Gargadar So Chapter 122 By M Shakur
Ahankali take iya bude idanunta ganin gari yayi haske yasa ta kalli wayanta da sauri taga 7:45, Subhanallahi tafadi da sauri ta tashi tashiga bayinshi tadauro alawala tazo tai salla ta idar tai azkar ta karatu ta gyara dakin tass ta kunna turare tawuce bayinta tai wanka har yanzu idanunta a kumbure closet nata ta shiga tasaka wani atampa riga da skirt dakeda red ajiki batasa komi a fuska ba tafito tasauko kasa kitchen ta shiga tayi tea a cup tafito tazauna tana kallon tea din wlh takasa sha sai kawai ta tashi taje kitchen ta ijiye tasa marfi tarufe tafito takoma sama ta shiga closet red mayafi ta dauka babba tayafa tafito tasauko kasa, crocks dake nan kasan falon na Khaleel tasaka tabude kofa tafito tana tafiya ahankali tawuce side nasu Mom.Gently tabude kofan da sallama a bakinta ta shiga ciki Momy ne kadai afalon ga plate na fruits tanaci cus yanaci fruits take faraci dasafe idan Excellency na gari tana breakfast da wuri but jiya da night yatafi France saisa take breakfast ita kadai ga ma’aikata a dinning na jera warmers, kallo daya Mom tama Hawwa ta dauke kai tacigaba da cin fruits abinta, dudda gaban Hawwa na fadi but har gaban Mom tazo ta duka ahankali tace “ina kwana Mom” dauke kai Mom tayi kaman bada ita take magana ba chan tace “lafiya” shiru Hawwa tayi still tana gabanta chan tace “Mommy dan Allah kiyakuri kiyafemin kinji Mom” kallonta Mom tayi tamata wani banzan kallo tace “tashi agabana” ahankali Hawwa ta tashi, gently tawuce wajen dinning saikuma tawuce kitchen, 3workers ne ke aiki an riga an gama breakfast na Mom dasauri suka gaida Hawwa. “Good morning Ma” gyadamusu kai tayi ahankali Hawwa tace “me kuke dafawa” babban ma’aikaciyan tace “an gama breakfast na Madam, tace ama Mr Khaleel kunu da akara shine zan fara yanzu” Dasauri Hawwa tace “ki barshi zanyi” batama jira amsan su ba tace “ina wajen wake? Da gero”?Dukansu suka nuna mata store sai kawai tawuce store ta debo wake da geron kunu tafara aiki sukace mezamuyi tace “no karki damu, kawai zan dinga tambayanki unda abubuwa suke” tafara aiki she will do everything in her power to win Khaleel’s love back.Kunu tashiga yima Khaleel, Mom na zaune a falo kusan 30min saikuma ta juyo badai yarinyar nan taje tana taya yan aiki yin aikinsu ba, juyowa tayi but bata ma iya ganin kitchen daga wajen, tashi tayi ahankali rike da empty plate na fruits nata tazo wajen kitchen din duk basu ganta ba turus ta tsaya tana kallon Hawwa dake buga kosai yan aikin sun zazzauna suna kallonta, yaune rana na farko da Momy ke ganin Hawwa babu mayafi dan ta rataya gyalen a kofa tana aiki gaskiya yarinyar is very very beautiful she cannot even lie and she’s tall and very pretty dan kitson datayi dan ya zubo a bayan wuyanta kuma gashinta da tsayi, tai shiru kawai tana kallon Hawwa somehow she’s seeing why yaronta ke sonta, Hawwa kaman taji ajikinta ana kallonta juyowa tayi ganin Mom yasa gabanta yafadi da sauri ta ijiye bowl din ta taho wajen kitchen din bayan taja gyalenta daga kofa ta yafa cus is her own way of showing iyayen mijinta tana girmama su, yan aikin na tashi suma dasauri, ahankali cikeda respect Hawwa tasa hannu takarbi empty plate dake hannun Mom, cikeda girmamawa tace “Momy kina bukatan wani abune namiki?” Tsayawa Mom tayi tana kallon Hawwa shekeke sabida mijinta yayi yaji itama tazo tawani biyoshi nan, saikuma cikeda masifa tace “me kikemin a kitchen nina aikeki”? Kanta na kasa tace “Momy kiyakuri kosai zanmai” dariyan takaici yakusa kufcema Mom tace “eh kin iya kosai amman baki iya kulamin da yaro ba mara mutunci kawai, kinaso ki kashemin dan dayadaya ne” Mom tajuya fuuu Hawwa tajuya takoma kitchen she just promise kanta she will show Momy she’s a good person and she will win Momy da Khaleel dukansu, komawa tayi tashiga soya kosan da ko’ina yacika da kamshi.Sai bayan yadawo daga masallaci yasami bacci, kamshin kosai daya ratsa hancinsa yasa ahankali yabude idanu hardly kamshin abinci ke shigowa side nashi wat happened yau kodan ba’a cika kosai bane anan he just hopes kosan will taste good kaman na Hawwa. Yadan sauke ijiyan zuciya sabida fadomai zuciya da Hawwa tayi, sannan ya tashi yafada bayi yayi wanka but still idanunshi jaaa closet nashi ya shiga yasa AMI Paris shirt just 2 buttons na kasa yasaka yana yasa wani 3qyater dark blue ya feffesa turare har wani dan ramewa yayi yasaka flops yashiga saukowa yana folding hands na riganshi Mom dake zaune tana bude news paper ta dago kanta takalleshi yarinta duk ya susuce yadawo wani kala tashi tayi tana ijiye jaridan cikeda so tace “Khaleely” he’s not happy kawai bayama walwala ko kadan tarasa wani kalan so yakema Shegiyar yar sandan nan mara kirki bayan ga mata wayanda suka fita sosai, ahankali yace “good morning Mom, an mini kosan”? Gyadamai kai Mom tayi takama hannunshi tace “let’s go lemme feed you” Hawwa na tsaye a kitchen tana karasa tuyan kosan taji Kamshin Khaleel ijiyan zuciya ta sauke ahankali kirjinta yahau bugawa.


