Hausa novels

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 82 Complete

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

 

Gaba ɗaya Aunty babba idonta bai hango mata su hosana ba,kutsa kai kawai takeyi cikin falon,hafsat dai tana la6e a bayanta,cike da fargaba,
Ƙarasawa sukayi wurinsu,daga bayansu Sehrish suka tsaya,hakan yasa bata samu damar ganin fuskokinsu ba,sai faman washe baki take yi,gaishe dasu Abba suka farayi,fuskar kowannansu awashe,”Ishaq shine baka sanar dani zuwansu ba,”acewar Abba,General ishaq yace”Ni kaina bansan sun karaso ba,nadaisan munyi dasu kan cewa zasu taho,”
Abusufyan yace”masha Allah hafsat ta girma sosai,ba don ina ganin hoton ta ba,da bazan iya gane ta ba,
Sunnar da kai ƙasa hafsat tayi tana murmushi ƙasa ƙasa,yayin da zuciyarta ke a cunkushe,
duk su hosana basu ɗauki muryarta ba,amma da zarar tayi magana sai sunji tamkar sun ta6a jin muryar matar dake magana,

Also Download>>> Mijin Malama Page 1 By Nimcy Sarauta

“Muna taya ka murna Abusufyan,ƴa’ƴa har ƴan uku Allah ya albarkaci rayuwarsu,Alla ya………’bata ƙarasa maganar ba sakamakon juyowar da sehrish tayi,Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu ji kake daram!!!dararam!!!yadda kasan ana buga ganga,Saboda tsabar kiɗima bata san lokacin da ta furta”Kutumar Uba….”gaba ɗaya hankalin kowa ya dawo kanta,jin ashar ɗin data buga,Hakan yasa Jahad da Hosana juyowa atare,Waro ido waje tayi hankalinta a matuƙar tashe,lokaci guda duk tabi ta gigice ta ruɗe ta rikice ta fita hayyacinta abunda batayi tsammani ba,la66anta har kerma sukeyi wurin nuna su da hannu tana ƙoƙarin tayi magana amma kermar da bakinta keyi ya hanata cewa komai,
Hankalin jahad ba ƙaramin tashi yayi ba,ganin matar da ta azabtar da rayuwarsu,ta ƙuntata masu ta kusa halakasu,hosana kuwa a matuƙar tsorace ta faɗa bayan Marshal Omar ta ƙanƙame shi tana faɗin”Ya Omar,bansan ganinta,tsoranta nake ji,itace matar da ta azabtar da rayuwarmu,itace tasa aje a jefar damu cikin daji,har wannan tsohon mutumin ya kusa cutar dani,don Allah ya Omar ku kureta,azzaluma ce macuciya ce,bata tsoran Allah,bata da tausayi kuma bata da Imani,
Hankalin kowa dake a wurin ya dawo kansu,gaba daya Abba dasu Abusufyan da sauran mutanen dake a wurin duk sun ruɗe sun gaza gane inda zancen nata ya dosa,Ishaq kuwa tun da yaga jikin Aunty babba na kerma,zufa na keto mata,ranshi ya bashi cewar tabbas ta aikata wani abu ne,saboda yasan halinta,muguwace kuma bata da gaskiya,Bashi ba hatta Marshal jikinshi yayi mugun sanyi,musamman da yaji hosana na fadin ta cutar da rayuwarsu nan ya fara tunanin Wasu abubuwa da yake zargi a lokacin baya,da kuma maganar da major ya ta6a sanar dashi na cewar baya son ya shiga tsakaninshi da matar Yayan shi,
hannu Aunty babba ta aza akanta tana faɗin”Shikenan An yanka ta tashi,amaimakon ta mutu,nashiga ukku ni laila,Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un wani tsautsayi ne da ƙaddara suka kawo ni gidan nan,’
Tunda Abbansu junaid yaji hakan yasan cewa tabbas akwai wani abu daya ta6a faruwa a tsakaninsu,koma dae menene bai kamata,su tuhumeta ba agaban ƙannen mijinta,a bainar jama’a kuma,ko ba komai Matar babban yayansu ce,
“Ya Omar dan Allah,tabar wurin nan wlh bansan ganinta,kashe mu take son yi,shiyasa ta biyo mu har nan,”gaba ɗaya kukan hosana ya cika kunnuwansu,’
Wani irin wahalallan yawu Aunty babba tazo haɗiyewa,nan take ta yanke jiki a wurin ta faɗi asume,da sauri hafsat ta tsugunna tare da tallabo ta,tana jijjjigata,

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

Gaba ɗaya duk sun kashe ma ishaq baki yama rasa abun cewa,tsananin baƙin ciki da takaici ya hanashi cewa uffan,jikinshi sae faman tsuma yake yi,burinshi kawai yaji abunda suka aikata ma yaran,da har suka tsorata da ganinsu,tabbas sai sunci Ubansu,muddin yaji wani da ba dai dai ba,don bazai yarda suja mashi tozarta ba a idon ƴan uwanshi,

Aunty Azmee ce ta taimaka wurin ɗebo ruwa suka yayyafa ma Aunty babba a fuskarta,ae tana farfaɗowa kamar wata zautacciya tayi zumbur ta miƙe,ko waiwayonsu ba tayi ba,ta watsa aguje,tayi cikin gidan,Allah kaɗae yasan inda ta kutsa kanta,

