Uncategorized

Jarumar Shirin Labarina Ta Auri Tsohon Dan Wasan Najeriya

A yau ne muka samu wani labarin cewar a jiya Juma’a, 26 ga watan Nuwamba, 2021, ne aka daura auren fitacciyar jarumar nan ta cikin shirin Labarina mai dogon zango, wato Maryam Wazeer, wacce ta ke fitowa a matsayin Laila. 

Ita dai Maryam Wazeeri ta angwance da ƙwararren dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya wato super Eagles, Tijjani Babangida.

Also Read: Shin ko kunsan dalilin yin kidnapping din Sumayya a cikin shirin Labarina kuwa?

Daman tunda aka dawo daga wannan Season din ba a ga fuskar jarumar ko sau ɗaya ba, haka yasa wasu daga cikin mutane suka fara raɗe-raɗin cewar iyayenta ne suka hanata.


Daga Ƙarshe muna addu’ar Allah Ya basu zaman lafiya ya kawo zuri’a ɗayyiba, yan baya ma Allah ya kawo masu mazaje na gari, Amin.

Back to top button