Hausa novels

Zakuna Biyar Page 40 By Princess Teema

DEATH OR LIFE. (DOL)Waɗan nan wasu magunguna ne da ake yi wa yara da sunan rigakafi, amma batu na gaskiya magunguna ne dake kashe garguwar jikin yara, tin yaro yana ƙarami zasu kashe mashi garkuwar jiki, hakan zai sanya jikinsa zata yi saurin karɓar kowacce irin cuta ce ta shigo, sannan jikinsa za yi wahalar karɓar magani.Kuga yaro yana ciwo ayi ta magani amma dik na banza, sai kuga kamar ba’a mashi komai, kuma ko sun girma jikinsu ba zai dinga karɓar magani ba, already an kashe masu garkuwar jiki tin suna yara, ba wanda zai zaci cewa maganin matsala ce, za’a ce rigakafi ne kawai, hmmmm bayan rigakafi babban cutarce a wajen.Al’ummar ƙasar Avaris sun gagara gane wani abu ɗaya, babu ta yadda za’ayi gwamnatinsu ta basu abu kyauta, kuma ta dinga binsu har gidaje da sunan yi masu, idan gaskiya ne a bisu gidaje ana raba masu kayan abinci da jari da ake cewa ana fitar masu mana, meyasa idan sun fitar da tallafin gwamnati sai dai su ce ka je ka cika form, ka bi layi, ka yi kaza, ka yi kaza?. Amma shi rigakafi za’a bisu har gida ne ana masu, har da rabawa yara sweet ko wani abin makamancin haka idan sun yi, kai mutanen cikin Avaris wani lokaci tamkar an toshe ƙwaƙwalwalensu, abin takaici sun kasa ganewa, wlh tallahi gwamnatinku ba zata taɓa binku in da kuke ta baku abin arziki ba, sai in cuta, cuta ce wannan za’a biku ko’ina a lallaɓaku, har kuɗi zasu raba maku dan ku yarda da su, da yake cutarku za’ayi, wlh dik wanda ya ci abin gwamnatin kyauta yasan akwai abin da zaka biya da shi, waɗan nan mutane nasa bada abu haka kawai, sai da babban dalili! Ku rubuta wannan ku ajiye.Ya rabb, ya ALLAH, ALLAH ka karkato da hankalin jama’ar annabi, ka ganar dasu! Musamman iyaye mata, sune ke bari anaiwa yara wannan gayyar tsiya, basu san cutar da rayuwar yaransu suke yi ba, da anyiwa yaro sau ɗaya shikenan an gama da garkuwar jikinsa, ya ALLAH ko shekara ɗari zai yi a duniya jikinsa ba zata dinga karɓar magani ba, sai dai ya samu sauki daga ALLAH, amma in bai da lafiya kun dinga kashe kuɗi a banza.Zubawa maganin idanu Leo ya yi, sai da ya karance rubutun jiki kaf, sun ɓoye ainahin manufar maganin da rubuce-rubuce na karya. Nisawa ya ɗan yi tare da zarar magani guda ya zura a cikin aljihunsa, ya sanya su Zaysh suka mayar da sauran a cikin kwali, da alama bincike zai yi a kan wanda ya ɗauka.Wucewa container gaba suka yi, a nan ma shi ya buɗe container. Ya rabb, Tramadol mai karfi sosai a cikin wannan container, waɗan da basu san me Tramadol ba, wani maganani da ake shigo da shi daga India, China, Pakistan, ana sayarwa da sunan maganin cuta amma batu na gaskiya wannan magani yana haddasa lalacewar kwakwalwa, im kasha sosai yana sanya hauka, tashin hankali, mantuwa, ga sa jaraba sosai.Leo sai da ya ɗan girgiza ganim waɗan nan uban tulin kwalin Tramadol ɗin nan, katon container irin wannan cire da manyan kwalinsa, ya rabb. Umarni ya baiwa su Noor da su mayar su rufe, sannan ya wuce gaba. A nan ma da kansa ya buɗe container.Ya rabb Codeine Syrup ne a cike a ciki. Codeine a idanun al’umma ana kiran sa maganin tari, amma ana sha ne dan maye, kuma mugun illatar da lafiya yake yi. Yana lalata hanta, hassasa matsalar numfashi, mutuwa idan an sha fiye da misali, manyan ƙasashe da dama sun haramta shigo da shi ƙasashensu, amma Avaris ta zama kwanton sharar ƙasashen dake son cin karensu babu babbaka, komai shigo masu da shi ake yi, saboda ƴan ƙasar har yanzu a kwance suke, sun ki tashi su farka su fatattaci dik wannan abin su tsabtace kasarsu daga gurɓatattu!.Kai kawai Leo ya jinjina game da cewa su rufe su shiga wata container. Haka kuwa aka yi, suka mayar suka rufe, suka wuce container na gaba.A wannan container na gaban cike yake da fake drugs, copyn magungunar gaske kenan, sunayensu da komai tamkar na gaske, sai dai ko kaɗan babu sinadarin magani a ciki, sai dai sinadarin guba mai cutarwa ne a ciki. Waɗan nan magunguna suna sanya ciwon koda, ciwon hanta, mutuwa a hankali, ka je sayen magani dan ka samu lafiya, sai a ƙara maka wata cuta, ya ALLAH kana ganin al’ummar annabi yadda ake yi mana, ya ALLAH ba zamu iya ba, sun fi karfinmu amma basu fi karfinƙa ka ba, ya ALLAH ka kawo mana ɗauki.Wucewa container gaba Leo ya yi. Wannan container shi kuma cike yake tab da manpower, king power, double action da makamantansu, ina maza masu shan man power? To albashirinku! Kuma ga naku ta iso! Dan balai ba zaka zauna yadda ALLAH ya ajiyeka ba, to ai zaka shawa kanka balai. To waɗan nan magunguna da ake shigo dasu da sunan man power ba ma a gwada su a asibiti ba, suna ɗauke da sinadarin da ke sa bugun zuciya su jawo bugun zuciya da sauri, mutuwar mazaje da yawa a sirrance ba tare da an san ainahin me ya kashesu ba, namiji zai mutu ba tare da yasan me ya kashesa ba, waɗan nan magunguna suna buɗe jijiyoyon namiji ne, ba karfi suke ƙara maka yadda kake tinani ba, buɗe jijiyoyinka suke yi, su bar iska ya shiga jikinka na wuce misali, su haifar maka da mutuwar gaba idan ka cigaba da sha, wlh suna sanya ciwon zuciya, saboda ita zuciyarka ba zata iya karɓar yadda jikinka zai buɗe ba, iskar dake shiga tana hura zuciyar take ta kumbura, idan namiji ya sha shi mai yawa a lokacin ma a take yake mutuwa. Sai ka ji masu sayarwa suna cewa baida side effects, sannu na ce, na ce sannu dan uban mutum!! Kai ni fa raina ɓaci yake inna ga ana cutar da bayin ALLAH, ina jin tamkar in zama namji irin sayyidina Ali.Wannan magana ta maganin karfin maza ta tina mun da wani da ya mutu a hotel bayan shan man power, ya ALLAH, maza su yi ta mutuwa a rasa me yake kashesu, jahilan cikin al’umma su yi ta tallar man power ba tare da sanin ainahin dame ake yinsa ba, suna kashe al’umma cikin rashin sani da sunan wai su suna neman kuɗi. To hajiya Jummai, fatan idan kin gama karantawa in ma mijinki yana sha zaki taka mashi birki! Idan kinga wani naki zai sha ki taka mashi birki! Dan zallar cuta ce a ciki! Dan haka ki yi gaggawar takawa mijinki birki, ki tattara sauran power da kuke da shi ki kunshe mashi kayansa a wando!Idan kuwa kinƙi dakatar da shi to fa ɗan karfin da yake da shi