Fentin Zina Page 33 Hausa Novel
****Kanta a duke har baba malam ya gama mata nasihar shi kamin ya sallameta bayan ya sanar da ita gobe zasu je da fateema su kwaso kayanta zai nemi mota.Godiya tayi ta tashi ta shige daki.Washe gari kamar yadda baba malam ya fada din kuwa sunje gidan suka kwaso kayan domin baba ba karamin na mijin kokari yayi ba shida mijin mama rabi wurin yi mata kayan daki harta da kujerun falon nata ne.Basu bar Koda tsinke ba idan na Ameena ne duka suka tattara har kujerun cikin sa’a har suka gama Abdul bai shigo ba sai maryam ce ta fara jefa musu magana sukayi mata banza data ga hakan sai taja kafafunta ta koma daki tana mai cike da farin ciki.A extra room din gidan baba malam suka shigar da kayan suka rufe kofar.Da dare da Abdul ya koma gida sai yaga kamar ba gidan shi ya shiga ba sakamakon ganin fakon da yayi a hargitse babu kujeru an cire su sannan ba’a share gurin ba ya shiga kwalawa maryam kira, ba jimawa sai gata ta fito cikin wasu kananun kaya riga iya cibi da bomshort ba laifi kayan sun dan karbeta. Yatsina fuska tayi tace baby lafiya kuwa wannan kira haka?.Harara ya doka mata yace meya samu falona haka ina kayan ciki suke?.Sosa kai tayi tana kara yamutsa fuska tace ai na zaci ka sani!. Yayi saurin katseta da fadin na san meye?.Tace dazun matar ka tazo da kanwar ta suka kwashe kayan daga na dakinta harna kitchen dinta dana falon duka kamar yadda ka gani kimai bat bari ba.Gaban shine yaji yayi wani irin bugu shi sam ya manta cewar kayanta ne duka shiyasa ya shantake kwafa yaja ya shige dakin shi, nanma sai ya sake tarar da wani bacin ran domin duk kayan daya kasance nata sai data kwashe hatta da bedsheets bata bar ko daya ba na kan gadon ma yaye shi tayi. Bazai iya ci gaba da tsayuwa a dakin ba hakan yasa ya fito ya shiga na maryam. Ya zauna a gefen gadon yace sa mun ruwan wanka in dan watsa.Cikin rashin damuwa tace na manta ban dora maka ruwa ba. Da mamaki yadubeta yace waterheater din meye amfaninsa?.Tace au ka manta shekaran jiya nace maka ya lalace ai ba’a gyara ba. Wani sabon haushine ya kama shi ya daiyi kokari ya danne yace toh naji muje ki saka mana abinci don na dawo da yunwa yau sosai banci komai ba tunda na fita.Tabe baki tayi tace ai kuwa yau saidai muje restaurant domin banyi girki ba infact nifa ban wani iya girki ba ba’a koya mun ba a gidan mu bana yi.Tsabar haushi da kaduwa rasa ma abunda zaice yayi dole da kanshi ya shiga kitchen din matyam din don yasan Ameena ta kwashe nata kayan ya dafa saukakakkar indomy ya fito falo ya zauna a dinining tunda nan a tsap dinshi yake, don dai yana sonta ne da yau yaci mutumcinta sosai ya dai daure ya kirata tazo suci ba kuwa kunya ta zauna ta hau zubawa cikinta sai data koshi.Anan suka bar kwanukan koda yace ta kwashe su cewa tayi itafa baza ta iya hidimar gida ba idan yana so ya kawo mata mai aiki kawai. Shiru ya mata don idan ya biye mata za suyi batacciya.Kwanciya yayi yana so yayi bacci amma sai me? Kasawa yayi yanata juyi a gado Ameena ce ke fadowa kwakwalwar shi dama tunanin shi yayi iyakacin kokarin ganin ya yakiceta amma abu ya faskara.Tun yana daukar abun wasa sai gashi ya zama gaske tunanin Ameena da kuma wata iriyar zazzafar soyayyarta sun mai kwaranya a zuciya da gangar jikinsa haka ko wani dare zai kwanta yana mafarkai akanta yama rasa inda zai tsoma Kansas yaji dadi, yayinda a gefen maryam kwata baya samun natsuwa sai kazantar bala’i da rashin ladabi zuwa yanzu halinta ya bayyana gare shi.