Halysaah Page 119 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 119Mikewa Hadiyah tayi ta nufi kofa ta fita daga dakin Hajja fuskarta babu walwala kwata kwata, Ajay ya bi ta da kallon gefen ido, dakin da Umminta take ta tafi, ta sameta ita kadai tana waya da Abbanta, zaunawa tayi har Ummi ta gama wayar tana kallonta da damuwa tace “Ya aka yi daughter? An maki wani abu ne?” Hadiyah ta kalleta fuskarta a daure tace “Ummi ta yaya wannan er iskar zata zo Convocation dina ta dinga yawo da designers? Jakan hannunta na yau ma fa designer ne haka ma na jiya, sai da na gaya ma Ya Jawwad shekaranjiya mu je inyi shopping jaka da takalmi for my Convocation kamar nasan abinda zai faru kenan amma yace min wai ya gaji i should use the one of my lefe bayan an gama Convocation din sai mu je ya siya mun wanda nake so, yanxu gashi wannan matsiyaciyar ta zo sai flaunting designers take making me look miserable ni da occasion dina, 3 of my friends fa sai da suka kirani daxu da safe wai they wants to be friends with her don Allah in hadasu da ita, basu san er talakawa bace matsiyaciya luck ne kawai ya kawota gidan sarauta, ni ko nace masu nima ban san daga inda take ba, uninvited guess ce” Ummi dake ta kallon Hadiyah cikin bacin rai tace “To ke da yace ya gaji baza ki takura masa ba, banda iskanci ma me yayi na gajiya sai kace wanda yayi dako? Baki ji nima yanda raina ya ɓaci ba jiya da na ga yarinyar, dama ashe ita Jawwad din yace sai ya aura?” Hadiyah ta hade rai tace “Don Allah ki dena cewa haka Ummi, wannan ai ya zama past tense, bana ma son Ina tunawa, my problem now is the type of bags and shoes and even clothe she is wearing, hatta jewelries dinta fa me tsada ne sosai Ummi, me yasa shigarta zai fi nawa?” Ummi ta daure fuska tace “Ki kirasa yanxu kice masa ke lallai lallai yau kike son ku je ku yi shopping din nan, go and dress up and call him immediately, tana matsiyaciyarta uban me zata nuna maki? abinda ma gidan da uwarta da Ubanta ke ciki Jawwad din ne ya siya, daga baya bayan nan kuma muke samun labarin hatta kudin makarantar ta da kudin hayan gidan da take a Amurka Jawwad ke biya ashe” Hadiyah ta bude baki tana kallon uwarta with shock tace “Don Allah da gaske Ummi? Is this how poor and wretched they are?” Ummi tace “Ba shi yasa Mami ta gigice ba ta fita hayyacinta sai da tasan yanda ta bi ta rusa auren sannan hankalinta ya kwanta, nima kuma daga bangarena ban zauna ba ina ta yin nawa abun na ganin auren bai yiwu ba, shi ne don tsiya shi kuma Mai martaba ya maida aure kan Junaid, Oho dai shi ya sani, amma Allah ya sani ni har yau da Junaid na so ki ba Jawwad ba cause Junaid is the Heir to the throne not Jawwad, I want nothing but the best for you, kema ki gaji kakarki ki zama Sarauniya watarana, amma hakan bai yiwu ba” Hadiyah ta wani kalli Ummi tace “To ni me zan yi da wanda yace baya so na Ummi, beside i love Ya Jawwad soo Much, ni shi nake so ba Junaid ba” Ummi ta taɓe baki tace “Amma dai ai ba haka aka so ba wai kanin miji yafi miji, Gobe za mu je Sheffield tare da Hajiya Shema’u wajen yarinyar ta Basira kinsan bata da lafiya, yanxu yaushe Jawwad din yace za ku koma Nigeria?” Hadiyah ta girgiza kai tace “Bai gaya min sanda za mu koma ba” Ummi tayi kasa da murya tace “Toh ban san kwana nawa za mu yi a can Sheffield din ba, ita kuma Fulani Hafsat naji tana cewa za su je America ban san me zata yi a can ba, kinga kenan duk watsewa za mu yi, to yanxu zan baki sakon da nace zan baki in case bamu hadu ba kun tafi Nigeria” Mikewa Ummi tayi ta kulle kofar dakin