Hausa novels

Wace ce ita (Who Is She) Chapter 76 Complete Novel

     *WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)*

NOTEWORTHY WRITERS ELITE✍️

Unique Barakancy🌹

SEVENTY-SIX📍

Kukan da umm take ta rikewa ta fashe dashi tana jijjigashi, gabadaya basirarta ta likitoci ta dauke mata saboda tashin hankali, ko magana ta kasayi illa kukan da takeyi tana jijjigasa, a halin yanzu ma bata da tabbacin a raye yake ko a mace dan babu abinda yake motsi a jikinsa…
Tana cikin wannan hali mami ta shigo sakamakon itama dad ya kirata ya fadamata an daura aure, tana shigowa taga umm tsaye akan deen sai kuka takeyi, rudewa itama tayi cikin tashin hankali tace;
“Innalillahi ya mutu ne? Jamila mun shiga uku, meya faru”…..
Fashewa da wani kukan umm tayi batareda ta juyo ta kalleta ba tace;
“Kun ki basa ita saboda be ce yana sonta ba, ya fada kuma kunyi tafiyarku babu wanda ya sauraresa, yanzu gashi ya mutu sai ku zuba ruwa a kasa kusha”….
Dafe kirji mami tayi a razane tace;
“Wace irin magana kikeyi haka, ya mutu fa kikace, A’a dan Allah, Doctor! Doctor!”…..

Download>>> Doctor Eesah Complete Novel

Ta fada tana fita daka dakin, direct office din Doctor tayi tana kwalla masa kira, kowa ya ganta yasan ba karamin rudani take ciki ba saboda yanda ta gigice lokaci daya, likitoci uku ne suka biyo bayanta zuwa dakin da Deen yake, suna zuwa sukace su koma reception su jira in allah ya yadda zasuyi iya bakin kokarinsu na ganin sun ceto ransa, fita sukayi daga dakin gabadaya sai sambatu suke, an rasa wanda ze bawa wani baki a cikinsu, umm sai cewa take lefinsu ne, sai maimaitawa take ansa masa ido gashi ya mutu hankalinsu ya kwanta…
Basu fi minti goma da zama a reception ba sai ga dad da abby sun shigo, umm na ganinsu ta mike da sauri, kamar jira umm take su karaso tace;
“Kukaki sauraransa kukayi tafiyarku wajen daurin aure, toh ya mutu sai ku zuba ruwa a kasa kusha”….
“Subhanallahi wa yace ya mutu?”..
Cewar abby hankali tashe…
“Oho, ni dai abinda zan fada muku shine tin muna imu imu kuje ku cewa yaran chan ya saketa dan wallahi bazata tare ba, ya saketa in aura ma saif ita, period”…..
Ajiyar zuciya abby ya sauke jin ta fadi haka yasan kenan saif be mutu ba…
“Boddi please calm down, everything will be alright Insha Allah, yanzu ina saif din yake?”…..
“Emergency room”….
“Ku kwantar da hankalinku da yardar Allah komai ze daidaita, kuyi hakuri”….
Cewar dad da sai a lokacin ya saka baki a sanyaye…
Mami kuwa batasa musu baki ba dan gani take ko magana tayi kara mata damuwa zatayi, gani take kamar tafi kowa shiga tashin hankali a halin yanzu, batasan haka take jin deen a ranta ba sai yanzu da ake batun mutuwa akansa, dama wani zubin bama gane darajar abu sai mun rasa ko mun kusa rasawa, tabbas tayi sake sosai akan rayuwar deen dukda yanada nasa kason shima amma nata yafi yawa, ko damuwarsa baya iya gayamata saboda basa samun jituwa, idan ya kawo abinda be mata ba memakon ta bishi a hankali ta nuna masa ba daidai ba sai ta fara masifa tana zaginsa, gabadaya sai ya daina gayamata komai nasa, dadin abun daya da yar uwarta yake shawarar duk abinda zeyi, ita kuma bata boye mata komai saidai tayi kamar batasani ba, yanzu da da bare yakeyi ai saidai taji kawai anayi.
(PS; a lot of parents are on this table, komai yaro yayi fada fada, zagi da masifa da sauransu, abinda basu sani ba kuma it done more harm than good because the children get comfortable with the masifa and zagi, at some point sai su daina jin tsoron wannan, sai yaro yayi lefi kaji yana cewa fada kawai zata mun inyi gaba abuna, whilst idan nasiha ne har sanyi jikin mutum yake koda for that time ne, kuma karya ne ayiwa mutum nasiha beji a jikinsa, lastly abinda kwanciyar hankali be bamu ba tashin hankali baze bamu ba, dan Allah dan annabi mu gyara)….
Zaman kurame suka cigaba dayi kowanne ka kalli fuskarsa kasan baya cikin yanayi me dadi..
Kusan awan su daya sai ga likitocin sun fito sunata share gumi, basu tsaya yi musu bayani ba sukace su samesu a office, da kyar mami da umm suka yarda suka zauna dad da abby kadai suka bi bayan likitocin….
Sai da suka zauna sannan daya daga cikin likitocin ya musu bayanin abinda ake ciki…..
“He is in a very critical condition, mun dai yi nasarar gano wasu pulse dake motsi a jikinsa which means yana raye sai dai gaskiya ya shiga coma dan babu abinda ke motsi a jikinsa, all we have to do now is pray and pray Allah ya taimakemu yasa ya farfado nan kusa”…..
Sun fi minti goma sha biyar suna tattaunawa kafin su tashi su fita duk jiki a sanyaye…..

Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam

Gurinsu mami suka tafi da niyar musu bayani sannan su kwantar musu da hankali a kumayi shawara ko a fita da deen waje in be farfado ba nan da kwana uku, suna zuwa suka tarar da wani tashin hankalin, baby tee ce su hajiya ruwaida Maman twins suka kawota a sume, daidai dawowar su abby akayi emergency da ita….
Rikicewa umm da mami suka karayi ko tambayar abinda ya faru sun kasayi, hajiya ruwaida ce tace suyita maimaita hasbunallahu wa ni’imal wakeel shine suka dan samu sanyi aransu amma duk da haka basa wani gane sauran maganganun da akeyi….
Ba’a dade da shiga da baby tee ba wata nurse ta fito ta fadamusu baby tee ta farfado amma sai kiran sunayen mutane take, da sauri umm tayi emergency room din without permission ba, mami na ganin haka tabi bayanta itama….
Da sauri suka karasa gaban gadon da baby tee ke kwance, baby tee na ganinsu ta fashe da wani matsanaicin kuka tace;
“Dagaske khaleel ya mutu ko mafarki nake? Dan Allah in ya mutu nima ku kasheni in bisa”…..
“Wani khaleel din?”…
Umm da mami suka hada baki wajan tambaya suna zaro ido….
Bata kara cewa komai ba ta cigaba da sambatun da basu gane inda ta dosa ba, sai maimaitawa take in khaleel ya mutu itama mutuwa zatayi….
Da kyar aka samu bacci ya dauketa bayan an mata allurar bacci, sai a lokacin mami da umm suka dan samu nitsuwa, fita sukayi suka koma reception inda suka barsu abby, sai a lokacin mami ta samu damar tambayar hajiya ruwaida abinda ya faru…
“Wallahi bamusan meya sameta ba mami, ihunta kawai mukaji ko kafin muje ta sume”….
“Okay amma naji sai wani irin magana take akan khaleel, we don’t understand at all”….
“Ikon Allah saidai mu bari in ta tashi sai muji”…..
Suna cikin wannan yanayi bappa ya karaso asibitin, direct office din Doctor su abby suka rakasa kamar yanda ya bukata, dalla dalla aka kara musu bayani akan sha’anin lafiyarsu duka daga deen har baby tee sannan suka kara tattauna yanda zasu shawo kan lamarin kafin bappa yasa a kira masa su mami suzo dan so yake su tattauna a sirrince, dakansa Doctor din yaje kiransu umm dan ya basu space kamar yanda yaga suna bukata, bayan fitar Doctor Abby ya kalli su dad yace;
“Ina fata baku ce musu komai ba?”….
“Na’am bappa”…