*****Ameena rayuwarta take gudanarwa cikin kwanciyan hankali don har wani kiba ta kara, bata da damuwar komai akanta saina rashin kudi wanda hakan ya sanya ta fara tunanin sana’ar da zatayi daga zarar ta fita iddah duk da baba malam da inna da yaya Abubakar suna kokari amma dawainiyar ta data yaronta yau da gobe shiyasa tayi tunanin fara sana’a ko zata ragewa kanta kewa ma duka kuma itama zataji dadin ace tana taimakawa iyayen nata bawai ta zame musu lalura ba gashi ana halin babu.Fateema ce abokiyar shawarar ta don haka ita ta fara fadawa kudurinta, nan kuwa fateema ta bata shawara dama can ta iya zanin gado da jakunkuna tunda dakin dake zauren gidansu tarkace ne a ciki ta gyara ta fitar da kofa ta waje ta mayar da gurin shago tasan baba malam bazai ki ba. Ameena taji dadin shawarar kuwa nan take bata bari ta kwana ba ta samu baba malam da zancen ya kuwa bata goyon baya sosai inda yace zai siyar da ragunanshi guda biyu ya siya mata keken dinki sauran abun yayan su zai karasa zasuyi maganar zuwa lokacin da zata fita idda shagon ya zama ready sai ta fara aiki kawai.Godiya ta hauyi tana cike da jin dadi wanda hakan ya kara saka baba malam cikin farin ciki ya rasa wani irin so yake mata aduk ‘ya’yan shi, da gudu ta fita ta sanar da inna abunda suka tattauna da baba malam inna ma tace baza’a barta a baya ba itama zata taimaka gurin bata jari.Ameena baki har kunne don dadi tanayi fateema na tayata.Da dare tana kwance suna hira da fateema jefi jefi sai ta jawo wayarta dake kasan pilo ta bude data tana so taga sakonnin da aka mata.Tana budewa wani bakon numberne ta gani da alamun magana har guda biyar, shiga kan number din tayi sakon farko sallamane na biyu gaisuwa ta cigaba da karantawa sai data kai kan na biyar din ta mike zaune da sauri tace wa fateema karanta wannan rubutun. Ta fada tana mikawa fateema wayar.Karba fateema tayi ta fara karantawa kamar haka.”Ban Tana tsintar kaina cikin nadama ba sai da nayi kuskuren korarki daga gidana, nabi duk wasu hanyoyi da zasu sa na samu magana dake amma kin toshe, Ameena ki sani ina miki sonda bazan iya rabuwa dake ba wallahi tsautsayine yasa na furta miki kalmar saki amma ina mai neman afuwar ki kiyi hakuri ki dawo dakin ki na maida auren mu, kada ki watsa mun kasa a ido nasan kina sona kuma kema bazaki iya rayuwa da wani na mijin ba idan ba niba muyi kawunan mu adalci, wallahi Ameena gidan babu dadi zuciyata kamar ana hura mata wuta ki taimake ni ki dawo gareni, ina jiran amsarki daga naki ABDULMALEEK”.Dariya sosai fateema tayi tace shashasha iska na wahal da mai kayan kara da yasan da cewar yana son naki ya iya sakin ki? Yana nan kuwa a gaban idon shi Allah zai kawo miki wanda yafi shi.Murmushi kawai Ameena tayi tace kanshi ake ji yo ni ko da akwai sauran zama a tsakani ma bazan koma masa ba bare kuma babu yama raina hankali da wayo na ne. Ta fadi haka lokacin data juya baya ta gyara kwanciyarta tace na kwanta sai da safe, ta rungume shureim dake baccin shi cikin natsuwa.