Halysaah Page 116 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 116Khaleesat na shiga apartment din ta samesa tsaye parlor, ta saci kallonsa zata wuce sama cikin tsawa yace”Come back here” Tsayawa tayi sai kuma ta juya ta kallesa ta bata fuska, using a serious tone yace “From henceforth Kika sake ce min zaki je wani waje zaki sha mamakin abinda zan maki i promise you, ba dai baki da kunya ba? Zan yi maganin ki” Kamar zata yi kuka tana turo baki tace “To ko ba karatu muka tsaya yi ba muna da Quiz da za mu yi” Da gudu Khaleesat ta wuce sama ganin ya nufota fuskarsa daure, ta shige dakinta ta kulle, sai da ta zauna gefen gado na kusan minti goma don seriousness dinsa ya tsorata ta, can ta e baki tamike ta shiga bandakin ta dauro alwala ta fito, bayan ta idar da sallah ta karasa bakin kofar a hankali ta bude tana leka downstairs amma bata ganin komai, corridor ta fito ta leka taga baya parlorn, a hankali ta fara sauka stairs har ta shigo parlon taga alamar ya tafi, dakinta ta koma ta dau duk kayan matan da Safiyyah ta kawo mata ta sake sauka kasa ta shiga kitchen tayi disposing dinsu a dust bin sannan ta koma sama, wanka tayi ta canza kaya zuwa na bacci, sannan ta dau wayarta ta bude ta kunna data ta kwanta, ko yunwa bata ji don hankalinta duk na kan abinda zata yi a wayar, hancinta ta kai wayar jin kamar kamshin turarensa a jiki, she was very surprise, ta sake shinshina wavar to be sure of it, taji kamshin turarensa dai wayar yake, can dai ta bude WhatsApp dinta, after waiting for some second for her messages ta fara scrolling tana neman numJay, dukiya dubawanta bata gani ba, ta shiga WhatsApp call logs dinta nan ma babu numbersa, mikewa zaune tayi with shock tana kallon wayar babu ko kiftawa, nan tayi searching Housemate da sauri taga bai fito ba, ta koma contact dinta nan ma taga babu number, kasa ko kwakkwaran motsi tayi a inda take zaune, cikin mutuwar jiki ta fara kokarin dialing number nasa thinking she still have it off hands kamar kwanakin baya amma duk yanda ta yi kokarin rubuto number sai taga ba haka yake ba, wasu hawaye ne suka cika idonta ta fada kan gado tana shesshekan kuka, ta yaya yasan password dinta har ya dau wayarta, is this even possible, ita bata taba bude wayarta a gabansa ba ai balle yaga password dinta, kuka sosai take ta ma rasa abinda take ji a ranta, me yasa zai dau mata waya bata nan… Washegari Khaleesat taki tafiya school tsabar bacin rai, tana ta kwance har karfe uku na yamma ko wank ta yi baballe breakfast, idonta duk sun kumbura don kuka, tun safe Safiyyah ke kiranta taki daga wayar daga karshe ma ta kashe wayar, sai kusan Magrib ta sauka kasa ta nemi abinda zata ci saboda yunwan da take ji, ga mamakinta sai taga foodstuffs bakin kofar kitchen din, da Household items for cleaning, ta hade rai ta tsallake kayan tayi wucewarta cikin kitchen din, bayan ta hada shayi ta debi cookies ta wuce sama abun ta….Washegari ma Khaleesat taki zuwa school tayi ta kwanciya a daki, wajen karfe sha daya ta kunna wayarta kamar Safiyyah jira take sai ga call dinta ya shigo, Khaleesat ta dinga kallon kiran kafin tayi picking tayi shiru, Safiyyah tace “Me yasa kika kashe waya tun jiya Khaleesat? Hope you are okay?” A hankali Khaleesat tace “Lafiya lau” Safiyyah tace “To me yasa kika kashe wayar? Kuma me yasa baki zo school jiyyau babayan kin san Friday ne Quiz din mu? Are you sure you are okay?” A hankali Khaleesat tace “Can you come over after school please?” Safiyyah tace “Sure, amma dai inji mijin ki baya nan?” Khaleesat ta hade rai tace”Bana son haka Safiyyah, it’s not funny” Safiyyah ta tabe baki tace “Toh naji, bayan azahar