Ruwan Zuma Page 40 Hausa Novel
(40) “Sun dawo da yaron gida Alhaji.” “Good, very good.” Fad’in Alhajin yana tafa hannayensa. ***************** Washe gari k’arfe bakwai Haydar da Mas’ud suka shiga asibitin da aka kwantar da Abul. A bakin room d’in da yake suka karb’i makullin d’akin daga gurin Nurse suka bud’e tare da kutsa kai ciki. Shigan su d’akin suka samu yana bacci mai nauyi har bakinshi a bud’e kamar wani matacce. “Ka dubi yanda yaron nan ya dawo. It’s like kwata-kwata baya cin abinci sai kayan maye.” Fad’in Mas’ud yana mai k’arisawa kusa da gadon. “Kayan shaye-shayen is their priority, abinci shine na biyu a gurinsu. Mu duba office d’in Doctor ko result d’insa ya fito mu kar6a.” Haydar dake tsaye a bakin k’ofa ya fad’a yana mai fita daga d’akin Mas’ud yabi bayanshi. Bayan sun isa office d’in Doctor aka fad’a musu bai iso ba sai k’arfe takwas. Hakan yasa suka juyo zuwa d’akin Abul suka zauna. “Yanzu daga nan meya kamata muyi?” Haydar ya tambaya. “Zamu fad’awa Kalti da Kakarsu cewa an sameshi, idan ya samu sauk’i zuwa nan da kwana biyu ko uku sai mu kaishi Maiduguri gurin Kaala Abdi.” Mas’ud ya amsa masa. “Hakan yayi daidai. Yanzu kam hankalin Laila zai kwanta tunda tasan inda yake, sai kuma babban abun shiryawarsa wanda sai an had’a da addu’a game da sadaka. Allah ya tak’aita masa wahala yasa daga yanzu yayi hankali.” “Amin Amin.” Mas’ud ya amsa yana kallon Abul daya fara motsa idanunsa alamar zai farka. A hankali Abul ya fara bud’e idanunshi yana rufewa dalilin hasken rana daya mamaye ilahirin d’akin, yana juyar da kansa yayi ido hud’u da Mas’ud wanda hakan yasa ya mik’e zaune cikin sauri tamkar wanda ya ga abun tsoro. “Ina zaka je?” Shine tambayar da Mas’ud ya masa yana dafa kafad’unshi duka ya mayar dashi zuwa kwance. Dafe kai Abul yayi tare da runtse idanunsa yana jin bak’in ciki a ranshi dalilin tunowa da yayi da abunda ya faru jiya, wato rabashi da suka yi da freedom d’insa. (A fad’arshi kenan) “Kayi sallah kuwa?” Wannan karon Haydar ne yayi maganar shima yana duban Abul. Abul bai ce komai ba haka kuma bai yi alama da zata nuna yaji me aka tambayeshi ba. “Kai ba magana ake maka ba kayi shiru kana jin mutane?” A fusace Mas’ud ya masa maganar. “To ai kuna gani yanzu tashina.” Ya fad’i hakan cikin rashin kunya. “Wannan ba amsa bace. Aka ce kayi sallah ko baka yi ba?” Mas’ud yaja kwalar rigarsa ya zaunar dashi. “Mas’ud don Allah ka barshi, gaskiyarshi ai yanzu ya tashi a gabanmu. Daa ban tambaya ba.” Kad’a kai Mas’ud yayi kana yaci gaba da kallon Abul yace, “Ka tashi kayi sallah. Ga band’aki nan a hanyar fita daga d’akin. And don’t even think about running away, saboda na nuna hotonka a bakin gate kan cewa in har aka ganka kai d’aya a kamaka a kirani. Sannan your condition da kuma gurbataccen k’afarka bazai baka daman guduwa ba.” Abul na hararansu ya mik’e da kyar ya shiga band’akin ba tare da sun taimaka mishi ba. A nan ne Haydar ya dubi Mas’ud yace, “Ya kamata Laila ta san me ake ciki don bana son tace na 6oye mata irin wannan abun har na tsawon lokaci haka.” “Gaskiya ne. Call her.” Da haka Haydar ya tashi ya fita daga d’akin yana danna wayarsa. A gindin wata bishiya ya tsaya yana murmusawa jin Laila ta d’auki wayar tana mishi sallama. Amsawa yayi kana yace, “Ba dai bacci kika koma ba bayan tafiyata?” “Ina