Uncategorized

Tambayoyi 100 Don Mata Akan Haila, Biki, Nifasi, Azumi, Sallah Da Hajji

 

 Daga, SP Imam Ahmad Adamu Kutubi

Bismillahir Rahmanir Rahim

TAMBAYOYI A KAN TSARKI, JININ HAILA DA NA BIKI

TAMBAYA TA 1: Shin mace mai jinin biki za ta zauna har kwana arba’in ne ba za ta yi Sallah ba kuma ba za ta yi Azumi ba, ko kuma abin Iura daga gareta za ta yi tsarki, ta yi Sallah kuma nawa ne mafi karancin kwanakin da za ta yi kafin ta yi tsarki?

AMSA: Mace mai jinin biki ba ta da kaiyadadden lokaci sai dai duk Iokacin da jinin ya zo mata za ta zauna ba za ta yi Sallah ba kuma ba za ta yi Azumi ba kuma mijinta ba zai iya saduwa da ita ba. Amma idan ta ga jinin ya dauke, wato ta tsarkaka ko da kafin ta cika kwana arba’in ne ko da jinin iyakacin kwana goma kawai ya yi ko kwana biyar kawai sai ya dauke, to sai ta yi wanka ta yi Sallah, ta yi Azumi kuma mijin ya sadu da ita babu laifi a cikin hakan.

Sai dai abin da ya fi muhimmanci shine shi jinin biki al’amari ne kebantacce kuma hukuncinsa yana ratayuwa ne da shi, wato idan jinin ya zo to hukuncinsa yana nan ba za ta yi Azumi da Sallah ba. Kuma idan jinin bai zo ba to hukuncinsa baya nan. Duk lokacin da ta yi tsarki to ta wofanta daga hukuncinsa.

Sai dai idan jinin ya karu matar ta zamo mai jinin Istihada, wato jinin ciwo ke nan, sai ta yi lissafln iya kwanakin al’adarta sai ta yi wanka ta yi Sallah. Sai ta nemi maganin wannan jinin na cuta.

TAMBAYA TA 2: – Mai tambaya yana cewa:- Mace ce bayan an yi mata aure da wata biyu bayan ta yi al’ada ta yi tsarki sai kuma ta fara ganin wani digon jini kadan; to shin wannan matar za ta sha Azumi ne idan lokacin Azumi ne ko kuma me za ta aikata?

AMSA:- Mas’aIoIin mata a cikin aI’ada da aure kogi ne wanda ba shi da iyaka sai dai ka’ida ta gaba daya cikakkiya shi ne idan mace ta tsarkaka ta ga tsarki tabbatacce daga al’adarta – wato fitan wani farin ruwa bayan daukewar jinin al’ada, to idan wani bakin jini ya zo bayan ta ga wannan farin ruwan ko wani fatsi-fatsi ko wani dan digon jini ko wani danshi to duk wannan abubuwan ba haida bane kuma baya hana Azumi da Sallah da jima’i domin shi ba Haida ba ne.

Ummu Adiyya ta ce mu ba ma kirga baki da kanknin jini wani abu (wato ba mu dauka haida ba). Bukhari ne ya fito da hadisin. Abu Dauda kuma ya kara da cewa idan bayan mace ta yi tsarki tabbataccen tsarki sai ta ga daya cikin wadannan abubuwa to ba zai cutar da ita ba kuma ba zai hanata Sallah da Azumi da saduwa da mijinita ba.

Sai dai yana wajaba a kan mace kada ta yi gaggawa wajen yin wanka har sai ta ga tabbataccen tsarki domin wasu matan daga sun ga jini ya bushe a gabansu sai su yi gaggawar yin wanka tun kafin su ga farin ruwan ko daukewar jinin gaba daya. Don haka ne matan Sahabbai suke aikawa wajen Uwar Muminai Aisha, Allah ya yarcla da ita, suke aikawa da auduga ajikin audigar kuma suna shafa jini sai ita kuma ta ce musu kada ku yi gaggawa har sai kun ga farin ruwa sannan ku yi tsarki.

TAMBAYA TA 3:- Me tambaya yana cewa:- Mene ne hukuncin samuwar mace a cikin Masallaci mai Alfarma alhalin tana haida don sauraron Hadisai da khudubobi? ‘

AMSA:- Ba ya halatta ga mace mai haida ta zauna a cikin Masallaci mai Alfarma ko wanin wannan masallacin daga cikin masallatai sai dai yana halatta a gareta ta wuce ta masallacin ko kuma ta dauki wani abu a cikin Masallacin da makamantan hakan, kamar yadda Annabi (SAW) yacewa A’isha yayin da ya umarce ta da ta dauko masa dardumar sai ta ce masa ai dardumar tana masallaci ita kuma ga shi tana haida, sai Annabi (SAW) ya ce mata ai haidan ba’a hannunki yake ba (wato za ta iya shiga masallacin don ta dauko dardumar.

Idan mace mai haida ta wuce ta cikin masallaci ta tabbatar cewa jinin ba zai zuba ba a ciki ba, to babu laifi a kan haka.

Amma idan tana nufin ta shiga ta zauna a masallacin ne to bai halattaba. Dalilin haka kuwa shi ne Annabi (SAW) ya umarci mata su fita zuwa gurin Sallah lokacin Sallar ldi ya umarci ‘yan mata da tsofaffi da budurwaye da masu haida sai dai masu haida ya ce su fita daga cikin filin Sallah su je gefe.

To wannan yana nuni a kan baya halatta ga mace mai haida ta zauna a masallaci don sauraron huduba ko don sauraron darasi ko Hadisai.

TAMBAYA TA 4:- Shin yana wajaba ga mace mai jinin biki ta yi Azumi, tayi Sallah idan jini ya dauke mata kafin kwana arba’in?

AMSA:- ‘E’. Idan mace ta samu tsarki, jinin biki ya dauke mata kafin kwana arba’in yana wajaba a gareta ta yi Azumi idan ya kasance a cikin Ramadana ne, kuma ya wajaba a gareta ta yi Sallah.

Kuma ya halatta ga mijinita ya sadu da ita. domin ta tsarkaka, bata tare da abin da zai hanata yin Azumi da Sallah kuma ya halatta a sadu da ita.

TAMBAYA TA 5:- ldan wani digon jini kadan ya fitowa mace a ranar Azumin Ramadana ita kuma matar tana Azumi shin Azuminta ya inganta?

AMSA: ‘E’. Azuminta ya inganta kuma wannan digon jini kankani ba komai ba ne domin daga jijiya yake.

Kuma Aliyu bin Abi Dalibi Allah ya yarda da shi ya ce: “wannan digon jini kamar habo ne na hanci, ba haida ba ne, haka AIi ibn Abi Dalib ya amtbata (RA)

TAMBAYA TA 6:- ldan mace taji dumin jinni amma jinin bai fito kafin magariba ba, ko kuma ta ji radadi na ciwon al’ada amma kuma jinin bai zo ba to shin zuminta na wannan ranar ya inganta ko kuma ya wajaba ta rama?

AMSA:- Idan mace ta ji dumi na haida kuma tana Azumi amma kuma haidan bai fito ba sai bayan Sallar Magriba, ko kuma ta ji radadi na haida amma kuma jinin bai zo ba sai bayan Sallar Magariba bayan fudowar rana, to Azuminta na wannan rana ingantacce ne kuma ba za ta rama wannan Azumin ba in na farilla ne kuma ladan Azumin bai baci ba idan Azumun ya kasance na nafila ne.

TAMBAYA TA 7:- ldan mace ta ga jini amma kuma bata tabbatar cewa jinin haida ba ne to mene ne hukuncin Azuminta a wannan rana?

AMSA:- Azuminta ya inganta a wannan rana domin asalin jinin ba na haida ba ne, har sai lokacin da haida ne ya bayyana a gareta” sannan Azuminta zai baci.

TAMBAYA TA 8:- Wani lokaci mace tana ganin wani gurbi na jini dan kadan ko kuma wani kankanin digon jini daban da wani lokaci fa ganshi a lokacin al’adanta, wani lokaci, kuma ta ganshi ba’a lokacin al’adarta ba, to mene ne hukuncin Azuminta a wadannan halaye guda biyu?

AMSA:- Amsar tambaya mai kama da wannan ta gabata a baya, sai dai idan wannan digo ya zo ne a lokacin haidarta.

Kuma ta Iura da cewa yana daga cikin jinin al’ada wanda ta san shi to wannan ya kasance haida.

TAMBAYA TA 9:- Idan mace ta ga jini a lokacin al’adarta, ta ga jini a ranar farko ammna a rana ta biyu ba ta ga jinin ba har tsawon wuni guda, mene ne a kanta, me za ta aikata?