zan taho” Khaleesat tace “Apartment dina za ki zo” Safiyyah tace”Apartment din ki? Har yanzu kina apartment din kenan?” Khaleesat tace “Eh” Safiyyah tace “Ohk to i will come in sha Allah after today’s class” Daga haka ta katse wayar, a hankali Khaleesat ta ajiye wayar hannunta looking so gloomy, mikewa tayi ta sauka downstairs har sannan foodstuffs din suna nan bakin kofar kitchen kuma bata ga alamar an shigo gidan ba duk yau, ta kwashi kayan abincin ta kai kitchen bayan ta ajiyes inda ya kamata ta hada breakfast ta fita daga kitchen din, sama ta tafi don kar ma ya zo gidan ya ganta a parlorn, bayan ta gama breakfast din tayi wanka ta shirya sannan ta zauna gefen gado har sannan tana jin ranta babu dadi, ko bude WhatsApp din bata sake yi ba duk da tasan Umma ta ajiye mata sako, a haka Safiyyah ta zo gidan ta sameta, Safiyyah na kallonta bayan ta bude mata kofa tace “Ikon Allah, me ya faru?Why are you like this?” Hawaye ya cika idon Khaleesat tace “Kinsan daukar wayata yayi ya goge number Housemate dina?” Safiyyah ta zaro ido irin tayi mugun mamakin nan tace “Ya goge number Housemate din ki kamar yaya? Ya san password din ki ne?” Khaleesat na shesshekan kuka tace “Nima ban sani ba, kawai i can’t find the number again, har chat din mu an goge gaba daya” Safiyyah ta zauna gefen kujera still looking surprise tace “Amma ta yaya kika san shi ya goge ne wai?” Khaleesat tace “Ba na zo downstairs debar maki kayan shayi ba, and we left him upstairs? To ni da na koma na dau wayar naji yana kamshin turarensa beside in ba shi ba aljani ne zai dau wayar ya goge min number?” Safiyyah ta gwalo ido tace “Kika sani? Idan aljanin ne fa yaga kina neman kai kanki wuta ya goge lambar?” Wani shegen kallo Khaleesat tayi mata, Safiyyah ta sauke wani ajiyar zuciya tace “To Allah ya kiyaye amma abu bai yi dadi ba, ta yaya za a goge number a whole Housemate din ki just like that a wayarki?” Khaleesat ta wani harareta, sai kuma tace “Ni dai bani wayar ki in dau number” Safiyyah tace “Wani number?” Khaleesat tace “Na Housematena”Safiyyah ta gyara zama tace “Tabb, ai tun da naga yanda ya dinga rungume matarsa suna makale juna kamar za su dawo daya na goge lambarsa a wayata don ina taya ki kishi, ta yaya ke kina nan kina gantalar da aurenki saboda shi, shi kuma yana can yana bidirinsa da matarsa? Ke kina ganinsu kinsan an dirji amarci yanda ya kamata, shi yasa naji haushi na goge numbersa” Khaleesat ta hade rai tace “Me yasa za ki goge don Allah? Me yayi maki?” Safiyyah ta mike tace “Kinga yunwa nake ji kamar in ci babu, don Allah ki taimaka min da abinci, in kin dawo sai mu duba call logs nasan zaki gane number ai, ko da na goge yana nan call log” Khaleesat tace “Toh bari in dafa maki Indomie” Tashi tayi ta tafi kitchen feeling so much relieved, Safiyyah ta tabe baki ta fiddo wayarta ta canza saving din number Housemate, can kuma tayi tunanin kar kuma ace Khaleesat ta san farkon numbers din nasa tana dialing ya fito, hakan yasa kawai tayi copying numbersa tayi pasting ta WhatsApp number dinta ta bar shi wajen, sannan ta goge contact din nasa a wayarta, har ma da chat dinsu na WhatsApp sai da tayi deleting ta yanda dai Khaleesat bazata ga number ba ko ta duba….Khaleesat was so disappointed bayan ta duba wayar Safiyyah gaba daya babu alamar number Housemate dinta, ga dai shi tana ganin number a idonta amma in ta rubuta sai taga ba haka yake ba, ita dai Safiyyah tayi tagumi tana kallonta with serious face, sai kuma tace”Wallahi da na sani da ban goge ba, ni kuma nan taya ki kishi nake tun da naga hotunan Convocation din da suka yi da matarsa, ban san ke ko a jikin ki ba, baki ma ji