ɗin zaku rasa, dan in yana da sauran shan ruwa a gaba bai mutu ba, to at the end abar tasa mutuwa zata yi ta daina aiki, kinga kuwa bai samu power ba wanda yake da shi kun rasata. Wata ma sai kuga ita ke sayawa mijin man power, su man power manya, zakuwa ki ga man power. Wlh mata tin wuri idan zaku tattara mazajenku ku turasu gudun motsa jiki da gym kullum dan su samo power ɗin asali is better for you, gym yana sanya jikin namiji ya yi karfi, dik wasu matattun jiyoyi zasu miƙe, yana ƙara girman gaban da kukewa haukar neman har kuke kai kanku ga halaƙar in da zaku rasa ɗan wanda kuke da shi. To maza, gym yana ƙara girman gaba da kuke so ɗin, ba sai kun sha man power ba zaku samu ingantaccen power da babu mix, sannan gym yana ware ƙasusuwan gaɓɓai yasa su yi kwari sosai, yana ƙara lafiya da daidaita zuciyar ɗan adam, kai in taƙaice maku kai da kanka in ka fara zaka ji jikinka ya canza, ya yi maka daɗi da sauransu.Mata ku tura mizanku gym ko dan su dinga ɗaukarku kamar ƴan baby suna jefawa gado kamar matan novel, da zarar yana jin komai girmanki zai ɗaukeki cak, to gashinsa ya yi kwari, amma yanzu kun kyalesa dik man gyaɗa da gishiri ya kashe dik wani karfin da yake da shi, ga wata musifa wai man power, ba dole a samu tangarɗa ba!.(Kuma mata masu shan hips and breasts enlargement yake kome? Ku jira, zan bangaɗo maku dame ake haɗasa, naku na nan tafe, ai nai alƙawarin sai fa na faɗi komai dake cutar da bayin ALLAH!) Container na gaba kuma maunguna ne irinsu diazepam, rohypnol, valium, magungunan bacci da kwantar da hankali a cewarsu, ana shigo da su da yawa ba bisa ƙa’ida ba, kuma ana bawa yara, mata, direbobi, musamman direbobi, za’a basu shi da sunan maganin hana barci, hakan na haifar da haɗasussuka a hanya, babban illar ce ga al’umma.Har kan Leo ya fara ciwo ganin waɗan nan ɓarna, amma ya daure suka je container na gaba. Suna buɗewa kwali-kwali na antibiotics ne a ciki, ana shigo da su suma ba bisa ƙaida ba, al’umma suna sha ba tare da sani ba. Kwayoyin suna cutar sosai, mutane su mutu cikin sauƙe, da ka yi zazzaɓi sai mutuwa. Time Leo ya duba a wayansa 2:30 ta yi. Cike da bada umarni ya ce su yi sauri gari ya kusa wayewa. Daga nan suka wuce container ta gaba. Suna buɗeta allurai ne dayawa a ciki, ai yana ɗaura idanunsa kan kwalaben alluran nan sai da ya ji gabansa ya faɗi. Soja da faɗuwar gaba ai kun san ba lafiya. Da yake basu da ishasshenlokaci a gurguje ya ɗauki alluran kwalba ɗaya ya zura a aljihunsa ya ce su mayar da saura su rufe tamkar ba’a taɓa taɓawa ba. Haka suka bi dik containers ɗin da suka buɗe, a kowani container sai Leo ya ɗauki abu ɗaya har suka isa kan miyagun kwayoyi, a nan ma ya ɗauki cocain ɗaya. Suka mayar da komai tamkar basu taɓa ba, sanna ya kwance karnikansa, ya ce Noor ya rike mashi ɗaya bari ya rike ɗaya, Noor ya ce. Shi wlh yana tsoron kare, basa haɗa hanya da kare, kada ku manta yana da cutar tsoro, tin ainahi haka yake da tsoron kare, kun gansa dai jarumi, wlh zai iya kama maciji, amma baya son kare ko kaɗan tamkar mai aljanu a kai.Miƙawa Zaynish igiyar karen Leo ya yi, ya karɓa ya rike, shi kuma ya riƙe ɗaya suka nufi hanyar komawa, yau ba barci akwai bincike kenan. Sun fara tafiya Vash ya karɓi igiyar karen hannun Leo dan ya taimaka mashi, saboda Leo ɗin ya fisu shan wahala, dik containers ɗin nan shi ya bubbuɗesu. Suna tafiya a hanya ne Vash ya ce. “Da mun cinnawa wajen wuta ai, komai ya ƙone su rasa shi”……. Nisawa Leo ya yi tare da cewa. “Ai bombing na wajen ba shi ne mafita ba, dakatar da masu aikata hakan ba shi ne ba, mu kama masu yi mu kashesu shi ne, idan har zaku rinƙa kama waɗan nan containers ɗin dik shime ne, in mun ƙona wasu waɗan nan yau, gobe zasu sake shigo da wasu, dan haka masu aikata hakan zamu raba da numfashinsu, shi ne ɓarna zata dakata!”. Noor ya ce. “Gaskiya Avaris ta kai maƙura a wajen lalacewa”…… Leo ne ya amsa da. “A wannan case ɗin navy suna da babban kamisho, sun taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar ƙasar nan, kome za’a shigo da shi daga waje ta ruwa ne, me amfaninsu da ba zasu dakatar da ɓarna ba? Ko dai dama an ajiyesu a bakin ruwan ne dan su dinga kamun kifi ko suna zaman kirga jiragen ruwan da zasu shiga su fita?”. Cike da takaici yai wannan magana, ya rasa meyasa yake jin tsananin kaunar kasar Avaris…. Ni kam na ce saboda ƙasar mahaifinka ne mana, ai jininka suna ciki, dole ka so ƙasar.Zaynish ne ya ce. “Amma idan navy suna da laifi kaso 40 cikin ɗari na lalacewar ƙasar to fa ministar of foreign affairs yana da kaso 55 cikin ɗari, ministan tsaro yana da 75 cikin ɗari, sai number ɗaya na ƙasan yana da 100 cikin 100!”. Kai Leo ya jinjina, su Noor dik kai suka jinjina, a dake Leo ya ce. “Ni ban yarda wani soja ya bani umarni a kan rashin adalci in masa biyayya ba!”….. Dikkansu basu fahimcesa sosai ba, Vash ya ce. “Kana nufin ba zaka yi wa AZURE biyayya ba?”.Kai ya jinjina. “Ba AZURE ba, dik duniya babu wanda ya isa in yi mashi biyayya kan cutar da al’umma! Wlh yadda na yi rantsuwa da ALLAH kafin in saka wannan kakin kan zan kare rayuka, dukiya, ƙasa bakiɗaya, to billahil lazi babu wani mahaluki da ya isa ya tilastani ya bani umarnin in yi shiru ana cutarwa! Sai dai a kasheni a kan haka, amma wlh dik masu ɓarna sai na dakatar da su, Navy sun yi alƙawarin kare bakin ruwa, ba zasu bar dik wata cutarwa ta ruwa ta shigo ƙasa ba, amma me muka kama yau? Ina suke da har suka bar hakan ke faruwa? Okey baa basu izini ba ko?”. Cike da takaici ya kai karshen maganar.A yadda ya yi magana yasa su Zaynish sun ji lallai ko zasu mutu ba zasu marawa karya baya ba, lallai zasu aiki dan cika alƙawarin da suka ɗauka. Cike da taƙaici Zaynish ya ce. “Hakika ba zamu zama karnukan farautar manyanmu ba! Lallai ba zamu karɓi umarnin rufe bakinmu a lokacin da ake zalunci ba, ba shakka sai dai a kashemu amma a kan gaskiyanmu!!”. Noor ya ce. “Dama ai mu mutuwa ba wata aba bace a wajenmu, sai da muka tabbatar cewa mutuwa ta fi takalmar sakawarmu sauƙi a wajenmu kafin mu yarda mu sanya wannan kaki, dan haka mu matattune dama, lallai zamu tsaya a kan gaskiya!”