Halysaah Page 48 By Khaleesat Haydar
We sell all kind of children school shoes, school bag, Lunch box, Readymade for children…. Atamfa, Lagos laces, veils, Handbags, shoes, lafaya, jewelries, kitchen items e.t.c….. All at affordable pricesAkwai adashin kayan kitchen, kayan yara and atamfa with laces if interested….Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/B5uR4Jfj6fZIIN0EIIHegMWajen karfe bakwai Khaleesat ta fito daga dakinta tana tafiya a hankali, duk da zazzabin da ta tashi da shi yau haka nan ta daure ta fito, tana hangosa kwance kan kujera yana danna wayarsa sai da gabanta ya fadi sosai, ta sauke kanta ta karasa har inda yake kwance ta durkusa cikin sanyin murya ta gaishesa, wayarsa kawai yake dannawa yaki kallon direction dinta balle ya amsa gaisuwarta fuskarsa a daure, bayan kusan minti daya ta mike jiki a sanyaye ta juya ta wuce kitchen, hawaye taji ya cika idonta ta kai hannu tana gogewa sannan ta fara preparing breakfast, bayan kusan minti arba’in ta fito daga kitchen din zata tambayesa ko ta kawo masa breakfast din yanxu duk da yanda gabanta ke faduwa, amma sai bata gansa a parlon ba, hakan yasa ta juya ta koma kitchen din ta dauko breakfast din ta kai dinning table ta ajiye, zata tafi dakinta kenan sai gashi ya fito daga nasa dakin har ya shirya alamar wanka yayi, tana kallonsa a hankali tace “Na gama preparing breakfast din” Banza yayi mata ya wuce ta, ta bi sa da kallo har ya shiga parlor, a sanyaye ta bude kofar dakinta ta shiga hawaye na taruwa idonta, ta zauna gefen gado tana goge hawayen a hankali, lamo tayi kan pillow tana shesshekan kuka, tunani iri iri ne ke mata yawo a rai, me ke faruwa da ita ne? Ko tana da wani ciwo ne da bata sani ba, who is she going to talk to about this? Hawaye taji na zubo mata sosai, how is she going to explain to Abdul that this isn’t her fault? Ta yaya zata fahimtar da shi ya gane? Tafi awa daya kwance tana saƙe saƙe a ranta, a hankali ta mike zaune jin alamar fitar motarsa daga gidan, da kyar ta mike daga karshe ta tafi parlor tana tafiya a hankali, dinning area ta nufa ta duba taga bai taɓa komai ba a breakfast din da ta ajiye masa, ta juya a sanyaye ta koma parlor ta zauna ta jinginar da kanta da kujera hawaye na sauka idonta, after a while ta tashi da kyar ta fara gyara gidan sannan ta hada shayi ta dawo parlorn ta zauna amma ta kasa sha saboda damuwa, daga karshe kawai ta koma dakinta. Wajen karfe uku taji ya dawo gidan, ita dai tana ta zaune dakinta bata fita ba, bayan kusan minti biyar ya bude kofar dakin nata, kallo daya yayi mata yace “You have Visitors” Daga haka ya juya ya bar wajen, tayi jim tana tunanin su waye visitors din, mikewa tayi ta dau veil din Abayan dake jikinta ta rufe kanta sannan ta fito parlor tana tafiya a hankali, buda ido tayi ganin Aunty Farida da Nenne da step mothers dinta zaune a parlor, da gudu ta tafi ta fada kan Aunty Farida ta rungumeta cike da farin cikin ganinta, Nenne ta hade rai tana kara hakikancewa kan kujera tana kallon TV da aka kunna a parlon, Aunty Farida ta dago kan Khaleesat tana kallonta ganin yanda ta rame, a hankali tace “Ya kike Khaleesat?” Khaleesat ta sauke idonta cikin sanyin murya tace “Lafiya lau Aunty, Ummana fa? Me yasa baku zo da su Islam ba?” Aunty Farida tayi kasa da murya tace “Ke baki gaida su Nenne ba” Sai a sannan Khaleesat ta tuna da sauran mutanen parlon, zamowa ƙasa tayi a hankali tana kallon Nenne tace “Ina yini Nenne?” Nenne tace “Akan me zaki ce