A fusace General ishaq zai bi bayanta,Abbansu junaid yayi saurin ruƙo hannunshi tare da cewa”kada ka bita,yakamata mubi komai a sannu,yanzu bamu kaɗai bane a wurin nan ba,akwai ƙannenka kuma akwai bare a wurin nan,”
Jinjina kanshi kawai yayi ba don ya haƙuri ba,
Batare da sanin kowa ba,hafsat ta zame jiki daga wurin,saboda wani irin mugun kallo da taga Daddynta nayi mata,bashi kaɗae ba hatta Marshal kallon tuhuma yake yi mata,hakan ne yasata ta sulale tabar wurin,sauƙinta ma basu ambaci sunanta ba,amma tasan dole sunanta ya fito aciki,kuma daddynta in ya tashi yanke hukunci hada ita zai haɗa ya yanke mawa,tabbas tayi dana sanin biye ma mahaifiyarta wurin cutar dasu hosana,gayanan sunja ma kansu,
Ruƙo hannun hosana yayi tare da janyota,ta dawo ta gabanshi,fuskarnan tayi jawur,sae faman kuka takeyi tana faɗin”ya Omar a koreta tabar gidan nan,bana son ganinta,bata da Imani,itace ta rufe mu acikin store tayi mana horon yunwa,ta dinga bugunmu da bulala,kuma ta dinga samu aiki,har gadon asibiti sai da aka kwantar dani…….’
Cikin sauri Omar ya sanya tafin hannunshi ya toshe mata baki,cikin lallashi yace”its ok hosana,na fahimce ki,zansa sojoji su koreta daga gidan nan hakan yayi maki,”
ɗaga mashi kai tayi alamar eh,sannan yace”kada na sake jin kukan ki to,ya isa haka,kalli fa ki gani duk kin 6ata kwalliyarki da hawaye,”
Curo handkerchief Abusufyan yayi daga gaban aljihunsa,ya ruƙo hosana,tare da sanyashi a fuskarta yana goge mata hawayenta,”Daddy matar can bata da Imani ko kaɗan,taso ta kashe ni,dan Allah ku sakar mata karnuka su rakata bakin gate,tabar gidan nan,”
Muryar abusufyan tamkar zaiyi kuka yace”Kiyi haƙuri kinji hosanata,zansa a koreta kamar yadda kikeso,amma yanzu kiyi shiru da bakinki,ki daina magana,banason ganin hawayenki,”
“Daddy bakasan yadda nakeji bane,zuciyata tafarfasa takeyi,raɗaɗi takeyi mun kamar ana rura garwashin wuta acikinta,wlh daddy waccen matar bazata ga Manzon Allah ba,sai ta shiga wuta,’
Hankali atashe Marshal ya daka mata tsawa har saida ta dawo cikin hayyacinta,fuskarshi a daure yace”kar na sake jin kince uffan a wurin nan,surutun ya isa haka!banace za’a kore ta ba,”
Saboda tsoratar da tayi da tsawar da yayi mata ne yasa ta faɗa jikin daddyn nasu ta ƙankameshi,tana faman sauke ajiyar zuciya,’
jikin kowa yayi sanyi,musamman Ishaq,bawan Allah duk yabi ya takure kansa,idanunshi sunyi jawur saboda tsabar 6acin rai,
Abba ne yayi ƙoƙari wurin dawo dasu daidai daga yanayin da suka shiga,daƙyar aka samu hosana ta zauna itama amma duk da haka tana yawan firgita wannan ya ƙara tabbatar masu da cewa ba ƙaramin Abu Aunty laila ta aikata masu ba,wuri kowa ya samu ya zauna agaban table ɗin dake a wurin wanda ke shaqe da abinci kala kala,nan fa kowa ya shiga bama cikinsa abinci,jikin Sehrish ba ƙaramin sanyi yayi ba,saboda ta gane dalilin dayasa su jahad suka tsorata da ganin matar,wato itace matar da Omar ya kaisu gidanta,wadda ta azabtar da rayuwarsu,kamar yadda jahad ta bata labarinta,kowa ya lura da yanayin yaran,sun kasa sakewa suci abinci sosai,ƙarshe sai dae Abusufyan ya dinga binsu one by one yana sanya masu abinci abakinsu suna ci,a haka har ya samu suka ci sosai,bayan sun kammala cin abincin,Junaid ya ɗaukko Camera ɗinsa,nan fa aka shiga ɗaukar hotuna,abun gwanin burgewa,Happy family,kowa sai da ya fito Hajiya azeema,su gwaggon katsina Saude,Dr harris,hatta ƴan matan da hajiya sarah tazo dasu,sae da suka fito akayi masu hotuna,mutun uku ne kawai babu a wurin Ammi wadda kowa ke fargabar fitowarta,bayan ita sae Haroon wanda ke ƙumshe acikin ɗakinsa,Sgr kuwa baya cikin gidan,tun wuraren ƙarfe uku yabar gidan,

Also Download Dr Eeshatt Romantic Hausa Novel Complete Document

Anyi masu hoto tare da mahaifinsu sun sanyashi atsakiya,sae wanda akayi masu tare da Abbansu junaid tare dashi kanshi junaid ɗin,kowa saida yayi hoto tare dasu,hatta Su twins da fawan dasu irfan,kowannansu sae da yayi hoto dasu,sun sha hotuna ba ƙadan ba,

Basu suka kammala ba sae wuraren sallar magrib,sannan kowa ya shige ciki domin yin alwala,

Kamar jira jahad takeyi su shiga ɗaki ta rufe hosana da faɗa,tamkar zata bugeta,”Sai yanzu na tabbatar da cewar ke cikakkar zararriyace baki da hankali,meyasa ba zakiyi shiru da bakin ki ba?don me zaki tona mata asiri agaban mutane”?
Fashewa da kuka hosana tayi tana faɗin”kada ki ƙara cemun zararriya,kuma naje na tona mata asirin,Ni bazan ta6a yafe mata ba wlh,kamar yadda ta cutar da rayuwarmu itama sai ta fuskanci sakamakon abunda ta aikata mana,’
“Hosana,karna sake jin kin tada wannan maganar,idan ba so kike ranki ya 6aci ba,”
“Wlh saina faɗima Daddy da Abba,kuma saina faɗa ma yaya Omar,sai dai duk abunda zai faru ya faru,’
rai a6ace tayi maganar,cakumar rigarta jahad tayi,tare da yin wurgi da ita,ta faɗa saman gadon tana kuka,fitowa Sehrish tayi daga cikin toilet,ganin jahad na ƙoƙarin bugun hosana yasa tayi saurin zuwa tare da ruƙo hannunta”karki kuskura kice zaki hukunta hosana!abunda tayi dai dai ne,koda ace ita bata faɗa masu ba,to ni saina faɗa masu abunda waccan matar ta aikata maku,saboda bata da Imani,muguwace ita,muddin akace za’a cigaba da yafe ma mutane irinta to tabbas bazasu ta6a canza halinsu ba!Suna buƙatar a ladabtar dasu,a hukuntasu,idan suka aikata ba dai dai ba,Ni hakan da hosana tayi ta burgeni,!”
Shiru jahad tayi,ta wani 6angaren zancen sehrish gaskiya ne,muddin ba’a ɗauki mataki ba akanta taga an ƙyaleta to tabbas bazata ta6a canzawa ba,amma yanzu idan suka hukunta ta dole nan gaba taji shakkar ƙara yin irin kuskuren da tayi abaya,

“Kin faɗi gaskiya sehrish,ni banyi tunanin hakan ba,kuma koda nake yi ma hosana faɗa,saboda 6arin zancen da tayi ne agaban mutane,bai kamata ta yi magana akan idon kowa ba,in ma faɗin ne Ya Omar yakamata ta sanar mawa,sae su yanke mata hukuncin da suka ga ya dace da ita,”
Ta ƙarasa maganar tare da ɗauke idonta daga kan sehrish ta mayar dasu kan hosana dake baje saman gadon tana kuka,nan take taji bata kyauta mata ba,hawa saman gadon tayi tare da janyota jikinta,tana lallashinta,daƙyar ta samu tayi shiru,daga bisani suka tashi domin yin sallar magrib,