. Vash ya ce. “Ba zamu taɓa bari a cigaba da cutar da al’umma ba, zamu zama sojoji na farko da suka fara gyarawa kowa zama a ƙasar nan!”….…. Leo ya ce. “Idan sun san wasu ai basu san wasu ba, ba zamu ki karɓar umarninsu ba, dan umarninsu doka ce, amma muna da damar yin abin da muke so a bayan idanunsu ba tare da sun sani ba ai, daga yau babu wani ɗan ta’adda da zamu sake kamawa mu mayar barrack, dik kashe shegu zaku yi”.Zaynish da ya fito daga Afirka me bai sani ba? A ƙule ya ce. “Abinda ko mun sha wahala, mun je yaki, a yakin har mu rasa ƴan uwanmu sojoji, mu sha wahala mu kama ƴan ta’addan mun kaisu ma bayan kwanaki sakesu ake yi wahalarmu ta tashi a banza, dan haka ina tare da kai, dik a daji zamu kashesu kisa mafi walaƙanci, mu jefa gawarwakinsu cikin manyan tekuna, in mun koma mu ce dik sun gudu, that’s all”.Noor ya ce. “Wannan umarni da ƙananan sojoji basa samu yasa suke shan wahala, suna filin daka amma wai suna jiran manya daga sama su basu izinin harbi, sai su tsaya ayi ta harbinsu! Abin taƙaici, amma zamu gwada masu kwarewa a kan aiki, zamu canza hukumar soja na duniya bakiɗaya”.Vash ne ya ce. “Ni wani kafurin ne ma ya kawo dokar idan kana filin daga ma sai ka nemi izinin harbi?”……. Zaynish ya ce. “Kafuran suna dayawa ai, amma zamu kafa tarihi a hukumar soja wanda ko mun mutu ƴan baya zasu yi amfani da salonmu, zamu canza hukumar soja a duniya bakiɗaya kamar yadda Noor ya ce, zamu bawa duniya mamaki, sai mun ɗara FIVE LION In Sha ALLAH”. Leo ne ya ce. “FIVE LIONS, kai watau AZURE ta jima tana yaye gwarazan maza fa”……… Noor ne ya ce. “Ni fa ina ganin IRON FIST ma daga AZURE suka samu horo, dan wani lokaci aikinsu yana mun kama da namu fa”………. Vash ne ya amsa da. “Ban san meyasa nike son tarihin FIVE LIONS har cikin raina ba, sojojin da suka shiga tarihin duniya a lokacin baya, sojojin da suka bada mamaki”. Leo ya ce. “Ina tinanin AZURE ta hora IRON FIST gaskiya, saboda nima irin aikin da suke yi yana bani mamaki, amma ni fa ina ji a jikina IRON FIST ba mugaye bane kamar yadda duniya ta ɗauka, kawai gwamnatin duniya ne ta nunasu matsayin azzalumai saboda suna rusa zaluncinsu”…….. E mana, jama’a jinin IRON FIST yana magana, kaifin kwakwalwarsu gado ce, kun ji yana hasashen ba mugaye bane.Noor ya ce. “Ai manyan duniya zasu aikata fin haka ma, da zarar ra’ayinka ya sha banban da nasu to fa kai ne ɗan ta’adda kuma mugu, su kuma asalin ƴan ta’adda mugayen basa kiransu da hakan saboda ra’ayinsu iri ɗaya”…… Kai kawai Zaynish ya girgiza, daga nan bai sake yin magana ba, ya yi shiru, suka cigaba da hira suna tafiya, sai da suka kusa isa wajen tantunansu ne Noor ya ce.”Zaynish lafiya ka yi shiru?”. Nisawa ya ɗan yi tare da cewa. “Babu komai bro”. Noor bai yarda ba, ya matsa ya rike Zaynish tare da tsayar da shi suna fuskantar juna, suka dakata da tafiya, cike da kulawa ya ce. “Bro, now we’re one family, bamu da iyaye da ƴan uwa a nan, bamu da kowa, why not ba zamu haɗa kanmu, mu rungumi juna ba?”. Matsawa Vash ya yi, ya dafa kafaɗar Zaynish yana faɗin. “Ka faɗa mana damuwarka mu yi maganinta a tare”…… Baya Leo ya koma ya jingina da jikin wata bishiya yana kallonsu bai yi magana ba. Nisawa Zaynish ya yi kafin ya fara basu labarin yadda ƴan ta’adda suka kashe mashi dangi, iya shi da sister ɗinsa kawai suka rage, ya basu labarin komai bai rage ba.Sun yi matuƙar tausaya mashi, Noor ya rungumesa game da cewa. “As from today we’re your family also, ba kai da Aunty Ummie bane kawai, akwai mu, we are brothers now! Zamu tsaya da kai dik wuya dik daɗi, promise that kaima kana tare damu”…….. Ajiyar zuciya ya sauke tare da rungume Noor. “We’re brothers now!”. Matsawa Vash ma ya yi, suka rungumi juna. Shi dai Leo yana gefe yana kallonsu bai tanka ba……. Wani irin haushi karnukan hannunsu suka fara yi, hakan yasa Noor janye jikinsa a miliyan ya ja da baya, ya tsorata da kukan karen. Ɗago kai Leo ya yi yana faɗin. “Me yake damun karnikan?”. Ya faɗa tare da kuna light ɗin hannunsa a kansu.Shiru Leo ya ɗan yi game da cewa su Noor su yi shiru, dan karnuka basa haushi banza, bare ma karnukan da aka baiwa horo irin wannan……. Tsit suka tsaya karnukan na cigaba da daka haushi. Lokacin guda cikin zafa Zaynish ya ture Leo tare da damke wukar da wani mutun ya zo ta baya zai daɓawa Leo ɗin.Take wuƙar ta fasa mashi tafin hannu dan bai sanya hand gloves ɗinsu na aiki ba, janye wuƙar baya mutumin ya yi, hakan yasa ta kara pasa tafin Zaynish. Kafin DOL su motsa sai ganin wasu jiga-jigan mutane huɗu suka yi sun bayyana kewaye da su, suna sanye da bakaken kaya na manyan ɓarayi, suna wani irin haki, da alama gudu sosai suka yi kafin su cim masu.Siririn tsaki Noor ya ja tare da cewa. “Ku zo da wuri mu baku a jikinku muna son komawa kafin gari ya waye”……. Zazzare wuƙaƙen hannunsu mutanen suka yi, miƙawa Vash igiyar karen hannunsa Zaynish ya yi, ya sanya hannu ya tsaga rigar jikinsa gida biyu, ya ɗaure hannunsa dake zubar da jini, har lokacin haske wata tamkar kamar rana yana haskasu.Komawa baya Vash ya yi ya jingina da jikin wani ƙaton dutse dake wajen, ya barwa mazajen AZURE filin su fafata shi kuma ya rike karnuka. Haɗe bayansu Zaynish, Noor and Leo suka yi suna kallon mutanen.Kansu mutane suka yi da wuƙaƙen, hakan yasa suka dare suka rabu. Wani irin faɗa suka fara gwabzawa na nuna banbanci kwarewa, sai dai sun yi mamaki ganin mutanen sun iya faɗa irin wanda ake koyawa sojoji.Mutane su huɗu, su kuma su uku haka suka fara gwabzawa. A tare mutane biyu suka yi kan Noor shi kaɗai, kaucewa wuƙar da suke ƙoƙarin caka mashi ya fara yi, while shi kuma Leo ya kwace wuƙar nasa mutumin ya jefar, sun fara faɗar hannu, wani punch Leo ya kai mashi a bayan kunne wanda yasa ya yi baya-baya ya faɗi ƙasa. Ganin ya faɗi ne yasa ya daka tsalle, ya taka wani dutse dake kusa da Vash, ya ƙara tsalle game da juyawa ya daki ɗaya daga cikin masu kawowa Noor hari da wuƙa, a wuya ya dakesa da ƙafansa, sai ga mutumin ya faɗi ƙasa. Dafa shoulder ɗin Leo Noor ya yi, ya daka tsalle ya taƙa ɗayan mutumin a fuska da waɗan nan shaggun tauraran takalman nasu, baya-baya ya yi ya faɗi ƙasa. Dafe shoulder ɗin Noor Leo ma ya yi, ya daka tsalle tare da juyawa ya