Karfe A Wuta Chapter 105 By Ayshercool
105Sake ƙasa yayi da muryarsa, ya ce “Ina sake roƙonki, ki bani dama, kin yi mini kuskuren fahimta ne kawai, ban san yaya zan yi miki bayani ba, amma za ki ga komai a aikace”Bakinta ta motsa za ta yi magana, amma a dole ta haɗiye maganar, biyo bayan dogon harshensa da ya saka a kan laɓɓanta.Bayan su Walid sun fita, ya kalli liti ya ce “Ina jinka, me zaka ce mini?””Wai wannan farar yarinyar yar uwar Nabilan ce ne?””Eh””To kuma har muka fito ba ka yi mata magana ba, ka san dai ka fini faraa’a da kalar masu kirki””In yi mata magana in ce mata me? Ko dai sonta ka ke yi ne?””To wa ya san mini ma, amma ɗan yi mata magana, gata can sai waya take yi “Walid ya ce “In yi mata magana in ce mata uban me? Kai ka yi mata mana, tun da sonta ka ke yi. Babanta dai tsohon soja ne, wallahi kayi masa shirme sanyawa zai yi kuratan nan, su yi maka dukan jaraba na gaya maka”Liti ya ce “Ta Allah ba taka ba, kuma a yanzu zan nuna maka banbancina da kai” kawai ya nufi in da Walida take waya, tana ta surutu da wata ƙawarta mai kwaliya, tana son tayi booking na bikin Nabila.Ta kammala ta juyo, ta ga Liti a tsaye.”Sannu dai”Ta ce “Yauwwa, ya gida ya shirye-shirye na ganku tare da wanda Arfa zata aura, ina kyautata zaton abokansa ne”Ya girgiza mata kai ya ce “‘yan uwansa ne mu”Tayi murmushi ta ce “Masha Allah, Ubangiji Allah ya sa zamu gani””Amin, ashe tana da ƙanwa babba kamar ke, ai mu ita kawai muka sani””Ai muna da yawa ma, ba a fiye ganinmu bane, daga makaranta sai gida”.Liti ya ce “Masha Allah, ai haka ake so, ki ce tare zamu yi hada-hadar biki, to Allah ya sa a gama lafiya, sunana Abdallah”Ta jinjina kai ta ce “To yaya Abdallah, sunana maryam ana ce mini Walida”Walid kuwa satar kallonsu yake yi, yadda liti ya nutsu yake baza capacity a gaban budurwa, kai ba zaka ce shi ne yake wani iya shegen ba, sai gashi yana ta hira da shi da walida, abin da haryanzu Walid ba ya iya sakin jiki yayi sosai da Shahida.Duk da Nabila ba ta saki jiki gaba ɗaya da Viper ba, amma ta ɗan ji sauƙin damuwar da take ciki, amma har a lokacin faragaba ba ta bar zuciyarta ba.Sai da ta kwana biyu aka sallameta, ta ɗauki hutu a wurin aiki, ta ma daina fita gaba ɗaya, sosai Nabila ta zama so silent, dan ma Sumayya na tare da ita, tana ƙarfafa mata gwiwa.Abbu suna ta shirye-shirye, suna zaune da shi da Viper da daddare, Shahida ma an gama gyara gidan da zata zauna, Abbu ya yi mata sababbin furnitures. A weekend za a kawo kayan lefe.Viper ya dubi Abbu, yadda yake ta kashe kuɗi babu ƙaƙƙautawa, dan haka yake cewa auren yara uku zai yi.Ga Viper, ga Walid ga kuma Shahida.”Abbu muna ta godiya Allah ya saka da alkhairi”Abbu ya ce “Da aka yi me?””Kuɗin da ka ke ta kashewa a kanmu””Amfanin neman kenan ai Al’amin, kuma a baya ai ban yi muku ba, Allah dai ya sanya alkhairi”Viper ya amsa da Amin, sannan ya ce “Abbu wata alfarma nake son sake nema a wurinka dan Allah”Abbu har so yake Viper ya nuna yana son yayi masa wani abu, hakan na sanya mishi nustuwa, ya ji cewa lallai ya yafe masa.”Ka ga ramma yar uwata ce, kusan ita da mahaifiyarta sukaɗai suka rage a ɓangaren mahaifiyata, da nake kallo ina jin daɗi. To naga ba tsufa tayi ba, kuma zamanta haka is not safe, na ce dan Allah idan da dama, ban takura maka ba, dan Allah ka