 

Download>>> The Governor Wife Book 1 Complete Novel 

Suka hada baki gurin basa amsa….
Shiru ne ya biyo baya har su mami suka shigo office din, mami a gaba sai umm biye da ita a baya….
Guri bappa ya nuna musu yace;
“ku zauna”..
Zama sukayi kowacce inka kalleta kasan ba a cikin nitsuwarta take ba…
Gyaran murya bappa yayi yace;
“Maganganu masu mahimmanci guda biyu zanyi amma kafin nan inaso ku sani komai na rayuwa mukaddari ne daga Allah, babu wanda ya isa ya tsallake kaddararsa in dai Allah ya hukunta, sannan kana naka Allah na nashi, na Allah kuma shine daidai, a kullum inaso ku zama mutane masu tawakkali da yarda da kaddara sai kuga kun samu rabauta a ranar gobe kiyama”…..
Jikinsu ne yayi mugun sanyi, dagaji kasan ba wani abu me dadi bane ze biyo baya, umm ko harta fara zubda hawaye kasancewarta mutum me rauni da tausayi, ji suke kamar su janyo zancen bappa suji karshen maganan, a lokacin babu irin tinanin da be zo musu ba, ita umm gani take kamar deen da baby tee ne suka mutu ake musu kwana kwana da nasiha…..
Numfasawa bappa yayi ya cigaba da cewa;
“so tari muna neman abu amma Allah ya hanamu, badan kuma bamu chanchanta ba sai dan ba alkhairi bane a garemu, sai mu godewa Allah a duk halin da muka tsinci kanmu saboda wataran za’a wayi gari bama raye gabadaya, dama duk me rai mamaci ne kuma muma zaman jiran lokacinmu muke hasalima wanda ya mutu ya fimu gata saboda kullum kara zunubi wanda yake raye yake shiyasa aka cewa wanda ya mutu ya huta, a wannan lokacin inaso ku jajirce musamman ke jamila da baki iya sa abu a rai ba, inaso ki zama me sassauta zuciyar da karbar kaddara a duk yanda tazo sannan a wannan lokacin zara’u na matukar bukatar taimakonku saboda kananun shekarunta, kullu nafsin za’ikatul ma’ut Allah yayi ma Ibrahim khaleel din zara’u rasuwa sakamakon hatsarin da yayi a hanyarsa ta zuwa daurin aurensa!”….
Ya karashe da fadin haka cikin alhini….

Tinda khaleel ya fita daga gidan take jinta wani iri, su hassy da suke expecting zata shigo da farin ciki sai suka ganta duk jiki a sanyaye, tambayarta suka hau yi meya faru tace musu bakomai she’s just feeling uneasy, babu yanda basuyi da ita tasha magani ba tace musu she’ll be fine ba sai tasha komai ba, karshe da taga sun dameta ta shige toilet, suna ganin haka suka fita suka bata space gabadayansu, tana jin fitarsu ta fito ta rufe kofa sannan tayi kwanciyarta a kan gado…
Gabanta ne taji yana wani mugun faduwa tayi saurin dialing number khaleel saboda shi kadai yake fadomata a yayinda takejin bugun zuciyarta na tsananta, bugu biyu ya daga kiran cikin tattausar muryarsa yace;
“my beautiful wifey me kamshi”…
Wani kakkarfan ajiyar zuciya ta sauke batareda tabi takan maganarsa ba tace;
“I hope you’re fine?”…
Dariya yayi cikin tsokana yace;
“I’m not fine har sai an kawo min ke dakina, kinga yanzu ma sauri nake na karasa gurin daurin aure, ni kawai ake jira a daura mana aure musha soyayya mai license”…