taka mutuminsa da ya taso yanzu yake ƙoƙarin nufosu, watau ya farfaɗo daga punch da ya sha…… Da karfi Leo ya riko waish ɗin Noor tare da ɗaga shi sama, Noor ɗin ya ware kafarsa ɗaya ya kaiwa mutumin da suke faɗa da Zaynish duka a gefen wuya, wannan duka ɗaya ba tashi Noor yai mashi, dan wannan shegen takalman nasu ya daki maƙogwaron mutumin wanda yasa ƙashin wajen ta ɓalle, kun san takalmansun nan ba karamar taurice da ita ba.Zaynish bai iya faɗa da mutumin sosai bane saboda yankar da suka mashi a hannu, so da hannu ɗaya yake faɗa shiyasa Leo ya taimaka mashi ta hanyar ɗaga Noor ya daki mutumin.Yana sauke Noor ɗin ya yi tsale ya yi backtorn ya taka ɗayan mutumin da ya taso yanzu a kai sai da ya koma ya zube a ƙasa. Tsalle Noor ya yi ya taka tsakiyar bayan Leo dake duƙe, ya ware kafafunsa ya daki guy da ya sake miƙewa a ciki, hakan yasa guy ɗin ya sake komawa ƙasa, ya durƙusa kan gwiwinsa yana nishi sama-sama tamkar yana son sumewa ne.Dirowa ƙasa Noor ya yi, yana dirowa Leo ya miƙe tare da dafa shoulder ɗin Noor ɗin, ya daka tsalle tare da ware kafafunsa ya sake kaiwa guy ɗin dake durkushen wani mugun duka a gefen wuya da kafarsa, hakan yasa guy ɗin yanke jiki ya faɗi baya numfashi.Dirowa ƙasa Leo ya yi tare da fara karkaɗe hannunsa alamar sun gama da su dikka…….. Vash ne ya cire bindigar dake wajensa yana faɗin. “Dik ku kashesu, ba za’a rasa mai sauran numfashi a cikinsu ba”…….. Hannu Leo ya ɗaga masu game da cewa. “Ku kamasu mu koma da su sansani, ina zargin ta yadda aka yi suka iy faɗar sojoji, lallai ba ƴan ta’adda bane kawai!”.Noor dake haki kaɗan-kaɗan ne ya ce. “Ina zargin navy ne!”…… A natse Zaynish ya amsa da. “Tabbas na zargi hakan nima”……. Vash ya ce. “Okey kenan Navy sun san da zaman filin da muka je yau kenan?”. Leo dake ƙoƙarin zare belt na wandonsa ne ya amsa da. “Suna da sani mana, sun san komai, kawai sun mayar da kansu karnukan farautar manyan Avaris ne shiyasa basa ɗaukar mataki”….. Zaynish ya ce. “Okey, watau sun ga shigarmu wajen?”…… Kai Leo ya jinjina alamar yeah sun gani. Cike da takaici Zaysh ya ce. “Okey, Navy na gadin ɓarnar manya ƙasa ba wai su dakatar da ɓarnar ba, watau masu gadinsu suka mayar da jami’an?”. Jinjina kai Leo ya yi alamar kwarai kuwa. “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ina ake son ƴan Avaris su sanya ransu? A hukuma azzalumai, a shuwagabannin azzalumai, a makaranta azzalumai, a kasuwa azzalumai, a asibiti azzalumai, a koina azzalumai, ina suke son jama’a su sanya ransu? Wa suke son su kaiwa kukansu ya tsaya masu?”..A taƙaice Leo ya ce. “ALLAH, shi kaɗai zasu kaiwa kukansu kawai, amma basu da wata mafita, a ko’ina akwai gurɓatattu”……. Vash ya ce. “Basa tsoron mutuwa”…….. Zaynish ya ja dogon tsaki game da cewa. “Sun manta akwai mutuwar ne ai, sun manta akwai ranar da zasu tsaya gaban ALLAH su zayyana dik abin da suka aikata”.Noor dake ƙoƙarin haɗe guys ɗin can ya ɗauresu da belt ɗinsa da ya kwance ne ya ce. “Ni fa ina son addinin nan naku, saboda naga akwai adalci sosai a cikinsa, kome zaku faɗa bisa adalci kuke faɗa”. Ai da sauri Leo ya ce. “Are you sure kana son shiga?”……. Kai ya gyaɗa a lokacin da yake ɗago guys ɗin ya saɓa a saman shoulder ɗinsa. “Ina son shiga, bro kyawawan halayenku sun ratsa zuciyata, ibadarku, komai naku akwai kyau, ina son shiga”…….. Da sauri Zaynish ya ce. “A’a to sauƙe waɗan nan mutane ka karɓi shahada yanzu”. Jinjina kai Leo ya yi tare da sauƙe mutumin da ya ɗauka a ƙasa, ya zo ya rungumi Noor yana faɗin. “Ba zamu iya jiran sai mun isa sansani ba, yanzu kawai ka furta shahada”..Ba karamin daɗi Noor ya ji ba ganin suna ta murna dan zai shiga addininsu, aikuwa hakan ya ƙara mashi kwarin gwiwa, sai ya sauƙe mutanen, Leo da Zaynish har suna haɗa baki wajen karanto mashi shahada, ya maimaita, ya ALLAH, su kaɗai suka san irin daɗin dake ransu, rurrungumesa suka yi, Vash mai karnuka ma zuwa ya yi zai rungumesa Noor ya ja da baya yana faɗin. “Bro, ba da dogs ɗin nan ba, ka bari sai mun koma sansani ka”.Murmushi Vash ya saki yana ja da baya. ALLAHU AKBAR, yau Noor ɗinmu ya zama musulmi, ya rabb, yau ranar murnace a garemu mu team NOOR.Haka suka kwashi mutanen, a lokacin 5 na asuba ta yi, gari ya fara haske, kai tsaye suka ƙarisa wajen sansaninsu, cikin dabara suka shiga sansanin, in baku manta ba ai fitar sirri suka yi, kai tsaye tantinsa Leo ya ce su kai mutanen, already biyu daga cikinsu sun mutu, ɗaurin goro yai masu ya barsu a ciki.Ya fito da sauri ya nufi wajen tekun nan dan ya yi wanka su yi shirin sallar asuba, lokaci ya yi, while a daidai lokacin ita ma Arya ta fito dan ta je ta yi wanka, ita tana son yin wanka a lokacin da jama’a suke barci, dan yana son shiga gefen tekun nan wajen ƙorama ta yi wankarta, bata son shiga toilet ɗinsu na nan sansani.Zuciyarta cike da tinanin su Leo basu dawo ba, dan ita tasan basa nan, ta damu sosai, kai tsaye cikin tabkin wajen ƙoramar ta nufa, hannunta rike da soap ɗinta and gel, ta ratayo towel ɗinta a wuya, while tana sanye da pjs a jikinsa, su V dik suna barci, saura sojojin wasu suna wajen wutar da suka hura, wasu kuma suna cikin tantunansu.Da yake wajen akwai duhu saboda duwatsun ƙoramun, sannan gari bai waye sosai ba, dan 5:20 ne a yanzu, so hakan yasa bata ga Leo ya cikin ruwan ba. A saman wata karamar dutse ta tsaya, ya cire pjs ɗin jikinta kaf, ta ware dogon silky ash hair ɗinta da ya kai mata har ƙugu, ya rage daga ita sai wani ƙaramin vest zuwa cibiya wanda bashi da hannu, daga ƙasa pant fari tas mai kyau.Zama ta ya bakin dutsen tare da sanya dogon kafarta dake ɗaure da diamond chain mai kyau a cikin ruwan, ita tana saka chain da waist beat dan kwalliya, amma su V basa sakawa. Ajiye kayanta da towel ɗin a saman dutsen ta yi, ta ajiye su gel ɗinta ma. Ɗan rintse idanu ta yi tana faɗin shiiii alamar ruwan da sanyi, sai kuma ta ɗan ja tsaki game da cewa. “Ko ina su sir Nirash suke? Sun samu nasarar abin da suka je nema? Ina masu fatan cin nasara”. Ta sake jan tsaki tare da datse idanunta, da sauri ta faɗa cikin ruwa tana faɗin shiii sanyi. Dik abin da take yi a kan idanun Leo, amma ita bata farga yana cikin ruwan ba, da yake yana can tsakiya. Linƙaya ta fara yi yana juyi a ciki tana jin daɗin ruwan………… Nima na juya alƙalamina dan ba’a kansu kawai zan ƙare page ɗin ba, zamu dawo anjuma mu ga ya zasu kaya a cikin ruwan nan, ga Noor ya musulunta, Zaynish da yankar wuƙa a hannu, ga haɗaɗɗun karnuka guda biyu da muka samu, ga waɗan nan miyagun da muka kama, kai ga-ga ɗin ma yawa me da shi fa. Bari dai mu je mu dawo. ————————–🔥CRYSTAL PALACE.”Daddy please talk to me, baka da lafiya ne?”