zama gwamnan Kano, yana tunawa itace take k’arfafa masa guiwa tana kuma mishi addu’an cikar burinsa, amma yau an wayi gari Umma bata k’aunar abunda ya ke k’auna, gashi har ta fara shiga tsakaninsu daga kwana d’aya da aurensu.A ranar da dare ma’auratan suka fara kwanciyarsu ta Sunnah wanda suka yi hakan a takure, domin Nazifi da Muna suka kwance a rumfarsu wai zafi ya damesu. Itama Umma a rumfarta ta kwana lokaci-lokaci kuma tana kunna rediyo. Gurin fita wanka sai da Aliyu yayi da gaske sannan Laila ta yarda, domin har kuka ta yi wai baza ta iya fita ta tsallake su Umma sannan su jiyo tana wanka a band’aki ba. Hakan yasa Aliyu yaji ya k’ara son barin gidan cikin gaggawa, saboda bayan k’in da Umma ke nunawa Laila to gashi ya had’u har da rashin sirri da suke dashi a matsayinsu na sabbin amare. Haka zaman gidan nasu ya kasance wanda Laila sam bata jin dad’insa matuk’ar Aliyu ya fita aiki. Tsakaninta da Muna kuwa ko gaisuwa baya had’asu, Umma kuma komai nata Laila ce ke mata, zata iya kwala mata kira don ta bata wani abu da ke kan kwabet d’inta yayin da ita Umman kuma ke kwance a kan gadonta. Idan a kan aiki kad’ai abun ya tsaya Laila baza ta damu ba, amma wasu maganganu da suke fitowa daga bakin Umman suna mata zafi a zuciya ba kad’an ba. Umma na yawan alak’anta Laila da zuwa gurin boka ko malamai ta hanyar habaici. Ko kuma watarana haka Umman zata zauna da Muna a rumfarsu suna hira ko labarin yanda Shuwa Arab ke asirce mazajensu su rabasu da ‘yan uwansu. Ranar da kunnenta ta ji Muna na bawa Umma labari wai Ummii (Maman Laila) ita ta hana kishiyarta Tabawa sake haihuwa, kenan suma maganar ta iso gurinsu kuma da alama sun yarda da hakan. Watansu biyar da aure Aliyu ya samu canjin gurin aiki dalilin bud’e sabon reshe da kamfaninsu ta robobi ta yi a Kaduna garin Gwamna. Muk’amin Manajan kamfanin aka bashi bisa la’akari da kwazonsa da manyansa suka yi. Su Umma sun yi murna sosai da wannan cigaban Amma Aliyu bai fad’a mata cewa zai d’auki matarsa su bar Kano ba. Ya je Kaduna yayi sati biyu ya gane yanayin aikinsa ya kuma samu gidan da zasu zauna, sannan ya koma Kano da niyyar fad’awa Umma akan washegari zai juya Kaduna da Laila.