Also Download ABBAN SOJOJI BOOK 2 Hausa Novel Complete Document

“uhm sai ka dawo toh, take care”…
Ta fada badan taji saukin abinda takeji aranta ba….
“Ana daurawa zan kiraki ince an dauraaaa, na zama angon fatima”….
Dariya kawai tayi tace;
“Okay bye”…
Sannan ta ajye wayar, kwanciya ta sakeyi zuciyarta cike da sake sake kala kala yayinda take jiran kiransa, tanaji ana mata knocking amma tayi kamar bataji ba, haka kowa yayi ya hakura ya tafi, dan bacci ne ya kwasheta a cikin baccin tayi wani mummunan mafarkin daya tasheta babu shiri, wai an kawo gawar khaleel cikin jini sai kuka sukeyi, bata gama dawowa hayyacinta ba taji wayarta na ringing, tana dagawa taga khaleel ne, wani irin farin ciki ne ya kamata da batasan sanda tayi decling call din ba, da sauri tabi bayan kiran amma ba’a daga ba, sai da tayi kira gurin so goma abinda bata tabayi ba a rayuwarta sannan aka daga, koda aka daga sai taji muryar wani bata khaleel ba wai su zo su dau gawa me wayar yayi hatsari, maganar data sata sakin wani ihu me karfi kenan da saida gidan ya amsa gabadaya shine su hajiya ruwaida sukayi rushing inda take, suna zuwa sukaga kofa a garkame, sai da aka kira carpenters suka balla kofar sannan suna shiga suka ganta a kwance a kasa a sume, shine sukayi rushing dinta hospital din da deen yake kasancewar nan yafi kusa dasu kamar yanda aka kai deen shima….

Also Download Ɗaudar Gora Page 8 By Billyn Abdul

Driving ya cigaba dayi cikin nitsuwa bayan sun gama waya da baby tee, kiran daddy ne ya shigo wayarsa wanda shima Allah ya basa ikon halartar daurin auren, ce masa yayi yayi sauri shi fa suke jira, bappa yace sai an fara daura nasu kafin nasu deen, amsawa yayi sannan daddy ya kashe wayar….
Befi 5mins da gama waya ba wani tsoho yazo ze tsallaka titi, ba shiri yayi saurin taka burki saura kadan ya bigesa, daidai ya taka burki motar dake bayansa da batasan tsayawa zeyi ba ta daki motarsa, a take motar khaleel tayi sama tadinga juyi harta daki wani gini sannan ta tsaya, baze iya cewa ga halin da yake ciki ba amma tabbas baby tee ce ta fadomasa a wannan lokacin, be kuma san ya akayi ba yayi dialing numberta saidai ko kafin ta dauka numfashinsa ya fara janyewa, allah ya basa sa’a ya cika da kalmar shahada(Ya Allah in tamu tazo kasa muyi kyakkyawan karshe mu cika da imani)…
Da gudu mutanen da accident din ya faru akan idonsu sukayi gurin motar khaleel da sauri, dakyar aka samu aka bude motar sannan aka cirosa, innalillahi kawai mutanen gurin ke maimaitawa saboda ba sai anja zance ba kallo daya zaka ma khaleel kasan baya numfashi amma duk da haka aka kira ambulance, sai suka dauko wayarsa da niyar dubawa ko babu password su kira mutanen daya kira karshe, suna fito da wayar sai ga kiran daddy, babu bata lokaci suka gaya masa me wayar yayi hatsari Allah yayi masa rasuwa, a rikice daddy yace a dakatar da daurin auren khaleel yayi hatsari kuma ya rasu, salati da sallallami masallacin ya dauka kowa yana ganin abun kamar a mafarki amma kasancewarsu maza masu taurin zuciya da tawakkali sai basuyi panicking ba in banda salati da kowa yakeyi..
Mikewa bappa yayi ya bada umarnin a daura dayan aurensu deen su zasu tafi inda akayi hatsarin…
Mahaifin eesha na jin haka yayi saurin cewa;
“ina da magana bappa”…
“ina jinka alhaji aliyu”…
Sunkuyar da kai yayi yana alhinin abinda ze fada saidai hakan shine maslaha a garesu baki daya…
“Tinda kaddara tazo da haka Allah ya yima wannan bawan allah rasuwa, ina neman alfarma a aurawa saifudden ita fatima, ita kuma aisha akwai wani dan uwanta daya dade yana sonta sai a daura dashi, ina zaton yana gurinnan ma”…..
“Wace irin magana kakeyi haka alhaji aliyu?”….
Cewar bappa cikin rashin fahimta….
Be boyewa bappa komai ba ya bashi labarin abinda ya faru a asibiti da sukaje duba deen kafin su tawo daurin aure, da yanda abun ya tsaya masa a rai saboda saif yayi matukar basa tausayi, ya karashe da rokon bappa akan dan Allah ayi yanda yace din…..