*****Abdul ya Kada samun sukuni duk ya kira numberta sai ace masa baya tafiya WhatsApp ma tayi blocking dinshi haka zalika Facebook ya rasa yadda zaiyi don shi yama manta saki uku ne a tsakaninsu duk tsammanin shi saki daya ne shiyasa duk yabi ya susuce ya siyi sabon sim shine ya mata message dashi ata WhatsApp har yake cewa wai ya maida ita, duk wannan zaucewar da yake kokarin yi maryam na sane dashi iya abunda ta sani kawai shine babu aure tsakaninshi da Ameena shiyasa ta kyale shi yayi ya gaji.Yana cikin kwanciyar shi ta turo kofar ta shigo ta tsaya iya bakin kofa tace baby yau anan zamu kwana kenan? Shiru ya mata ganin haka yasa ta tako ta hauro saman gadon ta kwanta ta zagaya hannunta ta daura a kirjinshi ta hau masa wasa.Duk ya game me take nufi sai ya mata banza tun tana yi a hankali har dai ta fara masa zazzafar wasa domin maganin matan data sha ya cita sosai babu abunda take muradi face biyan bukatar ta.Maryam ta lura da rainin hankalin shi wato ma yana saurarenta zai mata banza amma idan tashi bukatar ce dole sai yayi shiyasa ta zage ta fara neman yadda zata biya bukatar ta dashi yana ce mata ke kyale ni dan Allah bana cikin yanayin da zaki takura ni. Dago idanunta tayi da suka kara kankancewa tsabar jaraba tace ni yanzu nike so. Yace fyade zaki mun ne wai ina ce ki bari kina ci gaba?. Ya fada da dan karfi. Itama daga muryar tayi tace toh kai meyasa baka da tausayi ne? Kuma wallahi ka tsaya tunda hakkina ne idan kaki kuma wallahi ban yafe ba. Ta fada tana ci gaba da abunda take yi.Shi kuwa yasan gaskiya ta fada hakkinta ne amma bazata gane halin da zuciyarsa take ciki ba da ta tausaya ta rabu da shi, sai yayi shiru ya kyale ta ya gaji amma babu halin tashi don ta bada karfinta gare shi kuma bata abu na hankali, tun yana sanin duniyar da yake ciki har ya daina fahimtar komai ya tafi duniyar sumammu.Ita kuwa maryam saida ta gaji don kanta ta kyale shi, sai a sannan ta lura da ya suma, dariyace ta subuce mata tayi harda rike ciki tace rago kawai daga dan wannan sai ka suma lallai da sauran ka dole ma ka nemi magani don bazan iya rayuwa da ragon namiji ba alhalin da kuruciya da lafiyata. Tana gama fadinhaka ta fada toilet ta debo ruwa a buta ta kawo ta sheka masa ba tare da la’akari da yawansa ba. Farkawa yayi yana cewa maryam don girman Allah ki barni haka na gaji ruwan kaina ya kare. Dariya ta fashe dashi tace dube ka dan Allah na miji har na miji amma panko, ka bani kunya Abdul kuma bari kaji ni bazan iya zama da rago ba idan zaka nemi magani ka zama mai karfi a gidan ka toh, amma ya zama dole ka biya bukatata koda kuwa kullum zakayi suma biyu ne ban damu ba. Ta fada tana watsa hannaye.Wani irin takaici yaji har cikin zuciyar shi wanda ya saka hawaye tsiyayowa daga idonshi na gefen hagu ya ci gaba da kallonta yana jin inama da Ameena ce yasan ko kusa bazata tozarta shiba kuma bazata ci mutumcin shiba irin haka, bashida karfi a jikinshi sai yaja karamin tsaki kawai ya kawar da kai daga barin kallon ta.