*Aunty Babba*

Tunda ta watsa a gujen nan,ɗakin hayaam ta faɗa,jikinta sae faman rawa yakeyi,zagaye tashiga yi a ɗakin tana tunanin hanyar da zata bi ta gudu daga cikin gidan tun kafin ishaq ya waiwayeta,tsoranta karya bata takardar saki,don bata shirya yin zawarci ba,hannu ta aza aka tana fadin”Nashiga uku ni laila,na jama kaina masifa da bala’e,Ina zan tsoma raina inji daɗi,”tana cikin zancen zucin nan,hafsat ta shigo ɗakin,kamar jira takeyi nan ta shiga balbaleta da faɗa ta inda take shiga bata nan take fita ba,
“Don ubanki ki faɗa mun taya akai yaran nan suka rayu!nasan kinsan komai munafuka algunguma!”hafsat na ƙokarin buɗe baki,Aunty babba takai mata naushi a kumatunta,har sai da le6enta ya ɗan fashe,idonta jawur ta ɗago tare da kallon Mommyn nata idanunta cike taf da hawaye tace”Mommy!ni kika buga saboda zunubin da bani na aikata ba?
A faɗace Aunty babba tace”Zanci ubanki ko ki rufe mun baki,wlh hafsat kin cuce ni!Allah ya isa tsakanina dake!ae kinsan da zaman yaran nan acikin gidan nan, shiyasa don munafunci kika sanyo nikabi uban meyasa baki sanar dani ba tuntuni don inyi takaina!Kece kika tseratar dasu daga hannun baba alamu,in ba haka ba taya akai har suka kawo kansu cikin gidan nan”!?
Girgiza kai hafsat ta shiga yi yayin da idanunta ke fitar da wasu irin hawaye masu ɗumi,cikin shessheƙar kuka tace”banta6a dana sanin kasancewarki mahaifiyata ba sai yau!Kin jefani acikin masifa kin kuma zo kina neman ƙala mun sharrin cewa ni na tseratar dasu daga hannunshi,wlh Mommy bakiyi ba!duk wasu magayen ɗabi’u da halayen dana ɗauko naki ne,baki ta6a cemun nayi badai dai ba,baki bani tarbiya mai kyau ba,kullum gur6atamun tunani na kikeyi,saboda kar in dauko halayyar mahaifina,Ni banta6a ganin uwa irinki ba,Yanzu gashi nan daga ni harke wa gari ya waya?kuma inaso ki sani mommy,Ni bansan komai agame dasu hosana ba,bansan ya akai suka dawo hannun Ya Omar ba,Na faɗa maki hakan ne ba don ina jin tsoranki ba,sai don kisan cewar Bani na aikata hakan ba,Allah ne Ya Kamaki,ba yadda banyi ba don ki kyale yaran nan karki salwantar da rayuwarsu kika ki,kuma ni ce da hannuna na goge hotunan da hayaam ta tura maki a wayarki,saboda nafi son ki tako da ƙafafunki don ki gir6i abunda kika shuka……”

Also Download Wace ce ita (Who was she) Hausa Novel Complete Document

..saboda tsabar tsuma jikinta har kerma yakeyi,shaƙo wuyan rigar hafsat tayi da ƙarfin gaske,gadan gadan kasheta zatayi,kiciniyar kwace wa hafsat tashiga yi,suna cikin wannan halin,Amani da hayaam suka faɗo cikin ɗakin da gudun gaske sukayi kansu,daƙyar suka kwaci hafsat daga hannun Aunty babba,dafe maƙoshinta tayi tana faman yarfa hannu tana ambaton”ruwa!ruwa’
Da sauri hayaam ta fita waje,sai gata ta dawo da bottle water a hannunta mai sanyi,miƙa ma Hafsat ruwan tayi,jiki na rawa ta cire marfin robar tare da yin wurgi dashi,ta kafa robar abakinta tana kwankwaɗar ruwan,hayaam ce ta zauna a wurinta,tana lallashinta,
Rai amatuƙar 6ace tashiga fadin”ae da kun barni na kasheta don ubanta,wlh hafsat baƙin cikinki bazai ta6a kashe ni ba,Muguwa kawai,nafi kowa dana sanin haihuwarki,Ni ina kokwanton cewar Anya ba’a asibiti akayimun musanyarki ba,”
Fashewa da dariya Amani tayi tana tafa hannayenta,
Nan take Aunty babba ta ɗaure fuska,tana jifarta da harara,
Tsagaitawa tayi daga yin dariyar da takeyi masu sannan tace”Wannan abun daya faru nafi kowa farin cikinsa,tamkar na zuba ruwa a ƙasa na sha,”
“Amani baki da hankaline?kinsan me kike faɗi kuwa?wannan abun fa ya shafi kowannanmu,bai kamata ki dinga yi mana dariya ba,”Acewar Aunty babba,
wurga mata harara amani tayi tare da cewa”yadai shafe ku!karki kuskura ki ƙara mentioning ɗina aciki,domin kuwa bansan anyi ba,lokacin da kuka tsara muguntarku kuka cutar dasu,kunyi shawara dani ne?Kuma ae har shawara saida na baki akan ki daina azabtar da yaran amma kika ƙi ji ke ga shugabar azzalumai,wlh baku da imani zuciyarku ta bushe,kwakwalwarku a toshe take,tamkar ana zuba maku dussa acikin kawunanku saboda ɗabi’unku sak irin na kafuran farko ne,…..”
Waro ido waje Aunty babba tayi tare da faɗin”Ni kike faɗama wannan maganar!”
Amani tace”Kwarai kuwa dake nake,Muguwa macuciya kuma Azzaluma,zuciyarku ta ƙeƙashe Zalunci kawai kuka sa agaba,daku da uwarku Mammy,tsohuwar banza me shegen son kuɗin tsiya,wlh kunji haushin rayuwarku,shegen kwaɗayin abun duniya,ga baƙar zuciya,ga dogon burin tsiya ko tsoran mutuwa bakwayi…”
Tunkan amani ta ƙarasa maganar Aunty babba ta kwashe ta da tagwayen maruka,ji kake tasss tatasss!’kafin Aunty babba ta janye hannunta daga kan kuncin Amani,itama ta daddage da iya ƙarfinta na ƙarshe ta kikkifa mata maruka a jere kusan uku ji kake fass tasss taaasss!
dafe kumatu aunty babba tayi yayin da idanunta sukayi jawur,tunda take arayuwarta ba’a ta6a yi mata irin marin da Amani tayi mata ba,hasalima Amani shakkarta take ji,amma sai gashi yau ta cire yatsunta guda biyar cuf,ta kikkifa mata maruka,
Koda ganin haka,sae hayaam ta miƙe tare da ɗaga hannu zata sharara ma Amani mari,aikuwa hafsat ta yunkura tare da miƙewa ta damƙo hannun hayaam tana faɗin”baki da hankaline?matar da ta iya ɗaga hannu ta mari mommy har sau uku,itace zaki mara?kina tunanin cewa zaki iya rama mata ne,” dariya Amani tayi tare da cewa”ki barta inga ƙarshen rashin kunya,wlh dai dai nake da kowane shege acikin ku,Bana jin tsoranku a yanzu,tun ranar da Amal ta sanar dani komai game da ukubar da kukeyi mata tun daga ranar na ɗaura ɗamarar yin yaƙi daku,”
Hankali tashe hayaam da aunty babba suka kalli juna jin ta ambaci sunan Amal,
Hafsat ce tace”Amal na wurinki ne”!?
Jinjina kai amani tayi tare da cewa”Amal tana wurina!itace yarinyar dana zo da ita cikin gidan nan,kun so ku kashe mun ƙanwata,Amma Allah bai baku nasara akanta ba,Amal ta tako da ƙafafunta ta kawo kanta har cikin garin nan,”
Shiru duk sukayi suna sauraronta,
“Haƙƙin Amal kaɗai ya isa ya jefa rayuwarku cikin masifa,laifin me Amal tayi maku da har kuka wulaƙantar da rayuwarta?yarinya ƴar ƙanƙanuwa amma kukayi mata taron dangi wurin azabtar da ita,saboda tsabar mugunta irin taku,ƙiri ƙiri kuka hanani ganin Amal,ku ka yi mun ƙaryar cewar Amal ta 6ace ba’a ganta ba,mugaye kawai ashe gidan makwabtanmu kuke kaita kuna rufeta,duk in nazo har in bar garin,tana can arufe kamar akuya,ko abinci ma baku bata,wai ku wasu irin mutanene?wace irin zuciya gare ku…?
Kasa ƙarasa maganar Amani tayi saboda kukan daya ciyota,nan take ta fashe da wani irin matsanancin kuka,ba ita kaɗae bama hatta hafsat sai da ta zubar mata da kwalla,baƙin ciki kamar ta binne kanta,abun kunyar da mommynta ta aikata ba ƙaramin illa yayi ma zuciyarta ba,

