Uncategorized

Abubuwa 4 da ya kamata mace mai al’ada ta kauce masu

 Abubuwa 4 da ya kamata mace mai al’ada ta kauce masu

Assalamu alaikum yan uwa barkan da wannan lokaci, yau insha Allahu zan yi bayani ne akan wasu abubuwa huɗu (4) da ya kamata a ce duk mace mai period ta kauce masu, ga abubuwan kamar haka:

1. Ki guji shan ruwa mai sanyi ko lemun soda, sannan kada ki ci kwakwa a lokacin da ki ke period.

2. Ki guji shafa man shampoo a kanki saboda a lokacin da ki ke al’ada ko wace kusurwa da ke kanki a buɗe ta ke, shafa man shampoo ka iya haifar da ciwon kai mai tsananin gaske.

Shi kuma ciwon kai ba karamin illa yake yi wa mata ba, domin kuwa yana iya haifar maki da matsalar brain problem, ya yin da ki ke cikin kuruciyarki ko bayan kin manyanta.

3. Ki guji cin cocumber a lokacin da ki ke peroid saboda tana dauke da wani sinadari wanda kan iya dakatar da wani sashen jinin peroid fitowa daga mafitarsa acikin jikin ‘ya mace, wanda sakamakon haka kan haifar da toshewar mahaifa ya zama baza ki iya haihuwa ba.

4. Sannan na karshe a duk lokacin da ki ke peroid ana so jikin kada a buge shi da wani abu mai karfi musamman ciki, saboda yin hakan ka iya haifar da aman jini ko kuma mararki kan iya samun matsala wanda daga bisani a cututtuka su kamaki kamar: Ciwon Kansar Mahaifa da rashin haihuwa.

Jan Hankali:

Binciken masana ya nuna cewa shan kankana lokacin al’ada yana haifar da dakilewar jini  a cikin mara, sannan bayan shekara 5 zuwa 10 yakan iya haifar da cutar Kansar Mahaifa. Allah Ya kyauta dan haka iyaye mata sai a yi hattara a kuma lura.

Don Allah Duk wanda ya samu wannan sako ya tura wa yan uwa domin suma su amfana.

Allah ya datar damu, Amin


Back to top button