Uncategorized

Sokoto: Zanga-zanga ta ɓarke kan kamen da ‘yan sanda suka yi bayan kashe Deborah Samuel

 

Zanga-zanga ta ɓarke a garin Sokoto na arewacin Najeriya, inda matasa ke ci gaba da nuna ɓacin ransu kan kalaman ɓatanci da ya jawo kisan wata matashiyar ɗaliba mai suna Deborah Samuel.

 Masu zanga-zangar na neman jami’an tsaro su saki mutanen da suka kama da ake zargi da kisan matashiyar da ke karatu a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, wadda suka zarga da zagin Annabi Muhammadu (SWA).

 Matasan maza da mata suna aiwtar da zanga-zangar a wurare daban-daban a fadin Sokoto tare da ƙona tayoyi, da suka haɗa da Fadar Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III. Kazalika wasu sun yi cincirundo a ƙofar gidan gwamnatin jihar. BBC ta nemi ji daga bakin rundunar ‘yan sandan Sokoto amma ba su amsa kira ba.

 Rahotannin da BBC ta samu sun nuna cewa da farko zanga-zangar ta lumana ce, daga bisani sai ta rikide ta zuwa tamkar rikici, inda mutane suka dinga jefa duwatsu kan gidan sarkin Musulmin.

[Sautin Murya] Innalillahi wa’innah alaihi Raju’un kalaman da ta fadi akan fiyayyen hallita

 Wani da BBC ta zanta da shi da ke kusa da fadar sarkin a lokacin da abin ya faru ya ce jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin dakatar da matasan kutsawa fadar.

 “Da yawan yaran [‘yan zanga-zanga] na ganin sarkin ya goyi bayan yarinyar [Deborah], shi ne suke jefe-jefe,” in ji shi.

 

 Ya ƙara da cewa jami’an tsaro na ‘yan sanda da soja na harba hayaƙi mai sa hawaye, har ma an harbi mutum biyu.

 Shi ma wani da muka ɓoye sunansa saboda dalilai na tsaro ya tabbatar da harbin mutum biyu, yana mai cewa har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton matasan na ci gaba da jifa, su kuma jami’an tsaro na harbi.

 Haka nan an kama mutane da yawa, a cewarsa.

Related Articles

Sanarwar da ‘yan sandan Sokoto suka fitar ranar Alhamis ta ce sun kama mutum biyu da ake zargi da kisan Deborah, Kirista ‘yar aji 200 a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari,

 Sarkin Musulmi da Shugaba Muhammadu Buhari sun yi tir da kisan, suna masu kira da a gudanar da cikakken bincike don hukunta waɗanda suka kashe ta.

 Wasu bidiyo da hotuna da suka karaɗe shafukan zumunta sun nuna yadda matasan suka yi wa matashiyar duka kuma suka ƙona gawarta.

 Lamarin na ci gaba da ta da muhawara musamman a shafukan zumunta na Najeriya.

Back to top button