haushi ba, ai da ban goge ba in nasan haka” Khaleesat tayi mata banza ta kauda kanta trying hard not to cry, Safiyyah ta tabe baki a ranta tana mamakin halin Khaleesat. Khaleesat na zaune department dinsu tare da Safiyyah, fitowar su daga aji kenan sun gama group discussion don exams dinsu is around the corner, Safiyyah ta gama wayar da take ta juya tana kallon Khaleesat ganin fuskarta babu walwala kuma tayi nisa tunanin da take, Safiyyah tace “Me kuma ya faru?Sarkin ‘yan damuwa, Why is ur face like this?” Khaleesat ta dan yatsine fuska tace “Nothing, kawai na gaji ne sosai” Safiyyah tace “Kin gaji ranan Monday?Karatu kika yi throughout weekend ne?” Khaleesat ta girgiza kai tace “Laundry nayi kawai jiya” Safiyyah ta dan kalleta tace “To jiya din ya je apartment din?” Khaleesat ta juya ta kalleta kamar jiran tambayar take ta girgiza mata kai a hankali tace “Bai zo ba” Safiyyah tace “To wai ba nace ki kirasa ba Khaleesat?” Khaleesat tayi shiru don tun last week Safiyyah ke fama da ita ta kira Ajay don rabonsa da gidan tun ranan da ya ajiye mata foodstuffs da Household items, washegarin ranan kuma ya tura mata 5k dollars ta account dinta, and this was almost 2 weeks ago, amma tayi ta nuna ma Safiyyah ita bazata kirasa ba, Safiyyah tace “Ke in an gaya maki magana kwata kwata baki ji, nace ki kirasa don this is so unusual of him ace har sati biyu bai je apartment dinki ba to see if you are alright” Khaleesat kamar bazata tanka Safiyyah ba kuma sai ta bude jakarta ta ciro wayarta ta shiga call logs ta nuna mata, amsan wayar Safiyyah tayi taga ta kirasa har sau hudu a ranaku daban daban last week, amma duk bai daga ba, Safiyyah ta daga kai ta kalleta tace “Are you sure he is okay?” Khaleesat ta bude hannu alamar bata sani ba ita ma, bayan few seconds a hankali tace “Har WhatsApp message fa nayi masa but he didn’t reply” Safiyyah tace “To amma dai nace ki je gidan ranan Friday kika ki, kika san ko bashi da lafiya ne all this while? Kema kinsan no matter how annoying you can be haka nan yake maki duk duk abinda ya kamata, meyasa baza ki je gidan ki duba if he is okay ba” Khaleesat ta zaro ido tace “What if stepmom dinsa da aunties suna nan har yanxu? ni dai bazan je ba tsoro nake ji” Safiyyah ta wani kalleta tace”What’s ur business with them? Ai dai ko suna nan sun san ba wajen saurayinki kika je ba” Khaleesat ta tabe baki tace “Ba inda zan je ni dai, i am afraid of them” Safiyyah tace “To kin huta” Canza topic din Safiyyah tayi, ita dai Khaleesat tayi shiru bata cewa komai, kana ganinta kasan she is not herself kawai gata nan gata nan dai ne, Safiyyah tace “Yauwa wai har yanxu baki samu number Housemate din naki ba, ina ta son in tambayeki sai inyi ta mantawa” Khaleesat taki tanka ta, Safiyyah ta mata kallon gefen ido, she could see how disturbed she is, a ranta kuwa taji dadin kin picking calls dinta da Ajay yayi gashi ta damu ta rasa sukuni, after half an hour Khaleesat tayi ordering Lyft da zai maida ta gida don gaba daya bata ma san hiran da Safiyyah ke mata ba she is not just assimilating, ta ma rasa me ke damunta this past days don ko abincin kirki bata ci, karatun ma ko ta fara sai taga bata fahimta, haka tayi weekend kamar mara lafiya taji gidan ma duk ya isheta, har ta isa gida bata sani ba cause she was just sitted absently a motar har sai da drivern Uber yayi mata maganar sun isa, bayan ta sauka daga motar ta shiga apartment dinta ta zauna kan kujera ta jingina da kanta, kullum ta dawo gidan keenlv take kallon ko ina na apartment din ko zata ga alamar da zai nuna ya zo amma sai taga babu ko wani alamar da ya nuna hakan, after almost 10 minutes