Karanta>>> Matsi Ga Sabbin Amare Kafin Kije Gidan Miji.

Hayaam kuwa sae faman mazurai takeyi ita da aunty babba sunyi wuƙi wuƙi,basu da abun cewa,dama ance rana dubu ta 6arawo,rana ɗaya ta me kaya,
“Wlh kaɗan kuka fara gani!haƙƙin Amal da kuma haƙƙin waɗannan bayin Allahn da kuka cutar bazai ta6a barinku ku zauna lafiya ba,in har ba zaku canza waɗannan munanan ɗabi’un naku ba,mugunta da kwaɗayin abun duniya,dogon buri,rayuwar ƙarya,duk ku kadae gashi har yau Allah bai ta6a baku nasara ba,mutumin da bai ta6a sa Allah alamurransa ba taya zaiga dai dai”?
Tsoki Aunty babba ta buga tare da nuna mata hanyar fita daga ɗakin tace”zo ki fuce ki bamu wuri tun kafin ranki ya 6aci a wurin nan!shashasha kawai kina tunanin cewa kalamanki zasu iya tankwarani ne?duk duniya ba ayi mutumin da zai zauna yanayi mun nasiha ba,wlh ba ayi shi ba,”
Girgiza kai amani tayi tare da juyawa a fusace tabar ɗakin tana faɗin”Jiki magayi,”

Komawa Aunty babba tayi yaraf ta zauna gefen gadon tana faman cizon yatsa,miƙewa hafsat tayi tare da fucewa daga ɗakin,
Fitar ta keda wuya,Hayaam ta dawo gefen aunty babba ta zauna tana faɗin”Yanzu menene mafita”?
..fuskarta a hargitse tace”mafita ta wuce mu gudu salin alin batare da sanin kowa ba,”
“Saboda me zamu gudu?hakan na nufin cewa sun ci nasara akanmu kenan”?
“Hayaam ba zaki gane ba,ina tsoran in sake yin arba da hosana ne,bata da hankali,zata ci gaba da tona mun asirine a bainar jama’a”
“Amma Aunty laila,taya akai yaran suka zauna a wurinki har hakan ya faru?meyasa baki kashesu ba tun lokacin”?
Guntun tsoki taja tare da kawar da kanta gefe cike da takaici tace”sai yanzu nake danasanin barinsu araye,meyasa ban kashesu ba tun lokacin da suke a wurina ba?wancan shashashan mutumin dana bama aikin zubar mun dasu a daji bansan ya akai yayi sakacin da har suka ku6uta daga hannunshi ba,kuma tun ranar dana bashi su nake ta jaraba kiran wayarshi akashe kullum har na gaji na daina kira,duk shi ya kwafsamin wlh,yanzu yawo acikin gidan nan ma ya haramta agareni,Allah yaso Hafsat ta siya niqabi a kasuwa,zan kar6e shine in sanya a fuskata saboda gudun kar waccen mai ta6in hankalin cikin sun ta ganni…..’
Shiru suka ɗanyi na wani lokaci,zurfin tunani ta shiga yi kwatsam ta tuna da maganar nan da hajjaju ta ta6a sanar da ita kwanakin baya can da suka wuce lokacin su hosana na a gidan,
“Idan kin toshe waɗannan hanyoyin,ita kuma waccen ɗayar hanyar da ta riga isa inda baki so fa ya zakiyi da ita’
Jinjina kai Aunty babba tayi tare da faɗin”Allah ya isa tsakanina da hajjaju,sarai tasan komai game da rayuwar yaran nan amma taƙi sanar dani,babu yadda banyi da ita ba,amma taƙiya saboda tsabar baƙin hali irin nata,da tun farko ta sanar dani cewa ƴan ukune yaran akwai ɗaya dake aiki a gidan da tuni nasan abunyi,

wannan masifar har ina”?

“Amma kina ganin Ammi zata barsu ne acikin gidan nan?Jiya munyi plan ɗin cewa zaki kirata a waya ki sanar da ita cewa yaran shaggu ne,kin sanar da ita hakan,” ta ƙarasa maganar tana kallon fuskar aunty babba wadda ke a hargitse,jin maganar hayaam yasa ta ɗan jinkirta,kamar me nazarin wani abu can ta ɗan washe baki tare da cewa”Hakane!Wannan ita kaɗae ce hanyar da ta rage mun,jiya na kira ammi a waya kuma na sanar da ita cewar Abusufyan ne ya ta6a yi ma wata fyaɗe harta samu ciki ta haifesu,ina da tabbacin cewar AMMI bazata barsu su zauna ba,dole ta koresu ƴan jakar uban,wlh na tsani yaran can,na tsani mahaifinsu duk shine silar komai,ya tashi yayi aure batare da sanin kowa ba,gayanan ya jefa mu acikin masifa,ni duk bama wannan ba,taya akai AMAL ta gudo daga gida tazo Abuja wurin waccen baƙar munafukar?ta ya akai Mammy da Abrah su kayi gangancin da har AMAL ta gudu daga gida ta dawo wurin Amani?
Hayaam tace”Nima abunda nake tunani kenan,don ko aranar da zan bar gidan Amal na ƙunƙume aɗakinmu,zazza6i ya rufeta,Ni babban baƙin cikina ma,muna nan sake da baki,Amal na iya zuwa ta aure wani daga cikin matasan gidan,kinga ae shikenan mukuma tamu ta ƙare,maƙiyanmu za suyi ta cin nasara akan mu,’

Karanta>>> Ga Masu Neman Karin Kiba Ga Hanyar Da Zaku Bi

“Insha Allah hakan ma bazata faru ba,in har ɗaya daga cikinku ke da abra bai auri ɗaya daga cikin matasan gidan ba,to sai dai ayi Ragas,Uban kowa ya rasa,itama Amal ɗin tarasa,ita kuma waccen ƴar iskar sai nayi silar mutuwan aurenta,tunda har ta iya ɗaga hannu ta kikkifamun mari,wlh saita gane kuranta,kuma wlh billahil azeemu,muddin Ishaq ya sake ni,itama sai Abbas ya sake ta,inyaso sai muyi zawarcin atare,”ta ƙarasa maganar tana faman sakin huci,tayi danasanin zuwanta gidannan!