aureta.Hakan zai fi sama mata nutsuwa, tun da shi aure garkuwa ne ga mace, duk tsufanta kuwa.Abbu ya shafi gemunsa yayi murmushi ya ce “Yanzu dai ka bari na fara kawar da ku tukuna, ayi wannan maganar””Eh ai dama ba yanzu ba, na san da hidindimu a gabanka, idan Allah ya sa komai ya daidaita nake nufi””To ɗan gidan Abbu, Allah ya tabbatar mana da alkhairi”Al’amin ya ce “Na gode sosai da sosai, Allah ya ƙara arziki”Saura sati ɗaya biki, Viper ya aiko su Walid wurin Nabila, suka yi sa’a Walida ta dawo daga aike.Suka gaisa da su Walid, Liti ya ce “Walida, wurin sisternki muka zo an aiko mu, ko zaki yi magana da ita””Me zai hana” mintuna goma, sai ga Nabila ta fito, amma yanayin da suka ga Nabila, duk sai jikinsu ya sake yin sanyi, babu wannan karsashin nata, jikinta duk a sanyaye.Haka suka gaisa sama-sama, suka ce Viper ne ya aiko su da kaya su kawo mata.Ruwa da lemo ne carton hamsin, ga buhun fulawa har da kuɗi, wai ta ƙara a abin da za ta yi hidimar biki da shi.Tun da yaje dubata a asibiti, bai sake nemanta ba, ita ma kuma ba ta neme shi ba, ta so kiransa a waya, amma ta fasa ta jira Abba ya dawo ta nuna masa.Faɗa ya hau yi, a kan yadda yake ta ɗawainiya da ɗorawa kansa nauyi, ya kira Abbu yana mita Abbu ya ce “Haba ranka ya daɗe, ni ban ma san an yi ba, kuma abu ne da yakamata ya yi, dan haka ai babu laifi, amma ayi haƙuri idan mun yi laifi”Major ya ce “Ai an riga an zama ɗaya, a din ga sauƙaƙawa juna, wallahi mun tanadi komai na shirin bikin nan, bayan uban kuɗi da ya din ga turo mata na haɗa kayan lefe”Abbu ya ce “Kar ka damu fa, auren fari sadaka aka bashi ai, sisinsa ba ta yi ciwon kai ba, wannan kuwa ya daki jikinsa yayi, sai ya fi riƙewa da kyau”Major ya ce “Aishikenan, Ubangiji Allah ya sanya musu albarka baki ɗaya”Saura sati biyu biki, Abbu ya kai Major da Baba gidan Nabila, flat ne mai kyawun gaske, a cikin unguwar jambulon da ke Kano.Tun duniya na kwance, lokacin da baban su Viper ya fara tashen kuɗi, mahaifiyar su ta sanya ya saya wa Al’amin da Sadik gidaje, ta ce saboda maza ne, idan ya sai musu ya taimake su.A haka kuma da ɗan abin da take samu a hannunsa, da yan sana’oin ta, ta din ga sayen filaye tana ɗan ajiyewa.Aka zo ita ta rasu, Sadik ma ya rasu, dan haka Al’amin bayan gidan da yake da shi, da babu yadda ba ayi da Abbu ya sayar ba yaƙi, Rahila ma tayi ƙulafucin gidan ta gaji.Miliyoyi aka din ga ambatawa gidan ya sayar yaƙi, yanzu gashi ya yi rana, aƙalla Viper yana da gidaje huɗu, da manyan filaye biyu, dan ma ya bi gonar da yake da ita a ƙauye, ya saka an sayar tun Jauhar na raye.A auren nan Viper ba ƙaramin jin jiki yayi ba, duk da Abbu yana taimaka masa, amma kuɗaɗen hannunsa duk sun ƙare, a haka sai da aka sayar da filinsa ɗaya, saboda shi yake taimakawa Walid ma.A duk lokacin da ya tuna a yadda ya auri Jauhar, da a al’adance zai iya cewa auren sadaka, sai ya ji tausayinta, ko da wasa ba ta taɓa nuna masa, ta ji zafin irin auren da aka yi mata da shi ba.Liti duk da yana supporting ɗin Walid shi ma a kan shirin bikinsa, gefe guda yana ta karɓar kuɗi a hannun babansa, ya ƙara ƙawata wurin shayinsu aka mayar da shi joint.Kasancewar Viper ya kwana biyu bai je wurin ba, ranar da Liti ya addabe shi ya je, sai da ya zubar da ƙwalla.JAUHAR MEMORIAL JOINT. Haka aka rubuta a wurin, sannan