min ina wuni ni da nake er banza mara mutunci a idonki? Ita Faridar da kika makalewa kina shigewa jikinta da an biye ta tata da bata kashe auren nan har lahira ba? Da an biye ta Farida da Zahra’u idan kin ganki a wannan gida haka Allah ya tsine min albarka, to sai me don kin gan ni kin kauda kai kinyi kamar baki ganni ba da sauran matan ubanki? Ai babu komai” Khaleesat ta hade rai ta gaida su Mama Shatu dake zaune fuska duk babu walwala suka amsa mata babu yabo babu fallasa suna kare mata kallo, Nenne ta gyara zama cikin bacin rai tace “Banda matan ubanki da suka takura aje a san inda kike a ga halin da kike ciki sannan ni da na amshi sabon lambar Awdul wajen Farida nayi ta doka masa kira har yaje ya dauko mu ya kawo mu kin zata akwai wanda zaki gani a gidan nan ne? Ita farida Allah Allah take ta koma Legas ta ci gaba da tuwo tuwonta a can, uwarki kuma ba sanin ciwonki tayi ba balle ta samar mana hanyar zuwa ganin halin da kike ciki, amma me? haka nan albarkacin Ali nace dole dole sai naje naga halin da kike ciki, haka nan na uzura ma Awdul da kira yaje ya dauko mu, kuma Alhamdulillahi ga ki nan har wani haske kika kara alamar kina cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya da mijin ki, to meye zaki yi kamar baki taɓa sanin mu ba daga abun arziki dai” Mama Zubaida tace “To ai sai a zaga damu cikin gidan mu sa albarka tunda Allah bai yi mu za mu kawo amarya ba” Nenne tace “A’a, ba bin kwakkwafi da tsegumi ya kawo mu ba kaman en iska, tunda dai yarinya na cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya dama mu hakan ne kadai fatan mu, don haka babu me shiga mata ko ina a gidanta, in ma ce maku aka yi ku yi hakan don wata mugun manufa taku to baza ayi ba, don ni ban yarda da yanda ku ka dage sai an zo gidan Khaleesah ba tunda ni ba yarinya bace, dama kuma Ali yace ko minti sha biyar kar mu yi, da mun samu ganinta mu kamo hanya mu dawo tunda mu ba iyayen banza bane” Mikewa Khaleesat tayi ta tafi kitchen ta bude fridge ta dauko ruwa da drinks ta daura kan tray ta kai masu parlorn ta ajiye, ita dai Aunty Farida sai bin ta da kallo take don kana kallon fuskarta tasan akwai damuwa, gashi tana son kebewa suyi magana da ita amma tana gudun fitinar Nenne, Nenne na kallon Farida tace “Karfe nawa yanxu?” Farida tace “Uku da minti goma” Nenne na gyara mayafinta tana kallon Khaleesat tace “Toh kitchen za ki kai ni mu gana ko kuwa? in mun gama magana sai kije ki ce masa za mu koma ba zama muka zo yi masa ba” Aunty Farida ta dake ta mike tace “Kafin nan bari in ɗan yi magana da ita Nenne” Nenne ta kalleta da sauri tace “Ai ba kashe aure ya kawo mu ba Farida, in baza kiyi mata magana a gabanmu gaba daya ba to ki rike maganar ki kawai don ba alkhairi bane, haka kawai baza ki ja yarinya ki keɓe da ita ki kitsa mata tsiya da salon kashe aurenta ba” Aunty Farida ta dinga kallon Nenne, Nenne ta mike tana rike da babban jakarta tana kallon Khaleesat tace “Kai ni kitchen din” Khaleesat taji kamar tayi kuka bayan Nenne ta hana Aunty Farida tayi mata magana, rai babu dadi ta nufi kitchen Nenne na biye da ita a baya bayan ta jaddada ma farida a kunne kar ta bari su Mama Zubaida su shiga ko ina na gidan, su Mama Shatu da Mama Zubaida sai tabe baki suke, Nenne ta tura kofar kitchen din bayan sun shiga, tana kare ma kitchen din kallo tace “Maa sha Allahu kai kaji waje sai kace daki uku a hade, kuma iya girki kawai ake yi a nan?” Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, Nenne ta zauna kasan tiles din kitchen din ta zuge jakarta tana kallon Khaleesat tace “To kin tsaya min kerere a kai” Dukawa Khaleesat tayi a gabanta tana kallonta, Nenne ta fito da wasu kulle kulle har ƙashi biyar, ta dinga kwancesu daya bayan daya cikin nutsuwa, murya can kasa tace “Kin ga wannan?” Khaleesat dai kallon kullin da Nenne ke nuna mata kawai take, Nenne na magana a hankali kamar tana tsoron wani ya ji tace “Cikin ruwan wanka zaki dinga diba kadan kadan kina zubawa kiyi wanka, duk wani mugun abu da mutum zai maki ko kuma yayi maki to da izinin Allah zai koma kansa da zuri’arsa, sharrin zai lalace na har abada, Wnn kuma a kunu zaki dinga zubawa ki sha kayanki ke kadai, wannan girki zaki dinga yi maku da shi gaba daya ku ci, ba wani mugun abu bane kawai saboda zaman lafiyanku da kwanciyar hankalin ku babu kuma ɗan iskan da zai iya shiga tsakaninki da mijin ki, sai ki ga kanku ya hadu kuna ma juna nutsattsen soyayya bakwa son laifin juna, wnn na hayaki ne shima duk wani mugun abu idan an maki zai karye ya koma kan me shi da izinin Allah, da kyar aka tsam min wallahi, kin dai gansa ɗan mitsitsi ko Ali ban dibar ma ba tunda naga bashi da yawa na kawo maki ba don halin ki ba, wannan na karshen shi kuma na sha ne da wanka, in kinyi wankan sai ki kada shi ko cikin ruwan shayi ne ki dinga shan abun ki” Ita dai Khaleesat tayi shiru tana ta kallon abubuwan da Nenne ke mata bayaninsu sinka sinka cikin nutsuwa, Nenne ta gyara zama fuskarta a daure tace “Wallahi in kika sa nayi asaran lokacina da en kudadena kika ki amfani da wannan abubuwan da na shiga kauyuka takanas na samo maki to in na maki Allah ya isa sai ya bi ki tunda ni ba baiwar buzuwar uwarki bace, duk ita ya kamata ta maki wannan abun amma gantalalliyar bazata yi ba, dama kuma sari nasan ke da ita bakwa amfani da duk wani abun taimako da nake baku, wani lkcn matsalarku ce ma ke shafan ɗa na yayi ta wahala a duniya, to wannan in ma kinki yi wallahi kanki kika cuta don dangin Awdul ba mutanen arziki bane duk mun sani, kuma ba lallai su barki ki zauna lafiya a gidan mijin ki ba barin yanda suka dau ƙaran tsana suka dora ma ubanki saboda shi talaka ne, to ni dai gashi nan albarkacin ubanki na maki wannan wahala, haka nan na shiga wani kauye duk mayu na fito da kyar, to ya rage naki kiyi ko kar ki yi, in ma baki yi ba Allah ya isa” Khaleesat dake kallonta tace “Toh in ya gan su sai in gaya masa na menene su?” Nenne ta saki baki tana kallonta, a fusace tace “Ke dai sokuwa ce mahaukaciya, to uban wa yace maki a gabansa za ki yi? Yau naga bala’i, wannan wace irin shashashar yarinya ce? dama ba sai ya fita ba zaki yi maza kiyi duk abinda zaki yi kafin ya dawo? Ni da ban yi boko ba ma nafi ki hankali da wayo? wannan wace irin jaraba ce Zahra’u ta haifar ma Ali? To ki kwasa ki nuna masa tunda baki da seti” Khaleesat ta wani hade rai ta kauda kai, Nenne tayi kasa da murya tace “Ae sai ya fita duk zaki yi komai cikin sirri, yanxu boyewa zaki yi inda ko da wasa bazae gani ba” Khaleesat tace “Toh ae zae ji warin hayakin kuma, sannan ni bama ni da abun yin turaren wutan ai” Nenne tace “To dama ai shegen a gantale ya dauko ki bai bari duk mun shirya maki turaren wuta ba da sauran abubuwan da ake kai mata da su gidan miji, yanxu dai nasan shi zai maida mu gida ina da manyan robobin turaren wuta har biyu da na ajiye maki zan basa turaren da kasko ince ya tsaya gun masu siyar da gawayi a bakin hanya ya siya maki ko leda uku ne ya taho