*Boss Bature*

❤🤍❤

turo ƙofar ɗakin da ammi ta sauka akayi,Azmee ce ta shigo hannunta ɗauke da kakkauran tea ɗin data haɗa mata,a zaune ta same ta saman darduma jikinta sanye da hijabi,yayin da hannunta ke ruƙe da cazbaha,da alama sallah ta kammala yi,
Cike da girmamawa azmee ta ƙarasa tare da zuƙunnawa ta gaishe ta,”Ina yini Ammi,ya gajiyar tafiya,”
da buɗar bakinta sae cewa tayi”Ina Abusufyan yake”?
Azmee tace”sun fita sallar magrib,amma nasan yanzu suna kan hanyar dawowa gida,nan bada jimawa ba nasan zasu shigo ciki,”
Jinjina kai tayi tare da kai hannu ta ɗauki cup ɗin da azmee ta miƙa mata,abaki takai cup din ta kur6e sa kusan sau uku sannan tace”Idan sun dawo,kice su jira ni a palour gaba ɗayansu,inason ganinsu,”
Tuni Azmee tasha jinin jikinta,aranta tace”tashin hankali,’a fili kuma tayi saurin cewa”Za’a sanar masu,”sannan ta mike ta kama hanyar fita daga ɗakin,har azmee ta ruƙe handle din ƙopar zata fita,muryar Ammi ta katse mata hanzarinta da cewa”Next time idan zaki haɗamun tea,bana son sugar yayi yawa,sannan madarar tafi bornvitan yawa,da fatan za’a kiyaye,’
“insha Allah za’a kiyaye,ko akwai wani abu da kike buƙata”?
“Idan ina buƙata zan sanar dake ne,basai kin tambaye ni ba,zaki iya tafiya,”
jinjina kai azmee tayi kafin ta buɗe kopar ɗakin ta fuce,babban falo ta nufa tana tafiya tana jinjina wa izza irin ta Ammi,saboda tsabar masifa,ko bornvita azmee bata zuba a tea din ba,madara kawai ta sanya mata amma saboda hali irin na ammi,da ba’a iya yi mata gwaninta,ta buga warning akan madara tafi bornvita yawa,ko ta ina taga bornvitan”?akan tea ma tayi ƙorafin anyi ba dai dai ba,inaga In taji abunda Abusufyan ya aikata batare da saninta ba,tabbas akwai matsala,rayuwarsu sehrish tana cikin garari,don wannan guyababbiyar matar bazata barsu su zauna lafiya ba,acikin gidan nan,
Jin sautin muryoyinsu,yasa Azmee dawowa daga zurfin tunanin da ta shiga,dawowarsu kenan daga masallaci kowa bakin shi ɗauke da sallama suka shigo cikin Main palour din,Abba ne tare da Abusufyan sae junaid atare,bayansu kuma su Abbas ne da ishaq,Mg Osman da kuma Captain Adam,sai kanal yousouf da kuma Marshal wanda ke tare da Dr harris,a bayansu kuma akwai Fawan,twins,jabeer,irfan,khaleed dukansu dai suka shigo ciki,
ƙarasawa Azmee tayi wurinsu tanayi masu sannu da dawowa,daga bisani ta isar masu da saƙon ammi,nan fa kowa ya shiga fargabar dalilin tarasu da Ammi tace ayi,musamman Abusufyan yafi kowa shiga damuwa,tsayawa su kayi a tsaye kowa yana ta zullumin fitowarta,Abba dae sai ƙarfafa ma abusufyan gwiwa yake,akan ya jure,kada tsoro ya hanashi yi ma Ammi bayanin komai yadda zata fahimta,
Jin takun takalminta kwas kwas!yasa su yin saurin kai idanunsu akanta,fuskarta na manne da farin glass,kwata kwata babu annuri a fuskarta,yayin da hannunta ke ruƙe da sandar nan ta alfarma,Ƙarasowa tayi tare da samun wuri ta zauna saman 3 seater,sannan ta aza ƙafarta ɗaya bisa ɗaya,tare da kallonsu tace”Ku zauna,”

Karanta>>> Hanyoyin Da Ya Kamata Matan Aure Subi Domin Kara Inganta Zaman Aurensu: Malama Juwairiyya