AMSA:- Abin da yake zahiri shi ne lallai wannan tsarki ko kuma bushewar jini da bai zubo ba, wanda ya auku ga wannan mata a kwanakin haidarta to a lissafin haida yake ba’ a daukan shi tsarki, to don haka sai ta wanzu a cikin hani na abin da mai haila take bari – kamar Sallah, Azumi da sauransu.

Amma sashin malamai sun ce:- wacce ta kasance tana ganin jini rana daya washegari kuma ta ga babu jinin idan haka take yi to idan jinin ya zo haida ne, idan kuma ya dauke tsarki ne, sai ta yi ta kirgawa har sai ya kai kwana goma sha biyar, wato inya karu zata kara kwana uku, idan ya zarce ta yi wanka ta nemi magani. Idan wani watan ya zo za ta yi karin kwana uku to idan ya kasance kowane wata tana yin karin kwana uku amma jinin ba ya tsayawa har ya kasance ta zama mai al’adar kwana goma sha-biyar to daga nan ba za ta sake yin karin ba idan wani wata ya zo idan jinin ya wuce wadan nan kwanakin sai ta yi wanka, tayi Sallah, ta ci gaba da ibada sai ta nemi magani don ya zama jinin ciwo.

Kuma shi wannan karin kwanaki da ake yi ba’a lokaci daya ake yinsa ba idan da mata tana yin kwana uku ne da wani watan ya zo sai ta ga ya wuce kwana uku bai dauke ba to sai ta kara kwana uku ya zama kwana shida kenen idan yayi kwana shida bai tsayaba sai tayi wanka tayi Sallah ta nemi magani. To idan wani watan ya zo ta zama mai al’adar kwana shida kenan. Idan jinin yayi kwana shida bai tsaya ba sai ta kara kwana uku akai ya zama kwana tara idan ta yi kwana tara jinin bai tsaya ba sai ta yi wanka ta yi Sallah. To haka za ta yi ta yin kari har zuwa lokacin da zai kai kwana goma sha biyar daga nan kuma ba wani karin da za ta dada akai.

Wannan shi ne zance mafi shahara a mazhabar, Ahmad bini Hanbali, Allah ya jikansa.

TAMBAYA TA 10:- A rana ta karshe daga cikin ranakun haida amma kafin ta yi tsarki matar ba ta ga gurbin na jinin haida ba, shin za ta yi Azumin wannan rana alhali kuma ba ta ga farin ruwa ba, ko kuma ya za ta yi?

AMSA:- Idan ya kasance a al’adar matar bata ganin farin ruwa idan jini ya dauke mata kamar yadda ake samun wasu daga cikin mata, idan jini ya dauke musu ba sa ganin wannan farin ruwan daga baya, matar za ta yi Azumi.

Idan kuma ya kasance a karshen al’adar tana ganin farin ruwa idan jini ya dauke mata to ba za ta yi Azumi ba har sai taga wannan farin ruwan.

TAMBAYA TA 11:- Shin lallai ne mai haida ta canza tufafinta bayan ta yi tsarki kuma ta san cewa jini bai taba tufafinba kuma babu najasa a jikin tufafin?

AMSA:- Ba lallai ba ne ta canja tufafinta domin shi jinin haida ba ya bata jiki, shi dai jinin haida yana bata abin da ya taba ne kawai, wato idan ya taba abu to sai ya zama najasa saboda huka ne Annabi (SAW) ya umarci mata da su wanke tufafinsu idan jinin haida ya sameshi wato idan jinin ya taba shi kuma su yi Sallah da tufafin bayan sun wanke.

TAMBAYA TA 12:- Shin danshi da yake fitowa mace wannan danshin tsarki ne ko najasa, Allah ya saka muku da alheri?

AMSA: Abin da yake sananne dai a gurin ma’abota ilimi shine dukkan abin da yake fitowa daga hanyoyi guda biyu to NAJASA NE sai dai abu daya ne kawai ba najasa ba – shi ne maniyi. Shi dai maniyi abu mai tsarki ne in kuwa ba shi ba to duk abin da yake fitowa ma’abocin kazanta ne yake fitowa ta hanyoyi guda biyu. To wannan danshi najasa ne kuma yana daga cikin abin da yake warware Alwala kuma karin bayani akan wannan, ya kasance dukkan abin da yake fitowa mace na wannan ruwa najasa ne kuma dole ne ta sake Alwala. Wannan shi ne abin da aka samu bayan an yi bincike tare da sashin malamai.

Sai dai ni ina da dan damuwa domin sashin mata suna kasancewa tare da wannan danshi kodayaushe to abin da za ta yi shi ne ta yi mu’amala irin mu’amalar wanda yake da yoyon fitsari. Sai ta dinga yin Alwala a lokacin ko wacce sallah, idan lokacin sallah ya yi sai ta yi Alwala ta yi sallah.

TAMBAYA A KAN ALWALA

 TAMBAYA TA 13:- Shin yana halatta nayi AIwala alhalin a jikina ko fatata akwai wani nau’i na maiko ko man-shafawa?

AMSA:- ‘E”, yana halatta a gare ki ki yi Alwala koda a jikin ka akwai irin wadan nan man-shafawi da sharadin wannan man bai kasance wanda zai hana ruwa shiga jikin ka ba ne kamar (Jan-farce). Idan kuma ya kasance mai kauri ne wanda zai hana ruwan shiga fatar jikin wato kamar (Janfarce) to ba makawa sai an cire shi kafin a yi Alwala.

TAMBAYA TA 14:- Idan mace mai ciki ta ga wani jini kafin ta haihu da kwana daya ko biyu), shin za ta bar yin Azumi da Sallah saboda wannan jini ko ba za ta bari ba?

AMSA:- Idan mace mai ciki ta ga jini kafin haihu da kwana daya ko biyu tare da ita akwai tabbacin cewa wannan jini na biki ne, to sai ta bar yin Sallah da Azumi a daIilin wannan jini.

Idan kuma babu wata alama da ta nuna ya yi kama da na biki, wato idan ba jinin biki ba ne to wannan jinin ya zama gurbataccen jini, ba zai hana yin Sallah da Azumi ba.

TAMBAYA TA 15:- Mene ne Haida?

AMSA:- Haida shi wani jini ne da yake fita da kansa daga gaban mace. Wace za ta iya daukar ciki.

TAMBAYA TA 16:- Kashi nawa ne mata suka kasu dangane da haida?

AMSA:- Mata sun kasu kashi uku: (1) Wacce ta fara (2) Wacce ta saba (3) Mai ciki.

TAMBAYA TA 17: Nawa ne mafi yawan kwanakin haida ga wacce ta fara?

AMSA:- Mafi yawan kwanakin haida ga wacce ta fara kwana goma sha biyar ne (15).

TAMBAYA TA 18:- Mene ne hukuncin wacce ta saba yin haida?

AMSA:- Wacce ta saba al’ada ta san kwanakinta

Amma idan jinin ya wuce mata ya karu a kan kwanakin da ta saba, to sai ta kara kwana uku matukar karin kada ya wuce kwana goma sha biyar.

Kuma nayi bayanin yadda za ta yi karin kwanaki a kowane wata. Na yi bayani a baya.

TAMBAYA TA 19:- Mene ne hukuncin mai ciki? AMSA:- Haidar mai ciki bayan ya yi wata uku to haidar ta kwana goma sha-biyar ko kafin sha biyar.

Amma bayan ciki ya yi wata shida kwana ashirin ne, wato mafi yawan kwanakin haidar. Amma in ya wuce hakan to ya zama jinin ciwo, sai ta yi wanka ta ci gaba da ibadarta kamar yadda bayani ya gabata a baya.

TAMBAYA TA  20:- Mene ne hukuncin mata idan jinin ya dauke?

AMSA:- Idan jinin ya dauke sai ta kirga kwanakinsa har sai ta cika aI’adarta kamar yadda ta saba wato idan jini ya dauke kafin ya kai kwanakin da ya saba yi mata sai kuma ya dawo to sai ta dinga kirga kwanakin har sai ya kai iya kwanakin da ta saba yi. Kamar jinin ya zo yau sai ya dauke gobe sai kuma ya dawo, jibi to sai ta hada na yau dana jibin ya zama kwana biyu kenan to haka za ta yi ta lissafi har sai ya cika kwannakin da ta saba.

TAMBAYA TA 21:- Shin yana halatta ga mai haida ta yi Sallah da makamantan sallar?

AMSA:- Ba ya halatta ga mai haida tayi Sallah da Azumi da Dawafi da shafan Al-Qur’ani da shiga Masallaci.

TAMBAYA TA 22:- Shin za ta rama daga cikin sallah ko a Azumi?

AMSA:- Za ta rama Azumi amma ban da Sallah.