of sitting down at the parlor ta bude jakarta a hankali ta ciro wayarta, numbersa tayi dialing ta tsura ma screen din wayar ido, amma har ya katse bai daga ba, turo baki tayi ta ajiye wayar gefen kujera. Ranan laraba Khaleesat sun fito daga lectures Safiyyah sai bata labarin Get together din da za su hada bayan exams take, don har da ita a masu shirye shiryen get together din, ita dai Khaleesat kawai tana zaune gefenta ne tana kallonta, Safiyyah ta rike haba tace “Ai ko ranan karya zan ma Ya Musty ince zan je apartment din ki baki da lafiya kuma mijinki ya je Nigeria, don kusan till down fa za mu yi a partyn…” Safiyyah ta gaji da surutunta ita kadai ganin Khaleesat ba biyeta zata yi ba tace “Ni dai tunda ba mu da abinda za mu yi gobe a makarantar nan bazan shigo ba gaskiya bacci na zan vi, ko ke za ki shigo?” Khaleesat ta sauke boyayyen ajiyar zuciya ta girgiza kai tace “Ko ran Friday ma ni bazan shigo ba na gaji, zan yi karatu a gida” Safiyya tace “You look pale kamar baki da lafiya” Khaleesat tace “I am having headache” Safiyyah tace “To Allah ya sauwake, in kin koma gida sai ki sha magani” Khaleesat bata ce komai ba tayi order din Lyft da zai maidata gida,Safiyyah tace “Wai kar ki ce min har yanxu Ajay bai je apartment din ki ba?” Khaleesat ta daga kai ta kalleta tace “Ko ki rakani can gidan nasu yau?” Safiyyah ta rike haba ganin yanda tayi request din da sauri kamar tana jiran tayi mata tambayar, Can Safiyyah tace “Uhm, ni kaza? Salon Yaya Ajay ya kora ni ko ya hadani da karensa in shiga uku” Khaleesat tace “Saboda me zai kore ki? Abinda ke ce ma kika fara assuming ba shi da makarantar nan bazan shigo ba gaskiya bacci na zan vi, ko ke za ki shigo?” Khaleesat ta sauke boyayyen ajiyar zuciya ta girgiza kai tace “Ko ran Friday ma ni bazan shigo ba na gaji, zan yi karatu a gida” Safiyya tace “You look pale kamar baki da lafiya” Khaleesat tace “I am having headache” Safiyyah tace “To Allah ya sauwake, in kin koma gida sai ki sha magani” Khaleesat bata ce komai ba tayi order din Lyft da zai maidata gida,Safiyyah tace “Wai kar ki ce min har yanxu Ajay bai je apartment din ki ba?” Khaleesat ta daga kai ta kalleta tace “Ko ki rakani can gidan nasu yau?” Safiyyah ta rike haba ganin yanda tayi request din da sauri kamar tana jiran tayi mata tambayar, Can Safiyyah tace “Uhm, ni kaza? Salon Yaya Ajay ya kora ni ko ya hadani da karensa in shiga uku” Khaleesat tace “Saboda me zai kore ki? Abinda ke ce ma kika fara assuming ba shi da ba shi da lafiya? Kilan kuma hakan ne, don ni ban taba kiransa bai daga ba ko bai bi kirana ba, even the messages i sent him on Whatsapp tick just once, he is not online for more than a week, kuma karen baya gidan yanxu ai”Safiyyah tayi shiru tana kallonta ganin damuwar dake fuskarta, can tayi wani murmushi tace “Toh amma duk kinsan this is unusual of him amma kika ki zuwa gidan ki dubasa yau kusan sati uku?” A hankali Khaleesat tace”Allah tsoro nake kar inje su Aunty suna gidan har yanxu, ni tsoronsu nake da gaske” Safiyyah tace “To bari in baki shawara, bakin ki alekum ki shirya ki je da daddare, kinsan dai da daddare definitely suna daki balle wannan katon gidan ma har ki shiga ki fita babu wanda zai sani” Khaleesat tace “Tabdi, da daddare fa,Aa ni bazan iya zuwa da daddare ba” Safiyyah tac shikenan ke kika sani, tunda baki jin magana, kar ya sa ki je” A haka suka rabu Khaleesat ta koma gida gaba daya bata da walala, tana komawa nan parlor ta kwanta kan 3 seater saboda azababben ciwon da kanta ke mata, sai take jin kamar zazzabi ne ma zai ruteragashi ruwan shayi kawai ta sha kafin ta fita daxu, don ko girkin ma bata yi yanxu.
