Uncategorized

Sharhin Fim Ɗin Uku Sau Uku Episode 17 Season 2

 *SHARHIN FIM DIN UKU SAU UKU*

*_Gini Da Tubalin Toka_*

Sunan Fim: Uku Sau Uku

Kamfani: AnFara Multimedia

Labari da Tsarawa: Hussaini Ali Muhammad

Daukar Nauyi: Misbahu Aliyu Anfara

Shiryawa: Nura Aminu, Sagir Fashion

Umarni: Hussaini Ali Muhammad

Jarumai: Misbahu Anfara, Abba Elmustapha, Shu’aibu Lilisco, Kamsusi Umar, Dadi Hikima da sauransu.

Fim din Hausa mai dogon zango da na jure kallon sa duk da kuskuren da aka tafka tun a farkon labarin fim din.

Labarin wani matashi ne Faisal da ya shiga kalubalen rayuwa saboda talauci da ya yi masa kawanya, yana zaune da gyatumarsa da kanwarsa Wasila a gidan haya yana da budurwa Nafisa da suke son juna ta matsa masa ya turo ko su rasa juna.

A cikin wannan hali ne ya hadu da wata mata Hajiya Badiyya da ta nemi ya aure ta na kwana uku sannan ya yi mata saki uku za ta ba shi miliyan uku.

Ashe Hajiya Badiyya auren kisan wuta ta shirya don komawa gidan mijinta da ya tafka mata saki uku.

Ba a dade ba Abida ‘yar gidan Alhajin da Hajiya Badiyya ke son komawa gidansa ta bayyana gare shi da soyayya sannan ta nemi idan ya auri Hajiya Badiyya to kada ya sake ta ita kuma za ta ba shi miliyan shida.

A haka aka kulla rigimar fim din.

Related Articles

Babu shakka labarin ya kayatar ya kuma yi kyau, duk da ya yi kama da wani littafin Nazir Adam Salih.

Jaruman labarin sun yi kokari matuka haka mai ba da umarni, an samu rike hankalin mai kallo sosai.

Duk da wannan kokari da aka yi an tafka kuskuren da ya kamata mashiryin shirin da Marubucin labarin su tuntubi Malamai akan hukuncin sakin da Alhaji (mijin Badiyya) ya yi mata.

Abida ‘yarsa ce ta bugar da shi da kayan maye ta sa ya saki matarsa da suke matukarvson juna.

A ka’ida wannan saki bai saku ba, domin duk wanda aka bugar bai sani ba ya yi wani abu ba daidai ba shari’a ba ta hukunta shi (musamman a mas’ala irin wannan ta saki) don haka idan na ce an guna labarin ne da tubalin toka ban yi kuskure ba.

Akwai kananan kurakurai da ba sai na yi magana a kansu ba, amma wannan na ga ya taba jigon fim din ne sosai.

Back to top button