da makulli ta tafi gun akwatinta ta bude ta fito da kayanta daya bayan daya daga cikin akwatin sannan ta ciro wani zani da ta nannade wata leda a ciki, sai kuma wani babban ledan daban shi ma ta ciro a akwatin ta dawo kusa da Hadiyah ta zauna ta bude ledan farko ta fara ciro kullin magunguna da wasu kwalabe kanana, sai kuma tayi kasa da murya tace “Da kin san uban kudaden da na kashe kan su wallahi baza ki yi wasa wajen yin amfani da su ba Hadiyah, and it’s for ur own good not mine, idan kika yi shashanci wajen amfani da su wallahi kanki za ki yi ma, jajircewa za ki yi kiyi duk yanda aka ce….” Hadiyah tace “Me zai hana ni amfani da su Ummi” Ummi tace “Ko wanne da takarda a ciki na rubuta yanda zaki yi amfani da shi” Hadiyah tace “To, kin ma san me Ummi komai sai ya ce Maminsa abun nan ya fara bani haushi wallahi, why always her? gashi ita ma bini bini ta kirasa a waya ko muna tare, she always have one or two things to speak to him about ni kuma na tsani haka, ko kuma idan yaje bangarenta sai ya dade bai fito ba wani lokacin har minti ashirin yana yi wallahi, kafin fa mu zo convocation din nan har na dena zuwa bangarenta in gaisheta nayi pretending bani da lafiya don haushi take bani wallahi yanxu, ko wani abun dadi ya siyo min ita ma sai ya siyo mata ya kai mata fa kamar wata kishiyata” Ummi ta hade rai tace “To ke uban me yasa zaki dora ma kanki dinga zuwa bangarenta gaisheta? Wa yace maki ana wannan haukan? To kuna komawa gida kiyi cutting din zuwa wannan gaisuwan in kun hadu cikin gida ki gaisheta amma kar ki sake zuwa part dinta, ita sanda aka aurota ko da yaushe take zuwa gaida Hajja ba sai ta ga dama ba?? sannan ki kwantar da hankalin ki wataran in ance yace Mamin ma haushi zai ji, kar ki wani damu, yanxu dai ki bi wannan magungunan step by step babu mistake, shi yasa ma duk na rubuta maki a takarda kuma wallahi ba karamin kudi na kashe ba use them wisely” Hadiyah na murmushi tace “In sha Allahu zan yi using dinsu yanda aka ce Ummi” Ummi tace “Kwanaki kika ce ma yarinyar kanwar babanki you are in pain always during intimacy, har yanxu hakan ne?” Shiru Hadiyah tayi, sai kuma ta sauke kanta, Ummi ta hade rai tace “In zaki bude baki ki min magana ki bude baki, kunyar me zaki ji, ko kina da wata uwar bayan ni ne? Duk wani abu da ya dameki talk to me, ba sai ma kin je kina magana da kowa ba kina tona asirin kanki, I know you are confuse shi yasa kika ma Marwana magana, but I am always there for you my sweetheart, Kar ki ji komai koma menene ki dinga gaya min, I am ur mother and also ur best friend, isn’t this how I brought u up?” Hadiyah da ke ta tunanin irin azaban da ta sha during those period duk da ita ce tayi ta shige masa lokacin har komai ya faru, after that kuma yaki daga mata kafa, ta girgiza kai a hankali tace “A’a na dena ji yanxu Ummi” Ummi tace “Good, dama it’s just for a while, it’s always like that for every woman” Daya ledan Ummi ta jawo wanda ke dauke da authentic magungunan mata masu kudin gaske, nan ta dinga nuna mata su da yanda zata yi using dinsu daya bayan daya, bayan ta gama nuna mata ta ajiye ledan tace “To ita Mamin na zuwa bangaren ki ne?” Hadiyah ta taɓe baki tace “A’a, kawai sanda na dena zuwa gaisheta ne da yace mata bani da lafiya shine ta ke shigowa ta dubani kuma pretending kawai nake yi don lafiyata qlau, ko fita zata yi fa wani lokacin sai tace ya kai ta sai kace wani driver dinta, so annoying, wani lokacin sai ki ga ta sa shi yayi transferring huge amount of money for her businesses, kuma ko musu baya yi mata” Ummi