TAMBAYA TA 23 :- Shin karatunta wato (mai haida ya halatta?

AMSA:- “E”, karatunta ya halatta

TAMBAYA TA  24:- Menene ajikinta baya halatta ga mijinta a lokacin da ta ke haida?

AMSA: Farjinita ne ba ya halatta ga mijinta, kuma abin da yake tsakanin cibiyarta zuwa gwiwoyinta a lokacin da take haida, har sai tayi wankan tsarki, wato wankan daukewar jinin haida.

T AMBAYA  TA 25:- Mene ne Nifasi?

AMSA:- Shi Nifasi shi ne wani jini da yake fitowa a lokaci haihuwa.

TAMBAYA TA 26:- Shin Nifasi wato jinin biki kamar jinin haida yake a wajen hukunci? AMSA:- Jinin biki kamar jinin haida yake wajen haninsa, wato duk abinda ake bari idan jinin haila ya zo to haka ake bari idan jinin biki yazo kamar barin Sallah da Azwni da sauran ibada.

TAMBAYA TA 27:- Nawa ne mafi yawan kwanakin jinin biki?

AMSA:- Mafi yawan kwanakin jinin biki kwana sittin ne (60).

TAMBAYA  TA 28:- To mene ne hukuncin mace idan jinin biki ya yanke mata kafin ta cika kwanna sittin.

AMSA:-  Idan jinin ya dauke mata kafin,ta cika kwana sittin to sai ta yi wanka ta yi Sallah ta yi Azumi, idan Iokacin Azumi ne, kuma mijinta zai iya saduwa da ita tun da ta tsarkaka.

TAMBAYA TA 29:- Sannan kuma me za ta aikata idan jinin bikin ya dawo mata?

AMSA: Idan jinin ya dawo mata, idan ya kasance tsakaninsa da na baya wanda ya dauke din nan kwana goma sha biyar ne tsakaninsu ko kuma ya fi kwana goma sha biyar sai ya dawo, to na biyun nan haida ne.

Idan kuma tsakanin na farko da na biyun, wanda ya dawo bai kai kwana goma sha biyu ba, to sai ta hada lissafin kwanakin da da farko ya kasance daga cikan lissafin kwanakin jinin biki.

TAMBAYOYI A KAN AZUMI DANGANE DA MAI JININ HAILA KO BIKI

TAMBAYA TA 30:- Shin mace mai jinin haida da  mai jinin biki za su ci abinci su sha abin sha lokacin Azumin Ramadana?

AMSA: “E”.  Za su ci su sha abin sha a  Azumin Ramarlana, sai dai abin da ya fi kyau hakan ya zamo a asirce, idan ya kasance akwai wani daga cikin yara tare da wannan matar a cikin gida, domin cin abincin matar da kuma shan abin shan nata zai rikitar da yara, to don haka sai ta ci a boye kar yaran su gani. Bayan ya dauke sai ta rama Azumin da ta sha.

TAMBAYA TA 31:- Mene ne ra’ayin ka dangane da shan kwayoyi na hana jinin haida wanda yake zuwa a mata duk wata menene ra’ayinka dangane da kwayoyinn da ake sha don hana wannan wai don matan su samu su yi Azumi tare da mutane,  don kar su sha Azumi?

AMSA:- Ni dai ina gargadi ina tsoratarwa daga shan wannan kwaya, akawi cutarwa a cikinta cutarwa mai girma. Kuma na tabbatar da hakan ta gurin likitoci.

Kuma abin da za’ a gayawa mata shine:­ Wannan jini Allah ne ya rubutawa ‘yan Adam don haka su yarda da abin da Allah ya rubuta kuma su yi Azumi a lokacin da babu abin da zai hana su yin Azumin. Idan kuma ya zo lokacin da suke da abin da zai hana su yin Azumin to su sha Azumin suna masu yarda da abin da Allah mai Girma da Daukaka ya kaddara.

TAMBAYA TA 32:- Mene ne hukuncin dandana abinci lokacin Azumin Ramadana alhalin matar kuma tana Azumi?

AMSA:- Hukuncinsa babu laifi da shi idan dai akwai wata bukata da ta janyo zuwa ga yin hakan, sai dai matar kuma ta tofar da  abin da ta dandana da sauri kuma kar ta bari ya shiga cikin makwogwaron ta.

TAMBAYA TA  33:- Idan mace haidarta ta yanke kafin fitowar Alfijir amma ba ta yi wanka ba sai bayan fitowar alfijir yaya Azuminta?

AMSA: In mace jinin ta ya yanke kafin fitowar Alfijir ko da daminti daya ne matukar ta tabbar da jinin ya yanke da auduga ko da farin kyale to azuminta bai baciba. Don tayi azumine lokacin da jininta ya dauke. Kodayake ba ta yi wanka ba sai da Alfijir ya keto, to ba komai a kanta, hakanan kuma da za ta wayi gari da janaba amma ba tayi wanka ba sai bayan fitowar Alfijir to Azumin ya yi.

Da wannan ne na keso na ja hankalin mata don wasun su sukanyi bude baki bayan rana ta fadi amma basu yi Sallah ba sai jini ya zo musu suna gani kamar ba su da wannan Azumin. Wannan magana tasu ba ta da asali tun da tariga ta sharuwa kuma rana ta fadi, ko da minti da yane sai jini yazo mata to babu abin da ya shafi Azuminta.

TAMBAYA TA 34:- Idan mace mai jini biki jininta ya yanke kafin akwana arba’in (40) shin ya halatta ta yi Azumi ta yi Sallah?

AMSA:- ‘E’, ya halatta duk Iokacin da jini ya dauke wa mace bayan haihuwanta tilas ta yi wanka in a watan Azumi ne ta ci gaba da Azumin ta don ta tsarkaka. Don haka babu abin da zai hana Sallah da Azumi da kuma saduwa da mijinta

TAMBAYA TA 35:-  ldan mace al’adanta kwana bakwai ko takwas sannan jinin ya karu da kwana daya ko kwanuka biyu, to mene ne hukuncinta?

AMSA:- ldan mace al’adanta kwana shida ne, ko bakwai ko takwas daga shida sai yaki tsayawa ya kai kwana bakwai, ko takwas ko tara, ko kwana goma, kai ko kwana goma sha-daya. To za ta bar Sallah da Azumi, har sai jinin ya dauke. Don Annabi (S.A.W) bai iyakance iyakansa ba ya dangantan ne da gwargwadon al’adan da mace take yi. Don haka nema Allah (S.W.T.) yake cewa: “Suna  tambayarka meye hukuncin haila, sai Allah Ya ce kace  kazanta ce kula da wannan ayah. Duk lokacin da mace take tare da wannan jini dolene ta bar Sallah har sai ta yi wanka. In ya ragu a gwargwadon da take yi shi kenan. In kuma ya kara karuwa, matukar bai wuce kwana goma sha biyar ba. Amma ba’a lokaci daya ake karin ba kamar yadda ya gabata.

TAMBAYA TA 36: Wai tilas ne mace mai jinin biki ta zauna ba Sallah, ba ta Azumi har kwana arba’in? Ko kuma in ya yanke kafin kwana arba’in tana iya yin Sallah da Azumi?

AMSA: – Mace mai jinin biki ba wai sai ta kai kwana arba’in ba. ldan jinin ya yanke, ko bayan kwana goma ne ko kwana biyar sai ta yi wanka, tayi Azumi, ta yi SaIlah, har ma mijinta ya saduwa da ita. Koda a ranar da ta haihu ya dauke sai ta yi wanka ta yi Sallah.

TAMBAYA TA 37:- Idan mace taga dan digon jini kadan sai ta ci gaba da Azuminta har zuwa karshen Watan Azumi, shin azuminta na nan?

AMSA:- ‘E’, Azumin ta yayi, don wannan jini dan digonnan ba komai ba ne. Wannan jini yana daga jijiya ne. Don Hadisin da aka karbo daga Aliyu dan Abi Talib (RA) yace irin wannan digon habo ne kawai da ke fitowa daga hanci ba haida ba ne, haka  aka karbo daga Aliyu (RA).

TAMBAYA TA 38:- Idan mace mai haida, ko biki jininta ya dauke kafin fitowar Al-fijir, amma ba ta yi wanka ba sai bayan fitowar Al-fijir, shin Azuminta ya yi?