ga kan famfo ɗaya da aka janyo, liti ya ce “Ga sadaƙatul jariya, mun yi wa ƙanwarmu da ni da Walid, alkhairin Allah ya isketa har cikin kabarinta, ƙoƙarin inganta rayuwarka da tayi, ba kai kaɗai ta yi wa ba, har da mu”.Cikin wurin duk an rubuta, dan Allah ku karanta wa marigayiyya Jauhar ƙulhuwallahu ƙafa uku, Allah ya jiƙanta da sauran musulmi baki ɗaya.Idan Viper ya ce yana da kalamai, ko wani abu da zai yi, domin nu na godiyarsa ga bayin Allan nan da suka kasance da shi, a halin tsanani da na jin daɗi, to ya yi ƙarya.Su Abba sun yaba gidan Nabila ba kaɗan ba, manyan ɗakunta uku, da falo biyu, ga komai a wadace dai-dai misali.Duk da ba a rasa ‘yan tsegumi ba, da aka je jere, da suka din ga gulmar, a iyayi irin na Nabila, da yadda ta din ga dating manyan mutane masu kuɗi, ba su yi zaton zata ƙare a wannan gidan ba, duk da shi kansa yadda ake cewa ɗan daba ne, sun zata mara galihu ne da abin yi, dan sun raina kansu da suka ga gidan da ɗan daba zai saka amarya a ciki.Nabila dai ta kama wuridin ya haiyyu ya ƙaiyyum bi rahmatika astagis, aslih lii sha’ani kullahu, wala takilni ila nafsi, ɗarfatu ainin.Domin samun mafita a kan maganar aurenta da Viper.*****Rana ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, aka fara gudanar da biki, shi kansa Viper yayi rama saboda rashin hutu. Dinner da kamu, duk amare ne suka je ba angwaye, Nabila ta yi kyau sosai, farar fatarta tayi kyau da kaya da kuma kwalliyar da aka yi mata, haka ma Shahida ta sha kyau.Sumayya ma sai kai wa da komowa take yi, tayi kyau sosai da sosai.A hada-hadar kai komon biki, liti suka ƙara sabawa da walida, har da karɓar lambarta.Walid ya ce “Zaka gane kurenka, ka gama yi wa Nabila rashin mutunci, ka zo kana bin ƙanwarta, Allah ya kawo mata lokacin ramawa””Kai dai ɗan baƙin ciki ne, saboda Allah ya kawo maka lokacin aure, duk sai ku tafi ku bar ni, to baka isa ba”.An ci an sha, an yi biki lafiya aka kammala lafiya, da yamma aka fara shirin kai amare.Nabila na ta kuka, ba kuma wai dan zata bar gidan nan ba, kawai ji take auren Vipern tsoro yake bata ba na wasa ba.Abbu ya yi wa Viper da walid nasiha sosai da sosai, haka Shahida ya gargaɗeta a kan kar ta biye wa mahaifiyarta, ta ɗorata a kan keken ɓera, ta kashe mata aure.Ranar da aka ɗaura auren su Walid, a ranar Viper ya yi walimarsa, tare da abokansa, wanda dama su Walid ne, sai kuma sojoji.Amma ba a manta baya a harkar, dan hatta tsofaffin yaransa ‘yan cau-cau, da marasa ji sai da suka halatta, sai dai a wannan karon, ba rashin hankali aka yi ba, kamar yadda na auren jauhar ya gudana ba, kowa taitayinsa ya shiga, mussaman da sojoji suka cika wurin.Nabila ta rirriƙe sumayya tana kuka, ita ta zauna da Nabila, har bayan isha’i, kowa ya watse, ta kira wands zata aura, Faruk wanda ɗan uwa ne ga Alhaji mu’azzam.Amma fafur Nabila ta hanata tafiya, sai da Viper ya shigo.Kamar yadda ya saba komai nasa daban, shikaɗai ya shiga gidan, sai da Sumayya ta tafi ya rufe gidan, ya tsaya yana ƙarewa gidan kallo, ko ina hasken fitilar solar.Ya tuna lokacin da ya je wa jauhar, butsu butsu, Walid ne ma ya takura masa, ya haɗo shi da kayan dauɗarsa ya rako shi. Ɗan guntun murmushi ya yi, ya shiga ya iske Nabila a bedroom, ta ƙunshe kanta da mayafi.Ya ce “Ki taso ki yi alwala mu yi salla” a hankali ta