Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 7 Hausa Novel

Ranar talata ce Kuma a ranar Khadeeja take sa ran zata koma makaranta, tun dare ta sanarwa Mustapha. Ya amsa mata ba tare da wata matsala ba.Haka ta tashi tun kafin asuba ta shirya yaran tsaf, suna tafiya makaranta tayi Maza tayi wanka sannan ta dan rage aiki don tana da lecture 9am.Bayan sun gama breakfast ta mike daga dining table tana tattara plates din tana cewa ‘Babe bari na saka hijabi na sai kayi dropping dina a school.’Yace ‘Ok, but kada ki bata lokaci don kada ki makarar da ni.’Kusan a lokaci guda suka fito daga dakin kowa a shirye, sun kawo tsakiyar parlor ta dubeshi tace ‘Yau Kai zaka dauko yara ko? Don ni Ina da lectures 9am to 4pm.’Ya dan bata rai cikin nuna damuwa yana cewa ‘I thought Zaki dawo ki daukosu, kin san ni sai 5pm nake tashi daga wajen aiki.’’To ai ka ga nima sai 4pm.zan tashi, Kuma I can’t miss these lectures don last week ma ka ga ban je ba. Gara dai ka sami wani ya dauko su kawai.’Ya Bude motar ya zauna yayinda itama ta zauna a kujerar gaba, yace ‘To ai ko an daukosu ma wajen wa za a kawo su tunda ba kya gidan?’’Haka ne fa, most days ma lectures dina har 4pm ne.’Suka yi shiru na dan lokaci; gaba daya ma shi ya manta tana wata makaranta. Yanzu ya take so yayi da yaran? Wa zai daukosu Kuma wa zai zauna da su? Wannan ai shine an gudu ba a tsira ba.Muryarta ce ta katse masa tunani tana cewa ‘Babe ka ga da muna da Mai aiki sai ta daukosu ta shiryasu su tafi islamiyya kafin na dawo; musamman idan Babba ce.’Cikin jin dadi yace ‘kwarai kuwa, zan yiwa Yaya Jidda magana sai a sami Mai aikin kafin next week.’’No, ka bari idan na yiwa Mommy magana zata sa a sami kla garinsu, mutanen suna da Amana sosai ga aiki.’Ba tare da ya kalleta ba yace ‘Ki bari tukunna idan aka rasa a wajen Yaya Jidda sai a gayawa Mommy din.’Bata ji dadin wannan maganar ba Kuma ta san da ya kalleta da zai gane sai dai son zuciyarsa me a gabansa; don haka sai kawai tayi shiru. Bata son abinda zai hadata da Yaya Jidda don gaba daya matar ta fice daga ranta, ta kula kamar tana neman laifinta ne ido rufe.PAGE 24MIJIN MARIGAYIYAA Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)A bakin department kawayenta Maryam da Jamila suka tareta, ana ta ihu ana murna ga amaryar Babe. 9am to 11am suka fito daga lecture, wanda zai yi musu 12pm to 2pm ya aiko aka gaya musu ba zai zo ba. Don haka suka wuce hostel dakin su Maryam. Suna shiga Khadeeja ta nemi waje ta kwanta, Jamila ta tabata tace ‘Ke da zaki bamu labarin amarci Kuma sai ki kama wani bacci.’Ta bige hannunta tana cewa ‘Barni wallahi baccin da yake kaina ya fi na wata guda.’Maryam tayi dariya tace ‘Barta Jamila, kin san kwanan ibada takeyi.’ Haka sukayi ta hirarrakinsu a kanta tana ta faman bacci. Har suka gama hirarrakinsu tana bacci, don haka basu tasheta ba suka fice sayen abinci. Basu dade da fita ba ta farka, bayan ta wanke fuska ta yi alwala tayi Sallah. Ta zauna a kan dadduma tana tunani; tun ba ayi nisa ba ta gaji da auren Mustapha. To amma tana son shi, matsalarta kawai yaransa kuma da yanda ba zai bari tayi musu tarbiyya ba. Kusan tun da ya kawo mata yaransa bata huta ba, wannan baccin da tayi ji tayi kamar an dauke wani dutse da ta dade tana dakonsa. Ko Ina a jikinta ciwo yake, fatan ta kawai a samo Mai aikin nan ko zata huta. Duk da tana tsoron a kawo Mai aiki daga gidan Yaya Jidda; gani take kamar CCTV camera ce kawai za a kawo mata. Tana zaune tana wannan lissafin wayar Yaya Mama ta shigo; bayan sun gaisa tace ‘Ya na ji ki haka ne amarya? Ko bacci kike yo ne?’’Wallahi Ina hostel Yaya, kin ganni gyangyadi na gama.’’To ya maganar Mai aikin, tunda dai gaskiya aikin gidan nan ya fi karfinki ga yara hudu.’’Ya ce yayarsa zata kawo mai aikin.’’To ai shikenan, duk daya ne. Kawai dai idan ta zo sai ki sa ido, kada ki bari ta shisshige miki; ke ko a cikin gidan ki kula kada ki kuskura ki dinga barinta tana shigar Miki daki, kitchen da store ma duk ki kula da motsinta. Yaran ma ki dinga kula da alakarta da su idan ba haka ba sai ta zame muku fitna.’ Yaya Mama ta fada.Cikin sanyin murya tace ‘To Yaya.’Yanda taji muryarta Bai gamsar da ita ba tace ‘Ko da wata matsala ne?’ ‘No, ba wani problem. Ni ga ni ma a school na dawo sai yamma zan koma gidan.’’Ok, Mommy ma tace min kun je weekend.’’Eh.’Suka dan taba hira daga baya sukayi sallama suka ajiye wayar.Khadeeja ta bi wayarta da kallo kawai sai ji tayi tana hawaye; tayi kewar gida sosai, gaba daya a yanzu ma bata san me take so ba, kawai dai ta gaji.Motsin su Maryam ya sa ta share hawayenta ta basar.……..Kwana biyu da yin maganar kuwa sai ga mai aiki; dattijuwa ce Baba Habit. Yaya Jidda da kanta ta kawo ta.Sai da ta tafi sannan Khadeeja ta nuna mata dakin yara inda a nan zata dinga kwana. Ta nunnuna mata aiyukan kafin yaran su dawo daga islamiyya.Nan da nan ta fara ba tare da nuna wata kyuya ba, ga shi tana da hanzari wajen yin aikin.______’Yan kwanakin nan gaba daya bata jin dadin jikinta, gaba daya bata San me yake damunta ba.Ranar laraba ce, tana jin Mustapha yana tashinta daga bacci kafin asuba yana cewa ‘Ki tashi yara zasu makara fa.’Ta juyo tana yanutsa fuska tace ‘Babe bana jin dadi wallahi, daga kwancen nan ma ni jiri nake ji ga headache. Bana jin zan iya tashi yau.’Ya Mika hannu ya taba jikinta yana cewa ‘Subhanallah, me yake damunki?’’Nima ban sani ba.’ ta amsa muryarta na rawa.Ya matsa ya leka fuskarta, sai kuma ya sauka daga kan gadon yana cewa ‘Bari na gama da yara sai na kaiki asibiti, amma ki daure ki tashi ki shirya.’’To, ka bari gobe ma je asibitin mana.’’No, yau zamu je kin ga ana maganar za a saka lockdown saboda COVID 19 idan aka rufe ban san lokacin da za a bude garin ba. Gara muje mu gama komai a siyo Miki magani yanzu haka malaria ce.’ Ya fada sannan ya fice daga dakin.Baba Habi ce ta shirya yaran, duka da kasancewar ita bata iya girki ba haka suka hakura Afaf ta nuna mata ta dafa musu indomie. Bayan sun Sha shayi da burodi ta zuba musu indomie a lunchbox. Duk yanda ya so ga komawa baccin bayan asuba ranar haka ya hakura ya zauna a parlor din yana taya su shiryawa.Bayan ya Kai su makaranta ya dawo ya shirya, ya taimaka Khadeeja itama ta shirya suka wuce asibiti suka bar Habi a gidan.Suna zuwa likita ya tabbatar musu da cewa ciki ne da ita, aka bata magungunan suka taho.

Back to top button