AMSA:- ‘E’, Azumnta na nan, idan dai har ta yi tsarki kafin fitowar Al-fijir haka yake ga mace mai haida da mai biki, don wadannan suna daga cikin wanda Azumi ya wajaba a kansu. Don kamar wanda ya wayi gari ne da janaba, amma bai yi wanka. Don Allah (SWT) Yana cewa a cikin Al-Kur’ani  Mai  Girma, yanzu mun halarta muku ku sadu da matayenku a cikin daren Ramadana don neman abin da Allah (SWT) ya rubuta muku na arziki. Kuma ku ci, ku sha har sai bakin zare (wato fitowar Al-fijir). To tun da Allah (SWT) yayi izini ana iya saduwa da iyali har zuwa fitowar Al-fijir ka ga kenan wanka sai bayan Al-fijir ya keto. Sabo da Hadisin A’isha (RA), Annabi yana wayan gari da janaba wanda ya sadu da iyalensa. Wannan ya nuna Annabi (SAW) ba ya wanka sai bayan fitowar AI-fijir.

TAMBAYA  TA 39:- ldan mace ta ji alamun jini amma bai fito ba, ko dan dumi amma bai fito ba da ta duba, shin Azumin ta ya yi? Ko za ta rama?

AMSA:- Idan mace ta ji alamun jini ko dumi, amma bai fito ba, da ta duba ba ta ga jini ba amma ga shi tana Azumi, amma bai fito ba sai bayan faduwar rana to, Azuminta bai baci ba. Tun da jini bai fito ba sai bayan rana ta fadi.

TAMBAYA TA 40:- Idan mace ta ga jini amma ba ta san a’ina ta same shi ba, to menene hukuncin Azuminta?

AMSA:- Azuminta na wannan rana bai baci ba. Idan ta duba da wani kyalle ko auduga kuma dai ba haida take yi ba har sai ta sami hujja kwakkwara don asali ta dauka ba haida ba ne.

TAMBAYA TA 41:- Wani lokaci mace tana ganin digon jini kadan, a waje waje a jikin tufarta da rana; wani lokaci tana ganin haka lokacin al’adarta, wani lokaci ba lokacin al’adartaba, to mene ne hukuncinta a wannan lokaci biyu, ko halaye biyu?

AMSA:- Irin wannan tambaya mun amsa ta a baya to amma in ta ga wannan digon jini a ranakun al’adarta, to wannan ba tababa haida ne, ba ta da Azumin wannan rana.

TAMBAYA TA 42:- Mace mai haida ko jinin biki za ta iya ci da sha da ranar Azumi?

AMSA:- ‘E’, za ta iya ci da sha meye zai hana, amma ta ci a boye in akwai yara a gidan, don karya rikita yara kanana.

TAMBAYA TA 43:- In jini ya yanke a lokacin Sallar La’asar shin Azahar da La’asar ne za ta yi ko La’asar ne kawai?

AMSA:- Maluma sun yi sabani, wasunsu sun ce Azahar da La’asar ne za ta yi, wasu suka ce babu wani dalilin wajibcin Azahar a kanta. Don lokacin jini bai yanke ba, don Annabi (SAW) ) ya ce wanda ya riski raka’ah daya a Sallah La’asar, kafin rana ta fadi, to hakika ya riski Sallar La’asar. A wannan Hadisin a lura ya ce ta riski La’asar, bai ce ta riski Azahar da La’asar ba, sai ya ambaci La’asar kawai.

TAMBAYA TA  44:- Idan mace a lokacin da take al’ada, sai ta ga jini Iokacin al’adarta, sai ya yanke a kwana daya meye hukuncinta?

AMSA:- Idan mace ta ga jini a kwana daya, rana na biyu ba ta gani ba to wannan bushewar gabanta ne amma tana nan, sai ta zauna kar ta yi SalIah, kar tayi Azumi. Wasu malamai suka ce, in jinin zai zo kwana daya sannan kwana na biyu sai ya dauke, to ranar da ya dauke tayi tsarki sai ta yi wanka ta ci gaba da SalIah da Azumi, in kuma ya dawo to sai ta ajiye Azumi da Sallah. Har ya kai gwargwadon kwanakin da take ganin jini matukar bai wuce kwana goma sha biyar ba, in ya wuce kwana goma sha biyar, to ciwo ne sai ta nemi magani ta ci gaba da Sallah da Azumi.

 ABIN YI IDAN WANKAN JANABA DA NA BIKI SUKA HADU KAN MACE

TAMBAYA TA 45:- Mijina ne ya sadu da ni da na je wankan janaba sai na ga jinin haida ya zo min to yaya zan yi?

AMSA:- Wanda mijinta ya sadu da ita dataje wankan janaba sai taga jini yazo mata ba zatayi wankan janaba ba sai ta tsaya sai wannan jinin ya dauke sai tayi wanka daya da niyya biyu. Niyya ta farka don wankan janaba sannan kuma daga baya tayi niyyar wankan haida.

TAMBAYA TA 46:- Mace bata yi Sallar Azahar ba Iokacin Salar La’asar ta dauki buta za ta yi alwala sai jini ya zo mata. To idan jinin ya dauke za ta yi Azahar da La’asar ne ko meye hukuncinta?

AMSA:- Idan mace ba ta yi Sallar Azahar ba  har Iokacin Sallar La’asar ya shiga to idan jinin ya dauke za ta biya Sallar Azahar ne kawai banda La’asar don Iokacin sallar La’asar jini yazo mata, mai jini kuma lokacin da take jini babu Sallah a kanta

TAMBAYA TA  47:- Karshen daukewan jinin mace sai ba ta ga jini ba kuma ba ta ga farin ruwa ba, me za ta yi?

AMSA:- In ya zama al’adarta ya dauke kamar yadda wasu mata suke, to shi kenan sai taci gaba da Azumi. Amma in ya zama al’adarta tana ganin farin ruwa duk lokacin da jini ya dauke to ba za ta yi Azumi ba sai ta ga wannan farin ruwa.

HUKUNCI KAN DALIBA MAI AL’ADA DA KARATUN AL-QUR’ANI

TAMBAYA TA  48:- Mene ne hukuncin mace mai al’ada ta karanta Qur’ani, ko da ka ko ta rike Qur’ani a halin lalura ga shi ita kuma  dalibace. Shin ya halatta ta karanta Kur’ani da ka ko da littafi?

AMSA:- Babu laifi ga mai haida ko jinin biki ta karanta Qur’ani kan ta haddace kamar malama ko mai karantarwa. Wacce kullum sai ta karanta wani juzu’i da dare ko rana, babu laifi saboda lalura. Amma don neman lada bai halarta. Don mafi yawan malamai suna ganin mai haida ko mai biki bai halarta ta karanta Kur’ani ba.

TAMBAYA TA  49:- Mace mai haida ko biki zata iya canza kayanta, tare da tasan cewa jini bai shafi kayanta ba, shin dole ne sai ta kwabe kayan?

AMSA:- Ba wai sai ta canja kayanta ba don  jini baya bata shi, yakan bata inda ya taba ne. Don haka Annabi (SAW) ya umarci mata in suka ga jini a tufarsu, sai su wanke inda ya taba, su yi Sallah da tufar.

MATAR DA BIYAN BASHIN AZUMIN RAMADANA NA SHEKARU SUKA KAMATA

TAMBAYA TA 50:- Mace ce ta sha Azumin kwana bakwai lokacin da take biki, har wani  Ramadana ya zo ba ta biya ba har kuma cikin Ramadana na biyu shi ma ta sha na kwana bakwai, kuma ya zamo tana ciyarwa saboda rashin lafiya wanda take tare da shi. Sannan ga Ramadana na uku ya kusa zuwa, to mene ne hukuncin ta?

AMSA:- Kar mace ta zama kamar yadda tambayar yake, wato in ba ta da lafiya ne babu damuwa, lokacin da ta sami lafiya sai ta biya na shekarar can baya dana bara amma idan sakaci ne to, bai halarta a gareta fa sha Azum,i ta sake bata biya ba, har wani Ramadana yazo bata biya ba. In kuma tayi haka to tayi laifi. An sami Hadisi daga A’isha (RA), ta ce “ya kasance Annabi yana Azumi amma bana iya biya sai an shiga watan Sha’aban to idan muka lura da wannan Hadisi na A’isha (RA) yana nuna duk cewa yanda za’ayi mutum ya biya kafin Ramadan. To ita wannan mata ta duba ta gani in da ganganne ta yi gaggawan tuba ga Allah (SWT) ta kuma biya abin da ake binta. In kuma rashin lafiya ne, to Allah Ya sani, Shi Ya sa ta jinkirta shekara daya ko biyu, to babu laifi duk, lokacin da ta sami lafiya, sai ta rama abin da ake binta na ramuwa.

TAMBAYA TA 51:- Mace ne tasha Azumi, amma bata rama ba kuma ga sabon Azumi ya zo?