 

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

Ga mamakin bappa ko kafin yayi magana sai Abby yasa baki amma sabanin mahaifin eesha shi cewa yayi a aurawa deen duka su biyun, dad dai na tsaye ya rasa bayan wa ze bi..
Da kyar sukayi reaching agreement akan daurin auren sannan bappa da daddy da wasu daga cikin mutanen gurin suka bar gurin suka tafi inda khaleel yayi accident, suna tafiya ba dadewa aka daura aure kamar yanda bappa ya umarta…..

A tare suka dago suka kalli bappa in shock amma babu wanda ya iya furta komai, kwata kwata brain dinsu ya kasa digesting lamarin, abu kamar film kawai ace musu khaleel ya mutu?….
Gyada kai bappa yayi yana me tabbatar musu da abinda ya fada, yana sane ya cewa su abby karsu ce musu komai saboda yasan ba lallai suyi musu magana yanda shi ze musu ba….
“Abu na gaba shine an daura auran Saifuddeen da fatima da aishatu bisa ga alfarmar da ita mahaifin Aishan ya nema sakamakon halin da suka tsinci deen da sukazo dubasa”…..
Ajiyar zuciya me karfi umm ta sauke hawaye na silalo mata a idonta (ni unique banace na farin ciki bane kona bakin ciki?), tabbas ta taya saif murna badan taso mutuwar khaleel ba sai dan wanda ya fiso so ya karbi abunsa, fatanta daya Allah yasa eesha da baby tee su fahimci juna tinda kawaye ne sosai, shi kuma Allah ya basa ikon yin adalci a tsakaninsu…..
Girgiza kai mami tayi ta juyo ta kalli umm dan taga reaction dinta, sai taga bataga wani chanji ba, zancen zuci ta kamayi akan ya za’ayi a aurawa deen mata biyu, yama za’ayi yarinya kamar baby tee da taga rayuwa ta zauna da kishiya, tabbas ta jiyewa deen dadi daya samu baby tee duba da irin son da yake mata amma kwata kwata bataji dadi da aka daura da eesha ba itama, tinda kaddara ta gifta Allah ya kawo rabo ba sai eesha ta hakura ba, gabadaya sai ta manta ma da eeshan yar aminiyarta ce, kawai ta baby tee take, dama ance so sone amma son kai yafi….