motsa, ta saukko daga kan gadon, idanunta duk a kumbure, rabon da ya ganta tun a asibiti, ko ta waya ba su sake magana ba.Ta je ta fara yin alwala, shi ma yayi ya fito, amma ya ga ta ja ta tsaya a gefe.Sai da ya raɓata ya tayar da sallar sannan ta bi bayansa, bayan sun idar yayi addu’a gwargwadon abin da ya iya.Ya janyo mata ledojin da ya shigo da su, ya ce “Bismillah ga abinci, me zaki ci a nan?”Ta girgiza kai ta ce “Ba komai””Saboda me?” “Na ci abinci a gida”Kawai ya ce “Ok”Da ya motsa sai ta zabura, gaba ɗaya ta takura kanta, ta hana kanta sukuni.Ya tashi ya bar mata ɗakin, sai bayan awa guda, sannan ya koma, ta kwanta a ƙasa ta lulluɓe jikinta da lafayarta, sai dai tana jin motsinsa ta sake zabura ta tashi zaune.”Ki je ki kwanta, tun da bacci ki ke ji” sai da ta ɗan yi jimm, sannan ta tashi taje ta kwanta.Ya ɗaukko sabon bargonta ya ƙara mata, tana kallonshi yana rage kayan jikinsa, zuciyarta na tsananta bugawa tana rarraba ido, yana juyowa suka haɗa ido, tayi wuf ta shige cikin bargo.Yana kashe fitila, ta tashi zaune, yana kallonta, ya zo ya samu wuri a farkon gadon ya kwanta, amma taƙi kwanciya.A ransa ya jinjina hali irin na Nabila, ya san dai ba ta isa hana shi abin da yayi niyya ba, amma tabbas zai sha fama da taurin kai. A yanayi irin na Nabila, da ta rayu cikin ƙabilu, har ta bar Nigeria ta je tayi karatu, da yadda take gudanar da rayuwarta, sai ka zata a waye take, koma mutum yayi mata kallon mutuniyar banza, amma zunzurutun tsoro da tashin hankalin da yake tattare da ita, ko taɓata yayi sai ta kusa tara masa jama’a, abin da ba ta sani ba shi ne, zai iya shanye koma me yake ji ya rabu da ita. Kamar dai a zamansa da jauhar, da sai da ya fara gani a idonta, duk da shi akwai sabo sosai da sosai a tsakanin sa da ita.Ta sauran hasken da yake shigo ɗakin yake kallon yadda take gyangyaɗi a zaune, har ta gaji ta tuntsura, amma da ya juya sai ta tashi.Gidan ango Walid kuwa, halin ya ci gaba da gwadawa, shi ba tsoro ba, shi ba matsananciyar kunya ba.Bayan sun yi salla sun idar, ya gabatar mata da kaza da ɗan abin da ya sauwwaƙa.Ba ta ci sosai ba, su ka ɓuge da hirar yadda biki ya gudana.Ganin ta ɗauki kayanta ta shiga toilet, ya sanya ya bata wuri, yana sake ƙare wa gidan kallo, cike da nishaɗi.Da ya koma ta canza kaya, zuwa doguwar riga, ta bacci, da hijjabi.Sai wani raɓe-raɓe yake, kamar mai shirin aikata zunubi.Bacci ne yake shirn ɗibarta, saboda a gajiye take.Kwanciya Walid ya yi a bayanta, da kayansa na angwancin da komai, duk da yadda rigar ta dame shi, sai da ya ji uwar bari ya cireta. Ƙamshin turaren da take yi ne, yake ta ci gaba da fizagarsa, sai godewa Allah yake yi, wai yau shi ne yayi aure.A hankali ya kai hannunsa kan na Shahida, kamar mai taɓa wuta, ta buɗe idanunta, taga ɗakin ya gauraye da duhu.Ta ɗan motsa kaɗan tana ƙara jinjina tsagwaron kunya irin ta Walid.”Shahida””Na’am””Dan Allah ki na so na, ko kin aureni saboda kawai Viper ne ya baki umarnin hakan?”Sautin murmushinta ya ji, ta ce “Ba na ce ka daina faɗar sunana ba, idan ka faɗa sai na ji kamar ba ka so na, saboda yaya Aminu kawai ka aure ni”Da sauri ya ce “A’a ina sonki sosai, waye zai ce ba ya son mace kamar ki?””Kai manaz tun da kana faɗar sunana”Ya ce “Na daina, sweetheart ki ka ce na ce ko?” Sosai take yi masa