AMSA:- Wanda ta jinkirta ba ta rama ba har wani Ramadan ya zo, to ta tuba ga Allah (SWA) da wannan mummunan aiki da ta yi don bai halarta ba mutum ya yi jinkirin biyan Azumi har wani Azumi ya zo. Don A’isha (RA) tace: Anabina Azumin watan Ramadana amma ba na biya sai a watan Sha’aban. Wannan Hadisi na A’isha (RA) bai halatta ga mutum yayi jinkirin abin da ake binsa na Azumi har wani Ramadan ya zo ba. Don haka ta tuba zuwa ga Allah (SWT), in sabon Azumin ya wuce ta biya amma zata ciyar gwargwadon Azumin da ta sha, amma ya wuce ta rama.

 HUKUNCI KAN SHAN  MAGANIN HANA HAILA DON YIN AZUMI

TAMBAYA TA 52:- Menene ra’ayinku a kan mace ta sha kwayar hana ganin jini don ta sami Azumi tare da jama’a?

AMSA:- Ina tsoratar da wacce za ta yi haka don wannan kwayoyi yana cutarwa sosai. Domin likitoci sun yi bincike, yana cutar da mahaifa;  kan an hana jini fita kuma yana cutar da jijiyoyi, kuma yana cutar da jinin jiki don wannan jini Allah (SWT) shi ya kaddara wa mata ya fita to, hana shi illa ne babba don haka ne muke gani kiyi Azumi kawai lokacin da kika sami damar yi amma in jini ya zo ki bar shi ya fito in kin yi haka kin yarda da kaddaran Allah kenan. Bayan ya wuce sai ki rama.

TAMBAYA TA 53:- Wannene yafi, mace tayi Sallah a dakin tane, ko ta tafi masallaci, In ya zamo akwai wa’azuzzuka da tunatar wa?

AMSA:- Abin da ya fi, mace ta yi Sallah a dakinta, saboda hadisin Annabi (SAW), da yake cewa: gidajen mata shi ya fi alkairi su yi SaIlah a ciki don fitar mata akwai fitina a ciki. Don haka mace ta zauna a dakinta ya fi mata aIkairi. Dangane da wa’azi kuma da ta ji a masallaci da nasiha ta samu cassette ta sanya a dakinta ya fi.

TAMBAYA TA 54:- Yaya dandana abinci ga mace mai Azumi da rana, don ta ji ko gishiri yo ji?

AMSA:- Idan har an dandana ba a hadiye ba, aka tofar, wani abu bai wuce makogwaro ba, to babu damuwa, Azumi bai karye ba.

TAMBAYA TA 55:- Ni mace ce, cikina na yi bari a wata uku tun shekara guda banyi Sallah ba bar sai dana yi tsarki, sai aka ce min dole ne sai na biya wadancan salloli ni kuma ban san yawan su ba?

AMSA:- Abin da yake sananne ga malamai, in cikinta ya zuba da wata uku, idan halittarta uku na mutum cikakke, to wannan jini daya biyo jini ne na nifasi (wato haihuwa) ba za ta yi Sallah ba, ba za ta yi Azumi ba, idan kuma halittar bata cika ba wannan jini na ciwo ne, sai ta cigaba da SalIah, amma ta nemi magani. To sai ta yi tunani. in cikin ya zube ne ko ta yi bari, in ya kai kwana tamanin (80) sai ta biya Sallar kwana tamanin in kuma ba za ta iya sanin kwanakin ba, to sai ta yi ta yin SalIah har sai ta sakankance ta biya Sallah da ake bin ta.

TAMBAYA TA 56:- Nice tunda Azumi ya wajaba akai na inayi. Sai dai kwanakin da nake haida bana biyansu. To mene ne hukunci?

AMSA: – Amma abin akwai bakin cikin in wannan abin ya faru tsakanin matan muminai to ita wannan alamun abubuwa biyu: ko don jahiIci, ko don wulakanta addini. Dukansu biyu musifane. Amma dai shi jahilci, maganisa neman iIimi da kuma tambayar abin da ba ka sani ba. To, amma sakaci maganinsa tsoron Allah (S.W.T) da kuma kiyaye dokokinsa da kuma jin tsoronsa in mutum yana aikata wannan to, yayi gaggawa zuwa ga nemam yardan Allah. Don haka shawara ga wannan mata dangane da wannan aiki, ta tuba ga Allah, sannan ta yi kirdado ta biya gwargwadon ikonta abin da ta sha. Da wannan ne zata kubutar da kanta. Muna kuma roka mata Allah ya karbi tubanta.

MACEN DA HAILA TA ZO MATA BAYAN SHIGAR LOKACIN SALLAH

TAMBAYA TA 57:- Menene hukuncin macen da haida ya zo mata bayan shigan lokacin Sallah, shin ya wajaba ta biya in ta yi tsarki. Kuma mace ce ta yi tsarki kafin fitar Sallah (wato lokacin sallah)?

AMSA:- Idan mace haila ya zo mata lokacin Sallah, ya wajaba ta biya wannan Sallah wacce ba ta riga ta yi ba jini ya zo mata, don Iokacin ya yi bata riga ta yi ta ba; Don Annabi (SAW) yace duk wanda ya riski Sallah a cikin Sallah ya sami Sallah. Haka ma idan mace ta riski gwargwadon raka’a daya a cikin Sallah, to za ta biya wannan Sallah. Haka kuma in mace ta yi tsarki, sai ta sami ko da raka’ah daya ne to dole ne ta biya wannan sallah.

TAMBAYA TA 58:- Ina Sallah sai jini ya zo min?

AMSA:- Idan haida yazo wa mace, baza ta biya wannan Sallah ba in tayi tsarki. Don Annabi (S.A.W.) ya ce ai mata basa Sallah ba sa Azumi. Don haka malamai suka ce ba za ta biya wannan Sallah ba. Amma kan tayi tsarki ko da saura raka’a ah daya, to za ta biya wannan Sallah in ta yi tsarki a wannan Iokacin.

TAMBAYA TA 59:- Shin ruwan nan dake saukowa mata fatsi-fatsi ko fari-fari bayan haila ta dauke, shin najasa ne, ko ba najasa ba. Kuma kafin kowance sallah sai an sake alwala?

AMSA:- Wannan ruwa ba najasa ba ne sai dai in ya fito bayan an yi alwala yakan warware alwala, don ba sharadi bane ace abin da ke warware alwala ya zamo najasa. Don ga tusa ba ta najasa jiki amma tana fitowa ta warware alwala. Don haka in ya fito tana da alwala tilasne ta sake alwala. Amma in har ko yaushe haka yake fitowa to babu damuwa, ya zama irin mai ciwon yoyon fitsari kenan.

ALWALAR MACE MAI YOYON RUWA DA WASU HUKUNCE-HUKUNCE A KANTA

TAMBAYA TA 60:- Mace ce, ta yi Sallar Asuba da alwala alhali tana mai yoyon ruwa, ya halarta ta yi Sallar Walaha da wannan alwala?

AMSA:- Mai irin wannan yoyon ruwa baya halatta tayi Sallar Walaha da alwalar Sallar Asuba don kuwa ba bayan Sallar Asuba take za’a yi ba, sai bayan fitowar rana don ita mai wannan yoyon ai kamar mai ciwon istihala ne. Tilasne ta yi alwala a kowane Sallah. Annabi (SAW) ya ce mai istihala tilas ne ta yi alwala a kowane Sallah. Lokacin salloli kuma gashi:

1. Lokacin Sallar Azahar: Da zaran rana ta dan karkata da tsakiyar sama har zuwa La’asar.

2. Lokacin Sallar La’asar: Daga shigan SalIar La’asar har zuwa rana ta yi fatsi-fatsi har zuwa faduwarta.

3. Sallar Magriba: Daga faduwar rana har zuwa bayan jan dake yamma (wato Shafaq).

4. Sallar Isha’i: Daga bayan shafaq, kuma har zuwa dare na karshe, har zuwa fitowar alfijir.

5. Sallar Asuba: Daga fitowar alfijir har zuwa dab da fitowar rana.

TAMBAYA TA 61:- Ya halalta mace mai irin wannan ciwo ta yi Sallar nafiIa na rabin dare da alwalar Isha’i.

AMSA: Bai halatta ba har in ta kai rabin dare. Ta sake aIwaIa. Wasu kuma suka ce in dai ta tabbatar alwaIar tana nan ba sai ta sake alwala ba.

TAMBAYA TA 62:- Yaushe ne karshen lokacin Sallar Isha’i kuma yaya zan yi in gane?

AMSA:- Karshen lokacin Sallar Isha’i shi ne in dare ya raba. Yadda za’a gane haka kuma ta raba tun daga faduwar rana zuwa fitowar alfijir biyu. To kashi na farko Iokacin Sallah Isha’i kenan, kashi na biyu kuma shi ne lokaci na Sallar Isha’i da kuma Sallar Asuba.

TAMBAYA TA 63:- Wancan ruwa in ya zamo ya zo ya yanke sai kuma ya dawo, kamar ta yi alwala kafin Sallah sai ruwa ya dawo. To mene ne hukuncinta?