. Tamkar zata yi kuka ta yi maganar. Hannunsa yasa ya laluɓo nata hannun, ya ƙanƙame cikin nasa, can ƙasan maƙoshi ya ce. “Stop crying kada abin ya mun yawa kin ji my Cherry?”.Ajiyar zuciya ta sauƙe, da kyar ta iya cewa. “Daddy na bari, amma ka faɗa mun me yake damunka ne, baka da lafiya ne?”……. Ɗan matse hannunta a cikin nasa ya yi, yana ɗan lumshe idanu ya ce. “Ban taɓa maraicin uwa ba sai yau, ban taɓa jin zafin rasa Ummiena ba sai yau, my Cherry please ina son farinciki na musamman ta ɓangarenki kin ji?”. Ya faɗa tare da juyo da jikinsa ya kwanta a miƙe.Hannunta ɗaya ta ɗaura a kan lion chest ɗinsa. “My gentle chaos, zan yi dik iyawata wajen ganin na wanzar da farinciki a tattare da kai, yanzu dai faɗa mun baka da lafiya ne?”. Ta kai karahe tana ɗan sunkuyo da kanta a kansa kaɗan, ta ɗan ɗaura goshinta a kan nasa……… Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. “Lafiyata lou, kawai ina cikin damuwa ne, na tina Ummieta”.”Daddy na yi alƙawarin sanyaka farinciki tamkar yadda Ummie take sanyaka”……… Ɗan miƙewa ya yi, ya koma yai kwamciyar ruf da ciki, ya ɗago kansa suna kallon juna, zallar madarar kaunarta ne kwance a cikin kwayar idanunsa, in a low way sosai ya ce. “Are you sure?”. Ya faɗa yana ɗage mata gera guda. ALLAH sarki har ya mance me Abba yai mashi, masoyiya ta kwantar mashi da hankali.Tafukanta ta ware, kumatunsa dikka biyu ta tallabo, tana murmushi ta ce. “I’m very sure my gentle chaos”. Ta faɗa tana ɗan matse kumatun nasa……. Zuba mata idanu ya yi yana jin wani irin tsantsar kaunarta na ratsa mashi zuciya, haɗe fuskokinsu ta yi, ko kunyar kallon cikin kwayar idanunsa bata yi, a shagwaɓe ta ce. “My gentle chaos ina sonka sosai”. Wani irin kallon kauna ya ɗan bita da shi kafin in a low way sosai ya ce. “Love you more, from the button of my heart, love everything about, coz you’re special”.Ɗan ɗagowa ta yi, ta sumbaci gefen lallausan kumatunsa, tana murmushi. Hannu yasa ya shafi soft cheek ɗinta game da lumshe idanu, a cikin ransa yana jin zai samu hanyar rabuwa da Rimsha, shi bama wai rabuwa da ita ba, bai damu ba dan bai ɗauketa mace ba, bai yarda matarsa bace dama, amma dai koma me yana tsoron ɓacin ran Seraphina sosai, shiru ya yi yana tinani, can ya tina why not ya haɗa guru da Rimsha? Saboda Abba yana da abu guda ɗaya, idan Rimsha da kanta ta same shi ta ce bata son Aryan lallai zai yarda ya raba wannan aure, hakan kuma ba zata faru ba har sai Rimsha ta faɗa son wani.Da alama hanya ce ta haɗuwarta da guru wannan aure nasu, tabbas zai ɗauketa ya kaita gidansu, ta rayu a cikinsu matsayin sister ɗinsa, daga nan guru zai fara sonta, idan soyayyarsu tai zurfi Rimsha ba zata iya rabuwa da shi ba, tabbas zata faɗawa Abba bata son shi, shi kuma zai raba wannan aure nasu, daga nan shi kuma Aryan ɗin bayan ya saketa ya aura mata scorpion ɗin, tabbas zai wahalar da ita ta yadda ba zata taɓa jin son shi a ranta ba, hakan zai sa ta fara son guru da wuri ayi komai a gama. Lallai wannan shawara ta yi, tina haka yasa ya sauƙe dogon numfashi……. Lallai nima na shaida, wannan wata hanyace ta haɗuwar Rimsha da guru, ko kuma Lion da Rimsha ba……….. 👀Cikin zolaya ya ce. “My Cherry yanzu idan na ce mata biyu zan aura zaki yarda?”…….. Zazzaro idanunta a kansa ta yi, sai kuma ta tamke fuska tamau. “No daddy, ni kaɗai zaka aura, babu wani mata biyu!”. Tana hura dogon hancinta ta faɗa, zallar kishinsa ya gani kwance a cikin kwayar idanunta tin ma bata san menene auren ba.Kai ya jinjina tare da cewa. “Yadda kike son kawarki Rimsha ɗin nan ba zaki yarda ku auri miji ɗaya ba?”…….. Siririn dariya ta ɗan yi kafin ta ce. “Mijina ni kaɗai ne, ita ma mijinta ita kaɗai zata aura!”. ……. “But why?”. Ya tambaya cike da mamaki, dan ya zaci sai wacce tasan aure take kishin mijinta ai.Hannu tasa ta rufe fuska tana murmushi game da cewa. “Daddy ba kace in daina maganar da bata dacen can ba?”. Kai ya jinjina alamar haka ne ya hanata, ohk sai yanzu ya gane nufinta, watau ba zata yarda wata mace ta raɓesa har ya haɗa jiki da ita ba, lallai Seraphina ta wuci tinaninsa, miƙewa zaune ya yi, sai ya canza topic na hirar kafin ta jefa mashi wata maganar ta juya mashi ƙwaƙwalwa. Ƙarisa hayewa saman gadon ya yi tare da kwanciya da kyau, ya jawo pillow ya ɗaura a kan kirjinsa, yana binta da wani irin narkakken kallo mai narka zuciya ya ce. “Ina jin kamar ke na rumgume ba pillow ba, zan yi barci kada ki tasheni”. Wani haɗaɗɗen murmushi ta saki wanda ya fito da dimple ɗinta sosai, har wushiryar dake tsakanin fararen hakwaranta tas ya bayyana. “Daddy kana feeling love a kaina kamar yadda nike ji a kanka dama?”……. Kai ya jinjina mata alamar. Da sauri ta dawo kusa da shi, ta haɗe hannayenta ta kama kumatunta, cikin shagwaɓa ta ce. “Daddy, let feel our love”. “Sure?”…… Kai ta jinjina. “Let feel it daddy”……. Ɗan nisawa ya yi tare da ƙara ƙanƙame pillow ɗin a kirjinsa, kamar mai raɗa ya ce. “Give me some love words that will make my sleep more nice, idan na tashi zamu cigaba da hira, now I’m feeling sleeping, jiya ban yi barcin dare sosai ba”. Kai ta jinjina tare da matsar da face ɗinta dab shi…….. “Love you more my gentle chaos, a dik lokacin da ka ji kamar kana kaɗaici, remember that you have a beautiful wife, sister, baby, Cherry, beside you, ina tare da kai to make your smile more beauty, make your heart more peaceful, make your body more……..”