Uncategorized

‘Ya’Yan Buhari Guda Biyu Sun Rasu Sakamakon Cutar Sikila

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ‘yayansa biyu ne suka rasu sakamakon cutar Sikila.  

 Buhari ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a wajen wani gagarumin taro da ‘yan uwa da abokan arziki suka shirya masa kan bikin cikarsa shekara 80 da haihuwa a fadarsa.

Karanta>>> Yadda zaka shiga wayar abokinka ta cikin wayarka.

Yayin da yake jawabi game da rayuwarsa shugaba Buhari ya ce ‘ya’yansa biyu ne – da ya haifa tare da matarsa ta farko mai suna Safinatu – suka rasu sakamakon cutar Sikila.     

BBC Hausa sun rawaito Buhari ya ƙara da cewa hakan ya tilasta masa yin gwajin ƙwayoyin halitta a lokacin da ya tashi auren matarsa ta yanzu Aisha Buhari.     

Karanta>>> Yadda Zaka Sami Kyautar Kudi Ta Opera Mini

Ya ce ya dage cewa dole sai matar da zai aura ta kasance tana da ƙwayoyin halitta na AA, don kauce wa ɗaukar cutar Sikila ga ‘yayan da zai haifa kasancewar shi yana da ƙwayoyin halitta na AS.     

Buhari ya auri Safinatu a shekarar 1971. sun kuma haifi ‘ya’ya biyar tare da ita.

Karanta >>> Ga Wa Sabuwar Dama Daga Tashar Arewa24

Back to top button