dariya, ta ce “Au ni na ce ma, ba kai ka yi niyyar kirana haka ba”Walid ya ce “Daga cikin zuciyata ya fito, ki yi haƙuri wallahi duk ban iya irin wannan bane ba”Shahida ta ce “Yaya ya gaya mini ai, ku mazaje ne, ba ku iya soyayya ba, amma ni gaskiya ka koya” tayi maganar a shagwaɓe.”In sha Allah, zan sayo littafi ki din ga karanta mini kullum ina haddacewa” tayi murmushi tana jin yadda yake ta wasa da yatsun hannunta.”Shahida ban taɓa tunanin rayuwa zata canza, har na yi iyali ba, babu abin da zan ce wa Allah sai godiya, kuma babu abin da zan cewa Viper, sai Allah ya sa ya gama da duniya lafiya, bani da bakin da zan yi masa godiya, ya mayar da ni cikakken mutum””Ramawa kura aniyarta aka yi, ku kuka fara riƙarsa a yadda yake, ku ka mayar da shi mutum, Allah ya ƙara haɗa kanku””Amin sweetheart” dariya ta yi masa jin ya ce sweetheart.Walid ya gama noƙe-noƙen da jin kunyar, ya raya darensa.Sai dai ya shiga lissafi, duk da shi dai bai san dawan garin ba, amma kamar akwai banbanci tsakanin budurwa da kuma bazawara, amma bai mayar da hankali a kan tunanin hakan ba, saboda kukan da Shahida take yi, ya din ga bata haƙuri kamar wadda ya tafkawa laifi, har sai da ya bata tausayi.Washegari da safe ma, ita tana jin nauyinsa, shi ma sai sinne kai yake yi, lokaci lokaci yana sakin murmushi.Liti kuwa da kyar yayi bacci, saboda babu Walid babu Viper, yayi ta mita, wai suna can tare da bargo mai numfashi da sabuwar katifa, shi yana nan ya kasa bacci.Da sassafe Liti ya kira Walid a waya, Walid bai watstsake daga bacci ba ya ɗaga ya ce “Lafiya?””Au haka ma zaka ce? Koma kira ni ka ji yaya nake?”Walid ya ce “Haifarka na yi da zan kiraka da sassafe na ji yaya ka ke?””Allah sarki ni, wato kai yanzu ka yi ‘yanci, yayi kyau, na ce ba, ka rage mini kazar ko kuma yaya?””Eh, ta na wurin mai zamani ka kira shi ka karɓa”Liti ya ce “Ai da shi muka fara yin waya, Abuja fa zai tafi yau”Da sauri Walid ya tashi zaune ya ce “Haba dai?””Wallahi haka ya ce mini, cikin dare aka tura masa saƙo, gashi har aka gama bikinsa ɗan mama baya nan””Amma shi aikin nasu babu hutu kenan? Mutum yayi aure amma ace ya fito washegari””Kai ma dai ka faɗa””Bari na kira shi” sun yi sallama da liti, amma ya kasa kiran Viper, saboda kunya, shi tunani ma yake idan ya koma kasuwa ko zai iya kallon Abbu.Gidan Ango Al’amin kuwa, bayan sallar asuba Nabila ta koma bacci, ganin Viper bai dawo ba.Ƙarfe tara ta tashi, still baya ɗakin, ta kulle bedroom ɗin, ta shiga banɗaki ta yi wanka, ta duba jakarta ta ɗauki brush ta wanke bakinta.Ta canza kaya ta fita falo, tana kallon gidan.Kitchen ta leƙa, ta tarar har ya dafa tea, tana tsaye ta ji ya buɗe ƙofar falo, falon ta dawo a dai-dai lokacin da ya shigo.Ta ɗan maze ta ce masa “Ina kwana?””Ban ganshi ba” ya amsa mata, tare da wucewa digning, ya ajiye ledar hannunsa, ya dawo in da ya barta ya ce “Ga abin breakfast can, kazarki kuma da baki ci ba, tana kitchen.Ni an turo mini saƙo tun cikin dare, ƙarfe sha biyu zan bi jirgi na koma Abuja.Ba ta san lokacin da ta ce “Saboda me?” ba.”Harkar aiki””A kawo ni juya yau kuma ka tafi, yaushe zaka dawo?””Ina ruwanki da lokacin da zan dawo? Dama ai ba ƙaunar ganina ki ke yi ba, tun da an aura miki annoba, idan na matsa sai ki sarara”Cikin kuka Nabila ta ce “Ai dama na sani, a haka ka ke