. Fasa ƙarisawa ta yi, saboda tai mashi alƙawarin ba zata sake yin maganar da bata dace ba. To Tin da ta fara magana ya tsare ɗan bakinta da kallo, zuciyansa na ingiza shi da ya yi kissing ɗinta kawai, ya rabb, shi kaɗai yasan me yake ji a kanta, kome take yi ƙara kyau take yi, kome ta yi burge zuciyansa take yi, shirmenta abin so ne a garesa, kalamanta abin so ne a garesa, soyayyarta ya zame mashi jinin jiki. Matsawa ta yi ta ɗan sumbaci cheek ɗinsa tana faɗin. “Sleep well, make sure that i come into your dreams as your wife, ina kwance a saman kirjinka ina……”. Still kame bakinta ta yi, ta fasa ƙarisa maganar. Slowly ya lumshe idanunsa yana jin wani irin daɗi a ransa, lallai Seraphina ta fara natsuwa, sau uku kenan yanzu tana kame bakinta taki ƙarisa magana saboda ya hanata, kai lallai ya ji daɗi sosai yau. Ganin ya lumshe idanu ne yasa ta tsaresa da kallo tana jin sabon sonsa yana shigarta. After like 5 mins slowly ya waro idanunsa kai tsaye a kan face ɗinta, in a sleeping voice ya ce. “Stop looking at me Cherry”.One side smilling ta saki kafin ta ce. “Daddy ni da fuskan mijina zaka ce in daina kallonka?”. Tana turo baki ta kai karshe. Hannunsa ɗaya ya ɗaura a kan shafaffen cikinsa dake da guraye saboda gym da yake yi, in a sleeping voice ya sake cewa. “My cherry, I’m feeling hungry sosai, ban yi breakfast ba, dinner ɗin jiya ma ban ci ba”. Yana magana yana lumshe idanunsa, watau sai da ya zo wajenta ya samu natsuwar iya gane ashe yana jin yunwa.Da sauri ta ɗaura hannunta a saman cikin nasa, daidai in da hannunsa yake, sai ta ce. “Daddy tashi in yi feeding ɗinka, bari in je in haɗa maka abinci a kitchen”. Ta faɗa tare da yunkurawa zata miƙe, da alamar tausaya mashi sosai a kan fuskanta. Slowly ya riko hannunta cikin nasa, ɗan jawota ya yi, sai ta tafi gabaɗaya ta faɗo kansa, fuskokinsu yana saitin na juna, in a low way sosai ya ce. “Let me sleep first, idan na farka sai ki bani abincin a baki kin ji?”. Kai ta jinjina alamar to ta gagara yin magana, saboda yadda ta kalli kwayar idanunsa dab ita ya rikita zuciyarta.Slowly ya saketa game da lumshe idanunsa, kafin wani ɗan lokaci ya yi barcin gaske mai daɗin da ya jima bai yi irinsa ba. Shiru ta zauna tana ta faman kallonsa, bata son matsawa daga kusa da shi ko kaɗan, tana ganin kamar rabasu za’ayi idan ta matsa, har da kwanciyar ruf da ciki, ta ɗaura kanta a saman kirjinsa, tana kallon face ɗinsa, a hankali barci ya ɗauketa ita ma.CRYSTAL PALACE, idan na kira sunan CRYSTAL PALACE a yayin da muke cikin CRYSTAL PALACE ɗin muna labari to ina nufin zuciyar CRYSTAL PALACE gabaɗaya ne, watau gidan MUHAMMAD HAIZA’AN, gidansa ne zuciyar CRYSTAL PALACE, gidan da ya fita daban a tsarin ginin cikin CRYSTAL PALACE ɗin, gidan da aka ware a waje daban, yana gefe can, wani shinfiɗaɗɗen titi da aka shinfiɗa wanda ya miƙe har cikin gidan kawai abin kallo ne, kun san dukiya tai kuka ba kaɗan ba, ya rabb, tin daga farkon titin nan jiga-jigan jami’an SSO ne suke shawagi, ko tsuntsuwa basa bari ta gifta ta sararin samaniyar gidan Haiza’an, lallai na shaida dik wani karfin iko ya kare a wannan waje.Zaku rantse da ALLAH dik jami’an dake US aka zuba a wannan gidan, wasu irin guards waɗan da ko fuskansu baka iya gani face idanunsu dake rikitar da zuciyar bawa su ke gadin gidan, ya kuke tinanin san da yake raye kenan? Wai a haka ya rasu ne wannan karfin ikon! Ya ALLAH. To mu yi tattaki zuwa cikin gidan dan mu ga meke going a ciki, ya tsarin gidan yake tin da na ce ya fita daban da tsarin sauran gine-ginen dake cikin CRYSTAL PALACE ɗin. Jama’a ban taɓa tinanin za’a samu gidan da zai fi Black Tiger empire haɗuwa ba, sai ga CRYSTAL PALACE da kanta, ga kuma uwa uba zuciyar CRYSTAL PALACE watau gidan Haiza’an, ya ALLAH kai mana arziki mai albarka kawai.Siffar ginin gidan ya kasance irin ginin mediterranean ɗin nan ne ta gefe-gefe, daga ta gaban gidan kuwa zallar glass ne, girman gidan ya fi fili flot 20, saɓanin benayen CRYSTAL PALACE shi wannan gida yana da gate, an kewayesa ne, sai kun wuci gate uku manya-manyan masu cike da tsaro na ban mamaki kafin ku ƙarisa cikin gidan, sannan shi wannan hawa uku ne kawai.A gefe guda harabar gidan ga tampatsetsen lambu mai ɗauke da ƙananan arche, ƙananan ƙoramu ne da aka yi su dan ƙawata lambun, ga wasu irin fitillu da aka ƙawata lambun wanda ko dare ne zaku zaci rana ne saboda haskensu da ƙawarsu, uwa uba lambun da glass wall aka kewayesa, daga waje kana iya hango haɗuwarsa ta ciki, ya ALLAH, ga wasu kifaye orange and red da aka zuba cikin tampatsetsen glass suna ta yawo cikin ruwa, shi ma ya ƙara ƙawata lambun matuƙa, ga wasu flowers masu mugun kyau da ɗaukar hankali, a bakin kofar lambun daga gefe an yi wasu flower da aka shukasu aka yi siffar sunan HAIZA’AN’S GARDEN da su, jama’a wlh lambun nan ya haɗu fiye da yadda kuke hasashensa a ranku, kuɗin da aka narƙa a wannan waje, kai kuɗin mahaikatan dake gyran lambum nan kawai jarin wani ɗan siyasa ne a Avaris!. A budget ake cire kuɗin masu aikin gyaran gidan Haiza’an, a shekara ake lissafi a cire kuɗin masu gyaran gidan, akwai mata akwai maza, kowa da aikinsa, kullum na ALLAH sai sun share ko’ina sun gyara tamkar yana raye………… Jama’a baku tunanin bayan mutuwar daddy Haiza’an akwai abin da ya faru kuwa?.A tsakiyar tampatsetsen harabar gidan akwai wani waterfall wall, architecture design of gunking zaki ne dake faman fesa ruwa daga bakinsa, ya wage baki sosai ruwa na zuba ta bakin nasa, a ƙasa an yi mashi round tamkar rijiya ruwan da yake zubarwa tana taruwa a wajen, daga can ƙasa akwai hanyar da ruwan yake sake komawa bakin zakin, ba karamin ƙara gyara gidan wannan design ɗin ya yi ba. Ga wasu shuke-shuken flowers a gefe guda da suka ƙarawa gidan haɗuwa.A gefen dama akwai guest suite, ɗakunan baki guda biyu tare da toilet da kayan more rayuwa a ciki. A gefen lambu akwai tangamemen garage na parkin motocin wanda tsab zai iya ɗauke motoci 30 ciff, gate na shiga garage ɗin automatic ne, da kansa yake buɗewa da rufewa, har yau akwai jiga-jigan motocin daddy guda biyar ciff a fake, tsadaddun motoci ne da suka haɗa da Maserati Levante Trofeo, Rolls-Royce Cullinan, Bugatti Chiron Super Sport, Mercedes-AMG G 63 sai wata mota mai tuƙa ƙanta, motocin dik an rufesu da car cover.Sannan akwai katafaren swimming pool a ta gefen ginin ba harabar gidan ba, a ɗan gefe aka ƙawata shi, yana ɗauke da sky blue ruwa mai balain kyau da ɗaukar hankali. A