*****A kwana a tashi Ameena harta fita iddah kuma kamar yadda baba malam ya fada an bude mata shagon harma ta fara aikinta a ciki kuma alhamdulillah tana samun ciniki sosai Allah yama shagon albarka tana samun customers daga wata unguwar sosai kuma bata tsawwalawa a kayanta hakan yasa ake rububinta. Idan ka ganta cikin gida toh ta shiga sallah ne sai kuma zuwa karfe tara na dare take rufe shago ta shiga gida sam yanzu bata da lokacin batawa domin da zarar ta shiga gida wanka kawai takeyi ta kwanta.Tana zaune a shagonta ita kadai fateema ta shigo ta kofar cikin gida tace adda kinsan wani abu kuwa?. Ta fada tana zama a saman tabarmar dake shimfide a kasa.Girgiza kai Ameena tayi tace sai kin fada.Wallahi kawai ina zaune yau saiga kiran Dr. Anas nayi mamaki don an jima sosai rabon da mu gaisa, bayan mun gaisa yake tambayana ke nace ai kina shago yace bai gane ba har Abdul din ya barki fita shago, nace ba haka bane ai yanzu baku tare da Abdul kun rabu, salati ya dinga yi yace wallahi baida masaniya ko kadan don tun lokacin kafin Abdul ya kara aure ya masa nasiha akan ya dinga sassauta miki yana kyaitata miki suka yi baram baram sai watannin can ya kira shi suka gaisa daga nan basu kara magana ba har yau amma baiji dadin abunda ya faru ba wai dan Allah in baki hakuri.Ameena ta tari numfashinta da cewa wani hakuri zai bani shida baya da masaniyar komai kuma ma ai komai ya wuce ni a gurina, Abdul ya jima da zama tarihi a rayuwata zamaninsa ya jima da shudewa sam idan ba wani ne ya mun maganarsa ba bana ma tuna shi Cikin raina.Hakane adda dama babu amfani ci gaba da tuna shi din, Kuma kinsan wani abu?.Fateemaaa…. Taja sunan kamin tace kada dai in katse ki ina jinki.Tace Anas ne wai in bashi dama yana sona kuma da gaske yike wai aurena yike son yi shine nace mai zanyi shawara shiyasa na kasa jira sai kin shigo gida nazo in fada miki.Kama haba Ameena tayi tace iyyeee wato fateema an girma toh yanzu me kike so?Adda shawarar ki nike so duk yadda kika ce haka zanyi.Toh shikenan kada kiji kin damu shawara dai zan baki, Abdul da Anas abokai ne na kud da kud dinnan saidai kowa da irin halinsa, domin sunyi sabani a hali, Anas mutumin kirkine kuma bashida munafurci komai zaiyi yana yinshi straight forward sannan yana da tausayi ni dai a ganina ban hango wani aibu don yace yana son ki ba, abunda za’ayi kawai ki bashi dama mu kuma yi addu’ah Allah ya zaba miki abunda yafi zama alkhairi a rayuwar ki.Ameen Adda nagode!.Kada ki damu. Ta fada tana mikewa ta dauko wani yadin jakar data yanka tace barin dinka wannan, kema ya kamata ki fara zuwa muna aikinnan tare ko don gaba.Sosa kai fateema tayi tace ni kam kinsan son bacci ne dani ba lallai in iya ba.Kina wasa yarinya gara ki natsu ki kama kanki wata rana gidan wani zaki je wannan kiwyar bazata amfanar dake da komai ba.Zan daina ai insha Allah.Da dai yafi miki.–A hankali rayuwa ke tafiya Ameena ta maida hankalinta kacokam kan sana’arta zuwa yanzu ta shigar da shureim makaranta, kuma ba laifi yaron yana da ganewa sosai.Anas da fateema sun fahimci juna sosai har iyaye sun shiga maganar an tsaida biki wata biyu masu zuwa. Shirye shirye sosai akeyi a gidan inda Ameena ta dauki nauyin yi mata su zanin gado da labule dasu kayan kitchen………….EESHERT ADAMU