tace “Don’t worry, all that nonsense will come to and end soon, yayi resuming aiki asibiti ne?” Hadiyah tace “A’a sai mun koma zai yi resuming fully” Ummi tace “To yanxu ina zaki boye kayan nan kar wani ya gani?” Hadiyah tace “Cikin kayana mana Ummi” Ummi tace “Bazai ce zai bude maki akwatin ba?” Hadiyah tace “A’a, can kasan akwatin zan ajiyesa babu wanda zai gani” Ummi ta sake nannade mata ledan da zaninta, kayan matan ma ta kulle ledansa da kyau ta nannadesa da wani zanin sannan tace “A haka za ki saka su a karkashin akwatin, sannan ki kirasa kice ke shopping kawai zai kai ki, and you make sure duk abinda zaki dauka ya zamto designer ne a wajen” Hadiyah tace “Toh Ummi” Ummi tace “Amma dai je ki dauko akwatin naki, kar kije can dakin gantalallun ya matan can su saka maki ido” Hadiyah tace “Eh haka ma zai fi” Mikewa tayi ta nufi kofa ta bude ta tafi dakin da suke ita da cousins dinta ta dau akwatin ta zata fita, Iklima na kallonta tace “Can apartment din zaki koma ne Hadiyah?” Hadiyah ta yatsine fuska tace “A’a gyara kayan zan yi kawai” Daga haka ta fita ta koma dakin da uwarta take da akwatin nata. Khaleesat ta ɗaga kai ta kalli Baby da ta shigo dakin Hajja, Baby ta wara ido ta nufeta tace “Waow, kin yi kyau yau ma Aunty, I love your handbag, it’s soo cute” Tana fadin haka ta dauki jakar tana jujjuyawa with admiration, Khaleesat ta ɗan yi murmushi tace “Kina so ne?” Baby tace “Sure ina son irin sa” Khaleesat ta amshi jakar daga hannunta ta bude ta ciro wayarta dake ciki sannan ta mayar mata tana murmushi tace “To na baki” Ajay ya daga kai ya kalleta, ita dai taki yarda ta kalli inda yake zaune, Shahuda da Maryam dake dakin su ma sai da suka daga kai suna kallon Khaleesat, Baby kuwa har da tsallenta bayan ta amshi jakar tayi ma Khaleesat side hug tace “Thank you so much” Sai kuma ta nufi Ajay ta zauna gefensa tana nuna masa jakar tace “Yaya look, she just dashed me the bag” Ajay yace “Kin gode” Hajja tace “Ke haka ake yi Baby? Baki ga wayarta bane a cikin jakar?” Baby ta tura baki tana kallon Hajja tace “Ai dai tace ta bani kuma kin ji” Daga haka ta mike ta fita daga dakin looking so happy, Shahuda ta mike ta fice daga dakin, Hajja ta kalli Khaleesat tace “Ke kuma ai ba haka ake ba Jiddah ya za ki zo da abu tace tana so ke kuma ki dauka ki bata bayan kema amfani da shi kike, kamata yayi in ma zaki bata sai ko a gida amma ba a nan ba, kar ki sake yin haka” Khaleesat dai murmushi kawai tayi bata ce komai ba tana wasa da fingers dinta, Maryam ta tashi ita ma ta fita daga dakin cike da mamakin Khaleesat, wato ita ga ta isassa saboda ta nuna masu designers ba komai bane a wajenta idan tana son wani ma Ajay zai siya mata shi yasa ta kyautar da jakar a gabansu su gani, a stairs Baby ta hadu da Jay cikin farin ciki tana nuna masa jakar tace “Ya Jawwad look, matar ya Ajay ta bani jakar nan kyauta” Jay ya kalli jakar yace “Ohk… kin gode, is Hajja sleeping?” Ta girgiza kai tace “A’a tana zaune” Dakin ya nufa ita kuma ta sauka downstairs zata je nuna ma uwarta, Jay na shiga dakin suka hada ido da Ajay, shi ya fara dauke kansa ya karasa cikin dakin ya zauna, Khaleesat dai sai kallonsa take, Jay ya gaida Hajja, Hajja ta amsa tace “Duk yau baka shigo ba Jawwad ko kana can kana sana’ar” Calmly Jay yace “Eh bacci nayi” Hajja tace “Dama na fada, tunda naga baka shigo ba nace kana can kana ba bacci hakkinsa, to ka dai ci abinci ko?” Yace “Na ci” Mikewa Ajay yayi ya nufi kofa ya fita daga dakin, Hajja ta bi sa da kallo.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788*