cewa na baka chance ɗin, ko na baka chance ɗin, na san babu wani da zai canza, ba na gabanka, ba ni da wani muhimmanci a tare da kai, am regretting this marriage”Shareta ya yi ya wuce cikin ɗaki, ita da ta nuna ba ya gabanta, ko menene na ɗaga hankalinta kuma, dan kira shi wurin aiki oho mata.Duk da a zahiri shi ma bai so hakan ba, amma dolensa ya tafi muddin yana son yin galaba a kan Indabo, ta wani fannin kuma, yadda Nabilan ke treating ɗin sa, gara ya tafi kawai ya rabu da ita.Da fari kuka ta zauna tana yi, daga baya ta ga kamar ta faɗo ne, sai ma ya rainata, shi bai damu da ita ba, ita kuma ta damu da tafiyar sa.Ta haɗa abin kari tana karyawa, kamar ta na cin magani, ya sake fitowa ya fita, aka jima sai gashi da kayan abinci niƙi-niƙi.Ƙarfe sha ɗaya ya sameta a ɗaki, ta ɓuya tana matsar hawaye.Kamar bai gani ba, ya ajiye mata kuɗi ya ce “Na san maybe zaki yi baƙi, ga kuɗi nan, idan kina buƙatar wani abu, na san kirana a waya abu ne mai wahala, zaki iya kiran wanda ki ka ga ya dace kin yarda da shi, ya kirani ya sanar mini” har ya bar ɗakin ba ta ce masa uffan ba.Ya saɓa jakarsa ya fita, zuciyarsa na yi masa zafi, yanzu yana ƙoƙarin gazgata Nabila ba ta ƙaunarsa.Tafiyarsa babu jimawa kuwa baƙi suka din ga zuwa, dan haka sai damuwar ta ta ta ragu, sai dai ana watsewa komai ya dawo mata.Walid kuwa hankali kwance ya ci gaba da shan sharafinsa da amarya Shahida.Ranar da zai koma kasuwa, ta sha dariya har da riƙe ciki, wai kunya yake ji ya fita kasuwa ya haɗu da Abbu ma.Da kyar ya samu ya fita, Allah ya sa ranar Abbu bai je kasuwa ba, sai dai duk bayan mintuna kaɗan, yana maƙale da waya yana kiran Shahida, sai da ya ji kamar ya janyo yanna ta yi ya koma gida.Sai da liti ya gaji ya fara zage-zage da faɗar maganganu, Walid kuwa yayi masa banza, sai daga ƙarshe ya ce “Zafin gwaurantaka ke damunka, ba zan kula ka ba”Sannu a hankali baƙi suka fara ɗauke ƙafarsu daga zuwa gidan Nabila, hakan ya fara damunta, ga Viper tun da ya tafi babu ko flashing, hakan ya ƙara ƙona mata rai, ita kuma ta kira shi, gani take ta faɗo.Sumayya dai ta ci gaba da rarrashin Nabila, kusan duk kwana biyu sai ta zo wa Nabila, dan ta gaya mata Viper ya gari. Ita ma a hankali ta rage zuwa, an doshi sati uku, babu Viper babu labarin sa, ko baccin kirki ba ta yi sai aikin kuka, idan ta gaji kuma sai ta yi ta tasbihi, saboda yana daga abin da yake sauke mata fushi da wuri.Babu tsammani ta ji ana buga mata gate, ta tashi ta fita tana tambayar waye?.”Buɗe ki gani” tana buɗewa ta ga Walid da Shahida, murmushi tayi tana yi musu maraba.Sun yi ƙalau da su, daga shi har ita, Walid ya kuma nutsuwa, kuma cikin manyan kaya yake, yanayin yadda suke magana akwai fahimtar juna a tsakaninsu.Ita kuwa an zubar da ita a cikin gida, ya tafi aikinsa ko ta kanta baya waiwaya.Walid ya ce “Bari na tafi kasuwa, da yamma na dawo mu tafi, dama Viper ne ya ce wai lallai in kawo miki ita, ta tayaki hira, kaɗaici ya dame ki, na ce masa to ya dawo mana”Nan dai ya bar mata Shahida, shi kuma ya tafi.Shahida ta ce “Anty Nabila, maman dr. Duniya ce, ai ni mun ƙulla alaƙa da ita, ai yanzu na san nayi aure, wannan auren mai kuɗin duk ba shi ne ba”Nabila ta yi murmushi ta ce “Au da ba aure ki ka yi ba?””Taɓ, aka gama yi mini banke-banken magani, da shi da babu duk