rama na jiya ne da ka hanani yi.” Ta bashi amsa cikin murya irinta masu bacci. “Ko in dawo ne?” Ai da sauri ta bashi amsa, “No, no yi zamanka a office. Ban ce ba.” “Ya da saurin karaya haka?” Ya tambaya yana dariya don yasan meya aikata. “Ba wani karaya, just kayi zamanka.” Ta fad’a tana dariya k’asa-k’asa. “Raguwa kawai. Amm… ki shirya nan da minti talatin zan zo in kaiki wani guri.” “Ina kenan?” Ta tambayeshi cikin d’aurewar kai. “Hey, surprise ne.” “I hate surprises. Don Allah ka fad’a mini kawai.” “A’a, zaki gani in kin zo. Call me nan da thirty minutes. Love you.” Ya kashe wayarsa yana murmushi yana hasko yanda fuskarta zata yi idan ta kyallara ido taga Abul. Daga bayanshi aka yi gyaran murya ya juya da sauri yaga Mas’ud ne tsaye yana ta6e baki alamar dariya yake son yi. “Tun d’azu kana nan?” Haydar ya tambayeshi cikin mamaki. “Eh, nazo fad’a maka wani abu ne sai naga ka fara waya, so sai na jiraka.” “Kaji duk abunda na fad’a kenan?” Ya sake tambayarshi. “Well… wasu maganganun har bana son in tuna. But keep it up.” Ya buga kafad’ar Haydar sau biyu kamar wanda yak’e encouraging d’insa kana ya juya ya tafi yana washe baki. Girgiza kai kawai Haydar yayi yana murmusawa kana yabi bayan Mas’ud yana mamakin shine ya ta6a naushinsa akan Laila, amma gashi yanzu har tsokanarshi yake a kanta. Bayan ya shiga d’akin ya samu Abul na sallah amma k’afarsa da yake d’ingisawa bata barinshi yayi zaman sallah da kyau sai a karkace ko kuma ya mik’ata gaba. “Ko a ina aka karya masa k’afar sai Allah.” Fad’in Mas’ud yana kallon Abul cike da tausayi kamar bashi bane yanzun ya yiwa Haydar tsiya ba. Haydar bai ce komai ba domin shima tausayin yaron ne a zuciyarsa ganin irin wahalar da yake sha. Sai da Abul ya idar kana ya dubesu yace, “Don girman Allah ku barni in tafi, Uncle Mas’ud ku taimakeni kar ku kaini Maiduguri.” Haydar na jin hakan ya juya ya fice daga d’akin yana cewa, “Bari in sayo mishi abinci.” Kafin ya fita yaji Mas’ud na mayar masa da martani, “Can d’in ya fi maka nan kenan?” Yana fita ya samu restaurant mafi kusa ya sayawa Abul breakfast sannan yayi hanyar gida domin d’auko Laila. Kafin ma ya isa ta kirashi ta fad’a masa ta shirya, yace ta fito waje gashi nan zuwa. A bakin gate ya sameta sanye da hijabi mai hannu, tana d’auke da jakanta da wayarta a hannu tana dannawa. Yana parking ta isa gaban motar ta shiga gaba tana aika mishi da murmushi ganin yanda ya shagala da kallonta. “Baki san yanda hijabi yake miki kyau ba ko?” Ya tambayeta yana rankwafowa kusa da ita. “Laffaya fa?” Ta tambayeshi tana kallon kwayar idanunshi cikin son kasancewa dashi. “Shima yana miki kyau but ni kad’ai ya kamata in ganki a cikinsa saboda nan…” Ya ta6a cinyarta. “A mota muke fa.” Ta fad’i hakan tana d’age hannunsa tana mishi harara. “Damuwar mai gulma.” Ya fad’i hakan yana yiwa motar giya suka fara tafiya. “Baka fad’a mini ina zamu je ba.” “Surprise ne.” “Shikenan mu je.” Suna shiga cikin asibitin Laila ta kalli Haydar fuskarta babu wasa tace, “Waye ba lafiya? Me yake faruwa Haydar? Idan wani ne bashi da lafiya ka fad’a mini I’m not some fragile Baby doll da zan fashe don naji wani nawa bashi da lafiya.” “Kowa lafiyarsa kalau, da kuma wani bashi da lafiya da an kiraki a waya. Zaku gaisa da wani ne.” Ya fad’i hakan yana parking tare da kashe