A ƙasa su fawan suka zauna,yayin da Abbansu junaid,da abusufyan suka zauna asaman ɗayar 3 seater ɗin,ishaq da abbas suka zauna asaman 2 seater,Dr harris da Omar suka zauna a ɗayar 2 seater,dama 2 set ne na sofa a babban falon,manyan ne suka zauna saman kujerun,yayin da ƙananan daga kan Kanal yousouf suka zauna aƙasa,
Tsit falon yayi na wani lokaci,kai kace mutuwa ce ta gifta,ko motsin mutun bakaji a wurin,kowa ya kame kanshi,
ɗaya bayan ɗaya Ammi ta dinga binsu da kallo,kowa sae faman noƙe kai yake,shi dai abusufyan ya gaza sakewa,don ko idonshi bai ɗago ya kalle taba,
ɗaga sandar hannunta tayi tare da nuna Ayan tace”wannan dogon gashin fa?sai kace wani ɗan daudu meyasa baka aske shi ba?
cikin sauri Ayan yace”ƙuraje ne ke fitomun akaina duk in nayi yunƙurin aske gashin”
Ta6e la66anta tayi,kafin ta janye idonta daga kan Ayaan ta mayar dasu kan fawan,sunnar da kai ƙasa yayi yana ƴan kame kame,
“Ƴa’ƴan fatima kenan,ba zaku ta6a canzawa ba,yadda kasan sun haɗa jinsi da ibliss,ji bi ɗan iskan askin dake akanshi,hada kala ma ka canza mashi kaiga ƙeƙasasshe ko”?
Fawan akeyi ma faɗan Amma Abbansu ne ke jin maganar har cikin zuciyarshi,bakomai ya ɗan 6ata mashi rai ba,sai kalmar data faɗi na cewar kamar sun haɗa jinsi da iblis,abun ya tsaya mashi arai,jurewa kawai yakeyi,
ɗaya bayan ɗaya haka ta dinga sharrance su,har sai da tazo kan junaid wanda keta faman sakin murmushi kamar wani zautacce,
“Iko sai Allah!kai zonan,”da sandar hannunta tayi mashi nuni da yazo,miƙewa junaid yayi ya koma ƙasan kujerar da take ya zauna,hannu tasa tare da jan kunnanshi tace”Bakasan nazo bane?kowa na zuwa ya gaishe ni,amma banda kai,Abbanku ya sangarta ka ko?shiyasa ka fara jin kanka wani shege,”dafe hannunta yayi yana dariya yace”Ammi dan Allah ki sakarmin kunne na,Da zafi fa,Abba kana gani ko,”?
“Me Abban naku zai iya yimun bakasan cewa ni na tsugunna na haifesa ba,”
Zumbura mata baki junaid yayi tare da murguɗa mata baki,
“Fiye da haka ma zaka iya yimun tunda ubanka ya ɗaure maka mazauni,dole ka murguɗamun baki,ae bazan bar gidan nan ba,sae nasa an tura ka aikin soja,sannan hankalina zai kwanta,”
Bubbuga ƙafa junaid ya shigayi yana yi mata ƙunƙuni,hakan ba ƙaramin dariya yaso ya bata ba,amma bata bayyana hakan akan fuskarta ba,”
Shiru ta ɗanyi na wani lokacin kafin tace”kai irfan,tashi ka kiramun gwaggonku,tare da Auntynku Azeema inason ganinsu,”cikin sauri irfan ya miƙe tare da barin wurin ya wuce ɗakinsu gwaggo,
Bada jimawa ba,sae gashi ya dawo tare da gwaggo da hajiya azeema abayan shi,duk wannan surutun na gwaggon katsina,yau tsit kake jin bakinta,sae faman wurga ido take,wuri suka samu suka zauna,a saman sofas ɗin dake cin mutun ɗaya,
Bayan kowannansu ya natsu,Ammi ta tsayar da idanunta akan Abusufyan,wanda tunda suka zauna a falon,bai ɗago ya kalleta ba,
gyaran murya ta ɗan yi tare da ambaton sunanshi”Abusufyan”a firgice ya ɗago yana kallonta,bawan Allah harya fara haɗa gumi,ga yatsun hannunshi dake ta kerma,duk wasu alamu na rashin gaskiya sun bayyana a tattare dashi,Abba sai tausarshi yakeyi yana faɗin”ka kwantar da hankalinka,ka natsu dan Allah,duk kabi ka firgice,hakan ma zaisa taƙi yadda da hujjojin da zamu bata,”ƙasa ƙasa yake yi mashi maganar don karta ji shi,
ɗakyar Abusufyan ya iya amsa kiran da tayi mashi”Na’am Mommy,”
“Meyasa kabar ƙasar nan,batare da ka sanar mun ba?laifin me na aikata maka da har kake gudu na?sai kace bani na haifeka ba?bansan me ka ɗaukeni ba,’
muryarshi na rawa yace”Kiyi haƙuri Ammi,Nima bada son raina na tafi na bar ƙasar nan ba,nasan ni mai laifine a wurinki,ki yafe mun….’saukowa yayi daga saman sofa ɗin ya dawo ƙasa ya zuƙunna yana bata haƙuri,
“idan har dagaske kasan cewar kai mai laifine,meyasa da ka dawo Nigeria bakazo gida ka same ni ba,don ka nemi yafiyata ba”?
Shiru yayi yayin da idanunshi ke cike tab da kwalla,gaba ɗaya ya rasa inda zai tsoma ranshi,babbar damuwarshi shine,yadda zai fara yi mata zancensu sehrish,

Karanta>>> Domin Dawo Da Martabar Nonuwanki Cikin Sauki.

..hmmmm ta furta sautin tare da mayar da idanunta kan gwaggon katsina tace”Saboda yardar da nayi dake ne yasa na ɗamƙa maki Amanarshi,don ki ladabtar mun dashi,a tunanina zaki canzamin shi,ashe bansan nayi aikin banza ba,”
ɗaure fuska gwaggon katsina tayi,alamar ranta ya 6aci,
“Ammi dan Allah komai ya wuce,just forget about the past,haba dan Allah,komai ya wuce mana,taya za’a zauna ana ta faman nanata abunda ya riga ya faru.,.,..”
Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba,jin abunda Jahan ke cewa,yadda kasan wanda yasha giya haka ya shiga sambatu yana faman jan guntun tsoki ƙasa kasa,yunƙurawa Marshal yayi da nufin ya buge masa baki,Ammi ta dakatar dashi”basshi ya ƙarasa,ba laifinsa bane,gado yayi wurin Uwarsa,ae ni bansan yaushe ne ƴa’ƴan fatima zasu fara girmamani ba,amatsayina na wadda ta haifi ubansu,”
Rai a6ace jahan ya miƙe zai bar wurin Abbansu ya daka mashi tsawa tare da korosa yace”Koma ka zauna,Allah yasa inga ka ƙara cewa uffan a wurin nan,”
Komawa yayi gefen ayaan ya zauna yana faman hura hanci,
Jinjina kai Ammi tayi tana kallonshi tace”Nan gaba fa,in ban bi asannu ba,bugu yaran nan zasu fara kaimun,To Allah ya kyauta gaba,”
Abba yace’Insha Allah hakan ma bazata ta6a faruwa ba”
Shidai abusufyan har lokacin yana zuƙunne asaman guiwowinsa,cike da zullumin me zai biyo baya,
“Uncle ka tashi ka koma ka zauna,jikinka sai kerma yakeyi,Ammi fa ba abunda zata iyayi maka,”Sakin baki abbansu yayi yana kallon junaid dake magana,yana ƙoƙarin kashe wutar da jahan ke ƙoƙarin kunnawa shi kuma zai hura wata wutar,
Girgiza kai Ammi tayi tare da wurga ma Abbansu harara tace”Bazan iya zama agidan nan ba,yaranka sunfi ƙarfina,”sunnar da kai ƙasa abba yayi kafin ya ɗago yana kallon junaid da yayi maganar ya ɗan jefa mashi harara,
Suna cikin wannan Zaman sai ga hosana ta shigo cikin falon,tana neman warin ɗan kunnanta daya faɗi,’tashin hankali,gaba ɗaya hankalin kowa ya koma kanta,abusufyan kuwa arazane ya ɗago yana kallonta,ammi duk bata lura da ita ba har sai da Hosana ta buɗe baki tayi magana”Daddy ɗan kunnena ya faɗi a falon nan ban ganshi ba,’juyawa ammi tayi tare da kai idanunta kan hosana dake tsaye tana magana,a wani slow ta sanya hannu ta zame glass ɗin dake a fuskarta,tashiga ƙare ma hosana kallo,cike da mamaki tace”Ina kuka samu matashiyar yarinya acikin gidan nan”?sunnar da kai ƙasa Abusufyan yayi yana faman zare ido zuciyarshi tamkar zata faso kirjinshi ta fito saboda razana,
Shiru kowa yayi mata aka rasa wanda zai buɗe baki ya bata amsa,
Jin sunyi banza da ita yasa ta kira hosana da hannunta”Zo nan,”
Shiga ciki hosana tayi tare da tsayawa agaban Ammi tace”Gani,”
“Wanene mahaifinki a wurin nan”tayi maganar tana nunasu da sandar hannunta,
…murmushi hosana ta saki tare da ɗaga yatsan hannunta ta nuna abusufyan sannan tace”Gashi nan,shine daddynmu,ni dasu Sehrish da Jahad,”
..a wayance Ammi tace”Oh harku nawa ne a wurinshi”?
Hosana tace”Ƴan ukune mu,ko in kira maki su jahad ki gansu?”
Cike da mamaki Ammi tace”kira mun su in gansu,”da gudu hosana ta nufi ɗakinsu don ta kira su jahad,
Tashin hankali,
Wani irin gumi ne ya shiga fesowa daga jikin abusufyan,gaba ɗaya duk yabi ya kama kansa,jikinshi sae faman kerma yakeyi,bashi kaɗae ba hatta sauran dake a wurin zaune,kowa saida yasha jinin jikinsa,musamman Kallon da Ammi ta dinga binsu dashi ɗaya bayan ɗaya,kallon tuhuma,
Lokacin da hosana ta faɗa corridor ɗin ɗakunansu,hayaam na tsaye a wurin,tana ganinta tasha gabanta tare da cewa”daga ina kike”?
Murguɗa mata baki hosana tayi kafin tace”Ni bansan wacece keba,ki bani hanya in wuce,su jahad zan kira,wata tsohuwa ce fara tass take son ganinsu,”
Jin haka yasa hayaam ta gane cewa cewa AMMI ce ke son ganinsu,shu’umin murmushin nan nata tasaki,kafin ta matsa ma hosana hanya ta wuce,jinjina kai hayaam tayi tana faɗin”hada wani zumuɗin Ammi ta kirasu,basu son cewa watan korarsu daga gidan yayi ba,”tana ƙarasa maganar ta nufi ɗakin da Aunty babba take,tana shiga ta sanar da ita cewar ga Ammi can tasa a kira mata ƴa’ƴan Abusufyan,jiki na rawa Aunty babba ta taso,suka fito daga ɗakin domin suje yin la6e,don su ga irin korar karen da ammi zatasa ayi ma su Sehrish,