ɗaya, magani ya kusa illata ni, sai da na kwanta a asibiti, kuma na kasa faɗar abin da ya faru. Ga yan uwansa masifaffu, wai yana ta aure mata ba haihuwa, shi bai gaya musu shi ne mara amfani ba. Na sha wahalar auren nan, shekara uku sai da na ci na yi kallo, na zauna babu banbanci da ina gida, kuma kowa gani yake nayi aure a gidan hutu. Na cire kunya na gaya wa mama, wai sai cewa tayi, Allah ya rufa mini asiri zan tona wa kaina, nayi nayi ya sake ni yaƙi, ni kuwa na kaishi kotu, na ga zai saye su da kuɗi, na samu Abbu na gaya masa, aikuwa yayi ta faɗa”Nabila ta waro ido ta ce “Abbun ki ka gaya wa wannan maganar?””Eh mana Anty Nabila, da ace masa gani can da aurena ina ɓarna fa? Idan cin abinci da kallo na je yi, in zauna a gidanmu mana”Nabila ta ce “Gaskiya tun da na ji Hafsa ta yaba, kema kin yaba, na ƙara yadda da kayan maman dr””Sosai fa, zata baka abin da ya dace da kai, da aka yi mini auren fari, ai wata jahila aka samu ta din ga jibga mini kayan shashanci suka kusa kashe ni, ai maman dr tayi a rayuwa. Ni gidan Yaya muhsin duk da bashi da ƙarfi, ya fiye mini gidan tsohon mijina sau dubu, ga ci ga sha ga kwanciyar hankali, gashi lafiyayye, ban yi gyara a banza ba”Waro ido Nabila ta yi ta ce “Kin fi ƙarfina Shahida””Hmm ba zaki gane ba, matan da suka tsinci kansu a irin halin da na taɓa tsintar kaina, sun san takaicin abin nan. Kana gidanku baka san komai ba dama, ya fi sauƙi hankalinka a kwance yake, amma an aurar da kai, mutum ya san ba shi da lafiya, saboda zunzurutun zalunci, ya aureka, kuma yan uwansa su addabeka, baka haihuwa, wallahi na kusa gaya wa babarsa ranar da aka ishe ni, kawai nayi shiru”(‘yan uwa kar ku bari a baku labari, ko kuma a bar ku a baya, ku garzaya ku jarraba, kayanta, ga kyau ga kuma inganci 0706 971 1327)Nabila ta ce “To Allah ya kyauta, Allah ya ƙara muku zaman lafiya da fahimtar juna, tun da kin samu abin da ki ke so”Dariya tayi, ta ce “Amin, ina nan ina ta kwantar da kai ina lallaɓa abina, ko ƙuda bana son ya taɓa mini shi, ina matuƙar son sa da tausayinsa”Nabila ta ce “Yakamata, ai Walid mutum ne na gari”Sun sha hira sosai da sosai, dan sam Nabila ba ta bari, Shahida ta fuskanci damuwa a tattare da ita ba.Bayan tafiyar su, da daddare ta rasa abin yi, ta buɗe wardrobe ɗin Viper, ta sauke kayan tana gyarawa.Wani ƙaramin littafi ta gani, ta ɗauka ta fara dubawa.”Wannan littafin na master ne, kar ka manta ka karanta shi safe da yamma”Azkar ne aka rubuta shi, na safe da yamma da hausa, sai kuma Addo’in kwanciya bacci. “Ka kula mini da kanka sosai master, duk lokacin da ka karanta, ka yi mini addu’a”Ƙasa sai ta zana heart da sunansa, irin da na soyayyar ƙuruciyar nan.Shafa littafin Nabila ta din ga yi tana kuka, ta ce “Allah ya sa auren mijinki, kar ya zame mini cin amanarki ‘yar uwata, Allah ya sa ba ƙaddarar auren nan ne ya sanya ki ka bar duniyar nan ba, ina ƙaunarki duk da ban sanki ba”Sosai Nabila ta yi kuka, mai ban tausayi, daga bisani ta tashi jiki a sanyaye.Kamar wadda aka yi wa nasiha, washegari, ta tashi da matsananciyar kewar Viper, babu tunanin komai, ta ɗauki waya, ta din ga kiransa, amma wayarsa a kashe.Kawai sai hankalinta yayi matuƙar tashi.Madam halima ce ta kira Nabila, suka gaisa ta ce “Nabila, gobe Joseph zai zo da safe, zaku tafi Abuja, Viper babu