Three days later…..
A cikin kwana ukun nan daya wuce ba zasuce ga halin da suke ciki ba, tabbas mutuwar khaleel tashigesu saboda babu wanda ya basa mutuwa dama mutuwa ta lokaci daya babu jinya tafi shiga jiki, a ranar akayi jana’izar khaleel alhamdulillah ya samu jama’a sosai kasancewarsa mutumin kirki me zama da kowa lafiya, ta wani fannin kuma sun yiwa deen murna da Allah ya nuna kudirinsa da shirinsa akan lamarin, tabbas matar mutum kabarinsa, babu wacce take auren mijin wani haka zalika babu wanda yake auren matar wani, sai dai kwata kwata basa cikin nishadi saboda har lokacin ba’a samu kan deen da baby tee ba, gwarama baby tee tana farkawa tayita sambatu tana kuka har sai an mata allurar bacci sannan, deen kuwa tin ranar daya shiga coma har rana me kamar ta yau ko yatsunsa guda daya be motsa ba, taimakonsu daya umm doctor ce itama, kullum sai ta dubasa ta kuma bada assurance din yana raye amma da tini sunyi give up, a hakama anna kullum tazo sai tayi kuka tace su gayamusu gaskiya in ya mutu ne su sani, umm ce zataita kwantar mata da hankali duk da itama zuciyarta a dagule take..
A yau daya cika kwana uku suka fara shirin mai dashi asibitin umm na England saboda sai yafi samun kulawa achan, shirye shirye sukai tayi saboda da asuba suke so su tafi…

