Jaruma Nafisat Abdullahi na ɗaya Da cikin waɗanda aka fi nema a Google a shekarar 2021
Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi na ɗaya daga cikin jaruman da ake nema ruwa a jallo a Google 2020 a Najeriya.
Tauraruwar Labarina yia shiga sahun fitattun jaruman Nollywood na kudancin Najeriya, Destiny Etiko, Tonto Dikeh da Zubby Michael.
Amma Google ya sanya Nafisa a bangaren jaruman Nollywood maimakon Kannywood.
Nafisat ita ce ta shida a rukunin taurarin fim bayan Destiny Etiko, Zubby Michael, Pere, Tonto Dikeh, Iyabo Ojo da Olu Jacobs.
Haka zalika, Nafisa ita ce tauraruwar Kannywood ɗaya tilo da ta samu matsayi na 10 a fagen bincike na Google.
Za Ku Iya Karanta
✓ Maryam Yahaya bata jin magana wallahi – Datti Assalafy
✓ Tsohuwar Matar Adam A. Zango ta sake dawowa Kannywood Bayan shekaru 13
✓ Gwamna Aminu Tambuwal ya bada umurnin kamo mawakin da ya waƙe shugaban ‘yan bindiga Bello Turji
✓ Shatu Garba daga Kano ta lashe gasar sarauniyar kyau ta Nijeriya
Sai kuma Rahama Sadau, Fati Washa, Maryam Yahaya da Hadiza Gabon.
Abubuwan da ake nema a Google suna karuwa akai-akai duk rana.
Har ila yau, shafin yana tattara bangarori da dama kamar su; ƙungiyar mawaƙa da waƙa, wasanni da ƴan wasan kwaikwayo da kuma fina-finai kansu tare da tambayoyin da aka fi yawan yi akan su.
Nafisa tana da mabiya miliyan biyu a Instagram da 176,600 a Twitter da kuma wasu miliyan biyu a shafinta na Facebook.
A cikin finafinan da aka fi nema, ‘yan Najeriya sun fi neman bayanai game da Squid Game da Zuwa Amurka da Rayuwar Jima’i da Baƙar fata da Sanarwa.
Daga cikin wadanda suka mutu a shekarar 2021 akwai fitaccen malamin addinin kirista TB Joshua da mawaki Sound Sultan da Sani Dangote – kanin Aliko Dangote – wadannan suma suna ɗaya daga cikin waɗanda ake nema a Google.
Matakan shaharar Nafisat Abdullahi
Kamar yadda bayanai suka nuna, Nafisa ta fara shahara a shafin Google daga ranar 3 zuwa 9 ga watan Janairun 2021.
Hakan dai bai rasa nasaba da kammala kashi na biyu na fim dinta da aka dade ana yi ba, wanda zai fara fitowa a karshen watan Disambar 2020.
Neman Tauraruwar ya karu zuwa kashi 93 cikin 100 a watan Satumba, a daidai lokacin da shirin Labarina kashi na 3 yake kan ganiyar shahararsa.
Bugu da kari, masu binciken Nafisa Abdullahi sun ƙaru zuwa kashi 100 daga ranar 5 ga watan Disamba zuwa 11. Idan kuma ba ku manta ba, hakan yana da alaƙa da shafin kayan kwalliyar NAFCOSMETICS da ta kaddamar.
Mazauna Abuja babban birnin Najeriya ne kan gaba wajen neman jarumar ruwa a jallo, sai kuma Rivers da Legas da kuma Kaduna.
Sirrin shaharar Nafisa
Shekara biyu kenan rabon da aga jaruma Nafisa Abdullahi a harkar fim, sai kwatsam! Aka ganta ta fara fitowa a cikin shirin fim ɗin Labarina a shekarar 2020.
Fim din wanda Aminu Saira ne ya bada umarni, Nafisa ta taka rawa a matsayin jarumar da labarin ya faru akanta.
Tun bayan fitowar Labarina ba a samu wani fim da Nafisa ta fito a ciki ba wanda ya kai koda rabin fim ɗin Labarina a shahara.
Yayin da tauraruwarta ke haskawa, ta kaddamar da sabon kamfaninta na kayan kwalliya na Nafcosmetics a watan Nuwamba 2021.
Bugu da kari, tauraruwar ta shahara da tafiye-tafiye zuwa kasashen Turai da Amurka, inda take zuwa neman karin karatu ko yawon buɗe ido.
Kada ku manta ku ci gaba da ziyarartar wannan shafi namu mai albarka na Aihauanovels.com.ng Domin samun labaran Kannywood, littattafan Hausa, da dai sauransu.