Fentin Zina Page 10 Hausa Novel
Da fatan zamu kasance tare insha Allah, An gama free pages gashi bakuyi mun karar siyan littafina ba anya kuna sona kuwa?🤔 ku hanzarta ku biya kada ayi tafiyar babu ku a ciki.*****Da karfi Abdul ya banko kofar dakin Ameena ya shiga ya tarar bata ciki hakan ya tabbatar mai da tana kitchen a irin wannan lokacin, baiyi kasa a gwiwa ba ya bita can ya samu tana aikinta da natsuwa, cikin kaushin murya ya kira sunanta, Ameenaaa…..Dan firgita tayi kadan ta juyo gaba dayan jikinta tana kallon shi yadda yake huci ka dauka an kashe mai wani ne.Na’am Allah ya huci zuciyarka ina dai fatan lafiya?.Yazone da niyyar ya mata fada sosai ya gaggaya mata bakaken maganganu amma saidai baisan taya ba tunda yaji saukar muryarta cikin sanyi da kuma ido cikin ido data kalleshi sai yaji duk ya rasa kalaman shi ya shiga sosa keya irin na marasa gaskiya yace dama inji me kike shirin dafa mana muyi dinner dashi.Sarai ta game karya yake domin a fusace kuma a kausashe yayi kiran sunanta koma dai meye shiya sani tace duk abunda ya sawwaka don yanzuma na fara aikin girkin.Ok ok toh babu damuwa ki girka koma meye idan ya miki.Yasa kai ya fita a kitchen din, it a kuma ta tabe baki ta cigaba da aikinta.Daya koma dakin maryam toilet ya fada ya tube ya soma wankan soso da sabulu yanayi yana tunanin maganganun Ameena data turo mishi hakika yasan gaskiya ta fada, yana wasa da sallah bai cika yinta akan lokaci ba, sannan idan ta wuce ba lallai ne yake ramawa ba shi kanshi yasan da hakan domin yanzu ma ko sallahr asuba baiyi ba (wa iyazu billah, ‘yan uwa mu sani mutuwar mu bazata kwankwasa mana kofa ba, har wani irin dadin rayuwar duniya ne zai shagaltar da mutum daga kin yin sallah, Allah ka yafe mana.)Saida ya gama wankan sabulu sannan ya tari wani ruwan yayi wankan tsarki mai hade da alwala ya fito ya kalleta tana nan a yadda ya barta girgiza kai yayi itama batayi sallah ko guda daya ba yau yace.Ki tashi kidan daure kiyi wankan nan ya kamata kiyi sallah lokaci ya tafi sosai.Daga kwancen da take tace kada dai ka cemun hudubar matar kane yayi tasiri a kanka?.Idanma hakan ne ai gaskiya ta fada mun wanda yake hakkinta kuma.Au hakama zaka ce?.Kinga bana son jayayya ki tashi kiyi wanka kiyi sallah anjima zan kaiki ki gaida mahaifiyata.Gaskiya nidai masoyi daka barni na warke tukun dukma yaushe nazo da har za’a ce na fara fita yawo.Ba zan janye maganata ba please ki daina musu dani bana so.Tana yamutsa baki ta mike ta shiga toilet ta rufo kofar, shi kuma yatada sallah a nan dakin.Zuwa magriba Ameena ta gama jera komai a dining ta shiga dakinta tayi alwala ta fito ta tada sallah ta idar kenan akayi knocking kofar ta, tashi tayi ta bude Abdul ne tsaye daga bakin kofa yace zan kai maryam gurin mama ta gaishe ta ki samu kula ki sa musu abinci in kai musu.Sunkuyar da kai tayi tana wasa da ‘yan yatsunta tace baka fada mun zaka je gidan su ba dana hada girkin nayi dasu amma yanzu abincin baya da yawa iya wanda zamu ci na dafa sannan ina ciwon kai bazan iya shiga kitchen in dafa wani ba ga dare yayi insha Allah go be zan dafa nasu sai asa direba ya kai musu.Ni nace ki zuba musu ba shawara bace umurni ne wannan kuma kafin mu dawo ki tabbatar kin dafa abunda zamu ci.Batayi musu ba Allah yaso ta daman ta debi iya wanda zai