Karanta>>> Yadda Zaki Hada Sabulun Da Zai Sa Ki Dinga Kyalli, Santsi, Kamshi Da Kuma Maganin Kuraje

Bada jimawa ba,Hosana ta fito hannunta ruƙe dana sehrish,ɗayan hannun kuma ruƙe da hannun Jahad,jikinsu na sanye da hijab don tunda su kayi sallar Magrib basu ciresu ba,hosana ce kawai ta cire hijabin jikinta,ta yafa mayafi akanta,

da sallama a bakunansu suka shigo cikin falon,ya salam ae tuni Abusufyan ya zauna ƙasa dirshan yana lazimi,Abba kuwa sae faman jinjina kai yakeyi,gwaggon katsina kuwa tana ganinsu jahad ta shiga zare na mazurai don tasan cewa ƙarshe abun kanta zai ƙare ita da ta sanya mashi hannu ta ɗaure mashi mazaunai wurin yin auren batare da sanin Ammi ba,kowa dai yashiga zullumin abunda zai biyo baya,
Aunty babba kuwa suna la6e ita da hayaam sun kasa kunne suna jiran jin mai zai biyo baya,jikinsu sae faman tsuma yakeyi,
Zuba masu ido Ammi tayi tana kallonsu,one by one,ganin yadda matar ta ƙura masu ido yasa duk suka sha jinin jikinsu,daƙyar suka iya haɗa baki wurin gaishe da ita”Ina yini,”
Bata amsa masu gaisuwar tasu ba,sae nuni da tayi masu da sandar hannunta alamar su zauna,wuri suka samu agaban kujerar da su Omar ke zaune,suka zauna daga ƙasa tare da lankwashe ƙafafunsu,zaman cin tuwo,
Nuna Sehrish tayi da sandar hannunta tace”Ya sunanki”
Jiki asanyaye sehrish ta bata amsa da cewa”Sunana Sehrish,”
Ammi ta kuma cewa”wanene mahaifinki”?
wurga idanunta tayi akan Abusufyan ta nuna shi da hannu tare da cewa”Gashi nan,shine mahaifinmu”
jinjina kai Ammi tayi tare da kallon abusufyan wanda keta faman zubda gumi a fuskarsa,duk sanyin A.c din dake akwai a falon,
…hmmmm janye idanunta tayi daga kan Sehrish ta mayar dasu kan Jahad tace”Kefa ya sunanki”?
“Sunana jahad,”
“Wanene mahaifinki acikinsu,”
Juyawa jahad tayi tare dakai hannu ta nuna abusufyan tace”Shine daddynmu,”
Rai amatukar 6ace Ammi ta daka masu tsawar da ta gigitasu gaba ɗayansu duk suka razana,a tsiwace tace”Kowa ya zuba mun ido yana kallona,ba zaku faɗamun a ina kuka samo su ba?taya akai Abusufyan ya zama ubansu!”
Abba ne yayi ƙoƙarin buɗe baki yace”Ya’yanshi ne dagaske,kamar yadda suka faɗa Ammi,”
Aruɗe Ammi tace “Ni kake faɗama cewa ƴa’ƴanshi ne?kada ku raina mun hankali ta gidan ubanwa Abusufyan yayi aure da har zai haifi waɗannan balagaggun ƴan matan!”?
Fashewa da kuka hosana tayi,sehrish da jahad kuwa tuni hawaye sun soma wanke masu fuskarsu,jikin Marshal ba ƙaramin sanyi yayi ba,haka zalika sauran dake zaune a wurin,
“Abusufyan!ka faɗamun taya akai ka samu yaran nan?Na yarda cewa ƴa’ƴanka ne koda basu faɗamun da bakinsu ba,saboda ina ganinsu nasan cewa Jinina ne su,ko ba don kamanninka dake akan fuskarsu ba,So nake naji TAKUN hanyar da aka Same su!?nasan halinka tun fil azal baka rabuwa da mata,ka faɗamun gaskiya,ka ta6a yin mu’amala da wata ƴa’ mace ne har ta samu cikinka”?
A kiɗime abusufyan ya shiga yi mata rantsuwa yana faɗin”Wlh Ammi tunda nake arayuwata ban ta6a kusantar zina ba,Nasan cewa zaiyi wuya ki yadda dani,amma wlh saida na auri mahaifiyarsu sannan na same su,ga gwaggonan itace shaidata,”
Tamkar zata rufashi da duka haka tashiga balbaleshi da masifa”Bazan ta6a yadda da kalamanka ba,karka kuskura ka ƙara cewa ta hanyar aure ka same su,in ba haka ba saina ci maka mutunci a wurin nan!dama najima ina zarginka abusufyan,banta6a tunanin zakayi mun haka ba,ka cuce ni,bazan ta6a yafe maka ba,rashin jin maganarka har yakai ka kawo mun Shaggu acikin zuri’ata,bazan ta6a lamun ta ba……’
Rai a6ace gwaggon katsina ta katse mata hanzarinta da cewa”Ya isa haka,babu laifin abusufyan acikin wannan lamarin,Nice na aura mashi yarinyar da ta haifa mashi waɗannan ƴa’ƴan,don haka kidaina ambaton sunansu da shaggu saboda baki da hujjar yin hakan,bazan ta6a yarda a tozarta ƴa’ƴan abusufyan ɗina a gabana ba ehe,” kowa yayi mamakin yadda gwaggon katsina ta mayar ma Ammi martani,tamkar wata mai cikakken hankali,
“Dan Allah Ammi ki daure ki fahimce shi,rashin sanar maki da basuyi ba,shine babban kuskuren da Abusufyan da gwaggo suka yi,Gwaggo ta aikata hakanne saboda son da takeyi ma abusufyan wannan dalilin ne yasa ta aura mashi mahaifiyarsu batare da saninki ba,saboda tasan halinki,kin tsani auren bare,gashi shi kuma abusufyan ya kwallafa rai akan yarinyar,wannan ne yasa ta aura mashi ita,saboda gudun karya faɗa halaka…..  “Wani irin kallo da Ammi ta jefa mashi ne yasa shi dakatawa da yin maganar da yake,wato Abbansu junaid,
Aunty babba dake la6e ita da hayaam suna sauraronsu,saboda tsabar farin ciki kamar su zuba ruwa a ƙasa su sha,burinsu kawai Ammi ta koresu Jahad,
Kowa saida ranshi ya 6aci a wurin nan,saboda yadda ammi ta haƙiƙance akan cewar bazata kar6i shaggu ba acikin zuri’arta,a ƙarshe tace”na riga da na yanke hukuncin korarsu daga cikin zuri’ata,banason ganinsu,kuma duk wanda yayi yunƙurin binsu acikinku wlh saina tsine mashi yabi duniya,kuma zan yafe shine acikin ƴa’ƴa Na,
Wani irin matsanancin kuka su jahad suka fashe dashi,haka abusufyan ma kuka yake yi tamkar ƙaramin yaro,ƙiri kiri za’a rabashi da ƴa’ƴanshi,su Abba kuwa gaba ɗaya jikinsu yayi mugun sanyi,Hankalin Omar ba ƙaramin tashi yayi ba,haka zalika sauran kowa hankalinshi yayi mugun tashi,
Su aunty babba kuwa dake la6e,jin an kori su sehrish,yasa suka daka uban tsallen farin ciki,saboda tsabar dariyar mugunta,hada hawaye,da gudu suka koma cikin ɗaki,suna faman dariya,burinsu ya cika,