motar. “Shine surprise d’in?” Ta tambayeshi tana fitowa daga motar. “Not yet.” Ya d’auki abincin daya saya ya kamo hannunta suka shiga asibitin. A bakin d’akin Abul suka tsaya ya kwankwasa tare da murd’a k’ofar ya shiga Laila ma tabi bayansa da sallama d’auke a bakinta. Sai dai mutumin data hango zaune a kan gado shiyasa ta tsaya cakk tare da rufe bakinta dalilin kukan daya so kwace mata. A hankali ta taka ta isa bakin gadon bayan Mas’ud ya bata guri ta tsaya kan Abul tana tsiyayar hawaye. Shima ita d’in ya zubawa ido idanunsa cike da hawaye amma ya k’i bari su zubo sai cije le6ensa da yake yi yana d’aga idanunsa sama. “Abul ne fa!” Shine abunda ta fara furtawa tana ta6a fuskarshi wacce wasu gurare suke manne da bandaids. Kawar da hannunta yayi daga fuskarshi yana hangen bayanta inda Haydar ya jinginu da bango yana kallon reunion d’in uwa da d’anta. “This is all because of you, kai ka fad’a musu inda nake and I hate you for that akan wanda nake maka.” Abul yayi maganar cikin k’araji tamkar ya tashi ya shak’e Haydar. Juyawa Laila tayi bayanta ta dubi Haydar tace, “A ina kuka sameshi kuma yaushe?” “A Abuja, jiya muka d’aukoshi.” Gyad’a kanta tayi tana share hawayen fuskarta ta mayar da dubanta ga Abul tana kallonshi. “Ka rame, kayi bak’i, ka kod’e sannan ga ciwoka duk a jikinka Abul. Wannan shine rayuwar daka za6arwa kanka? Me ribar wannan rayuwa in ba asara da kaico ba?” “Ribar shine bana kusa dake da Toy Boy d’inki.” Haydar dake baya yayi murmushi yana tunanin waye toy tsakaninshi da Laila bayan abunda ya faru jiya da dare. “Har yanzu bakinka bai mutu ba. Ina rok’ar maka shiriyar Allah.” Ta fad’i hakan tana murmusawa kamar ba magana mai zafi ya fad’a mata ba tana goge hawayen fuskarta cikin dakewa. “Zan wuce aiki Laila, sai na dawo.” Kafin ta bada amsa Abul yayi caraf yace, “Kiji yanda yake kiran sunanki kamar bashi yake sunkuyawa yana kiranki Hajiya idan zai gaisheki ba. Wannan kuma shine abun kaico.” Ya dallawa Haydar harara wanda sai yanzu ya lura ya k’ara haske yayi k’iba. “A dawo lafiya and thank you.” Ta gyad’a kanta alamar she mean it. “Take care.” Da murmushin da bai bar bakinsa ba Haydar ya fita tare da Mas’ud aka bar Laila ita da Abul. Abincin da Haydar ya shigo dashi ta tashi ta d’auko kana ta bud’e take away mai d’auke da Chips da kwai sai hot chocolate a cikin disposable cup, da kuma Apple guda hud’u da ruwan gora. A gefenshi ta ajiye mishi kana tace, “Bismillah.” “Bazan ci ba.” Ya bata amsa. “Okay.” Da haka ta rufe abincin ta koma ta zauna tana kallonshi tana murmushi, can k’asan zuciyarta kuma farinciki take ji kamar zata zauce. Daa ba don Abul na d’akin ba daa ta nunawa Haydar farincikinta tare da godiya thou Mas’ud ma ya cancanci godiya amma ba irin na Haydar ba. Abul da kallon ya isheshi ya kwanta ya juya mata baya yana mamakin yanda bata takura mishi yaci abincin ba, hasalima ya lura duk abunda ya fad’a bata mishi fad’a balle ta nuna ranta ya 6aci. Wani ciwo yaji nan take a k’irjinshi yayi saurin mik’ewa ya fara kakarin amai. Da sauri Laila ta jawo k’afarshi k’asan gadon tana tambayarshi me yake damunshi. Ganin amai yake son yi yasa ta taimaka mishi ya tashi yana digar da wani abu mai yauk’i a bakinsa ta kaishi band’aki ya tsugunna gaban toilet yana cigaba da zubar da abun. “Sannu Abul. Sannu kaji?” Shine