Download>>> Bintu Diyar Bayi Ce Book 1 Complete Document

Da misalin karfe takwas umm da wani wani Doctor suka shiga ICU inda deen yake, dama umm kadai ake bari tashiga saboda sauran duk wanda ya shiga sai ya fito yana kuka yana cewa deen ya mutu, ita da kanta umm so tari tana zubda hawaye a boye dukda ta saba da irin haka ta kuma san tabbas yana raye, saidai duk sanda ta kallesa sai taji zuciyarta ta karye knowing abinda yaja masa ciwon, kullum addu’a take Allah ya tashi kafadunsa ko one minute bazata kara ba zata masa albishir……
Kamar koda yaushe pattern of breathing dinsa ta fara dubawa dan taga ko ansamu chanji sannan ta duba oculovestibular responses da motor responses nasa, dan zaro ido tayi jin kamar yana responding, dayan likitan na ganin haka yayi saurin matsowa shima ya fara duba eye movement dinsa saidai kash basu samu response ta nan ba wanda suna matukar bukatar hakan….
Dafe kai umm tayi tanajin ba dadi aranta..
“Shima ya mutu ko?”…
Umm ta tsinto muryar baby tee a kusa da ita kamar wacce aka jefo, unbelievably umm ta dago tace;
“waya bari kika shigo nan? Yaushe kika tashi? Let’s go”…
Ta fada tana kokarin kamo hannunta, janyewa baby tee tayi ta karasa daidai kan deen tasa hannu ta zare oxygen din dake daure a hancinsa ta fashe da kuka tace;
“Wallahi sai ka tashi, saboda me kowa ze mutu”….
Rige rigen janyeta akayi tsakanin umm da doctor din, umm tayi nasarar janyeta shi kuma Doctor yayi saurin maida masa da oxygen, ruko hannunta umm tayi tace;
“Waya ce miki ya mutu? Bakisan cire oxygen din da kikayi bane zesa ya mutu?”…
Baby tee na jin haka ta sake fuzge hannunta ta koma gaban gadon a guje kamar zararriya tana fadin;
“Bari in duba ko be mutu ba toh”….
Dafe kai umm tayi ta sake biyota tana kokarin kamota, Doctor din na ganin haka yace;
“Who is she to him?”….
“His wife!”…
Umm ta bashi amsa a takaice…..
“Then allow her be, he can listen so he’s probably hearing all what she’s saying, in Allah ya taimakemu sai ya iya jinta ya farka Doctor”….
“Hakane but can’t you see the way she’s behaving stupid tana zare masa oxygen”….
“Ina zuwa”…
Ya fada yana karasawa inda baby tee ke tsaye daidai kan deen tana kokarin sake mai da hannunta kan oxygen din, gabadaya batasan me takeyi ba….
A nitse yace;
“Kwantar da hankalinki be mutu ba fa, ki masa magana ze jiki amma karki cire oxygen din saboda shi yake basa support, kinji ko?”….
Ga mamakinsa sai yaga ba musu ta gyada kai sannan ta janye hannun, komawa ta daya barin tayi ta hau kan gadon ta zauna a gefensa ta fara tatta basa tana ihu tana fadin;
“Ka tashi mana, yaya ka tashi, kowa ya mutu an barni ni kadai dan Allah ka tashi”….
Doctor na ganin haka ya koma kusa da umm suka hau kallon baby tee cike da mamaki, kasa kasa umm tace;
“I hope she’s not hitting him”….
“No I don’t think it’s painful, but I thought she’s your daughter doctor”..
“She is”….
“Thought bata da aure, I’m still surprised she is his wife”….
“Yeah magana ce bata kawo magana ba”….
Shiru yayi ganin batasan conversation din suka cigaba da sauraran zantukan baby tee da take ta cewa sai ya tashi, ba abinda yake bawa umm mamaki sai yanda take maimaita kowa ya mutu ya barta sai shi kadai ya rage saboda haka ya tashi….
A bazata baby tee taji an janyota, juyowa tayi da sauri ya samu damar dora ta akan kirjinsa, da sauri ta dago tana kallonsa taga babu oxygen a hancinsa, tana surutu batasan ma ya farfado har ya cire ba, hannunsa yasa ya zagaye kugunta sannan ya rungumota sosai murya a dishashe kamar me mura yace;
“Why are you shouting baby girl”…
Dagowa ta sakeyi tana kallon idonsa da yake a rufe, a shagwape kamar zatayi kuka tace;
“Ba kaine inata cewa ka tashi kaki ba”….
“Kwantar da hankalinki gashi na tashi yanzu”….
“Toh ka bude ido ka ganni mana”..
“Ina ganinki ko a haka pretty, meyasa kikasa hospital gown, ko kema kin biyoni lahira ne?”…..
Zaro ido tayi tace;
“Kana nufin muna lahira ne ba duniya ba?”…..
“Eh mana”….
Ya fada har zuciyarsa dan tsakani da Allah ya dauka ya mutu….
Kokarin tashi tayi ya hanata, dole ta koma ta kwanta tace;
“Toh ina khaleel yake ance shima ya mutu yana lahira?”…..
“Dagaske?”…
“Eh”….
Hancinsa ya chusa a wuyarta a hankali yace;
“An daura muku aure kafin ya mutu?”….
Ture kanshi tayi tace;
“Bansani ba”…..
Tabe baki yayi yace;
“Ko an daura muku ya warware tinda munzo lahira, yanzu sai a mana wani ni dake”…..
Hankalinta ne ya tashi ganin fa dagaske maganar lahira yake tace;
“Ni wallahi ban mutu ba saidai in kai kadai ne ka mutu, gaba su umm a tsaye ba”…..
Dagowa yayi dan ya tabbatar da abinda take fada yaga umm da mami har dasu abby, dad da bappa duk sunyi cirko cirko a tsaye suna kallonsu…..

I am making this post due to so many requests, especially from my Facebook and Whatsapp fans, I have seen all your dms and calls and I’m extremely sorry for not replying and picking the calls as I’m so busy due to ramadan…..
Nifa da cewa nayi sai bayan ramadan zamu dora because I feel it’s odd reading novel during ramadan and yanzu anyi aure, ofcourse the upcoming chapters have to be spicy😉 lol😅…..
Well I want to know y’all suggestions in the comment section, mu tsaya anan immediately after sallah mu dora ko kuma muyi mu gama kafin sallah??…

 

Karanta>>> Wace Ce Ita (Who is she) Complete Novel

Back to top button