gefen pool akwai glass wall na tennis, basketball, filin wasanni na tennis da basketball har ma da football.A gaban zakin wani tampatsetsen baranda ne a wajen wanda babban parlo door yake kansa. Kai mu haura ground floor dan wlh ƙawartuwar harabar gidan nan ya zarce in iya faɗa maku shi lokaci guda, sai a hankali.Mu lula grand entrance hall, babban kofar shiga ground floor, kofar ya haɗu, ga kakkafar tsaro da idan ba mamallakan ginin ba babu wanda ya isa ƙetarawa izuwa ciki, ya fi kofofin CRYSTAL PALACE tsaro da amfani da kimiyar zamani.Kana shiga kofar akwai wani dogon corridor mai kyau wanda yake ɗauke da fitilar chandeliers a tsakiyar corridor ɗin daga sama, duk tsawon corridor din nan sai da chandeliers ɗin nan ya kusa kai ƙasa saboda tsawo da haɗuwarsa.Idan ka wuce corridor ɗin sai haɗaɗen automatic door, kana buɗesa da wani katafaren living room zaka fara cin karo, haɗuwar parlon nan ba zai faɗu ba, kusan za’a ce five in one ne parlon, dan haɗaɗɗun luntsuma-luntsumar sofa set kala biyar ne a cikin parlon, kowani set ya haɗu matuƙa.A cikin parlon akwai door da zai sadaku da tamgamemen mediterranean kitchen, kitchen ne mai siffa ra gargajiya, amma su gas na zamani ne a cikinsa, da alama daddy yana son gargajiya, dan a waje harahar gidan cikin wannan lambu akwai hut da aka ƙawata har guda uku, sai dai bukkar ba’a kewayesu da komai ba face glass, samansu kuma exactly bukar da ake yi a ƙauye, cikin bukkokin kuma haɗaɗu kujeru ne na zama dan shaƙatawa, to da alama yana ɗan son gargajiya.Iya wannan kitchen ɗin ne a ground floor, sai wani haɗaɗɗen butterfly stair case da ya yi sama izuwa first floor, nan ma akwai babban parlo two in one, sai master suite, katafaren ɗaki mai ɗauke da babban balcony da ke kallon wajen harabar gidan da sauran cikin CRYSTAL PALACE ɗin. Sai katafaren toilet mai ƙunshe da jacuzzi da shower mai ban sha’awa.Bayan master suite akwai luxury bedrooms guda uku, ɗaya ɗakin yara ne, biyun kuma ɗaya na matar gida, ɗaya kuma babu kowa a ciki sai kayan alatu da aka zuba. Kowanne ɗaki na da toilet haɗaɗɗe da balcony, ga furnitures made in Dubai masu matuƙar kyau da tsada. Bayansu akwai dining hall, shi ma dik glass wall ne, daga parlon first floor ɗin kana hango cikin dining hall ɗin, katan table da haɗaɗɗun chairs guda 24 ne a ciki, sai show glass da ake zuba cups and plates a cikin dining hall ɗin, ga haɗaɗen decorations, and daga cikin dining hall ɗin kana iya hango wannan haɗaɗɗen lambun na waje mai ɗaukar hankali. A gefen ɗakin daddy Haiza’an akwai family lounge, wani ɗaki ne na taron iyali tare da TV mai faɗi da sofas masu taushi. To mu haura last floor muga me a ciki, ni fa ina son in ga na ɗauko maku abubuwan da cigabansa bai zo mana Naija ba, dan ni a tinanina da yadda na ɗauki rubuta littafi ana rubuce-rubuce ne dan ƙaruwar al’umma da wayar masu da kai game da basu ilmin da ALLAH ya hore maka wanda su basu sani ba……..Kazalika kuma makaranta a tinanina kuna karance-karance ne dan ku samu ƙarin ilimi, so bai kamata ace kuna karanta abin da muke da shi a Naija ba, abin da already kun san shi sai dai ayi ta maimaitawa, shiyasa dik rubuce-rubucena yake ketarawa ƙasashe, mu zaƙulo abubuwan da baku sani ba dan ku sani ku kara samun ilmi, kunga ko baku je ƙasashe ba kun san me yake wajen, wannan shi ne kun yi karatu mai riba, kun kara samun ilmi!.Last floor. Tampatsetsen gym room ne a wajen da aka ƙawata shi dan motsa jiki tare da kayan zamani, sai haɗaɗɗen cinema room dan kallon fina-finai mai ɗauke da fitillun chandelier da kujeru masu taushi dan zaman kallon film da family.Baya ga shi akwai haɗaɗen roof terrace a saman, wani ƙaramin filin shakatawa ne, tare da barbecue station da kujerun hutawa. And daddy yana da home office na musamman dan aiki, tare da shelves da table na zamani……. A can sama kololuwa wajen sauƙar madaidaiciyar private jet ɗin daddy ne, akwai haɗaɗɗen jirgin da kowa zai yi mafarkin mallaka a wajen an faka shi, jikin jirgin ɗauke yake da sunan MUHAMMAD HAIZA’AN da harafin larabciTo nifa my people wannan lambu na daddy ya tafi dani, dan haka ko aiki ne su Lion su ɗaukeni a wannan lambu, dan gaskiya ina son rayuwa a cikinsa, ya haɗu ne. Jama’a ALLAH ya mana arziki mai albarka, ya bamu lahira mai kyau, amma gaskiya zuciyar CRYSTAL PALACE ta haɗu, haɗuwa fiye da tinani. ————————Kwance Lion yake a saman bed ɗin daddynsa a master room ɗinsa, ya tada kai da laps na wani kyakkyawan mutum wanda kana ganinsa kasan jininsu ne, dan akwai kamanni ta jini a tsakaninsu. Mutumin na sanye da tail coat a jikinsa, yana rike da hannun Lion ɗin, ɗayan hannunsa kuma yana shafa haɗaɗɗen golden hair ɗin Lion cikin tausasawa da nuna tsantsan kauna. Wannan mutumi ba kowa bane face Hussain ɗin daddynsu, ɗan biyun mahaifinsu wanda shi ya reni su Lion ɗin, da Lion ya shiga damuwa ne ya zo gidan daddyn nasa, sai ya ƙira uncle ɗin nasa kan ya zo su haɗu, kun san da cewa uncle ɓoye kansa yake yi? Baya son duniya ta san yana raye, yanzu haka duniya dik sun ɗauka ya mutu ne.To meyasa yake ɓoye kansa? Ya aikata wani laifi ne?. Muje zuwa alƙalamina zai amsa masu.”Zayra’an!”. Daddy ya faɗa yana riƙo hannunsa a cikin nasa da kyau, shiru Lion bai amsa mashi ba, da alama ya yi barci. Ɗayan hannunsa daddy yasa yana ɗan shafa kansa a hankali, slowly ya ɗago idanu ya fara bin room ɗin da kallo, komai yana nan yadda yake, babu abin da aka taɓa face gyaran da ake yi wa komai.Lokaci guda daddy ya ji tamkar Hassan ɗinsa yana raye, idanunsa na mashi kizo lokacin da dad ɗin Lion ya tsaya a gaban parlo, yana ɗaura necktie a wuyansa, cike da tsantsar kaunansu yake cewa. “Hussain ka tashi ka bar mun gida, ka bar mun yara cikin kewa da kaɗaici, ka je na sallameka, kuma kada ka sake zuwa sai na nemeka”…… Mom Lion tana sauƙowa ta ce. “Zaka koran mun ƙani a kanka yake zaune ne?”