AMSA:- Indai ya zamo yakan yanke ya dawo to hukuncin sai ta yi alwala ta yi SalIah. In kuma babu bayanin lokacin yankewarsa to sai ta yi alwala ta yi Sallah a lokacin kowa ne SalIah. Babu komai a kanta.

TAMBAYA TA 64:­ Mene ne hukuncin wanda  wannan ruwa ya taba rigarsa? Ko jikinsa ko tufafinta?

AMSA:- Tun da ba kazanta ba ne babu komai akai sai dai in najasane to sai a wanke tufar ko jikin da ya taba.

TAMBAYA TA 65:- To yaya amsa kan wannan yoyon ruwa bai zo daga Annabi (S.A.W) alhali mata suna son a warware musu matsalolin addininsu?

AMSA:- Saboda wannan yoyon ruwa ba duka mata ne suke yi ba, maIaman Usul sun ce dan kadan ba ya cikin lissafi.

TAMBAYA TA 66:- Wasu suna cewa kai ne ka ce ba sai an sake alwala ba ga mai yoyon wannan ruwa?

AMSA:- Wanda ya ce haka ba gaskiya ya fada ba. Ina gani dai kila ya fahimci maganata ne inda na ce ba ya warware alwala.

HUKUNCIN JININ BIKI DA KE FITOWA MATA KAFIN HAILA

TAMBAYA TA 68:- Mene ne hukuncin jinin baki da ke fitowa mata kafin haila, kwana daya ko biyu yana fita fari, siriri kuma kamar zare, ko makamancin haka, to kuma in yazo bayan. haila menene hukuncinsa?

AMSA:- In ya zo kafin haila to wannan alamar haila ne kuma haila ne amma in ya zo bayan haila to sai ta jira kadan. Don wannan bakin ruwan yana tattare ne da haila, sai ta jira kadan har ta jira daukewarsa.

Don A’isha (RA) ta ce kar ku yi gaggawa har sai kunga farin ruwa fat. Allah shi ne mafi sani.

HUKUNCE-HUKUNCEN HAILA KAN MACE MAl AIKIN HAJJI DA UMRAH

TAMBAYA TA 69:- Mace ce ta yi niyyar Haiji sai jini ya zo mata. Da suka zo mikati jinin bai dauke ba. Sai ta yi wanka tasa harami suka zo Mina sai jini ya dauke to sai ta zo ta yi Umrah, ta gama cikin tsarki ta zo tana Dawafin aikin Hajji sai jini ya dawo. Sai taji kunyar bayyana wa waliyin ta har ta gama aikin Hajji sai da suka dawo garinsu sai take fadan wannan matsala. To mene ne hukuncin ta?

AMSA: Inta tabbata wannan jinin haidane yam mata to wannan Dawafin baiyiba sai ta dawo ta sake wannan Dawafi in kuma jinin ba jinin haila bane cikowan jama’ane wajen aiki ko wani ciwo ko matsatsi to wannan Dawafinta yayi, kenan hajinita yayi.

TAMBAYA TA 70:- Mace ce ta zo da niyyar Umrah bayan tayi harami, bayan ta zo Makka sai jini yazo mata kuma mijinta ba zai iya jirantaba to menene hukunci a nan?

AMSA:- ldan haka ya faru in mazauna Saudiyyane tayi Umrah amma in ba mutumiyar kasar ba ne, dawowa zai yi mata wahaIa sai ta yi kunzugu ta yi Dawafi, ta yi Sa’ayi, ta rage gashinta, a wannan lokaci don Dawafinta ya zamo lalura kenan – lalura kuma tana haIalta abinki.

TAMBAYA TA 71:- Mace ce musulma haida yazo mata a kwanakin Hajji, menene hukuncinta?

AMSA:- Wannan ba zai yiwu mu amsa ba sai munganta mu tambaye ta, awane lokaci ne haida yazo mata don haida baya hana wani aikin Hajji, wani kuma yakan hana don haka ne babu yadda za ta yi Dawafi sai tana da tsarki. Amma shauran aikin za ta iya yi.

TAMBAYA TA 72:- Ni ce na zo da mijina daga Madinah don aikin Hajji na yi duk aikin Hajji amma Dawafin aikin Hajji ya zo min sai na yi hadaya na yi komai na dawo gida da niyyar  shekara mai zuwa inyi Dawafin Ifada da na Ban Kwana, sai wani ya ce min ai Hajjin ya baci tun da ban yi Dawafin Ifada ba wai, sai na sake aikin Hajji gaba daya. Shin gaskiya ne?

AMSA:- Kai wannan bala’ine babba ga mutum ya amsa abin da bai sani ba. Hajji ki bai baci ba, ba don kina iya komawa kiyi Dawafil Ifada. Don shi Dawafin ban kwana baya kan mata masu haida. Don hadisin Dan Abbas (RA) ya kamata masu aikin Hajji ko Umurah su zama karshen rabuwan su da Makkah, dawafin ban kwana. Amma mata masu haida sai Annabi (SAW) ya yafe musu. Wannan kenan in kin je kin yi Dawafin Ifada to Hajjin ki ya yi daidai.

TAMBAYA TA 73:- Mace ce mai jinin biki a rana ta takwas amma ta fara tana da tsarki, za ta iya wanka sannan ta kara Dawafin aikin Hajji?

AMSA:- Bai halatta ta yi Dawafi ba har sai ta sakankance jinin ya dauke, yana gama daukewa sai ta yi wanka ta yi Sa’ayi, to shi kenan saboda an tambayi Annabi (SAW) menene hukunci wanda yayi Sa’ayi kafin dawafi, Annabi (SAW) ya ce hajji ya yi ba komai.

TAMBAYA TA 74:- Mace ce ta yi niyyar ta yi aikin Hajji alhalin tana mai haida lokacin da ta zo Makkah sai ta wuce Jiddah daga can Jiddah sai ta yi tsarki ta yi wanka ta kuma zo ta yi aikin Hajjin to shin aikin ya yi?

AMSA :- Hajjin ta yayi daidai babu komai a kanta.

TAMBAYA TA 75:- Nice na tafi don yin aikin Umrah sai jini ya zo min na zauna a Makkah sai nayi tsarki sai na yi niyyan Umrah a Makka sai nayi aikin Umrah shin Umrah ta ta yi?

AMSA:- Umrarki ba tayi ba. Don yadda za a yi mutum ya wuce mikati babu harami. Don kina iya aikin Umrah da Hajji dalili kuwa Asma’u bint Umaisin matar Sayyidina Abubakar ta haihu a Zul-Khulaifa sai ta aika tana mai tambaya ko tayi Hajji? Sai ya ce mata ki yi wanka, kiyi kunzugu kisa harami don jinin haila kamar jinin bikine. Duk hukuncinsu daya don haka ne sai mu ce wa matan za ta yi Umra amma in tana haila ta yi wanka ta yi kunzugu ta sa haraminta amma ba zata shiga Dakin Ka’aba ba sai ta zauna a dakinta har sai jini ya dauke don haka Annabi (SAW) yace wa Ai’sha (RA) lokacin da take haila duk abinda ya kama na aikin Hajji za ki yi  amma ban da Dawafi har sai kin yi tsarki.

Wannan shine ruwayar Imam Bukhari amma a ruwayar Imam Muslimu, abin da yace, Ai’sha lokacin da tayi tsarki sai tayi Dawafi sannan tayi Safa da Marwa sai ya nuna kenan ashe mace in tayi niyyan Hajji ko Umrah sai haida yazo mata kafin Dawafi to za ta zauna ba za tayi Dawafin ba, ba za tayi Sa’ayi ba har sai ta tsarkaka. Amma da ta riga tayi Dawafi da ta gama sai jini yazo mata to ko da batayi Sa’ayi ba to tana iya yin Sa’ayi. Don Sa’ayi babu sharadin tsarki daga haila.

TAMBAYA TA 76:- Nine na zo Makka dani da matata domin yin Umrah to da muka zo nina riga na gama Umrah ita kuma sai haila tazo mata, to yaya za muyi?

AMSA:- Dangane da matarka dole ne ta jira har sai tayi tsarki kafin ta yi Umrah. Domin lokacin da Safiyya jinin haila ya zo mata sai Annabi (SAW), ya ce ko tsararriya ce, sai Sahabbai suka ce ai ta yi Dawafil Ifada sai ya ce to ta yi kunzugu. Wannan hadisi yana nuna  Annabi ya ce ita katangaggiya ce, yana nuna cewa idan mace ba tayi Dawaful Ifada ba sai haila ta zo mata to to tilasne ta jira sai ya dauke tayi Dawafi, haka ma mai Umrah idan haila ya zo mata dole ne ta jira kafin dawafi.