ishe ta takai dakinta, don haka yanzu kitchen ta nufa ta dauko kular da take saka musu abinci idan bukatar hakan ta taso ta juye musu shi duka ta mika mai kulan, karba yayi yana kwalla kiran maryam.Baby….Bude kofar tayi ta fito ta tako ta isa ta jingina a jikin shi tana cewa wash masoyi nagaji radadi nake ji sosai.I’m sorry ki daure baza mu dade ba.Ya juya ga Ameena yace kin daiji abunda na fada?.Ta gyada kai, maryam cikin son neman magana tace maman shureim sai mun dawo ta fada tana daga mata ‘yan yatsunta tare da kashe mata ido guda daya.Daga haka suka wuce ita kuma ta tattare gurin ta kai kitchen ta koma dakinta ta rufo kofar ta bar makullin a jiki ta zauna ta jayo kulan abincinta ta bude fridge ta dauki fanta ta soma ci tana danna waya cikin son mantar da kanta halin da take ciki.Data gama cin abincin ta shiga toilet tayi wanka lokacin isha tayi tayi brush ta daura alwala ta fito ta tada sallah data idar ta kwanta ta ci gaba da danna wayarta.******Gidansu mama suna zazzaune a falo da sauran bakin da basu tafi gida ba ana hira yayi sallama aka amsa masa ya shigo tana binshi a baya.Inda babu kowa nan ya zauna itama ta zauna a kusa da shi, ya gaishe su itama ta gaishe shi kannen ahima suka gaida su suka amsa.Don neman suna sai ya gabatar musu da abincin da suka kawo a matsayin amarya ce tayi musu da kanta, aiko sunji dadi don har kasa boyuwa murnar su tayi, yayinda mama take ji a ranta yanzu ta samu suruka.Koda isha tayi a gurin ya barta yaje sallah ya dawo kafin suka musu sallama suka baro gida a mota yake ce mata kinga yadda mamata ta karbe ki hannu bibbiyu tana farin ciki ina fatan zaki riketa tamkar mahaifiya a gurin ki? Ya fada yana kallonta.Kallon shi tayi a zuciyarta tace kaji wani rainin wayo amma a zahiri fadada murmushi tayi tace haba ai tama wuci haka sosai Allah ya bamu ikon yima iyayen mu biyayya.Ameen yace yana karya motar daidai kan gate din gidan su ya kuma cewa bayan ya danna horn, kinyi sallah dai ko?A’a akwai mutane sosai bazan iya sallah a wurin ba sai na shiga gida.Ok kawai yace yaja motar suka shiga ciki ya rufe ta ya zare makullin suka shiga gida, kan dining ya fara kallo yaga kota yi abunda ya sakata duk da yasan bata da taurin kai amma haka kawai zuciyar shi ke ingiza shi ganin sunyi hayaniya.Baiga ko cup daya saman dining dinba sai yayi tunanin bata kammala ba yasa ya nufi kitchen din ita kuma maryam dama tun shigowar su ta shige dakinta.Tura kofar kitchen din yayi yaga wayam babu alamun an daura girki hakan ba karamin fusata shi yayi ba ya fice fuuu ya tsaya a kofar dakin Ameena yana bugu kamar zai ballata yana ambaton sunanta cikin karaji.Tana kwance tana danna wayarta hankali kwance ta fara magana a hankali.Kama gaji ka bari niba baiwar gidan ku bace don kaddara ta fada mun bazan lamunci kayita cimun mutumci saboda wannan dalilin ba lokaci yayi da zan tashi tsaye in kwaci encina da kaina tunda bani na tsarawa kaina rayuwa ba kuma saida na fada maka komai game dani kafin kayi auren mu balle kace na yaudare ka, da ita amaryar taka baku gaba na amma bazan bari ku takani ba don naga ita ma tana jida rawan kai..Ameenaaaa…….Ya fada yana dukan kofar da iya karfin shi…CHARGE NA YAYI KASA KUYI HAKURI DA WANNAN.Mun kammala free pages insha Allah.EESHERT ADAMUMATAR MAJEEDADI✍️