.”Tuba nike ranki ya daɗe”. Dad ya faɗa yana miƙa mata hannu kan ta bashi wayansa dake hannunta……… Rintse idanu daddy ya yi, wani dogon numfashi ya ja game da sauƙewa a hankali, ya fama ciwon dake ransa na tina rayuwar baya. Dawo da kallonsa a kan kyakkyawan fuskan Lion dake ta zuba barci ya yi, cikin barcin ma sai sauƙe ajiyar zuciya yake yi alamar ya fara samun peace of mind, ALLAH sarki, idan ya tina rayuwar iyayensa in bai zo ya ga second daddyn nasa ba baya samun natsuwa, ganinsa kawai shi ne kwanciyar hankalinsa, shiyasa ya gudu ya bar su Aryan tin asuba.”Ina sonka sosai Zayra’an, ina sonka fiye da kaina, ba wanda nike gani in ji daɗin rayuwata face kai da ƴan uwanka, ina rokon ALLAH ya bani ikon cika alkawarin dana ɗaukarwa ɗan uwana na kula daku”. Ɗan motsawa Lion ya yi, hakan yasa ya zame hannunsa daga cikin na daddy, ya gyara kwanciyansa da kyau, ya cigaba da barcin da bai samu damar yi daren jiya ba…….. Sake riƙo hannunsa gam daddy ya yi tamkar ance za’a rabasu ne, ya yi shiru yana ta kallon fuskan Lion. Slowly ya jingina kansa da jikin headboard na gadon, ya ɗan lumshe idanu cike da tinanika kala-kala.Barcin good 2h Lion ya yi, daddy na zaune bai motsa ba gudun kada ya tashesa. A hankali ya waro idanunsa da suke jajir saboda barcin bata ishe shi ba. Kai tsaye sai kan fuskan daddy….. “Dad”. Ya furta yana miƙewa zaune, kallon farko ya zaci dad ɗinsa ne ba daddy ba. Slowly daddy ya yo ƙasa da kai yana faɗin. “Ka tashi?”. Kai ya ɗan jinjina game da cewa. “What says the time?”…… Laluɓo waya daddy ya yi, ya kunna light ɗin screen………. 4:00 PM. Iska mai ɗimi daga bakinsa ya furzar game da miƙa hannu ya jawo nasa wayan. “Daddy let me call Aryan, nasan yanzu yana can ya damu da rashin sanin ina nike”.Cikin zolaya daddy ya ce. “Sai yanzu ka tina da shi kaima ai”….. Shiru bai yi magana ba, ya fara laluɓar number Aryan, ya danna kira. Sai dai a lokacin dik suna barci a kan gadon Seraphina, wayar tana silent basu ji ma, message Lion ya rubuta mashi kan yana lafiya kuma yana dawowa yanzu. Wayoyinsu kusan a haɗe yake, sun saita shi ta yadda idan ya turawa ɗaya saƙo dikkansu saura ukun zasu samu saƙon.Yana tura masu ya zuro kyawawan kafafunsa ƙasan bed ɗin, jikinsa dik a mace ya miƙe tsaye, toilet ya nufa, da kallo uncle Hussain ya bisa har ya shige katafaren toilet ɗin daddynsa, ajiyar zuciya Uncle ya sauƙe game da gyarawa ya kwanta. After 2 hours, Lion ne tsaye a tsakiyar master room na daddyn nasa, yana sanya botiran tail coat na jikinsa, ya rabb, kayan sun zauna a jikinsa matuƙa, tamkar dan shi aka yi su, yai wa kaya mugun kyau, ya tara kitson kansa ya ɗaure, jade eyes ɗinsa sun ciza sosai, kyawawan soft lips ɗinsa sun ciza pink matuƙa, fuskansa ya yi very fresh sosai, ya ƙara kyau da cikar haiba da kamala. Uncle dake zaune a kan gado yana kallonsa ne ya ce. “Zayra’an please ka dawo gidan nan da zama, tsawon shekaru 10 kenan yanzu ina binka kaki yarda, meyasa baka son zama a nan ɗin?”..Shiru ya yi bai amsa ba, har Uncle Hussain ya fidda ran zai amsa mashi ma sai kuma ya ji in a low way ya ce. “Nothing, kawai bana son gidan ne”.”Please, even because of Nirash, ku dawo ku raya gidan nan, ku sake raya ruhin Haiza’an ɗina, ku farfaɗo da gidan”……. Nan ma shiru for good 3 mins ya yi kafin ya ce. “Zaka dawo mu zauna a tare a nan ɗin?”……. Rass uncle Hussaini ya ji gabansa ya faɗi, amma sai ya daure da cewa. “Zan yi tinani, amma idan na aminta zan dawo mu zauna gabaɗaya zaka dawo?”. Kai kawai ya jinjina ba tare da ya sake yin magana ba. Shiru uncle yai yana tinanin yadda zai dawo gidan su haɗe waje guda, da kuwa abin zai yi making sense. Katse mashi tinani Lion ya yi da cewa. “Bye uncle”……. “Bye my beloved son”. ……. Daga haka bai sake magana ba ya fice waje, ya bar uncle, dik lokacin da yake so zai iya tafiya, shi dai ya koma benensu.Yana fitowa waje wasu karfin jami’an SSO suka nufosa da gudun gaske, hannu ya ɗaga masu tin ma basu ƙariso ba, baya son hayaniya da gayya, baya cikin wani good mood sosai. Sauƙowa kasar wannan baranta ya yi, ya nufi gate na fita, da kafa zai koma benensu ba sai ya ɗauki mota ba, dama da kafa ya zo. Kafin ya fito sai da ya sanya wannan haɗaɗɗen nose mask ɗin nasu a face ɗinsa, sannan ya fito ya nufi benensu, a cikin ransa yana jin kamar zai iya dawowa gidan nasu da zama.Dik in da ya zo ƙetarawa sai waɗan nan jiga-jigan jami’an sun kame tamkar basa numfashi sun sara mashi, bai ɗago ya kalli kowannensu ba, bai tanka kowannensu ba, ya wuce kai tsaye ya nufi benensu.———————-🔥KHAIZA’ANS HOUSE.Sai da aka zubawa Rimsha ruwa 3 bottle kafin su samu kanta ta farfaɗo, da kuka ta farfaɗo tana faɗin. “Abba yanzu uncle Aryan ɗin ne mijina?”…. A lokacin Abba baya kusa, sun baro room ɗinsa da ita, Faryan ya ɗauke zuwa room ɗin Ammie.Rungumota Ammie ta yi, ta hau rarrashinta tana bata baki, sai dai ina Rimsha taki yin shiru, in short sai da ta ɗauki kwanaki uku tana wannan kuka na ta shiga uku, dik Abba bai san tana yi ba, a rana ta huɗu ne ta kama Monday, a wannan ranar da asuba Faryan ya ce ta shirya ya kaita school.Jin cewa aurenta ba zai hanata school bane yasa ta ɗan saki jiki, burinta dik ta je makaranta su haɗu da Seraphina ta faɗa mata abin da aka yi mata, dik tayi sanyi baiwar ALLAH, daga umm sai uhm-uhm ta zama, bata hira, ta takura kanta sosai, amma yau da zata je school har da ɗan murmushinta. Ta shirya tsab cikin uniform ɗinta, har ta rame uniform ɗin yai mata yawa. Faryan na tsaye a parlo ta fito rike da rucksack ɗinta, karɓa mata ya yi yana faɗin. “Mu je in kaiki da wuri, Abba na jirana zamu je mu ɗauki amaryar Yah Harleen”. Kallonsa ta yi, muryarta a dashe sosai ta ce. “ALLAH yasa tana da kirki”……. Da amin ya amsa game da riko hannunta, suka nufi waje yana kara yi mata nasiha, yana tausan zuciyarta, yana faɗa mata kalamai masu daɗi, yana tunatar da ita ALLAH ya ce Annabi ya ce, a haka suka nufi school ni kuma na nufi DOL kafin mu dawo mu bisu school ɗin. ——————–🔥D-O-LNutso take yi a cikin ruwan cike da farinciki, yana tsoma gashin kanta can kasan ruwa tana ɗagosa ruwan dake biyo gashin ya ƙara wanke mata fuska, hakan ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba. Shi kuwa tamkar gunkin da aka sassaƙa haka yake tsaye a cikin ruwan ware kitson kansa dan ya wanke golden hair ɗinsa. Tsoma kanta ta yi cikin ruwan tana ɗan juyawa, ɗagowa da zata yi tana faman yin sama da kanta sai ji ta yi………..

Back to top button