TAMBAYA TA 77:- Mace ce mai haila tana iya yin Sa’ayi? Kuma idan mutum ya shigo ta Safa da Marwa zai iya yin nafilar gaisuwar masallaci?

AMSA:- Ba shakka wajen Sa’ayi baya cikin Dakin Ka’aba don haka ma aka sa wata gajeruwar katanga tsakaninsa da Masallacin Ka’aba. Don haka ne da ace yana cikin Masallacin Ka’ aba da mace in tana jinin haila ba dama ta yi Sa’ayi don haka ne ma idan mace ta riga tayi Dawafi amma bata yi Sa’ayi ba sai jini ya zo mata tana kunzugu, wannan kenan ya nuna mace tana zuwa wajen Safa da Marwa koda tana haila ne, ita kuma wacce ta shigo ta Safa da Marwa ba laifi tana iya yin sallar nafila ta gaisuwar masallaci.

TAMBAYA TA 78:- Na taba yin aikin Hajji sai jini ya zo min sai naji kunya ban gayawa wani ba sai nayi Sa’ ayi, mene ne hukunci?

AMSA: – Bai halatta ba ga mace ta yi Sallah tana da jinin haila ko jinin biki, a Makkah take ko a garin da take, kai koma a kowanne waje take saboda Annabi (SAW) yace mace in tana haila ba za ta yi Azumi ba. Saboda haka Dawafin nan da tayi bai yiwu ba amma Sa’ayin da ta yi ya yi, wannan aikin da ta yi laifi ne ya kamata ta tuba ga Allah Ta’ala. Dole ne ta sake yin Dawafi na dole in matar mai aure ce mijinita ba zai sadu da ita ba, ta yi wannan Dawafin in kuma ba ta da aure ba za’a daura mata aure ba sai ta yi Dawafin. Allah ne mafi sani.

TAMBAYA TA 79:- Idan mace haila ya zo mata ranar Arfa, yaya za ta yi? .

AMSA:- Idan haila ta zo wa mace a Arfa to ba damuwa sai tayi kunzugu tayi dukkan abin da alhazai suka aikata, sai dai ba za ta yi Dawafi ba sai ta yi tsarki.

TAMBAYA TA 80:- Idan mace bayan ta yi jifar Shaidan saura Dawaful Ifada sai jini ya zo mata ga shi kuma tana tare da abokan  tafiyarta za su koma garinsu kuma ba zata samu daman dawo ba yaya za ta yi?

AMSA:- Idan har ya zama haka, to abin ya zama da lalura kenan sai tayi kunzugu tayi Dawafi haka nan da hailarta, ba komai akanta. Wallahu A’alamu.

TAMBAYA TA 81:- Idan mace jinin haihuwa ya dauke mata kafin kwana arba’in, shin tana iya yin Hajji? In kuma jinin bai dauke ba ga shi kuma ta riga tayi niyyar Hajji yaya za ta yi ASMA:- Idan mace jinin haihuwa ya dauke mata kafin kwana arba’in sai ta yi tsarki ta yi Sallah ta yi Dawafi. Hajjinta ya yi.

Amma idan jinin bai dauke ba ga shi kuma tayi niyyar yin aikin Hajji to sai tayi duk aikace-aikacen Hajjin ta kuma yayi, amma ba za tayi Dawafi ba sai tayi tsarki.

TAMBAYA 82:- Shin yana halatta ga mace mai jinin biki ta karanta Al-Kur’ani? Kuma shi yana halatta a sadu da ita kafin ta cika kwana arba’in ko a’a? Kuma idan ta cika kwana arba’in amma ba tayi wanka ba shin ya halatta a sadu da ita ko a’a bai halatta a sadu da ita ba?

ANSA: Alhamdu lillahi, saduwa da mace kafin jini ya yanke mata haramun ne. Dukkan malamai sunyi ittifaki akan haka. Idan kuma jini ya dauke kafin kwana arba’in ya wajaba a gareta tayi wanka, ta yi Sallah sai dai ana bukatar kada mijinita, ya sadu da ita kafin ta cika kwana arba’in. Ba haramun bane. Amma karatu idan ba ta tsoron mantuwa in bata yiba to kar ta karanta Kur’anin. Amma idan tana tsoron idan bata yi karatunba zata manta to sai tayi karatun. Idan kuma jinin ya dauke sai tayi wanka, tayi Sallah’ ta kuma yi karatun Al-Kur’anin.

Idan kuma akwai wani uzuri da ya hanata yin wankan kamar rashin ruwa ko kuma wani ciwo da take da shi, sai tayi taimama tayi taimama kamar yadda za ta yi wanka. Wallahu a’alamu.

SALLAR RAMAKO CE TA FI CANCANTA A YI KO SALLAR NAFILA?

TAMBAYA TA 83:- Shin Sallar ramako itace tafi cancanta ayi ko kuma Sallar nafila ce tafi cancanta ayi?

AMSA:- Idan ana bin mutum SalIah ta wajibi to shagaltuwa da biyan wanan Sallah shi yafi dacewa maimakon shagaltuwa da SalIar nafila.

TAMBAYA TA 84:- Idan gashin mace ya fito tana Sallah shi Sallarta ta baci ko bata baca ba?

AMSA:- Idan gashi ya fito, kadanne ko kuma wani sashi daga jikinta ya fito dan kadan to ba za ta sake Sallah ba a gurin mafi yawan malamai kuma wannan shi ne mazhabar Abu Hanifa da Ahmad.

Idan kuma wurin daya fito yana da yawa ta sai ta sake SalIar akan lokaci, agurin dukkan malamai da kuma shugabanni na mazhabobi guda hudu, da kuma wadansu sun yarda. Wallahu a’alam.

TAMBAYA TA 85:- Idan mace ta yi Sallah kuma digadiganta sun fito waje wato sun yaye daga cikin zanin, shin Sallarta ta inganta?

AMSA:- A cikin wannan akwai jayaiya a gurin malamai, amma a mazhabar Abu Hanifa, Sallarta ta inganta. Wannan shine daya daga cikin maganganu biyu.

Amma a dayan magana Salarta ba ta inganta.

TAMBAYA TA 86:- Shin shafar mace yana warware Alwala ko a’a?

AMSA:- Amma warware Alwala in an shafi mace a mazhabar Malikiyya idan shafar ta kasance don sha’awa ne to Alwala ta karye. Amma idan ba don sha’awa bane ba ta karya Alwala.

TAMBAYA TA 87:- Shin yana halatta a sadu da mace mai haila ko ba ya halatta?

AMSA:- Baya halatta a sadu da mace mai jinin haila a lokacin da take cikin jinin. Haka kuma mace mai jinin biki haramunne a sadu da ita a lokacin da take jinin. Dukkan malamai sun yi ittifaki akan haka. Sai dai ya hallata a gare shi ya ji dadi da ita, amma ban da saduwa.

HUKUNCIN NEMAN AURE A KAN NEMAN AUREN WANI

TAMBAYA TA 88: Shin yana halatta ga mutun yayi neman aure akan neman auren wani mutum?

AMSA: Baya hallatta ga mutum yayi neman aure akan neman auren dan uwansa idan har an amsawa na farko kuma an karkata zuwa gareshi, dukkan mallamai sunyi ittifaki akan haka kamar yadda Hadisin Manzon Allah (SAW) ya nuna cewa (baya halatta ga mutum yayi neman aure akan neman auren wani) – wato Musulmi danuwansa.

TAMBAYA TA 89: Shin za’a iya binne banasariya tare da Musulmai? ldan mace banasariya ta mutu kuma mijinta Musulmi ne kuma a cikinta akwai jinijirin wata bakwai to shin za’a binneta a makabartar MusuImai, ko a makabartar Nasara za’a binneta?

AMSA: A’a baza a binne ta a makabartar Musulmai ba kuma baza a bimeta a ta Nasara ba domin ta hada dangi da Musulmai da kafiri. Kuma ba’a binne kafiri tare da Musulmai, kuma ba’a binne Musulmi a inda ake binne kafiri, sai dai za’a binneta ne ita kadai a wani guri dabam, sai a sanya bayanta  ya kalli al-Kibla, domin fuskar yaron yana kallon bayanta ne. Idan aka binneta a hakan ya kasance fuskar yaron Musulmi tana kallon al-Kibla, kuma shi yaron ya zama Musulmi saboda baban shi Musulmi  ne koda babarsa ta kasance kafira. Wallahu a’alam.

TAMBAYA TA 90: ldan mace tana yin Sallar nafila da daddare amma wani lokaci tana gajiya da tsayuwa to sai aka ce mata ai ladan wanda yayi Sallah a zaune rabin lada ya ke da shi na Iadan wanda yayi Sallah a tsaye, shin haka ne? Wanda yayi Sallah a zaune rabin ladan yake dashi?