“Ku tashi ku fuce daga cikin gidan nan tunkafin insa ayi waje daku,”jiki asanyaye suka miƙe tsaye jahad ta ruƙo hannun sehrish da jahad acikin nata,tafiya sukeyi kamar wanda aka zarewa laka,yayin da hawaye ke gangarowa daga idanuwansu,yunƙurawa abusufyan yayi da sauri zaibi bayansu,aikuwa abba yayi hanzarin damƙo rigarshi ya janyoshi,ya dawo da shi saman sofa din,a haukace ya shiga kiciniyar kwace kanshi yana fadin”Ka barni yaya hossein wlh sai dai ta tsinemun amma bazan bari rayuwar ƴa’ƴana ta wulakanta ba,duk inda zasu je ƙafata kafarsu,”ganin abusufyan na ƙoƙarin zaucewa yasa su Marshal Omar dasu ishaq da abbas suka rurrukeshi,sai faman hargowa yakeyi,yana kokarin kwacewa don yabi bayansu sehrish,

bazasu iya jurar ganin halin da mahaifinsu ke ciki ba,hakan ne yasa suka fuce waje da gudu suna kuka,tamkar ransu zai fita,sae faman shessheƙar kuka sukeyi,

Suna cikin wannan yanayin Motar SGR,ta shararo da gudu cikin gidan,a tsiyace su kayi parking ɗin motar,tunkan Amstrong ya buɗe mashi motar,ya sanya kafarshi tare da harba murfin motar,ya fito daga ciki,kai tsaye ya nufi wurinsu Sehrish dake a tsaye suna kuka,kwata kwata basu lura dashi ba,sae dai suka ji an ruko hannayensu,Jahad da hosana,a firgice suka ɗago suna kallonshi,”ku wuce mu shiga ciki,”yayi maganar tare da jan hannunsu,sehrish ma tabi bayansu suka koma cikin falon,jin sallamar Sgr yasa hankalin kowa komawa kansu,ganin ya dawo dasu sehrish yasa kowa ya shiga sauke ajiyar zuciya,Zuba mashi ido Ammi tayi tana kallon ikon Allah,
ƙarasawa cikin falon yayi tare ce masu sehrish”Ku samu wuri ku zauna,”jiki asanyaye suka samu wuri ƙasa suka zauna,suna faman sauke ajiyar zuciya,
Zama sgr yayi asaman sofa,tare da aza ƙafarshi ɗaya bisa ɗaya,yayin da yake fuskantar Ammi wadda ta zuba ma sarautar Allah ido,
Sai da ya mula yasha iska sannan ya soma magana
“dama saida raina ya bani cewa hakan zata iya faruwa,that’s the reason why na tanadin hujja ɗaya kuma kwakkwara wadda zata wanke zargin da kikeyi akan abusufyan da kuma waɗannan triplet ɗin,”
Ƙarasa maganar yayi tare da sanya hannunshi cikin aljihun wandon jeans ɗin dake ajikinshi,ya zaro wayar shi,

*mu haɗu On monday don jin yadda zata kaya,*

_har yanzu wasu basu gode mun akan long page ɗin da nake sawa,in banda ma rashin godiyar Allah irinta ɗan adam,a ƙalla yawan one page da nake sawa Yayi fiye da 3 page na wasu masu rubutan,Allah har mamaki nakeyi in naga page ɗin wasu writers din,duk read More 3 ne amma ni kaga page mai read more 9 har 12 ina sakawa,ƙaramin page ɗina shine zaka ga read more 6,zama nakeyi inyi rubutu kamar zan kashe kaina,amma wasu saboda rashin godiyar Allah suna zuwa sunayi mun complain ɗin wai adinga posting sau biyu?a iya sanina Vip ne ma ake sanya 2 page,amma ni ina sanya maku kusan 3 page a hade duk da hakan baiyi maku,idan so kuke sai in dinga raba maku shi uku,saboda na lura hakan yafi maku,kunfiso ku ganshi arabe,bakomai ne yasa ma nakeyin page masu tsayi ba face don in samu intakaita labarin saboda yana da tsayi,idan kuma aka cigaba da raina abunda nake sanyawa wlh zan mayar dashi ne read more uku in tafi dai dai da kowa👍_

 

Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

 

 

Back to top button