abunda take ta nanatawa tana tsaye a kanshi hankalinta a tashe. Ya kai minti biyu yana zubar da yauk’in sannan ya daina a galabaice. Laila da kanta ta wanke mishi bakinshi kana ta taimaka mishi ya dawo kan gado ya kwanta lokacin da Mas’ud ya shigo tare da Doctor. “Ya gama aman? D’azu na shigo na jiku a band’aki yana yi.” Laila da tarin damuwa a fuskarta ta amsa masa da cewa, “Ehh ya gama. Doctor me yake damunshi? Amai yayi kamar majina babu alamar abinci a ciki.” “Hakan zai iya yiwuwa saboda effect na drugs da yake sha ko wani ciwon. But ga result d’insa ya fito…” Ya bud’e file d’in dake hannunsa yana karantawa can yaci gaba, “Yana d’auke da malaria, ulcer, typhoid wanda yake k’okarin bata mishi hanji and he is malnourished.” Doctor ya d’ago idanunsa yana kallon Abul yaci gaba, “Hanjinka yana k’okarin lalacewa ya tsinke domin rashin cin abinci da kuma turawa cikinka abunda baya buk’ata. You are one lucky lad da za’a fara maka treatment kafin lokaci ya kure.” Laila dake kusa da Abul sai nanata ‘Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun’ takeyi a zuciyarta. “Ya samu yaci abinci koda zai yi amai domin kad’an zai zauna. It’s a long process kuma sai ya daure, Allah ya bada lafiya.” Ya rubuta magungunan da za’a sayo ya mik’awa Mas’ud ya fita. “Kalti zan je d’auko magani, ko akwai wani abu da kuke buk’ata?” Girgiza kanta tayi tana cewa, “Babu komai, ko akwai abunda kake buk’ata Abul?” “Ya taho mini da Codein.” Abul ya bata amsa yana tsareta da ido. “Wannan ne bazaka samu ba.” Fad’in Mas’ud kana ya yiwa Laila sallama ya fita. Laila da bata nuna komai a fuskarta ba ta k’ara jawo abincin ta bud’e mishi tana mai ajiyewa a gefenshi. “Ya kamata kaci abinci don nan gaba idan yunwa ta maka yawa zaka yiwa kanka lahani.” “As if you care!” Ya fad’i hakan cikin 6acin rai. “I do care, amma ba kamar daa da zai dameni har ya shafi rayuwata ba. I care ta yanda zan fawwalawa Allah lamarina in kuma yarda dashi kan cewa hakan yana cikin k’addarata kuma zai gyara a lokacin da yaso. Idan zan iya sacrificing a lot for your happiness Inaga kaima ya kamata ka gwada sau d’aya for me, that’s if you are not selfish which you are.” “I’m not selfish.” Ya bata amsa hawaye na taruwa a idonshi. “Ka fad’awa wani Abul, duk abunda kake yi saboda kai ne ba don ni ba. Baka ta6a damuwa da farincikina ba sai naka, kafi son mahaifinka akan ni dana sha wahala da kuma bak’in ciki saboda ku. For once na nuna ina son abu amma ka kasa mara mini baya sai ma tona mini asiri da kayi da kuma jefa kanka a halaka. Sai dai bazan fasa maka addu’a ba, domin ita kad’ai ce abunda zan iya maka don nuna so da kuma gatana a gareka. Kaci abinci.” Hawaye ne ya zubo kan k’uncin Abul yana cije le6enshi bakinshi na 6ari. “You had so many options amma kika za6eshi.” “That’s my life Abul. Ni nake da za6in wanda zan rayu dashi ba wasu zasu za6a mini ba. Bana son k’ara jin wata magana kaci abincinka.” Ya kai minti biyar a haka sannan don karan kanshi ya d’auki abincin ya fara ci yana kur6an hot chocolate d’in. In bai manta ba rabon daya ci abinci mai kyau irin haka tun rabuwarsa da Sadistic Faruq. Jiya kuma a hanyarsu ta dawowa gida an saya mishi abinci amma yace bazai ci ba, sai dai daga Haydar har Mas’ud babu wanda ya mishi dole. Wannan bak’ar yunwar ne take addabarshi amma