maki da shi, sai ki dinga hurawa a kaskon tunda ga AC a parlon nan da nan zai kama maki in kika hura” Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba, Nenne tace “To shikenan ki maida ni mahaukaciya ina kokarin taimakon rayuwarki” Khaleesat tace “Na ji” Nenne tace “Yauwa to, yanxu gasu nan maza ki je ki boye inda bazai gan su ba kwata kwata” Khaleesat ta amsa ta nemi waje a nan kitchen din ta boye, Nenne tace “Yauwa to haka ake yi, yanxu maza tafi ki ce masa zamu tafi kar ya ga mun zaune masa a gida, dama ni wnn abubuwan yasa nayi ta doka masa kira yau kwana uku kenan, har Allah yayi ya zo ya dauke mu” Mikewa Khaleesat tayi ta fita daga kitchen din Nenne na biye da ita murya can kasa tace “Ko ruwan gidansa mu dai bamu sha ba balle yace” Khaleesat na tafiya a hankali ta nufi dakin Abdul, knocking tayi tana jiran ya amsa, after almost a minute ya bude kofar, ta sunkuyar da kanta tace “Za su tafi” juyawa yayi ya koma dakinsa, hakan yasa ta dawo parlor, Nenne na kallonta tace “Kin gaya masa?” Kai ta gyada mata ta tafi kusa da Aunty Farida ta zauna a kasa, Su Mama Shatu kana ganin fuskokinsu kaga bakin ciki da hasadda karara a kwance, bayan kusan minti biyar Abdul ya fito daga dakinsa yana murmushi yace “Har za ku koma Kaka?” Nenne tace “Wallahi kuwa Awdul, ai dama ba zama za mu yi ba, ni dai nayi farin cikin ganin jikata cikin kwanciyar hankali dama duk haka muke so” Shi dai bai ce komai ba, Nenne ta mike tace “Don haka yanxu sai ka maida mu gida kawai” Abdul yace “Toh naga ko abinci bata baku ba ai” Nenne tace “A’a mu muka hanata don duk a koshe mu ke, ruwan ma in ka lura ai bamu sha ba” Shi dai murmushi kawai yayi, a haka Nenne ta kada keyarsu Mama Zubaida da Mama Shatu suka fita daga parlon, Ita dai Khaleesat na biye da su duk jikinta a sanyaye, Aunty Farida ce last din fita a parlorn, tana kallon Khaleesat tayi kasa da murya tace “Za ki ga sako na ajiye maki bayan throw pillow din kujeran da na zauna, kar ki damu kafin in koma lagos zan samu lokaci in zo ni kadai kin ji?” Kai kawai Khaleesat ta gyada mata, Bayan Abdul ya bude motarsa ya kalli Khaleesat da duk jikinta yayi sanyi ganin su Aunty Farida za su tafi, yace “Mu je sai mu yi dropping din su mu dawo” Nenne dake kokarin shiga bayan mota ta dakata tace “Toh ai babu waje a motar, a ina zaka dora ta Awdul?” Aunty Farida tace “Sai ta shiga gaban motar Nenne ni in koma baya” Nenne tace “A’a babu ruwana wallahi, a irin narka narkan jiki na Shatu da Zubaida mu uku ma ya muka kare a baya balle kin shigo cikinmu Farida? Ko dai a cinyar su zasu dora ki?” Shi dai Abdul murmushi kawai yayi, Khaleesat tace “Toh ni sai in zauna a bayan” A fusace Nenne tace “To ke dole sai kin bi mu ne kamar en matan amare? Kawai don na zo gidanki sai in koma gida da ciwon jiki? ni wallahi in da matsi a mota ma bana shiga, da mun sani da bamu taho da Zubaida ba don duk ita ta cika waje…” Abdul ya kalli Khaleesat yace “Don’t worry, ki koma ciki kawai” Hawaye ne ya cika idonta tana kallonsa, Aunty Farida ta yi ma Nenne wani kallo ta shige gaban motar, Nenne ta kyabe baki ta shiga bayan motar tana hararansu Zubaida da su ma duk suka shiga motar kuma babu warce tayi gigin gogan jikin Nenne a cikin motar, Nenne tace “To duk ku sauka Khaleesah ta fara shigowa ta dawo kusa da ni tunda ba wani auki gareta ba, ku ne abun tsoron dama” Babu musu duk suka sake sauka daga motar suka koma gefe, Nenne na kallon Khaleesat tace “Ba sai kin yi kuka ba, shigo ki