AMSA: “E” haka ne, an samu hadisi daga Manzon Allah (SAW) yace:- “Wanda yayi Sallah a zaune yana da rabin ladan wanda yayi Sallah a tsaye” sai dai idan mutumin ya kasance yana yin Sallah a tsaye ne to sai wani dalili ya sa shi ya kasa tsayawa to Allah zai ba shi ladan wanda ya yi Sallah a tsaye. Saboda hadisin Manzon Allah (SAW) yace: “Idan bawa yayi rashin lafiya ko yayi tafiya to za’a dinga rubuta masa ladan aikin daya kasance yana aikatawa lokacin da yake da lafiya kuma in tafiya yayi bai samu daman yin wannan aikin ba to shima za’a dinga rubuta masa ladan aikin da yake yi a lokacin da ya ke gindansa.”

Kuma ko da mutum ya kasa yin Sallar gaba daya sabo da tsananin rashin lafiya to Allah yana rubuta masa ladan SaIlah dukkanta, saboda niyyarsa daya kasance akanta.

TAMBAYA TA 91:- Tambaya game da tufafin mace da kuma bayyana shi?

AMSA:- Yana halatta ga mace ta bayyana adonta na sarari a cikin Sallah, amma banda na boye, amma magabata sunyi jayayya a wajen ado na sarari. Sunyi maganganu guda biyu, Ibn Mas’udu da wadanda suke tare da shi sunce:- Ado shine fuskarta da hannayenta, misali kwalli da zobe. To akan wadan nan maganganu guda biyu ne malaman Fiqhu suka yi jayayya a wajen kallon matar da ba ta mutumba, wadansun su sun ce:- ya halatta a kalli matar amma bada nufin sha’awa ba, a kalli fuskarta da hannayenta. Amma wannan mazhaba shine mazhabar Abi Hanaifa da Shafi’i.

Amma a mazhabar Ahmad yace:- Baya halatta a kalli ko ina, domin dukkan mace al’aura ce  – ko ina aI’aura ne a jikin mace, har ma farcenta shima al’aura ne. Wannan shine maganar Imamu Malik, wato mazhabar Imamu Maliki.

TAMBAYA TA 92:- Shin ya halatta ga mace taje Hajji ba tare da muharraminta ba?

AMSA: Idan matar ta kasance ta tsufa kuma har ma haila ta yanke mata kwatawata saboda tsufa, kuma ta yanke tsammani daga yin aure kuma bata da muharrami, to za ta iya tafiya yin akin Hajji da wanda ta amince masa. Wannan Magana ita ce daya daga cikin ruwaya biyu daga Ahmad, da kuma  mazhabar Imam Malik da Shafi’i.

TAMBAYA TA 93: Shin ya halatta a dauki Al-Qur’ani ba tare da AIwala ba?

AMSA: Dukkan Mallaman mazhabobi hudu un yi ittifaki akan ba’a daukan AI-Qur’ani sai da tsarki kamar yadda Annabi (SAW) ya fada. A cikin wani Iittafi da ya rubutawa Amru dan Hazim cewa:- “kada mutum ya shafi AI-Qur’ani sai in yana da tsarki”. Kuma lmamu Ahmad yace: Babu shakka IallaI Annabi (SAW) ya rubutawa Amru wannan magana, kuma haka Salmanul Farisi ya fada, da Abdullahi bin Amru da wasunsu.

TAMBAYA TA 94:- Mace ce take tambaya,  ance mata idan haila ta sameta ko janaba to kar tayi alwala kuma kada ta sanya ruwa ta wanke can cikin farjinta, shin hakan ya inganta?

AMSA: Alhamdu Iillahi, baya wajaba akan mace idan tayi wankan daukewar jinin haila ko wankan janaba ta sanya ruwa ta wanke can cikin farjinta, yin hakan ba wajibi bane.

TAMBAYA TA 95: Wasu mata ne guda biyu suka yi jayayya. Daya tace: “Dole ne sai an shigar da dan yatsa an wanke cikin farji, wato wajibi ne yin hakan. Daya matar kuma tace: “A’a ba wajibi bane a wanke can cikin farji sai dai kawai a waje-wajen sa amma banda cikin farjin. To wace magana ce tafi inganci a cikin wadan nan magana gudu biyu.

AMSA: Maganar da take ingantacciya ita ce: ‘Ba wajibi bane ta wanke can cikin farji ba, amma in an wanke ya inganta ya halatta.

TAMBAYA TA 96: Shin idan aka tilastawa mutum ya saki matarsa ba tare da wani daIili na Shari’a ba, shin sakin ya yiwu?

AMSA: Baya halatta a tilastawa mutum yayi saki idan kuma aka tilasta shi yayi saki to sakin bai yiwu ba a gun malamai gaba daya. Domin babu saki akan wanda aka tilastawa. Domin baya halatta ga mutum yayi biyayya ga a abokin halitta cikin sabawa mahalicci.

Saboda haka sai ya ki bin mahaifiyarsa akan hakan idan kuma ya yi sakin akan an tilasta masa to sakin bai yi ba.

HUKUNCI KAN IYAYE MASU NEMAN KASHE AUREN ‘YA’YANSU

TAMBAYA TA 97:- Shin idan mace ta nemi ta raba ‘yarta da mijinta amma sai ‘yar taki biyayya ga mahaifiyarta ta akan baka. Kuma idan uwar  ta tsine mata tsinuwar zata kama ta?

AMSA: ldan mace tayi aure to ba wajibi bane akanta tayi biyayya ga iyayenta wajen rabuwa da mijinita ko kuma aikata wani aiki na sabon Allah, sai dai wajibi ne akanta tayi biyayya ga mijinta in dai baya umartar ta da aikata sabon Allah. Amma indai yana umartarta da aikata sabon to sai tayi biyayya ga mahaifanta don su rabu da mijin.

Amma idan mijin nata baya umartanta da aikata sabo to shine mafi cancanta tayi masa biyayyya kamar yadda Hadisi ya bayyana, idan mata ta rasu kuma mijinta ya yarda da ita to zata shiga Aljannah. Sabo da haka idan mahaifiyar tana son ta raba ‘yar ta da miji to ta zama shaidaniya, to baya halatta ayi mata biyayya akan haka.

Kuma ko tayi mummunan addu’a akan ‘yar tata wato (ta tsine ma ta) tsinuwar ba zata kama ‘yarinyar ba. Amma idan uwar taga cewa shi mijin yana sa matar a hanyar sabon Allah to sai ta umarci ‘yar da tayi biyayya ga Allah da Manzonsa domin shi ne wajibi akan dukkan Musulmi.

WASU HUKUNCE-HUKUNCE KAN SAKI DA MAYAR DA AURE

TAMBAYA TA 98: Idan mutum ya saki matarsa saki uku kafin ya sadu da ita, shin zai iya mayar da ita?

AMSA: Alhamdu lillahi. To saki uku kafin a sadu da mace da kuma wacce aka sadu da ita haramcin wannan aure daidai yake, matar ta haramta a gare shi ko ya sadu da ita ko bai sadu da ita ba indai ya yi mata saki uku to ta haramta a gareshi har sai ta auri wani. kuma ya sadu da ita, kuma wannan haramci ya tabbata a gurin malaman mazhabobin hudu babu sabani a cikinsa.

TAMBAYA TA 99: ldan mutum ya auri mata bai sadu da ita ba, bai taba ta ba, sai kuma ya sake ta saki uku sai kuma wani ya sake auren ta shi ma sai ya sake ta saki uku tun kafin ya saduu da ita kuma bai taba ta ba. Shin ya hallata ga wanda ya fara sakin ta da farko ya sake aurenta?

AMSA: Idan aka saki mata saki uku tun kafin a sadu da ita to hukuncin daidai yake kamar wacc aka sake ta bayan an sadu da ita a wurin malamai hudu. Matar bata halatta a gare shi ba har sai ta sami wani mijin kuma sai ya sadu da ita, wato miji na biyun. Idan kuma na biyun ya sake sakin ta alhali bai sadu da ita ba, to bata halatta ga na farko ba.

TAMBAYA TA 100: Idan mutum ya auri mata amma bai sadu da ita ba har tsawon shekara daya sai kuma ya sake ta kafin ya taba ta to shin ya halatta a gareshi ya auri uwarta bayan ya saki yar?

AMSA: Baya halatta ga mutum ya auri mahaifiyar matarsa, ko da bai sadu da yarinyar ba ya sake ta. Ba ya halatta ya auri uwar. WaIlahu a’aIam.

ALHAMDU LILLAHI ALLAZI BI NIAMIHI TATIMMUSSALIHATI

Back to top button