da bazai ci abincin ba. Cikin k’ank’anin lokaci ya cinye komai Laila ta mik’o mishi ruwa yace bazai sha ba. Kafin ya k’arisa magana ya fara kwaza amai a jikinshi wanda saura kad’an ya ta6a Laila amma tayi saurin matsawa baya. “Subhanallahi. Sannu.” Shine abunda ta fad’a tana mai zagayowa ta gefenshi ta sunkuyar masa da kanshi kasan floor. Wani aman ya sake yi yana rik’e da cikinshi yana nuk’urk’usu dalilin azabar da yake ji. Sai daya gama ya koma ya jinginu da gini yana mayar da numfashi idanunshi har sun kad’a sunyi ja. “Bari in kira masu aiki su gyara gurin.” Fad’in Laila tana fita daga d’akin cikin sauri. Tana fita Abul yayi saurin sauk’owa daga gadon yayi hanyar fita, amma kafin ya kai k’ofa jiri ya d’ebeshi ya zube a nan ya buge kansa. A nan Laila ta dawo ta sameshi bai ma san inda yake ba, hankali tashe ta k’ara fita ta kira Doctor yazo ya fara dubashi. Kayan jikinshi aka cire mishi aka barshi daga shi sai boxers, kana aka canja mishi bedsheet aka mayar dashi kan gado duk bai sani ba. “Babu komai Hajiya zai farka anjima.” Fad’in Doctor kana ya fita. Ana gama gyara d’akin Laila taja kujera ta zauna a bakin gadon tana goge mishi fuskarsa daya 6ata. Tausayinshi ne cike fal a ranta har idanunta na tara kwalla. “Ya Allah don girmanka da ikon mulkinka ka shirya mini d’ana. Ya Allah karka d’aukeshi a wannan hali daya jefa kanshi. Allah ka sanyaya mishi ranshi kaji kanshi.” Ire-iren addu’an da take tayi kenan har ta gama gyarashi sannan taja wani bedsheet d’in ta rufe masa jiki. Wayarta ta d’auko fara kiran Sabrin ta mata albishir sannan ta kira Ummii da kuma k’awayenta Hajiya Maryam da Shatu. Mas’ud ya shigo ya ajiye maganin a saman mini fridge dake d’akin kana yace, “Lafiya naga an cire masa kayanshi?” A nan Laila ta bashi labarin abunda ya faru ta k’arisa da cewa, “Watakila guduwa yaso yi sai jikinshi ya badashi ya fad’i a gurin.” “Zai aikata. Domin jiya har so yayi ya tara mana jama’a bayan mun tsaya sallah wai kidnapping d’inshi muka yi. Sai dana nuna musu hotonan mu tun yana yaro har girmansa sannan aka yarda da zancena.” “Allah ya kyauta. Amma kana ganin zai bar shaye-shayen nan cikin sauk’i kuwa?” Ta tambayeshi cike da damuwa a fuskarta. “Bai dad’e a rayuwar ba, so ina ganin barin kayan mayen bazai yi wahala ba.” “Allah yasa.”“Amin.” Ya amsa mata kana ya fara bata labarin yanda Haydar ya sameshi. Sabrin ce ta fara zuwa, tana ganin Abul ta sake ledan hannunta tayi kanshi tana kuka. “Me amfanin kukan Sabrin? Kiyi shiru please.” Fad’in Mas’ud da baya son ganin kukanta. “Mama ya dawo fa, da gaske Yaya Abul ne.” Murmusawa Laila tayi tace, “Shine Sabrin. An samu Abul.” Godiya ta yiwa Allah kana ta koma kusa da Mamanta tana tambayar Mas’ud a ina aka sameshi. Kafin a bata amsa Yaya Madu da matarsa tare da Ummii suka shigo. Nan d’akin ya cika da ‘yan uwa da abokan arziki ana taya juna murna. Yaya Madu da kyar ya amsa gaisuwar Laila kana yaje kan Abul ya tsaya yana kallonshi, can kuma ya fita bayan ya yiwa Ummii magana kan cewa idan sun gama su kirashi. K’arfe sha d’aya Abul ya farka yaji hayaniyar mutane a kusa dashi. Ganin ‘yan uwansa yasa yaji yayi kewarsu. Nan kuma aka fara mishi sannu da jiki babu wanda ya tambayeshi rayuwarsa ko kuma ya mishi fad’a. Fruits Laila ta bashi yaci sannan ta bashi maganinsa ya sha bayan