matso kusa da ni mu ga adadin wajen da zai rage, in ya kama wata sai ta hau adaidaita sahu” Khaleesat ta goge idonta ta karasa ta shiga cikin motar ta matsa kusa da Nenne, space din da ya rage a motar tsaf zai dauke su Mama Zubaida, Nenne ta tabe baki tayi kasa da murya tace “Duk fa wari suke, in Farida ta shigo nan ai jikina za su rakube in ta shakan wari su cuce ni, in de ba kusa dani Faridan zata dawo ba, kuma Zubaida duk ta fi warin, banda akwai turare da AC a motarsa ai da mun ji kunya” Ita dai Khaleesat bata ce komai ba su Mama Zubaida suka shigo motar Nenne na yatsine yatsine, a haka suka bar gidan. Sai kusan karfe biyar suka isa Mariri, bayan Abdul yayi parking dai dai kofar gidansu Khaleesat Nenne ta bude motar ta sauka tare da Khaleesat, su Mama Zubaida ma duk suka sauka da Aunty Farida suna ma Abdul godiya sannan suka shiga cikin gida, Nenne na gyara gyalenta tace “To Allah yayi maka albarka Awdul mun gode, amma dai zan yi maza in karasa gida akwai sakon Khaleesat da zan dauko in bata tunda Allah ya kawo ku ta tafi da kayanta kawai” Yana zaune driver seat ba tare da ya juya ba yace “Toh Kaka” Tana kallon Khaleesat tace “Mu je ki taho da sakon” Khaleesat bata ce komai ba ta fara bin Nenne zuwa gidanta, bayan sun yi nisa Nenne tace “Ai kinga shegen bai ce bari ya karasa gidan nawa da mu a motar ba, gaba daya baya ganin mutuncin gidana dama” Ita dai Khaleesat tayi kamar bata ji me tace ba, har suka isa gidan Nenne Khaleesat na gaisawa da mutanen anguwan, Nenne tace “Munafukai, sun yi mamakin ganin ki haka ai, kinsan duk ca aka yi kin shiga duniya kin gudu, sai daga baya kuma aka ji kina gidan mijin ki” Murmushi kawai Khaleesat tayi, bayan sun shiga gidan Nenne ta dauko turaren wutan ta saka su a katon leda da kasko biyu sannan suka fito, suna isa kofar gidansu Khaleesat Nenne ta saka ledan a bayan motar Abdul tana cewa “Kaga har mun dawo Awdul, dama turaren wutan ne ba wani abu ba, don haka ku yi maza ku tafi kar Magariba ya tarar da ku a hanya” Yace “To Kaka” Khaleesat na kallonsa tace “Zan shiga in gaida Ummata” Bata jira cewarsa ba ta shiga cikin gidansu ya bi ta da kallo, ko minti uku bata yi da shiga dakin Ummanta ba sai ga Nenne, tana tsaye bakin kofar dakin bayan ta dage labule tace “Abun kuma ba hauka bane ai, taso ki fita yana jiran ki…” Khaleesat ta daga kai tana kallon Nenne, Nenne tace “Ae sai yayi mana kallon mutanen banza marasu hankali, taso nace ki fita kar ki ja mana reni” Umma na kallon Khaleesat tace “Ku je Khaleesat, kin ga yamma tayi” Fuska a daure Khaleesat ta mike ta fita daga dakin, Nenne ta rakata har bakin motar Abdul, tana shiga gaban motar yayi ma Nenne sallama ya ja motarsa ya bar wajen, har suka isa gida ana kiraye kirayen magrib bai ce mata ba, ita ma bata ce masa komai ba, bayan yayi parking ya sauka motar ita ma ta sauka, tana tafiya a hankali ta bi bayansa suka shiga gidan, Kitchen ya shiga direct, har zata wuce dakinta ta tuna sakon da Aunty Farida tace ta bar mata kan kujera, ta karasa inda Aunty Farida ta zauna ta dauke throw pillow din wajen ta dinga kallon Dollars din dake ajiye da wayoyi biyu, daukan 1000 dollars din tayi wanda Jay ne ya bata da zata dawo Nigeria, ta dau wayoyin biyu, daya na Ajay daya na Jay, lkci daya jikinta yayi sanyi hawaye suka cika idonta, muryar Abdul taji a kanta yace “What’s that?” Da sauri ta boye hannunta a baya tana kallonsa tsabar yanda ta gigice.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
