Uncategorized

Yadda Zaku Duba Sakamakon Jarabawarku Ta Neco A Wayoyin Hannunku

Ga sauƙaƙan matakan da za ku bi domin duba sakamakon jarabawar ku ta NECO kamar haka:

 

Da farko za ku shiga Browser din wayarku, Sai ku danna gurin bincike (Search), Sai ku rubuta Adireshin result.neco.gov.ng Sannan  ku danna Alamar Enter ko kuma Search a Wasu Injinan Binciken

i. Bayan Shafin ya buɗe zai baku wasu Akwatina guda Hudu kamar yadda kuka gansu a sama, Akwati ta Farko An rubuta Exam Year, Abinda ake bukatar ku sanya a cikin wannan Akwati shi ne Shekarar da kuka rubuta Jarabawar taku ta NECO Misali 2021,

ii. Sai kuma Akwati ta biyu da zaku ga an rubuta Exam Type, Abinda Ake nufi a wannan Akwatin shi ne wacce irin Jarrabawa kuke son bubawa, Misali SSCE Internal June/July, SSCE External November/December, Basic Education Certificate Examination, ko Kuma Nigerian Common Entrance Examination, To a wannan gidanne zaku saka irin Jarrabawar da kuke son subawa, Misali muce SSCE Internal June/July.

iii. Sai kuma Akwati ta Uku wacce zaku ga An rubuta TOKEN, Abinda ake bukatar ku saka a wannan Akwatin sune Lambobin da kuka saya a Shafin hukumar domin duba Sakamakon Jarrabawar taku, Misali 1630589940

iv. Sai kuma Akwati ta Hudu kuma na karshe a cikin Jerin Akwatunan, Wacce zaku ga an rubuta Registration Number, Abin da Ake buƙatar ku saka a wannan Akwatin itace Lambar rijistar Jarabawar ta Neco, wacce zaku ganta a jikin katin ku na Jarabawa (EXAM Card), kuma zaku ga a karshenta da Akwai wasu haruffa guda Biyu.

• Bayan kun gama Shigar da wadannan bayanan, Abu na karshe da zaku yi shi ne ku danna mabullin CHECK RESULT, wanda zaku ga an rubuta Kuru-Kuru a cikin koren Gida a karkashin wadannan Akwatunan,

    To kuna danna wannan Mabulli na CHECK RESULT, nan da nan Sakamakon Jarrabawar ku na NECO zai bayyana gami da fitowa Dara-Dara a fuskar Waya ko Na’urarku Mai kwakwalwa.

     

Muna tafe da bayani kan yadda ake sayen lambobin duba sakamakon jarabawar ta NECO na Token Code nan gaba kadan Insha’Allah.

Back to top button