lafiya”Ƙirjin Nabila ya buga da ƙarfin gaske, ta ce “Meya same shi?””Ban sani ba, Joseph ne ya zo yake gaya mini, dan haka ki zama cikin shiri” kuka ta saka wa madam, tana tambayar ta, idan wani abun ne ya same shi ta gaya mata, amma ta ce mata ba ta sani ba.Ana idar da sallar asuba ta shirya, cikin matsanancin tashin hankali, addu’a kawai take yi Allah ya sa yana lafiya.Ta waya suka din ga communicating da Joseph, ya zo gidan, ya ɗauki Nabila suka tafi, sai da ta tambaye shi ko ya san wani abu a kai, amma ya ce mata bai sani ba.Sumayya ce ta kira Nabila, ta ce mata maza ta hau social media ta duba meke faruwa.Hannunta na rawa ta buɗe tana duddubawa, wai tsohon riƙaƙƙen ɗan daba Aminu Viper, ya koma ɗan ta’adda, bayan da yayi attacking ɗin manyan mutane ciki har da honorable Indabo, da bindiga a wani guset house da yake Abuja.”Impossible, this is not true, Vi ba zai yi haka ba, dole akwai wani abu a ƙasa”Sai daf da azahar suka isa barrack ɗin da yake aiki a Abuja.Nabila sama-sama take numfashi, a ganinta gawarsa kawai za su nuna mata.Wani ɗaki aka shigar da ita, yana kwance a kan gado, ana ƙara masa jini, da gudu ta ƙarasa gaban gadon da yake, bakinta na rawa tana faɗin Innalillahi wa Innalillahi raji’un.An nannaɗe kafaɗarsa da bandeji, ga cikinsa gefe a kumbure. Alamu ya nuna harbinsa aka yi a kafaɗarsa.”Vi, ka tashi dan Allah ka tashi””Madam ki yi haƙuri, bai daɗe da samun bacci ba”Ko ta kan mai maganar ba ta bi ba, ta ci gaba da kuka.A hankali ya buɗe idonsa, ya ɗago ya kalleta.”Vi, meyafaru haka, garin yaya aka harbeka, da gaske zuwa ka yi ka kashe indabo, meyasa zaka yi attacking ɗin sa haka?”Lafiyayyen hannun ya ɗago, ya shafi fuskarta, ya ce “Aiki mu ka je, ban yi attacking ɗin kowa ba. Mun yi negociating da wasu hukumomin na tsaro ne, aka je gidan, amma an ce na yi laifi, zan iya fuskantar hukunci, na yi harbi ba a bani umarnin hakan ba, duk da yaransa sun yi yinƙurin kashe ni.An kama Naja’atu Bunkure a gidan, da ƙanan yara mata da ake lalatawa da kuma maza, gidan da aka yi sanadiyar ran Nura ne, kuma mun kama makamai a gidan, da wasu manyan ƙusoshin gwamnati duk a gidan. Hukumar soja ba sa zargina sa ta’addanci, wannan sharrin media ne, da nake kyautata zaton mutanen Indabo ne suka saka ayi mini hakan, hukuncin da zan fuskanta na harbi ne ba ayi mini uzuri ba, ina da abubuwa da yawa da tun a baya na so mu tattauna, amma baki bani chance ba, baki bani da ma ba Abla, akwai abubuwan da nake buƙatar aiki da ƙwaƙwalwarki, saboda ta kan yi mini jagora a wasu abubuwan, amma ki ka ƙi saukko ki fahimce ni”Ƙanƙame shi ta yi tana kuka ta ce “Am sorry Vi, ka yi haƙuri dan Allah, amma zan ɗauki kowane irin mataki, wallahi babu mai hukunta mini kai, wahalar da ka sha ma ta isa haka, wace irin ƙasa ce wannan? In dai ina raye babu wanda zai yi maka wani hukunci babu shu”Ya saka hannu yana shafa kanta ya ce “Dan Allah ki zauna tare da ni abla, zamanki a kusa da ni, yana bani ƙwarin gwiwa ina jin am safe idan muna tare, tun ba yanzu ba Please” ya ƙarasa maganar muryarsa na rawa.*GA MASU JIRAN DOCUMENT, ZA SU IYA PAYMENT YANZU, FEW PAGES YA RAGE, ONGOING PAGES NE 500 COMPLETE DOCUMENT KUMA 1K. VIA 0009450228AISHA ADAM JAIZ BANKSAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143Ayshercool08081012143