ya mata musu. Sai bayan azahar Ummii suka tafi, Laila ma ta koma gida aka bar mas’ud da Sabrin kula dashi kafin ta dawo. Sai bayan la’asar ta gama abinci ta koma asibitin bayan tayi waya da Haydar ya fad’a mata bazai dawo da wuri ba. Bayan isha Haydar ya shigo asibitin ya samu Mas’ud ne kad’ai da Laila kowa ya watse hatta Sabrin ta koma gidanta. Sai a lokacin ya yiwa Abul magana yace, “Ya kake jin jikin naka?” Abul bai kulashi ba illah hararanshi da yayi yana aika mishi mugun kallo. “Baka ji ana maka magana bane?” Mas’ud ya kwa6eshi. Cikin k’unk’uni ya amsa ba tare daya daina hararan Haydar ba. Basu jima ba suka tafi bayan sun bada gadin Abul gurin d’aya daga cikin yaron shagon Mas’ud wanda zai iya kula dashi kuma ya hanashi guduwa. Laila da dama bata zo da motarta ba ta shiga ta Haydar for the first time suka kama hanyar gida wajen takwas da rabi na dare. “Zan sha ice cream.” Tace dashi tana ta6a hannunsa. “Sai kuma me?” Ya tambayeta yana murmusawa. “Da gurasa.” Dariya Haydar yayi yace, “Gurasa dai?” “Ehh.” “Haka kawai kika ji kina son gurasa ko dai dama tun d’azu kina son ci?” “Kai fa ka tambayeni na kuma baka amsa.” “Baki bani amsa ba.” “K’amshinsa naji yanzu.” Da mamaki Haydar ya juyo yana kallonta yace, “A cikin motar nan?” Gyad’a mishi kai tayi kana ta kunna wak’a tana canjawa, can kuma ta kashe gaba d’aya ta gyara zamanta ta d’aura k’afafunta kan cinyar Haydar. “You are playing a dangerous game Laila. A mota muke.”“So?” Ta tambayeshi tana k’ok’arin mishi cakulkuli amma ko gezau bai yi ba. Da haka suka isa inda zai saya mata ice cream d’in ya fita bayan ya muntsini k’afarta. Daga nan kuma yabi inda zai samu gurasa ya saya mata aka had’a mata a gurin suka dawo gida. Suna shiga gida Haydar ya kwanta a kan kujera ya rufe idanunsa, dalilin gajiyan jiya daya kwaso gashi yau bai samu ya huta ba ya tafi office ga zirga-zirgan asibiti. “Ka gaji ko?” Laila ta tambayeshi tana zama a k’asan kujeran da yake. “Kamar an mini duka haka nake jin jikina, ga bacci nake son yi sosai.” “I thought kace zamu yi hira yau.” Bud’e idonsa d’aya yayi kana ya mayar ya rufe yace, “Laila kenan.” Dariya tayi kana ta bud’e ledan gurasan ta fara ci tana had’awa da ice cream. “Baza kaci bane?” Ta tambayi Haydar wanda ya sauk’o da hannunsa ya tura cikin rigarta. “Um um.” Tana gamawa ta kai sauran kitchen kana ta kashe wutan falon tare da kulle k’ofar ta tashi Haydar wanda ya fara bacci suka shiga d’aki. Cikin gyangyad’i ya cire kayanshi ya kwanta yana cewa, “Ki mana addu’a please.”“Kar kayi bacci ka jirani in fito daga band’aki muyi magana.” “To.” Kawai yace. Laila kuma wanka tayi kana ta fito ta samu Haydar har ya fara minshari. Bata so hakan ba domin ta so suyi hira kafin suyi bacci. Tana gama abunda zata yi ta kwanta ta musu addu’a ta shafa musu. Kallonshi ta tsaya yi yanda yake bacci so peaceful and innocent. Kyau ya mata bana wasa ba don haka ta kai hannunta kan fuskarshi tana shafawa. “Laila.” Taji ya kira sunanta tare da jawota jikinshi yaci gaba da baccinsa. Murmushi tayi mai k’ayatarwa kana ta kai hannu ta kashe bedside lamp ta koma jikin mijinta ta kwanta tana manna hancinta a k’irjinshi yanda zata shak’i k’amshin jikinshi da kyau. “Thank you for being there for me Ruwan Zumana.” Ta fad’i hakan duk da tasan bazai ji ba.
Mum Fateey 👌



