Ma’anar Mafarki
Asslamu alaikum mafarki gaskiya ne kuma hanyace da ake sanar da Bawa wani al amuran rayuwansa mai kyau Ko marassa kyau, mafarki baiwane wadda Allah yake yiwa bawansa a barci amma akwai mafarki wadda shedanu ke sanyawa bawa don saka shi cikin wasi-wasi.
Tajallin mafarki
Shine samarda mafarki a yayin kwanciya da sananin tsoro ko kwanciya da tunanin Abu ko son abin,kamar masoya sukan kwanta da tunanin son junan Su hakan ke sa mafarkan Su Bai cika Zama gaskiyaba.
Mafarkin abin da ka kwanta Dashia Rai Bai cika Zama gaskiya .
A zahiri ruwan sama alhairi ne, da alkhairi da arziki wajen wasu wadan su kuwa ukuba ne Ko bakin ciki Ko na dama. Idan ruwan sama ya kasance yayyafi ne to wadata ce da arziki, idan idan kuwa aka taka ruwa da tsawa to Yana nunawane abisa wahala da hadari idan a kebantaccen wurine wadda aka sani to Yana yin bakin cikin da zai Sami mazauna wurin.
1. Mafarkin saukar ruwan sama mai sanyi ba iska ba tsawa, to bushara ne na samun wata ni’ima da kwanciyar hankali a wannan shekara.
2. Mafarkin ruwan sama mai yawa da iska sannan yana rusa gine gine da binaye to wannan yana nuni zuwa ga wata hasara da dukiya ko rayuwa.
3. Mafarkin kana tafiya ruwa ya tare ka a hanya ka kasa samun hanyar fita yana kwadaitar da ka zama mai godewa Allah bisa dukkan wata ni’ima da yai maka.
4. Macen da tayi mafarki taga ruwa a cikin rami yana nuni da zuwan jinin al’adabta a wadannan kwanakkin.
5. Mafarkin wanka a cikin ruwan sama yana nuni da wanke wasu tarin zunubai da samun gafara a wajen Ubangiji.
6. Mafarkin shan ruwan sama na nuni da samuwar waraka na wani ciwo a jiki ko samun mafita na wani kunci ko wata damuwa da wata jarrabawa a rayuwa.
7. Mafarkin ana sheka ruwan sama ba iska ba tsawa ka fake kana ta kallo,na nuni da saukar rahama ne da alamun samun natsuwa da kwanciyar hankali a wannan shekarar ga wanda yaiyi mafarkin.
8. Idan kana a cikin wata damuwa
Ko wani matsi ko wata bukata da ta gagareka sai ka yi mafarkin ruwan sama na sauka to kayi hankuri jarraba kane ubangijinka ke yi karshe zaka ji dadi Domin zai daukaka darajarka, ya biya maka bukatunka, ya yaye maka damuwa ya faranta maka rayuwarka. Sai kayi hankuri ka nace da addu’a, sauki na zuwa.
9. Idan kana rashin lafiya, ko kana jinyar wani marar lafiya sai ka yi mafarkin an yi ruwan sama har gini ya zube, Subhanallahu! da yiwuwar wanda yaiyi mafarkin ya rasu,ko wanda kake jinya din ya rasu.
10. Idan lafiyarka lau kai yi mafarkin ruwan sama ya rusa gini to da yiwuwar waninka ne ya rasu.
11. Idan kaiyi mafarkin kana wanka tsirara a cikin ruwan sama mutane na ta kallonka to in kayi aiki na alhairi ka daina fadi kuma ka rinka yi dan Allah.
12. Idan kuwa aka yi mafarkin ruwan ya game gate makil to Yana nuna Garin zasu shiga wani wahala ma wuyacin.
13. Idan kuwa aka ga gari mare hadari yayi gangami a at abaka ruwa ta Ko ina to hakika mutane zasu Sami wadata da farinciki.
Allah shi ne mafi sani.